Showing 84001 words to 87000 words out of 145961 words

Chapter 29 - ZUCIYA COMPLETE

ku tafi wani guri a daren nan."

Baki ta turo tace "Wani ne."

Yace "wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?"

Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace " to meye a ciki? Tunda so na yake?"



Me? Bakida hankali ne?" ya fada a zuciye, ta kalleshi tace " ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba."

" who said that?" shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba.

Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sann

an yace " karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa."

Tace" Akan me?"

Yace " Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?"

Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace " ba

zan iya rabuwa da shi ba."

Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace " ni kike fadawa haka?"

Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sa

i dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la'asar....Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma'a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud'e a hankali.

Idanunta suka cicik

o cikin sanyin murya tace " Yaya why are u doing this to me?"

Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace " Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba."

Tace " ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?"

Ya kara kankameta yace " Na rasa me ke damuna, ni ka

ina abin na damuna."

Ta dago da jikinta tace " karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka."

Kallan mamaki ya mata yace " Ke halal dina ce bawai haram dina ba."

Wani murmushin takaici tai tace " Halal? Since when did i became your hal

al?"

Yace " What?"

Ta rufe ido sannan ta bud'e tace " Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?"

Kallanta yai sai da

i kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace " ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan."

Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata.

Jiki a sanyaye

ya bud'e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba.

Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pai

n?"

Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa.......

*#ASHRAFEENAH TEAM*

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ay

ushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*51*

   Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye.

  Kawu ya kalleshi yace " Asim meye hakan zaka shigo k

o sallama?"

 Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace " in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su."

  Kawu ya daka mai tsawa yace "Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka d

inga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?"

   Asim ya kafe Mumy da ido yace " gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba."

  Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace "Bangane karuwa ba?"

  Asim ya

i wata dariya yace " Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d'anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi."

  Mikewa Mumy tai tace "Nafi?bangane abinda kake nu......"

 Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waj

e, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kusa da Mumy ya jawota jikinsa yace "Karki damu munfi kowa sannin Ashraf mun kuma san bazai aikata abinda suke fadaba, Anisa kawai suke tayawa kishi ba komai ba."

   Idanu Mumy ta runtse jin zage zag

en da akeyi yayi yawa, nan suma suka fita, Umma ce taci damara ita da 'ya 'yanta maza, Anisa na tsaye sai matsar kwalla takeyi.

    Fada sosai ne ya kaure a waje banda zagi da cima Ashraf mutunci ba abinda sukeyi, mumy ganin bazata iya daure wa ba yasa

tasa baki aikuwa kamar jira Umma take har cewa take zata daki Mumy kuma yau dole ne Ashraf ya saki 'yarta dan bazata yarda da cin mutuncinsa ba, sai dai zancen saki burga ce kawai takeyi dan tasan bazai yiwu ba.

 

   Little wacce hayaniya yasa ta fito

tai tsiru tana jin su duk jikinta yai sanyi, bata taba ganin gidansu a haka ba.

   Suna tsakiyar zage zage sai ga motar Ashraf ta shigo gidan, nan fa kowa yabi motar da kallo dan ganin abinda sukaji, Ashraf kam tunda ya shigo yake mamakin taruwar ta men

ene, itakam Nafi kanta na kasa sam bata gansu ba, yana fitowa ya zaga inda Nafi take ya bud'e mata ta fito, kallan takaici tamai.

  Zata wuce taji kafarta ta hard'e ta kifo zata fad'i ta gaba, da sauri ya tareta, hannunsa yasa a kugunta d'aya kuma ya ri

ke hannunta.

  Sallati suka saka, Umma ta shiga tafa hannu tana sallalami, Mumy ma idanu kawai ta rufe, kawu kuwa ko ajikinsa sai ma farinciki da yake.

  Nan Asim ya nufoshi a zuciye, Anisa kam zama tai a kasa ta kara sa wani sabon kukan.

  Itakam

Nafi kallan Ashraf tai sannan a hankali ta zare jikinta ta kalleshi tace "Thanks."

