Showing 51001 words to 54000 words out of 57925 words

Chapter 18 - kuyanga complete

Amana ne akaimin

Ya tsahir

ta tareda share zufa agoshinsa kana yaci gaba yana duban jakadiya



" kintabbar maganar da kika fada gaskiya ce babu karya aciki?



Jakadiya cikin karfin guiwa tace dashi

"Walh tallahi mai martaba banyi karya akan wannan zanceba Yarima Jinin wazirine ba jinin

kaba shida Fulani suka Samar da cikinsa inkuma sun musa to na yarda akawo qur,ani dukanmu mu ukun mu dafa



Fulani tayi saurin cewa " karya kike munafuka walh baki isa ki tozarta niba Allah ya LA,anceki jakadiya da kike so kisheganta min d'a....takawa ya

buga mata tsawa



Tuni tayi saurin yin shiru ganin ransa ya baci ta gama tunzurashi da yawa



Yakalli waziri yace "Waziri kaji abinda jakadiya tace akanku amma abokiyar mu,amalarka ta musa kaikuma me zakace shin gaskene ko karya take muku a dauko qur,anin Ku d

afa

Waziri ya share gumi yana muxurai kansa akasa yace " Allah yakara maka lfy zancen jakadiya gaskiyane amma INA Neman afuwa kayafemin ayimin rangwamen hukunci Fulani ta cutar dani domin tun kafin samuwar cikin yarima ita ta matsanta min tayimin tilas ak

an saina sadu da ita wai ta Dade dakai baka haihuwa nikuma alokacin taga me dakina ta haifi tagwaye ta rasu shine take kwadayin ta sami ciki dani inyaso saitace nakane saida muka kai ruwa rana na amince mata jin tace zatayi min sharri ta hanyar yimin asir

i inyaso inna aminta ta asiri saita fito tace nayi mata fyade to jin hakan yasa na amince ba shiri har mukayi sau

hudu ciki ya shiga shikenan ta kyaleni amma ta gindayan sharudan masu yawa akan inna fada zatasa akasheni



Waziri ya tsahirta jin kukan Yarima

agun

Takawa ya bashi umarnin ci gaba da maganar



Waziri yaci gaba da fadin "ina Neman sassauci Ranka ya Dade na munafurceka naci amanarka amma ayi duba akan maganata tsoro ne yasa na aikata kuma akan makarkashiyar da aka shirya na kawar da kai adoron duni

ya aka saceka duk wannan ma gaskiya ne Fulani ce ta shirya Amma shima dasa hannun yariman..…



Takawa yaja ajiyar zcy tareda share wata kwalla me zafi data kwaranyo akan kuncinsa



LAMIDO yaji tausayinsa matuqa lallai wannan lamari yakai matuqa bacin rai bai

taba ganin hawaye ko bacin ran takawa ba sai yau



Kowa agun yai shiru yana jiran yaji hukuncin da takawa zaiyi musu

Sarki Abdallah kowa yasan adalin sarki ne amma ayau duka gun ana ganin duk adalcinsa da kawaici da hkr to babusu gareshi yau



Yadubi Fulani da

kanta ke kasa kunya ta gama kamata shin ma dawane idanu zata kalli mijinta da D'anta Yarima?



Takawa yace da ita "Fulani kin cutar dani kin cutar da kanki kin kuma cutar da rayuwar Yaron ki kinkuma sab'awa mahaliccinki tabbas ko ban miki hukunci ba to All

ah zai miki nashi me tsanani kuw



Yayi shiru Jim kadan yaci gaba da cemata " hukuncinki na farko anan shine daga yau ni Abdullahi na yanke igiyar Aurena akanki guda daya na laifin da kikai min na cin amanata Dole kuma kibar min gidana tunda akullum shirin k

i shine kiga bayana da ahalina Dan haka bazan yarda kici gaba da zamar min ackn gidana ba zanso inga gidana yayi lfy



Tafashe da kuka tana faman rantSe rantse wai ta tuba tayi nadama bazata karaba ya yafe mata



Murmushin karfin hali yayi yace mata "Hhhmmm F

ulani kenan ai bani zaki nema yafiya saita ubangijinki da D'anki domin kin masa babbar illah na silar zuwansa duniya ta hanyar da bata daceba

kin kuma bashi gurbatacciyar tarbiyya



Yarima kuka yakeyi yau da idanunsa ayau yayi nadamar duk wani Abu dayasan y

a aikata agidan maras kyau da ace yasan matsayinsa tuntuni da bai yadda yabari yayi bakin jini agun kowa ba da yasamo soyayya agun Takawa kota halin kakane yau yayi nadamar zuwansa duniya inama ba fulani ce mahaifiyar saba

