Showing 57001 words to 60000 words out of 145961 words
baya ko digon santa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ta j
uya a hankali tai ciki.
Tana shiga ta cilar da wayar akan gado tana kallan Little tana mata dariya, ta wuce toilet.
A gaban madubi ta tsaya bayan tayi alwala ta kalli kanta a cikin ranta tace "dama kema kinyi laifi tun farko, kinfi kowa sani
n Ashraf yafi karfinki meya kaiki???? "
Hawayenta ta share sannan ta fita jiki a sanyaye.....
Bayan tayi sallah little ta dameta da zancen Al-Amin itakam shiru kawai tai, dama bata kunna wayar ba balle ma ya kirata.
Ganin taki kulata yas
a itama Little d'in tai shiru, itakam Nafi kwanciya tai kamar mai bacci sai dai ranta fal yake da tunani kala kala.
Shikam Ashraf yana shiga mota yai wani huccin takaici, meye nashi na zakewa haka? Wata zuciyar tace to yarinyace karama ko kara
tu bata gamaba ko kunya ace tana xama da saurayi a mota? Ai amanace ita agunsa shi ya d'aukota daga wani garin dolene ya kulada ita kafin mazan zamani su hure mata kunne.
Ya d'an bigi sityari kadan yace " me yasa nai haka agaban wannan yaron? Salan
ya rainani? Ya kara jan tsakin takaici, haka ya gangara gun abokinsa nagun aiki dazai amshi takardu ransa duk a jagule.......
Washe gari Nafi bayan ta tashi daga bacci ta fita zuwa kitchen nan suka gaisa cikin farinciki da kewar juna, ta zake
ta shiga tayasu aiyukan girki.
Sun gama ta fito kenan sukai kicibis da Umma, had'e rai Umma tai tace "ke wacece a kuma wani dalili kiika shigo mana kitchen? "
Nafi tad'an rusuna kad'an ta gaisheta sannan ta mike tsaye tace "Umma baki ganeni ba? "
Umma ta kar had'e rai, Nafi tace " nice fa Nafi. "
Umma ta kara kallanta ba shakka itace, ta d'an harareta tace " uban me kike anan ba dama kina makaranta ba?? "
Nafi tace " ai dama ana hutu nice dai kawai ban dawo ba. "
Umma ta kara h
ad'e rai tace " to yanzu gulma ce ta dawo dake ko me? "
Nafi kam murmushi ta saki dan itakam bataji haushin kalaman Umma ba ta kalleta tace " Umma na shiga ciki. "
Ran umma ya b'aci ganin yanda yanda yarinyar ma ba a kula ba, gashi tasan yariny
a da take 'yar riga yanzu ta girma? Gashi dai ba wanka tai ba amma gata tsaf, ba kamar wannan kucakar tada ba.
*Anan ne zan dakatar da wannan littafin nawa mai taken Zuciya kowa da irin tasa, ina fatan zaku jirani zuwa bayan sallah in Allah ya
kaimu.*
*Yanda zamu fara azumi lafiya Allah ubangiji yasa ku gama lafiya, ya kuma bamu ikon yin ibada batare da gajiyawaba, ya karemu daga duk wani abu dazai d'aukemana hankali agun ibadaunmu, ya yafemana kura kuranmu, ya kuma sa mu gama da duniya
lafiya.*
Ameen suma Ameen.....
*Nagode kwarai da irin san da kukema littafin nan, banida abinda zancemuku face godiya, Allah yabar zumunci, ya kara mana kaunar junan mu.*
*Duk wani masoyin wannan Littafin ina mika sakon gaisuwata gare
ta/shi, na gode kwarai da kauna.*
*Sai Allah ya Kaimu Bayan Sallah in Muna da Rai da Kuma Lafiya.*
❤
💛💛💙💜💜🖤💟💟
[6/28, 1:51 PM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
*na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*W
attpad As_AyusherMohd*
*Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu Wata'ala, muna kara godiya gareshi da ya nuna mana watan Ramadan lafiya yasa mukai ibadun mu lafiya, sai fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu...(Ameen)*
*Inama dukan d'okacin maso
yana barka da sallah da kuma fatan alkairi a ko ina suke...*
Allah Ubangiji ya Maimaita mana Ameen..
{ *34*}
Umma ta juya cikin takaici da niyyar lalai sai ta sa a kori yarinyar nan kafin ta zamar musu masifa.
Nafi kam har tayi gaba ta tsaya
tare da juyowa tabi Umma da kallo, kai ta girgiza ta juya zata wuce ta hango Asim ya nufo Umma da sauri kamar zai fad'i da kasa, kallan yanda yake baza sauri take da alama akwai magana da yake san isarwa cikin gaggawa shi yasa yake wannan saurin.