  Bai amsa mata ba sai kallanta kawai da yakeyi, kai ta juyar gefe dan batasan kallan nan, Asim ta gani ya iso gun a zuciye ya dunkule hannu zai naushi Ashraf da sauri ta

shiga gaban Ashraf ita naushin ya sameta, iya karfinsa ya sake wanda naushin sai daya sa tai baya.

  Ashraf ya razana da sauri ya tarota ya shiga kiranta, su Umma ne dukansu suka karaso gun suka cigaba da sallalami, Umma ta kallesu ya wani rungumota yan

a kiran sunanta.

 Tace "Lalai Ashraf bansan haka kake ba sai yau, to dama mahaifinka ya mutu kafin ka mallaki hankalin kanka, uwarka ta kasa hakura ta zauna tai tarbiyarka saboda bazata iya zama ba namiji ba ta auri kaninsa ta ma manta da danta, dama in

a zakai hankali?"

  Ashraf ya d'ago ya kallesu dukansu, Mumy ya kalla wacce ke matsar kwalla a gefe, ransa ya kara b'aci ya kalli Nafi wacce bata farfado ba, sannan ya maida dubansa kan Umma yace " kun taremun jikin mota ina bukatar fita dan kaita Asibi

ti."

  Asim ya kara zuciya zai kara kai mai naushi wani kallo da Ashraf ya bugamai yasa ya tsaya, Ashraf ya nunashi da yatsa yace "Don't you dare think of something like this again, dan banaji zan yafema inka kuskura ka kara tunanin abu irin wannan, kas

an ni kasan kuma abinda zan iya."

   Umma ta kutuntumo Ashar ta maka mai tacigaba " dan marasa tarbiya har mu zaka nunawa bariki? Daga kai har wannan tsinaniyar karuwar taka?jiki duk a kya mushe? Zaka wulakanta matarka ta suna akan wata can karuwa?"

   Ashraf ya kallesu, sannan yace " In kun gama zaku iya matsawa? inada gun zuwa na dauka na sanar daku."

  Kawu ya matso gunsa yace "Kai Ashraf bakada hankali ne? Akan me zaka dinga neman fita da yarinya bayan ka bar matarka ka dauketa kun tafi wani gu

n?"

  Ashraf ya kalleshi yace " Me kuke san ji daga gareni? Kafin ku tambayeni komai na dauka kowa a nan ya amince da abinda zuciyarsa ta fadamai?"

  Kawu ya hade rai yace " Ko ma menene dole ne gobe wannan yar kauyen mara asali ta koma kauyensu sabo

da yarinya guda d'aya bazai yiwu mu cigaba da samun sab'ani ba."

  Little ce ta mikamai ruwa a jarka data d'auko ya amsa sannan ya sa mata, numfashi taja sannan ta mike zaune, sai dai gefen fuskarta har ya tashi, Ashraf ya mike tsaye yace " who said tha

t?"

  Kawu ransa ya b'aci yace "nine na fad'i haka kuma nine shugaba a gidan nan dolene ta koma kauyensu goben nan, bazan juri ganin tana neman lalata mana zumunci ba, yarinyar da ko asalinta bamu sani ba."

  Nafi kam yanzu ta fahimci da ita ake, jik

i a sanyaye ta mike zata wuce, hannu Ashraf yasa ya riko nata hannun, cak ta tsaya sai gabanta kawai da yake fad'uwa, Ashraf ya kalli Kawu yace "Zumunci?wanne kenan? Banaji na sanshi, sannan maganar yarinya babu wanda ya isa ya sata ta tafi dan kuwa nine n

a kawota nine kuma nakeda hakkin sata ta tafi."

  Kallansa tai cikin takaici, tasani bazai iya cewa matarshi bace ita, yana gani yana kuma ji ana ce mata karuwa, hannunta ta fizge sannan ta kalli Kawu tace "Kawu kuyi hakuri zan tafi gobe in Allah ya kai

mu."

  Tana fada ta juya, hannu yasa ya kara rikota nan ta shiga kokarin kwacewa, Mumy tace "Ashraf wai ke kakeyi hakan? Bazaka saketa ba?"

  Murmushi ya sakar musu yace " What should i do?"

  Kallansa sukai cikin alamar tambayar, yace " ya zanyi?

