Showing 1 words to 3000 words out of 48142 words

Chapter 1 - DIJEN KAUYE COMPLETE

29 Aug 2026

6

[23/02, 7:17 pm]

πŸ„

*DIJEN KAUYE...*

πŸ„





πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•



πŸ•πŸ•πŸ•πŸ•



πŸ•πŸ•



πŸ•



_Dasunan Allah mai Rahama mai jinkai Ina godiya Ga Allah Daya Bani ikon Sake Rubuta wannan Sabon Novel Din nan n

awa Fatana Allah Yasa Nagamashi Lfy Allah yasa Masoyansa Suji Dadinsa Sukuma Amfana Dashi Amin_

Shekarar rubutawa watan hudu, 2019...

*SADAUKARWA GAREKU MASOYANA MASU MUHIMMANCI DA AMANA*



*Sis Nerja,art YARIMA SUHAIL*



&

*CLASSIC FEEDO SUHANA*

&

*FRESH UMMIEY XEEY*

&

*Itz B Y ebrerheem*

&

*Maman Gausiyya*

&

*Sis Snaanerh*

*True life Story*

*Nabilancy Luv*

πŸ’˜

(Auntyn S&S)

Page 1

to 5

Hankalinta a kwance take damun furarta tana yan wakokinta cikin harshen fillanci, kwatsam babu zato babu tsammani taji an rufe mata idanu ta baya.

Ta tsaya cak! Da damun furar tana shakar kamshin turaren tafin hannun wanda ya rufe mata idanun.

Tasan waye ko da kuwa ba ta juya ba, ta haddace kamshinsa, Abokintane wato Abdulhamid wanda take kiransa da Abokin birni

Murmushi tayi tareda cewa, "wallahi na ganeka Abokin birni ne..."

Ya cire hannunsa daga fuskarta a hankali yana fara'a ya

dawo gabanta ya durkusa yana kallon kyakykyawar fuskarta.

Ta ajiye kwanan robar da take damun ta kalleshi da mamaki tace "Abokin birni yaushe kazo?"

Yayi dariya yace, "Yanxu yanxu muka shigo kauyen naku jakata kawai na jiye a gidan gona na taho wa

jenki Ζ™awata ta birni."

A tare sukayi dariyar kiranta da yayi Ζ™awarsa ta birni.



"Amma dai kai kadai kazo ko?" Ta tambaya.

Ya girgiza kansa yana mai nuna mata bayanta yace, "Kalli can ki gani."

Ta juya a hankali tana Mai dora idonta a kansa,

a take taji wani k'ululu ya tokare mata makoshi, ranta yayi mugun b'aci da wannan bak'in toxali da tayi da rana tsaka, wannan shi ake kira da mugun gamo.

Ta ki jinin ta ganshi, ta tsaneshi kamar yadda shima ya tsaneta.

Abdallah kenan yaro matashi

Ι—

an

kwalisa me ji da kansa, me takama da arxikin da Allah ya baiwa ubansa, mutum ne Wanda ba ya son ganin talaka a kusa dashi, yana da shariya gashi miskilin gaske.

Abdallah Cousin ne ga Abdulhakim wanda jininsu ya matukar haduwa very close suke tun suna y

ara suke kwana daki guda har yanzun da suka girma basu raba daki ba, saidai Kuma Halayyarsu ta bambanta don kuwa shi Abdulhakim mutum ne mai son mutane, bashi da damuwa ga wasa da dariya, ba ya da wulakanta Ɗan Adam.

Abdallah yana da wani boyayyen halin

da yake boyewa, Wanda bai taba bari Abdulhakim ya ganoshi ba wato shaye-shaye, yana shan giya, tun suna malesia ya koyi sha shida abokansa na sheke aya har da neman mata yake yi wanda a boye yakeyi domin bai taba bari Abdul din ya gane ba.

Sigari kawai

da ya kamashi yana sha saida ya dauke masa wuta, saida yayi wata uku baiyi masa magana ba kafin daga bisani ya dawo yana kulashi shima don Abdallan yayi kwantan bauna ya nuna masa cewar ya daina sha shiyasa ya sauko daga fushin da yayi dashi suka koma kam

ar yadda suke a baya.