Umma
tana hangoshi da ganin yanayinsa yasa tai hanyar b'angarenta da sauri itama, Nafi har ta juya zata koma d'aki taji sam hankalinta ya kasa kwanciya, a hankali ta tako tazo wajen b'angaren Umma sai dai ta rasa tayayya zatai karyar da zata shiga?
Shiru ta
i ganin ba halin shigan yasa ta juya da niyyar komawa, Asabe mai aiki a kitchen ta hango ta nufo gun rike da tire babba da kuloli akai, Nafi ta karasa gunta da sauri tace " Asabe ina zuwa?"
Asabe tace " Umma zan kaima kumallon ta."
Nafi ta amshi tiren
tace " Barshi ni bari na kaimata dama ciki zan shiga."
Cikin rashin damuwa Asabe ta bata tare da kad'a kanta ta koma inda ta fito, Nafi kam da sauri ta nufi kofar Umma, gabanta kam sai dukan uku uku yake saboda tsoro sai dai ta rasa dalilin dayasa zu
ciyarta keta tunzurata akan lalai ta shiga.
Murd'a kofar tai a hankali ta shiga da sallaha itama ciki ciki tayi ta.
Batai mamaki ba dan dama batasa a ranta za ta gansu a falo ba, nan ta wuce cikin tsoro ta ajiye tiren akan dinning sannan ta kalli d
'akunan dake falon guda biyu, a ina suke???abinda ta fad'a kenan a ranta.
Lalab'awa tai ta karasa d'akin farko,tare da sa kanta a jikin kofar kamar munafuka, jin alamun rashin mutum yasa ta karasa d'ayan, zuciyarta sai kara tsananta take da fad'uwa w
annan karan bata sa kanta a kofa ba tana zuwa jikin kofar d'akin taji cikin fad'a wanda yasa ta tsorata taji Muryar Asim yace " Umma nikam bakin ciki kasheni zai yi dan nikam indai har na cigaba da ganin Ashraf to fa lalai inaji ni zan bar gidan nan."
Gaban Nafi ne ya yanke ya fad'i me kenan? Ta fad'a a ranta.
Kafin ta nemo amsar tambayarta taji Umma tace " ni d'in ce maka akai farin ciki nake in na ganshi? To amma ya zakayi....???"
Cikin fad'a Asim ya katse Umma da cewa " Yanzu sam 'yan gun aikinmu
basa karramani magana ma ba yimin suke ba, sannan yanzun nan abokina na gun aiki ya sanar dani cewa shareholders na company d'in sun yi meeting akan a dawo da Ashraf matsayina inyaso ni sai a ragemin matsayi, nifa wlh in bakuyi wasa ba zanyi aika aika."
Umma ta gyara zama tace "Asim kayi hakuri abi maaganar nan a hankali."
Cikin zafin rai yace. " a hankalin me? Ni wlh har yan daba na kira kafin nazo nan na sanar dasu inya fito aiki anjima su tareshi su kawar mun da numfashinsa."
Jikin Nafi
kam rawa kawai yakeyi, har tsuma takeyi saboda tsananin tsoro da fargabar abinda yau kunenta yake jiye mata.
A tsorace ta juya cikin tsananin tsoro da firgici tai waje har kafarta na hard'ewa ta fad'i kasa.
A d'aki kam Umma ta kalli Asim tace " Asim
yau lahadi naga ba aiki?"
Asim yai wani murmushi yace " ai shi zai je saboda akwai wani project da sukeyi shi da 'yan team d'insa."
Umma tai ajiyar zuciya sannan tace " baka ganin anyi gaggawa in aka mai illa tun yanzu? Asim yai tsaki yace " Ill
ar me? Shima Abban ai yafi kowa san Ashraf ya mutu."
Umma ta jinjina kai sannan tace " Aneesa fa?"
Asim ya kara jan tsaki yace " kyale wannan in ya mutu taji ta cafki dukiyaa a hannu kina ganin zata damu?"
Umma tai murmushi sannan tace " duk d
a Neesa na tsananin san Ashraf banaji tana sansa kamar yanda takesan kudinsa dan na tabbata da bashida komai duk sanda takemai bazata tab'a aurensa ba."
Asim yai kwafa yace " Ni wlh na tsani ma na gansu tare, nifa inaji duk duniyarnan ba wanda na tsan
a kamar yaran nan."