Tunda Nafisa matata ce wacce na aura kafin Anisa, ya zanyi in ban rike hannun matata ba?"

    Gaba d'ayansu cak suka tsaya kamar abu mara motsi Nafi kam kallansa kawai take sai dai tsoro ya cika mata zuciya, a da tana so taji ya fada with full confid

ence akan ita matarsa ce to meyasa yanzu taji gaba d'aya ba haka ba?"

  Ashraf ya kalleta yai murmushi yace "muje ko?"

 Hannunta ya ja suka fara tafiya binsa kawai takeyi, sukam kowa ya kame ya kasa motsi, suna matsawa daga gunsu Nafi ta had'iyi wani a

bu tace "Yaya mai ka aikata?"

  Murmushi ya sakar mata yace "what? Are u scared?"

  Kallansa tai batace komai ba, har d'aki ya kaita yazaunar da ita tare da kallan inda aka nausheta yace "Me yasa kika taremin d'azu?"

  Kanta na kasa tace " nima ba

n sani ba."

 Yai murmushi yace " sanda naga kin taremin naushin da ya kamata ya sauka a jikina lokacin jinai komai ya daukemin a kuma wannan lokacin na gane meke damuna."

  Kallansa tai kallo mai alamar tambaya, kiss ya manna mata a kuncinta yace " Fee

na I think I Luv You."

    Kallansa tai gabanta ya tsananta fad'uwa baki ta shiga motsawa tana san tai magana ta kasa, Ashraf ya jawota jikinsa yana daga tsaye ita kuma tana zaune akan gado, yace " Be strong dan nasan akwai yaki babba a gabanmu, sai dai

karki damu kowa zai gaji ya bari."

  Kai ta jinjina mai, yai murmushi sannan  ya saketa ya fita.

   Ko kallan inda suke baiyi ba yai b'angarensa.

  Anisa da gudu ta mike tai b'angaren Umma ta shige d'aki ta kulle, maganin Umma ta gani kawai ta de

bi guda 10, ta hau had'iya, kankace me jiri ya debeta ta fadi kasa ta suma, nan su Umma suka tadda ita a kwance, da gudu Asim ya d'auketa ya sata a mota sukai Asibiti.

 

  Nafi kam tana nan a zaune Little ta shigo da sauri bata mata magana ba kawai ta

zari mayafi tai gaba, Nafi ta mike da sauri tace "Little ina zaki a daren nan?"

 Little bata tanka mata ba tai waje, jikin Nafi yai sanyi ta zauna a kasa ji take kamar tasa kuka, sallama taji ta mike ta leka, mai gadi ne ya miko mata leda yace " gashi i

nji yalabai."

 Yana bata ya juya ya tafi, bud'ewa tai taga magunguna, dana shafawa dana had'iya.

  Ta mike tai sallar isha'i sannan tasha, akan sallayar ta zauna kawai tana addu'oi Allah yasa komai yazo mata da sauki......

  Nima nace Amin.....

  Su Anisa kam dukansu har Mumy aka nufi asibiti, emergency akai da ita, likitoci suka dukufa akanta, sun dade kafin su gama aikinsu, suka kallesu suka ce " Kuna ina duk yawanku yarinya na neman kashe kanta?

   Umma ta harari Mumy tace "Likita masifa

ce ta taso mana, bamu fargaba ta shiga d'aki."

  Yai dan hucci sannan yace "She is no longer in danger amma sai kun jira zuwa anjima kafin ta farfado."

  Yana kaiwa nan yai waje, Umma ta kalli Mumy tace " Lalai danki dan masifa ne, bala'i ne kuma an

noba ne."

  Mumy cikin takaicin kalaman Umma tace " Malama kisan abinda zaki dinga gada nasan yayi laifi amma ko kadan bai cancanci kalamai irin wannan ba daga bakinki ba, dama kowa na gidan."