Abdulhakim ya tsani mutum mai halin banxa ballantana kuma shaye-shaye shiyasa bai taba yin abokiba saboda baya son tension.

Dije ta hade girar sama da ta kasa tana watsawa Abdallah Wani banzan kallo sannan ta juya ta kalli

Abdulhakim tace "Abokin birni,Kai me yasa wani lokacin kake da kwashe-kwashe ne, haba, me yasa kaxo min da wannan me bakin halin? Ace mutum kullum fuskarsa a turbune kamar bayan tukunyar tuwon gidan gandh."

Abdulhakim yace me zaiyi idan ba dariya ba sa

ida yayi Mai isarsa sannan yace, "Haba khadija ya xakicewa

Ι—

an uwana mai bakin hali don Allah kada kisake aibata masa suna kinji."

Tace, "Wannan Kuma da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, amma kasan dai jinin mu bai haduba ko? Kasan baya sona yatsa

neni, Kuma nima gaskiya ba son ganinsa nikeyi.."

Abdallah daya karaso gun ya katseta da sauri, "Ke kaxamar Ζ΄ar kauye ba gunki naxoba kuma nima ba qaunar ganinki nake ba, gun dan,uwana naxo."

Ya nuna Abdulhakim, "kai kuma ko ka taso kazo mu wuce muyi

abinda ya kawomu ko kuma walh in dauki mataki don yanzu sai inyiwa Daddy waya in shirya maka sharri."

Dijeh a cikin ranta tace, "Zaka aika mugu Mai Bakin hali."

Abdallah ya hade rai, "Kaga Mallam bana son rashin mutumci, ka tashi mu bar wajen Nan k

o muyi fada."

Abdulhakim yace, "Fada dai Bai wuce damben dokeni in dokeka."

Abdallah ya taso mashi da Fada, "Eh gwara muyi fadan, Mun dade bamuyiba dama gara muyin indai akan wannan bakauyiyar kucakar ce kuma kasani ba inda zan motsa walh kafata kafa

rka, banza mara aji."

Abdulhakim yadawo da kallonsa gun dije da take hada kayanta zata bar wurin tun kafin wannan mugun ya kaita wuya tayi mashi babu dadi azo ana wallahi tallahi da ita.

Abdulhakim ya hau bata hakuri don yaga kuka takeyi.

"D

akata khadija, tsaya kiji, nawane duka furar zan biya ki koma gida ki huta kawai."

Da muryar kuka tace, "Ka barshi kawai nagode ko iya cin zarafin dan,uwanka ya isheni a yau."

"Oh my god khadija, kin san ban so ranki yake baci akan wannan mugun, kh

adijah idan da sabo yaci ace kinsaba."

Ta rike kugu ta kalli gefe tace, "abokin birni ya kamata ka barni kamar yadda dan,uwanka ya bukata tunda mutunci ne a tsakaninmu ba wai soyayya ba."

Ta kalli inda Abdallah yake tace, "Kai Kuma idan tsammaninka

soyayya mukeyi shiyasa kake wulakantani to ba soyayya mukeyi ba, mutunci ne kawai da mutunta juna Wanda ka gagara ganewa."

Abdallah ya taso mata, tayi mashi banza, tace, "Abokin birni kawai ka tafi."

Abdulhakim Yace, "naji amma kinsan Allah ne yah

adamu bashi ba ballantana ya rabu kuma kinsan nayi sabo da shan furarki, kin san dai duk lokacin da naxo kauyen nan sai nazo nasha don haka ki zubo min a leda in tafi da ita ko kuma walh inkai kararki gun Addaji ince yau kinmin rowar furarki mai dadi."

Ta duka a hankali ta juye masa furar data gama damun aleda takulle tabashi

Yakarba yana cewa "nagode ga kudin."

Ta sunkuci kayanta tayi gaba ba tareda ta kulashi shida kudin nasa ba.

Abdallah yaja tsaki yace, "Banxa kaxami mai shan kayan kax

amai, kai dai walh kalar zaren ba kalar yadin bane."

Harara Abdulhakim ya maka masa, "ka shiga hankalinka zan b'ata maka Rai walh, ina ruwanka cikinka ko nawa?"

