Showing 1 words to 3000 words out of 57925 words
KUYANGA
(Tare da ci gaban sa Gimbiya Zeenatu)
NABILA ALIYU T/WADA
(NABILANCY LUV..AUNTY S&S)
SHEKARAR BUGU 2022
LITTAFAN MARUBUCIYAR
1-Zaman marina
2-Tagwaye
3-Tauraruwa me wutsiya
4-Ranar wanka
5-Dana sani
6-Zeenatu Yar jarida
7-Ali
Gadanga
8-Makauniya
9-Idan kunne yaji
10-Kyan Tafiya
11-Gajimare
12-Mata jigon Al'umma
13-Kuyanga da Gimbiya
14-ZeenaTu.
15-'Ya'Yana
16-'Yar Talla
17-'Yar halak
18
'Yar makafi
1
9
-'Yar fillo
20
-'Yar Baba
2
1
-'Yar mace
2
2
-'Yar Gudullen sarki
Gaisuwa
ga kafa
tanin Kawayena da mukai makarantar legal da abokanan Arziki da kuma kawayena na AYI FADA A SHIRYA GROUP INAJI DASU.
JINJINA
Ga Dangina Ahalina masu Albarka wato Iyalan margayi Ali Ahmad Daura city da kuma Ahalin kakana Dan Daura me bindiga dana Kakana Sa
manja Audu ina jinjina muku kaf dinku Allah yakara mana zumunci da kaunar juna.
Fatan Alkairi da jinjina
gareki Yar uwata ta jini inaji dake sister Maryam Hassan Jikar samanja Audu mrs Habibu Aliyu Akilu Allah yaraya muku yaranku ya kara muku
kaunar juna.Allah ya daukaka Maryoti collection gurin saida kayan yara dana manya d lesika da atamfofi na hanyar fansheka titin zawaCiki.
Addua da fatan Alkairi
gareku 'ya'yana Zainab Sayyada da kuma fatima shahida Allah yarayamin ku S and S Allah
yabaku ilimi me Amfani ubangiji yasa naga Aurenku.
Sadaukarwa
Gareki uwa ma bada mama Haj. zainab Samanja Audu Mamana takaina Allah yaja kwana.Allah yajikan Ali ahmad mahaifina sadaukarwar tasu ce Allah yajikanshi.
Jinjina da ban girma
ga kafatanin abo
kan Aikina na Aminci Radio da kuma wanda muke waka dasu da kaf masu studios ina miko jinjina har daku abokan Aiki da muke fassarar film tare musamman kamfanina dana Ke aiki cikinsa wato BADAWA SOUND RECORD na gaida oga Imrana badawa baban hanif
agurin kawa
yena Asaka da kuma Yan Dangana kafataninsu da Yan layin marmara kawaye na Yarinta.
Sai Online fans grp
Musamman dan ku Online fans
Taskar Nabilancy 1-2-3
da kuma Kainuwa Writers Association ina yinku sosai kamar yanda kuke yina
GAISUWA TA MUSAMMAN
Ado Ah
a
Mad g
i
d
a
n dabino
(M.O.N)
uban taro kuma uban qungiyata ta Kainuwa writers.
sai
Yan commettee
Bashir Umar Aminci radio
Ibrahim indabawa
jamilu jibeka
jamila Abdullahi Rjyr lemo
Gimbiya Rahma
Abu hisham
Jidda washa
Khadija jornalist
Fauziyya Auwal
jingau
kabir Anka fagge
mukhtar karami Abu hisham
Ayuba muhd Dan Zaki
Abu s
KUYANGA
S
arki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata UMMAH
Mebi mata itace Saratu MAMAH sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma FATU akece mata
UMMAH m
acece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da du
k
wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D'anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa y
aki dawowa Yasamu guri xan babu kwaba babu harara.
Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho dashi. Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi zai laluba yadau
ra masa Aure da koma wacece Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana raye raye.Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa
mesuna RIHANNA wacce duk wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d'anshan mintinta tasan takan iya kulawa da d'a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amm
a ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari yasakeba. Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan
sarkine me jiran gado
Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn.Sarki Abdallah
akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine sarki agarin Yasan da cewar
Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi
yahuta acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa LAMIDO
Ummah bata kau
nar FATU da D'anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya bata dametaba.
Kowane d'a daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi
Amma tun tasowarsu da suka
girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na
bata yaro da canza masa halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya yakoyo wasu dabi'un Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan nata Turai yakuma gamsu MAMAH ma batag
a laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun
Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai
Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta
******
Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure
yake baya futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away
Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta
ta biyoshi ta nemi inda yake Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn gidan
Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin ma kwana biyu yabata zaitafin
Da tunani
n yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun
Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar Alfarma ta sarauta
Bayi maza D
a kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu ga Yarima sarkin gobe
Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba
Farace shar gata da h
ips ga nashanu suncika mata kirji
Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira
Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi
Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi "me kikeyi acan?