Da jajayen idanunsa yadubi Fula

ni yace " kin cuceni kin kwareni kazamar kwara wacce babu hanyar gyarawa walh bazan taba ganin mutuncinki ba tunda har da hankalinki kika take Sani na yanda Allah yayi hani da aikata zina, zinar ma me matuqar datti da tarin zinibi na Matar Aure da Allah ya

LA,anta walh INA nadamar zamowarki mahaifiya gareni



Ya tashi ahankali yaje gaban Takawa yaduqa yace "kagarceni kayafemin A yau INA kara Alfahari dakai Dan Allah kasamin Albarka ko nayi rayuwa me kyau agaba yau naga Aya tinda gashi an haifeni ta hanyar zin

a, nima kuma na haifi yaro ta hanyar zina abaya tabbas Abinda yafaru dani ayace, Dan Allah ka karbeni amatsayin danka koda nasan banida gadonka amma zanci gaba da zama dakai zankuma ci gaba da kallonka amatsayin mahaifi domin waziri bai isheni kallo ba



Tak

awa ya dagoshi yana fadin " adolenka waziri shine jigo kuma bangwanka dole ka daraja shi ka mutumtashi inhar kana so na rike ka na amshekan kamar yadda ka bukata



Yarima ya goge hawaye yace "to zanyi yadda kace nagode



Ya taka gaban su FAATU da MAMAH abin

tausayi yace musu " Ku yafemin abaya na nuna muku rashin girma da rashin biyayya amma duk hakan yakasancene ta sanadin rashin dace da uwa tagari daga yau kune iyayane zanci gaba da mutum taku INA sonku har raina



MAMAH da FAATU sukai murmushi suntausaya ma

sa suka dafashi sukace kada yaji komai ya

wuce zakuma sujashi ajikinsu



Yaje gaban LAMIDO nanma yanemi yafiya gunsa



LAMIDO ya dafashi tareda rike hannunsa yace "Dan,uwa na yafe maka kada kaji komai kamanta da komai ya wuce kuma kananan amatsayin na Dan,uwa



Yarima yayi masa godiya



Takawa yadubi waziri yace dashi

"Kai kuma kaci amanar abota sannan kajawa kanka faduwar mutumci da kima agidan nan abinda kukai min kuma Ku da Allah amma tunda kace abisa tirsasawa akai hakan to zaka fuskanci



Hukunci me sauki



Yakalli yarima yace "ko da kaji na amince maka zan karbeka naci gaba da rikon ka ahannuna sbd rufin asirinka don kada mutane su farga sugane to Dole kaima zan hukunta daidai da abinda ka aikata nasawa akashe Bawa MAHBUB sannan kanada la

ifi na hada kai da cutar dani DA kukai kaida mahaifiyarka



Yarima yaringa kuka da idanunsa zcyrsa ta karye duk Fulani ce taja masa koma meye

LAMIDO ckn kwantar da murya yacewa takawa " Ranka ya Dade INA Nema masa Alfarma akan ajanye masa yin hukuncin akan

sa domin dazarar anyi masa wani abun na tsaro kona horo to tabbas Duniya zata iya farga da wani abun kuma ina Neman alfarmar jama,ar wannan guri dasu saya wannan maganar ta yarima mu lullube mubar abin tunda haka Allah ya rubuta saiya farun



Takawa yahau g

yada kansa yana fadin "Shikenan na karbi batunka Bakuma naso kowa ya futa da wannan maganar



Manyan gari su liman sarkin fada,zagi dasu dagaci da masu unguwannin dake gurin da Fadawan dasuke zaman fada suka ce Angama bame daga zancen insha Allahu



Hindu tana

gefe tsuru tanata jin zuciyarta na bugawa lallai tana cikin tsaka me wuya Ashe dama da shege take Zaune tabbas ita kuma haka Allah yai da ita



Gashi tana sonsa!gashi sun fara haihuwa dashi inhar ta barshi to zata kwaru haka zalika

d'anta shima zai cutu



Maf

ita daya ta fitarwa zuciyarta tayi hkr itanma ta raka dashi ahakan tunda yanada kadarori kuma yanada ilimi gashi wayayye burintane dama taga ta zauna da wayayye me ilimi da kyau arayuwa danta Nasaba ai me saukine saita fada za,a gane kuma still ai yana gi

dan ba,a juya masa baya ba ballantana su shiga uku



Kafin taron ya watse Saida Takawa ya yankewa jakadiya hukuncin zama gidan kaso na shekara biyar domin tasami horo acan kafin nan halinta zai gyaru