"Ai walh da insha wannan furar kazamar gara na kwana dubu da yunwa...mmmttsssa ya bug

a masa tsaki ya juya zai bar gun

Abdallah yai gaba yana masa dryr mugunta

shikuma Abdulhakim yabi bayansa yanata yi masa mitar abinda yayiwa dije

~~~~~~~~~~~~

Koda suka isa Gidan gonar dadyn nasu kowa safgarsa yashiga yi, ran Abdulhakim abace y

ake ko kula Abdallah baiyiba na tsahon wasu awanni yana fushi dashi.tunanin abinda zaiyi masa ya huce kawai yake.

Shiko Abdallan Ya nuna ko ajikinsa, saida yaga da gaske fushin Abdul din yake kafin nan yaje yasameshi awata yar rumfar shakatawa yaxauna a

kusa dashi yace "Abokina har yanzun fushi kake dani ko?"

Abdul hakim yayi biris da shi, ya cigaba da karatun news paper dinsa.

Abdallah ya kwace news paper din yace, "Kai dan iska ni zaka juyawa baya akan waccen kucakar yarinyar da bata kai ta kawo b

a, kana nufin har anxo lokacin da wata zata shiga tsakaninmu, lallai kuwa, nan gaba ban san ya zakayi min ba idan ka nunata a matsayin wacce zaka aura na hana."

Murmushi Abdulhakim yayi yace, "Kana bani mamaki Abdallah kana yin abun da bai cancanta ba,

wannan ba halin gidanmu bane, wannan wulakanta dan adam din da kakeyi sam momy da dady basu koyar mana da hakan ba, sunbamu tarbiyya kuma sun nusar damu cewa talaka da mai kudi da dan kauye da dan burni duk daya yake a wajen Allah madaukakin sarki.wannan b

a dabiar arziki bace saka Wani adamuwa Sam Hakan Bai ba. There are All together dai...."

Yai saurin katseshi da cewar..

"Naji Amma kasani ai ba matsayinmu daya a duniya ba," Abdallah ya fada da zafin rai da daga murya.

"Kai kake ganin hakan, kuma

lamarin Allah baida wuya, xai iya maida mai kudi ya dawo talaka haka zalika zai iya maida talaka ya dawo mai kudi, ko kuma dan kauye ya dawo dan burni harma yafi dan burnin bude ido da iya mu'amula ta wayewa, ita yarinyar da kake rainawa sai Kaga ta waye h

ar ta fika wayewa da ilimi."

"Walh karya kake duk inda dan kauye zaije baxai taba wayewa ba dole sai ya nuna kauyancinsa, kawai dai kowa ya xauna a matsayinsa, kai dai kawai saboda an tabo waccen yarinyar shine ka zama mai wa,azi."

Dariyar maganar

Abdallah taso sille masa amma sai ya dake yace, "To amma ai kaima asalinka dan kauyen ne, ko har ka manta ne da a nan aka haifi mahaifin daddy, nan ne asalinmu dan dai mun rasa kakannin namune da sun rikeka agunsu ai."ya Kara she da Raha.

Wani naushi

ya kawo masa dan jin haushin lafazinsa ya kai masa duka. Abdulhakim yagoce da sauri yana dariya.

Shikenan fa suka shirya, dama haka suke fadansu ba ya nisa suke shiryawa su koma kamar komai bai taba faruwa ba.

πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Nan fa aka shiga hirar duniy

a amma saida ya tursasa Abdallah akan lallai wai sai sunje ya baiwa dije hakuri na yanda ya sakata kuka.

Abdallah yaja tsaki yace, "Allah ya kiyaye in baiwa sa,ar kanwata ta biyu hakuri, haba, ai walh ko za.a kasheni bazaniba sam baka isa ba, itama ku

ma bata isa ba, kawai saboda kana sonta sai ka bakanta min."

Abdallah yace, "nifa babu soyayya a tsakaninmu kawai amintace da haduwar jini."

Tsaki Abdallah yakara ja yace, "hhhmmm iska yana wahalar da Mai kayan Kara, Kai dai kaji dashi, ace duk

yaran cikin gidanmu ba kai aminta dasu ba sai wannan yarinyar, haba mutumina nafi kowa sanin halinka."

Abdulhakim yace, "Amma dai ka san ina da tunani, ba kamar kai nike ba."

Abdallah ya mike yabashi guri yana zaginsa, "aikin banxa akwai mara ha

nkali irinka dan,iskan kauye."

πŸ˜…πŸ˜…

Da yammaci sakaliya Abdulhakim yashirya tsaf yatafi gidansu dije yadade a kofar gidan kafin yasami dan Aike yaturashi gidan yayo masa sallama da ita.

Bata d'au lokaciba tafito tana ganinshi ta hau dariya tana fad

in, "Walh na dauka ko ba zaka biyo baya ba, da baka biyo sawu ba da na kara fushi akan wanda nikeyi."

Abdulhakim yayi dariya yace, "Aww dama fushi kike da abokinki bai saniba?"