Umma ma tai tsaki tace " ai nima dashi da uwarsa sune mutanen dana tsana kaf duniyar nan."
Nan suka zauna suka cigaba da sake sakensu.
Nafi kam dakyar takai kanta falon b'angarensu, ta zauna akan kujera har yanzu jikint
a rawa yake, sam kwakwalwarta ta kasa d'aukan abinda ta jiyoma kanta.
Dif taji kwakwalwarta ta d'auke sam bata tunanin komai sai da wasu dakiku suka shud'e sannan taja wani dogon numfashi sannan ta mike a zabure tace " Ya Ashraf????"
Jitai idanunta
sun kawo kwalla ace d'an uwanka na jini???wannan wace irin rayuwace???? Sanar dashi zatai?? Zai yarda da abinda zata fad'a??ko Little zata fad'ama??kai ta girgiza tace"kar itama in tada mata hankali..."
Wata zuciyar tace Mumy fa???kai ta girgiza da s
auri tace " Mumy kuma da wani idan zata zauna dasu??"
Kanta ta dafa dataji ya sara, can tace " Kawu fa???"
Hucci ta saki cikin damuwa tace " shikuma matarsa ce da d'ansa."
Kan kujera ta fad'a wasu hawayen suka sake zubo mata, Ya Ashraf me ka
i ake neman halakamin kai???ta fad'a cikin wata irin murya mai ban tausayi.
Agoggon bango ta kalla karfe tara, karfa Ya Ashraf ya fita??? Da sauri ta mike kawai ta nufi b'angarensa, hankalinta bai tsaya ba sai da ta isa kofar b'angarensa, me zata cem
ai??? Shiru tai ta tsaya agun kamar abu mara motsi, dan batada amsar tambayar nan.
Tana tsaye ba mafita har dakika goma suka shud'e, motsin bud'e kofa ne yasa ta dawo hayyacinta, idanunta ne suka firfito cikin tsoro, ta kalli kofar.
Ashraf ne ya
fito, jitai gabanta ya fad'i cikin mamaki ya kalleta, sai dai kafin yai magana sai ga Aneesa ta fito rike da jakarsa, fuskarnan tata a had'e da alama ranta a b'ace yake.
Cikin mamaki itama ta kalli Nafi, "Malama wacce ce ke? Me kuma kike anan?"
Nafi ta had'iye yawo cikin tsoro ta kalli Ashraf, shima kallan mamaki yake mata, Aneesa ta kara kallantaa yanzu kam kallan rashin mutunci ta mata.
Tace " Ke malama wacece ke? A wani dalilin kikazo min kofar miji??"
Nafi kam jira take Ashraf yai maga
na sai dai abin haushi gani tai ya d'auke kansa, tare da amsar Jakarsa zaiyi gaba, jitai idanunta sun fara cikowa ita gani take ai ya kamara Ashraf ya sanar da Aneesa, ganin ya fara tafiya ga tana so ta tsaidashi daga fita waje, sannan ga Aneesa ta tsareta
da ido yasa duk ta rikice.
Shikam Ashraf haushin abinda tai jiya da daddare ne yasa yaki kulata, Aneesa ta bud'e baki zatai magana kawai Nafi tai baya luuu jikake ta zube a kasa, wannan ita kadai ce mafita a gareta abinda ta fad'a kenan a ranta tare
da runtse ido.
Aneesa ta d'anyi kara tare dayin baya cikin tsoro, hakan yasa Ashraf ya juyo da sauri, cikin rud'ewa yasa ya karaso inda take, sannan ya d'agota tare da cewa " Nafeesa!!Nafeessa!!."
Sai a lokacin Aneesa ta gane waccece, kallan Ash
raf tai duk ya wani rud'e haushi da kishi suka kamata a zuciye ta matso tace " Aljanu ne da ita??"
Ran Ashraf ya b'aci ganin yanda tai maganar cikin rashin kulawa, yace " bishiyar kuka ce a kanta..."
Ya mike a zuciye ya d'agata ya nufi mota da ita,
Nafi kam haryanzu gabanta bai bar fad'uwa ba tanaji ya bud'e bayan mota ya sata a ciki.
Tanaji ya bud'e gaban mota ya shiga, ya tadata tad'anyi zafi sannan yaja motar suka fita, suna fita daga gate d'in gidan sai taji yace " Will u get up now?"
I
danunta ta kara runtsewa a ranta tace " badai dani yake ba?"
Ashraf ya kalleta ta madubi sannan yace " abinda kika koyo a makarantar kenan? Pretending??"