*#ASHRAFEENAH TEAM*

*1LOVE

💞

**ZUCIYA*

_ĸow

a da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*52*

_Ga masu min korafi akan yin da nake sau d'aya, kuyi hakuri inada uzuri ne, ni kaina inaso inga nayi dayawa dan in kamalla littafin, sai

dai ina kara baku hakuri, dan Allah kuyi hakuri da page d'ayan da nakeyi, in har na samu dama nima zan yi sama da page d'aya......Nagode da kauna, Allah yasa ku fahimceni._

*ZUCIYA*

_ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*

ayushermohd.

blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*

💡

*52*

_Ga masu min korafi akan yin da nake sau d'aya, kuyi hakuri inada uzuri ne, ni kaina inaso inga nayi dayawa dan in kamalla littafin, sai dai ina kara baku hakuri, dan Allah kuyi hakuri da page

d'ayan da nakeyi, in har na samu dama nima zan yi sama da page d'aya......Nagode da kauna, Allah yasa ku fahimceni._

Sun dawo gida aka bar Umma kadai acan, Mumy ta kalli agoggon jikin mota karfe 12, lalai dole ta hakura sai zuwa gobe ta samu yin ma

gana da Ashraf in ma wasa yake to lalai kar ya sake mata irin wannan wasan.

Shikam Ashraf hankalinsa a kwance yai baccinsa, itakam Nafi akan sallaya tai bacci tana jiran Little.

Little ta shigo taga Nafi na bacci, shiru tai ta tsaya tana kallant

a har ta kai hannu zata tasheta ta koma kan gado ko me ta tuna? Sai naga ta fasa, kayanta ta cire tai kwanciyarta.

Mumy tana shiga b'angarensu taga Kawu a tsaye sai zirga zirga yake, yanzu in har da gaske Nafi matar Ashraf ce kenan ko sun kawar da

Ashraf itama tanada gadonsa? Gadan me? Bayan ba wanda yasan da auren iya kaci su karyata hakan.

Ya zarfafa a tunani sam baiji sallamar Mumy ba sai jiyai ta dafashi, kallanra yai sannan ya zare hannunta ya koma kan kujera ya zauna tare da daure fuska,

Mumy ta karasa gunsa tace " Me ya faru?"

Ya kalleta yace " Abinda yaran nan yai yana matukar damuna, nasan Ashraf bai daukeni a matsayin uba ba sai dai ban taba tunanin zai wulakantani haka ba."

Mumy tai ajiyar zuciya tace " nikaina abin nan ya t

abani, sai dai ina gani ya fadane kawai, gobe zanje in mai magana ai aure ba hauka bane."

  Washegari da sasafe su Nafi na bacci sukaji buga kofa kamar za'a b'ala kofar, a razane suka tashi, Little ta bud'e kofar da sauri.

   Anisa ce a gefenta kuma

Umma ce fuskarnan kamar me? Banko kofar sukai tare da shigowa ciki suka gifta Little tare da wucewa gurin Nafi wacce ta mike zaune sai dai kana ganinta kasan a tsorace take, Anisa ta karaso a zuciye ta d'aga hannu zata kifa ma Nafi mari, da sauri Nafi ta r

ike hannunta duk da tana tsananin tsoron yanda taga fuskokinsu sai dai bazata yarda da duka ba kuma.

   Anisa ta kalleta cikin tsananin kishi tace " ke har kin......."

Umma ce tai saurin kifa ma Nafi wani wawan mari ba tare da ta zata ba, Nafi ta sake

hannun Anisa tare da rike kuncinta ta kafe Umma da ido, Umma cikin mamaki tace " ni kike ma wannan kallan?"

   Nafi ta dauke idanta jitai Anisa ta rufe ta da duka gaba daya hannayenta, Little ta karaso zata tare, Umma ce ta riketa tace "meye naki a ciki

? Ke bakya kishin cin mutuncin da akama 'yar uwarki?"

  Little ta tsaya jiki a sanyaye, Anisa kam ta dage sai sauken takaicin ta take akan Nafi, can Nafi ta mike ta rike hannun Anisa, tace "Yaya Nisa inaji yanzu kin huce ai ko?"

   Anisa tai sototo t

ana kallanta, Umma tace " mene?"

 Nafi wacce taji zafin dukan iya zafi ta daure tace " gani nai dukan ya isa haka inkuma ba kasheni takesan yi ba."

  Umma a zuciye ta fizgo wayar charger dake jikin socket tai kan Nafi zata daketa, Nafi ganin ba sarki a

ikam ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login