Ta murguda baki tace, "eh mana bayan a gabanka dan shigegen can yagam

a cimin zarafi amma baka hanashi ba, baka rama min ba, nazaci zaka samu wata kalma mai zafi ka watsa masa da shima zaiji haushi amma sai ka tsuke Bakinka kayi shiru ka barni da Fada ni daya, to ka Fada mashi ya shiga taitayinsa Dani tun ban yi mashi babu d

adi ba azo ana wallahi tallahi .."

Yanda take Mul..mull da Dan mitsitsin bakin nata ita adole ta iya tsiwa sai abin taso Bashi Dariya, sai ya murmusa yace, "Sabr dear to yi hakuri kada ki gota mashi muqamuki azo ana wallahi tallahi Din."

Tace, "Awww

dariya na baka, to yayi maka kyau."

Abdulhakim yace, "To ai kece khadija, uhmm, kiyi hakuri na rasa yadda zanyi da Abdallah akan ya daina maki hakan amma abinda naga yafi kawai idan har yayi maki ki rinka ramawa, kada ki dubeni, nine na saki domin in na

fiye shigar maki zamu rinka samun sabani da shi."

Ta gyada kanta tace, "to shikenan aiko walh bazan taba raga masa ba, dama albarkacinka yakeci tunda kuwa ya bani wuka da nama Aiko ya Tara ya samu, yana Fada min ciwo zan kira mashi mutuwa, dukkanin W

anda yayi min kan Kara sai nayi mashi na itace ya shekara ya shekare yana amfana."

Abdulhakim yayi dariya yace, "Yauwa ta wajena, Hakan za,ai yanzun dai muje ciki in gaida Addaji."

Tace " to muje."

Har cikin dakin addaji ta kaishi suka gaisa

cikin mutumci da Addajin sannan suka fito kofar gidan.

Sunyi hirarsu cikin raha yana ta janta da wasa suna dariya.

Lallai wannan haduwar jini tana da ban mamaki.idan ka gansu tamkar masoya,insuka hadu suna Jin nishadi tamkar Kuma Kar su rabu sukej

i,a labban Abdul Bai taba furta Mata Kalmar So ba,ko zai so mairo aganinsa tayi kankanta saidai raino to bareshi ma atsarinsa soyayya ba kusa ba dai.

Zakuyi mamakin jin cewar sbd dije kawai Abdulhakim yake zuwa gidan gonar tasu

Amma Kuma tambayar a

nan shine to shi kuma Abdallah sbd wa yake xuwa knn?

TARIHINSU..

Alh Mustafha hamshakin me kudine yana zaune da matarsa a unguwar shagari kwatas dake Zoo road

Matarsa daya mesuna hjy Samira mace me kirki da son jama.a kamar dai mijinta ga alkairi

Yaransu biyar aduniya banda uku da suka rasu

Aunty Maryam itace babba tana Auran wani tsohon dan majalisa me kudine shima sosai.

Abdallah shine me binta shekararsa talatin da biyu, Bashir shine na uku yana karatunsa a KUT wudil bording shi ba.a

futar dashi wajeba Shida kannansa mata Zannurat da Mubina kusan sa,annin juna ne kusan shekara biyune tsakaninsu Dan momy kwanika tayi alokacin, zannura ce babba tana Nouthwest sai mubina data gama secondry dinta yanzun zata fara karatun gaba da sec.din

Mahaifin Abdulhakim shine Alh Mahmud kanin Alh mustafha ne Allah yayi masa rasuwa, tun Abdulhakim yana yaro sukayi accident shida matarsa hjy shafa,atu suka rasu dama shikadai ne dasu daga nan ne Kuma rikonsa ya dawo hannun dan uwan baban nasa.

Rikon tsakani da Allah ya samu a gidan basu nuna bambanci a kansa, dukkanin abun da sukayi wa Abdallah shima zasuyi masa, wani xubinma har nashi gatan yanafin na Abdallah da yake akwai dukiyarsa agun Alhajin gadonsa knn.

Abdulhakim yabaiwa Abdallah s

hekara uku Amma a idanu mutum bazai ce ba har sai an fada dan Abdallah yafishi auki, yanayinsu ba daya bane ba, Abdulhakim dan jikine dashi shiko Abdallah kakkaurane

Abdallah da Abdulhakim kud da kud suke basu taba fada ba inba na wasaba kuma Abdallah

yana bashi girmansa suna mutumta juna sosai wani baya zartas da wani abun saida shawarar dayansu

Zannurat tana matuqar son Abdulhakim Amma takasa gaya masa saidai alamu da take nuna masa Amma ya kasa fahimtarta.

Dayawan lokuta intai masa abinda za

i gane son da take masa inyai biris saidai mubina tayi Mata dariya tace Mata iska na wahalar da me kayan Kara...yarinya kiyi biyayya in kulla abin...

Hade Rai take ko takai Mata duka dayake ta rainata dayawa ma insuna fada sai momy ta shiga tsakani.