Da rawar murya tace "ina..,ina yin..,Shara nakeyi..
.Yace "Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza?
Tayi kasa da kai tace ckn rage murya "Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin.Yace "MAHBUB!wanene kuma MAHBUB?Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi
Tace "Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi
Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu yaga tana motsashi ahankali
Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai
Wani
abu yaringa ayyanawa aransa
Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun
Tayi
saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu
Yace mata "meye sunanki?
Tace " sunana KUYANGA!!Yace "ke Sunanki nace zaki fadamin
na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa.
Tace "Sunana ZEENATU
Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa
Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidi
ma daga me matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana karba tanaci
Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi Ya amsa da ka
Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri
Saida suka futa kana yag
yara zama yace "UMMAH Barkanki da warhaka
Tayi murmushi " Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar Allah.
Yayi murmushi yace "Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda matsala tabangarenki zaki sharen h
awaye Mai martaba kawai nakeji
Tace "fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka
Yace "Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarn
i intafi.
Tayi murmushi "Angama Yarima yaushe kake son katafin?Yace "Jibi nashirya tafiyar
Tace "Jibi jibin nan? Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida akeso kahaye karaga wataran yaxa,ayi aga baka xama abaka.
Yace "kada kid
amu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi
Tace "kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau.
Yayi murmushi yace "Yawwa nagode Ummah saidai kuma.……yai shiru yana sosa keya
Tace "ehe!fadi mana
yakai
shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka.
Yace ckn rage murya "Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan.Murmushi tayi tace "bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke ka
nada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar?Take yahau kwatantata
Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta
Jin
mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya
Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa
Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake
ganinta
Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba
Tsaki yaja Aransa yace "to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita.mai Martaba Sarki Abdallah yayi shiru bay
an gama jin Bayanan da Ummah Tazo masa dashi natafiyar Anwar Turai
Yakalleta yana murmushi yace "Naga alamar yaronnan inmuka ta tashi bazai gyara halin saba Nikam bana sonsa da zaman wajen nan nafisonsa akusa damu domin Aure nake so yayi tunda yakai munzal
in Aure ko Lamido yanzun ya isa Aure barantana shi
Ummah tace " Aure ai nufin Allah ne baisamu wacce tayi masa bane shiyasa saimu tayashi da Addu,a kada mutakura masa Tunda can din yafi jindadi gara kabarshin yaje aidebe kewa yakeso yayi
"Kina baiwa yaronn
an gudummawa naga alamar bakya son yagyaru shiyasa kike daure masa gindi
Ta dafe kirji tacanza fuska
"Kamar yaya? Nikam walh babu wani daure masa gindi danakeyi kawai bana son yashiga takurane da damuwa Tunda shi bayaro bane da hankalinsa ai ko yana nesa d
amu bazai lalace ba shiriya fa ta Allah ce Addu.a kawai yadace muringa binsa dashi.Mai martaba yace "Amma dai kinsan bazaki hada halinsa dana Lamido bako? Lamido yafishi nutsuwa da hankali harma biyayya da ace Lamidon ne babba dana more....
Ta katseshi ta
na kuka "Kawai dai kace kafison Lamido akan shi nikam walh banajin Dadi sai inga kamar kana nunan banbancine kuma komai lalacewar Yarima ai dai shine babba kuma dole shizai zama sarki acan gaba....Yakatseta dacewa "Saurara Fulani kinsan dacewa Adalin Sarki
me kamun kai shike cancanta da yin sarauta akowace masarauta dan haka dole sai inyarima yakasance da hakan sannan zai mulki garin nan inko bai canzaba to Al,umma bazasu soshiba Tunda ko a yanzun sunfara farga da banbancin halayyarsu
Tace "To walh koma meye Nikam Bazan taba barin Wani bayan Yarima ya mulki garinnan ba inba shiba dan haka koma meye za,a yi masa shine dai gaba
Yadaga mata hannu "ya isa meye na tada hankali da kuka indai wannan maganar mulki ce Allah ketsara komai bamu z
amu tsara ba tafiya turai kuma Yaje yaita tafiya Nadaina hanashi tunda bakya so inhana din duk randa yagaji da zuwa yadaina Amma kusan da sani zanbashi mata nan ba dadewa ba
Har zatayi magana kuma saita fasa tunda bazata ari bakin yariman ba tasan halinsa
sarai shima bazai so Auran hadiba.Ta mike tafuce batareda ta gaya masa cewar da "yar rakiya zai tafiba wannan tafiyar tasan Sarkin bazai bariba
*****
Ana gobe zai tafin Ummah tasa aka kira mata KUYANGA
Koda tazo ckn biyayya ta durkusa gabanta tana jiran u
marni domin tayi tsammanin aiki aka kirata tayi
Ummah tace mata "Kuyanga Zeenatu ko?Ta daga kai sama
"To kifara shiri daga yau gobe zaku tafi turai keda yarima zakijene domin kiringa hidimta masa komai nashi kece basai yace ba indai aikin wahalane kada ki
bari yayi Har sai ranar da yaga damar dawowa zaku dawo tashi kije.