Nafi kunya da takaici duk suka kamata ta kara danna kanta kujera, gefen titi ya gangara yai par
king sannan ya juyo ya kalleta yace " Kin tashi ko sai na fitar dake waje da kaina?"
Nafi ta mike zaune tare da zunburo baki gaba kanta na kasa, ya kura mata ido yace " me kike san fad'amin?"
Kallan mamaki tamai, tace " ya akai kasan abu nake san
fad'a?"
Kallanta yai sannan ya kalli window yace " inba abu kikesan fad'amin ba me zai sa kizo b'angarena kinsan inada mata kizo ki tsaya a waje?"
Baki ta tab'e a ranta tace " da cewa nai bakada mata?"
Ya kalleta sannan taji yace " da alama k
in manta inada mata inba haka ba mezai sa kije b'angaren? Ai sai ki kirani a wayar Little ko ta saurayinki."
Nafi ta saki baki tana kallan sa tace " to ni menace?"
Ya juya kai sannan yace " Ki tambayi abinda kika ce a zuciyarki."
Nafi tai sh
iru rai b'ace.
Ashraf yace " to fad'amin? Menene?"
Nafi tai shiru tare da maida kanta kasa.
Ashraf ya kara had'e rai yace "zan saukeki fa inja motata inyi gaba ko ce miki akai banda abinyi??"
Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, cikin wani irin mur
ya tace "banifa da lafiya, xaka saukeni."
Wani murmushi ya saki na rainin hankali yace " harda karya kika koyo a makarantar? "
Ta kalleshi sannan ta d'an shagwab'e murya tace " nifa Yaya ba karyar dana koyo."
Har cikin ransa sai dayaji wani
abu, sai dai ya sake dakewa yace " ke jiranki nakeyi ko?"
Nafi ta kalleshi tace " Yaya dan Allah kar kaje gun aiki yau."
Kallan mamaki ya mata yace " bangane ba? Ke harkinkai matsayin da zaki hanani abu?to ko Aneesa bata samu wannan matsayin ba."
Nafi ta kalleshi cikin wani yanayi tace " Na sani Yaya banida wannan matsayin kuma ban kai kaina wannan gun ba, sai dai ba dan nibaaa ba kuma dan halina ba sai dai ka duba darajar Allah ka hakura da zuwa aikin nan yau."
Ta karasa magana tare da k
awar da kanta alamar idanunta nasan kawo kwalla, kallan mamaki yake mata, sai dai yanzu yasan tabbas da wani abun.......
*THE INNOCENT TEAM*
🏌🏻
♀
[6/30, 12:30 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Wattpad As_AyusherMohd*
{ *35*}
Yanda yake kallanta yasa ta had'e rai tare da maida kallanta wajen window, itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma 'yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata
tsauri.
Ga mamakinta jitai yace " tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida."
Nafi ta kalleshi a tsorace tace " Sauka zanyi a haka??"
Kai ya d'aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace " taya zan iya fita ah
aka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud'in da zan tafi da kaina."
Ya d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b'aci a zuciye ta matsa da niyyar bud'e kofa, har ta zura kafa d'aya zata fita sai taji yace " shigo in aji
yeki ba dan halinki ba inada abinyi."
Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud'e kofa zata fita sai kuma ta juyo ta
ce " Yaya ina zaka?"
Kallanta yai yace " banaji wannan yana d'aya daga cikin damuwarki tunda dai baki fad'amin me kike nufi da kar inje aiki ba, kin kuma san halina ba a sani abu."
Nafi ta kalleshi cikin kulawa tace " Yaya tunda kaga na furta hak
an ai kasan da dalili, in ba haka ba meye nawa da zance karkaje aikinka?ni ba matarka ba?"
Juyowa yai ya kalleta kalamanta na karshe sun tsayamai a wuya, sai dai ya share yace " ke nake jira zan fita ko?"
Nafi batasan sanda wani takaici ya kamata
ba ta kafeshi da ido na takaici, kallanta yai sannan ya juya ya d'au wayarsa, bakin ciki ya hanata d'auke idanunsa daga kansa jitai ya tada mota, alamar zan tafi, takaici yasata ta fito daga motar a zuciye tana kallo yaja motarsa ya tafi, tabi motar da ka
llan takaici.
Wannan wani irin mutum ne, duk yanda na damu da rayuwarsa amma shi ko a jikinsa?? Sai ma rashin mutunci ne zai biyo baya?.
Sam ta kasa d'auke idanunta daga hanyar daya wuce, jitai an dafa ta a firgice ta juyo, Mumy ta gani tsaye itada
Little.
Nafi tai saurin share kwallarta sannan ta kakaro