~~~~~

Labarin Dije Yar Fulani...

Dijen kauye marainiyace Asalin iyayanta sun rasu, mahaifiyarta na haifarta ta rasu a ranar yayinda shi kuma mahaifinta saida ta fara girma sannan ya rasu, a nan Kuma Rikonta ya koma hannun yayarsa da suke uba daya dan b

aida kowa sai yar'uwarsa da kaninsa akauye, su biyu ciki daya shikuma uwarsa daban amma sai idan an fada sannan mutum zai sani kasancewar kansu a hade yake.

Addaji itace marikiyar Dijeh tana sonta sosai, Addaji bata taba haihuwaba shiyasa tamaisheta

tamkar yar cikinta, fulanine su usul ma kuwa

Dije yarinyace mai karancin shekaru amma tanada girman jiki shekararta goma sha shida amma saika zaci tayi shekara ashirin.ga gabunta na faramci da sokonci.

Sai idan ta buga sokonci ne zaka gane yar

inta na tare da ita.

dije kyakykyawa ce sosai gashinta har gadon baya saidai baya samun gyara, gata da son tayi gayun kuma a kullum tanaso taga mutum dan gayu shiyasa Abdulhakim yake burgeta gashi tana burin taga taje birni tayi rayuwa acan saidai kum

a batada kowa acan ta yaya knn zataje birnin ???

Yaushe burinki zai cika……?

πŸ˜‚

Yours Nabila Aliyu Tudun Wada Inkiya Nabilancy love *Auntyn Sayyada da Shahida*



_Dijen k'auye_









*Nabilancy Luv*

πŸ’˜

(Auntyn S&S)

5-10

Kwanansu daya akauyen Dan Rogo suka kammala abinda sukeyi suka hau shirin komawa gida

Akwai ma,aikatan dake kula da kaji da Ragunan da shanun dake ckn babban kangon da yaxama gidan gonar do

min garke guda aka ajiye shanu da ragunan ga bangaren kaji masu kwai daban marasa kwai daban

Duk Wani guri da zakaje ka samu kwai acikin Dan kauyen to masu shagunan anan gidan gonar suke samu ta hannun Ma,aikatan Wanda Su Abdallah insunzo Sukan lissafa

su fitar da abinda aka samu ta ciki Kuma suke fitar da albashin Ma,aikatan Dan ba Ζ™aramin kudi ake samu ba.

A duk ranar da sukazo har su koma suna kula da koina da komai har dusar awakai da dusar kaji sukanga Babu matsala a wannan bangaren kafin sutafi

saidai sujewa Da Daddy lissafi da yanda ake ciki,shiyasa kafin aga kafarsa a kauyen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login