KUYANGA
Tace "Angama Ranki yadade.
Ta mike tafuce daga dakin fulanin
Koda takoma sashinsu zama tayi a inda suke zama da MAHBUB Ta zabga tagumi tashiga tunanin wai itace zataje turai tabdij
an lallai zataji dadin Rayuwa zata canza tawaye tunda tashigo gidan sarki tun tana karama bata taba futa wajen gari ba sai gashi abin farin ciki zata keta hazo
TO ABIN BAKIN CIKIN FA? wata xuciyar ta tambayeta tare dayi mata tunin abinda zatajeyi turai dak
uma tuni da wanda zataje din
Take fuskarta tacanza daga walwala zuwa Damuwa
Zuciyarta tahau bugawa to shin wane irin zama zasuyi Alhalin halinsa bame kyau bane?ance yana shan giya ance yana neman mata zance ya yadu agidan dan dai ana boyewane kada aji aba
kin mutum a hukuntashi.
Jitayi antabata afurgice tadago kanta saitaga ashe MAHBUB ne abokinta abokin sha,awararta
Takalleshi kawai yau babu dariyar datakeyi masa
Yazauna kusa da ita yafahimci akwai damuwa yau kenan
Yacire mata tagumin da tayi yace " *ZEENA
H*! Haka yake ce mata
Takalleshi akaro na biyu tasunkui dakai
Yace mata "meya faru naganki ckn damuwa anyi miki wani abin ne bayan nabarki anan din?
Ta dago ahankali tace "Bayan barinka nan gurin aka aiko kirana daga Fulani
Koda naje kiran saitake gayamin
wai infara shiri gobe Yarima zaiyi koma Turai dani xai tafi domin hidimta masa da koma kuma inmun tafi ba ranar dawowa harsai inyagaji yadawo dankansa
MAHBUB yadafe kirjinsa tareda Rintse idanu yana kiran sunan Allah
Tabbas
yashiga tashin hankali domin ay
au yashiga halin dabai taba shiga ba arayuwarsa tunda yazo duniya
Yana bude idonsa kwalla nabiyo baya yace mata "ZEENAH tafiyarki Turai tana daidai da tafiyar farin cikina nackn gidannan Domin kece me deban kewa akoyaushe kuma ke nake kallo nake jin dadi
koda ina ckn jin Yunwa ke nake kallo naji nakoshi kinsan da cewa Nadade ina son.Yayi shiru yana goge kwallar datake gudu akuncinsa
Yakalleta ido da ido yace "ZEENAH bantaba gaya miki Sirrin zuciyata ba saiyau, yauma dole ce zata saka domin naga zakiyi nisa
dani Walh ZEENAH zaman da nake dake bana abokantaka bace Na SO Ne zallah dan Allah kisoni koda bazamui Aure ba kice kema kina sona ko naringa tuno kalmar inajin Dadi
KUYANGA
Taji wani yarrr!ajikinta taringajin shigar wani abu tundaga tafin kafarta har
zuwa kwanyarta tabbas Tafahimci wannan abun dayake shigarta bakomai bane illah Son MAHBUB ada itakam tadaukeshi aboki amini amma ayau saitaji yanayin yajuye mata da So
Tabbas tana sonsa itama bayama data tuno zasuyiwa juna nisa saitaji xcyrta ta karye hawa
yen da basu zubo ba saigashi sunxubo ganin nasa ma sunzubo din
Tace ahankali " MAHBUB meyasa baka gaya min tuntuniba meyasa kaboye sai yau da muka makarowa juna zaka fada yanzu gashi zanyi maka nisa
Yace "Duk nisan da zakiyi indai kina sona to tamkar muna
tare ne kedai kitaimaka ki furta min ko naji dadi.
Takalleshi tayi murmushi tasadda kanta akasa tace
"INA SONKA MAHBUB."!
yai ajiyar zuciya tareda yin hamdala ga Allah yace "nagode naji dadi ki rikemin Alkawari ki rike amana kikuma kula inkun tafi
bamu da ikon kanmu ZEENATU akarkashin ikon Sarki da Matansa da "YA"YANSA muke bamu isa muyi musu da Umarninsu ba sai yadda sukayi damu amma kada kiyi biyayya da aikin zalinci kada kisake acuceki kikasance me addu,a aduk inda kike
kikuma zamo me kamun kai a
duk inda kika tsinci kanki domin kada ayi miki cutar da zata karya miki Lagon Rayuwarki.
Taja ajiyar zuciyar Zuciyar xuciya tace "Naji na amince nakuma gode da Shawararka ya