Haka Waziri shikuma shekara biyu zaiyi yaci albarkacin ab

ota da amintaka da yarima cewar Sarki Abdallah



Ita kuwa Fulani yace mata hukuncinta makamancin na waziri yakamata ya yanke mata shine daidai ita to amma taci albarkacin Aure daya hadasu domin Aure yanada Kima da daraja Dan dai ita bata daukeshi dasu bane s

annan mahaifinta aminin mahaifinsane itama jinin sarautace dama Gasa akasa yayi na jarumta domin ciwo wasu gwala gwalai ko "Yar sarki



Alokacin yana saurayi kenan kuma dayayi wannan gasa yaci akazo bada abinda akacin su biyune dama sai gashi ana bude abin

da yaci akaga sunan " Yar sarki shaidar ita yasamu kenan zata zamo matarsa to dayake alokacin bai futar da macen Aure ba saikawai yahakura ya karba mahaifinsa ya Goya masa baya tunda akwai aminta ajunan iyayan nasu ita lokacin Fulani ma ko saninsa batayi

ba saijin sunansa DA takeyi dakuma kyansa da ake kwarzantawa kuma cikon ikon Allah tana ganinsa taji yayi mata



Dama alokacin Gasace ta ta gudu akan doki atsaye kuma da kafa guda zakayi gudun



To dama yanda yake jarumi me cikar jarumta ba tsoro haka dokins

a yake don haka sai suka kara shida abokinsa kuma sukaci



Su uku suka jera suna gudanar da gasar



Doki dayane ya Gaza kuma jarumin kai ya fado Dan wani attajirine shi dama ba jinin sarauta bane kuma shine Saurayin Fulanin alokacin



Su biyun dai su sukaci ga

sar inda kuma kyautar Fulani ta

fado kansa dayar gasar gwala gwalan ta fada kan Dayan da sukai gudun dokin akansa



To kunji yanda akai har Sarki Abdallah ya Auri Fulani

*********

Tunda akai kowa na gidan jikinsa yai sanyi Yarima ko iya futowa bayayi do

n kunyar jama,ar da akai abin agabansu ykyi

Bayama LAMIDO da Iyayansa matan



Shiko LAMIDO nuna masa yake komai ya wuce yama cire abin aransa har kiran yariman yakeyi awaya su gaisa dayajishi kwana biyu



Hindu kuwa dake awayece kazar Birni mindikiskis tayi t

ashige jikinsu MAMAH ranar sunar G.ZEENATU akai sabga da ita taringa sakarwa me jego fuska har hannu tasaka akai aiki da ita

Cab !KIN MAKARO KUMA TA BAYA TA RAGO



G.ZEENATU kuwa tasami labarin komai agun mijinta tasha mamaki amma dayake ita din bame

tsawwalawa bace saikurum tace Allah yakyauta



Fulani bata bar gidan sarki Abdallah ba saida akai sati tana dibar kayanta aboye tana aikewa gida domin tayi musu tazayyanewa iyayanta tana kuka



Inda sukuma sukace bata kyautaba ta kuma cuci kanta Dan haka baza

su saka bakiba tunda ta cutar da Sarki cuta me yawa Dan haka tazo ta zauna agida ga gurinan tazo ta share daki ta zauna zamanma kadai punishment ne ko zasu bawa sarkin Hkr saita gwaru tukunna



Asatin data bar gidan Asatin shima Yarima yakoma Turai sbd akw

ai wani kamfanin turare da suka taba Neman yayi aiki dasu abaya yaki amincewa yanzu ya shiryi aikin dasu



Kamar yadda yaje yiwa takawa sallama kafin yatafi Takawan yasa masa Albarka yayi masa fada akan rayuwa ya karfafa masa guiwa haka Hindu ma ta karfafa

masa guiwar tace masa "Dadyn Ciroma kajure kada ka daga hankalinka domin Duk

abinda kaga yafaru da bawansa rubutaccene bazaka taba gujewa kaddarar kaba kazama me tawakkali kaji



Yakanyi murmushi ya gyada mata kai kawai

***********

*BAYAN SHEKARA 18*

Gimbi

ya Zeenatu na Zaune akan kushin tana waya da Aliya kawarta dake Turai tana cewa mata " wai yaushe zakizo kasar ne ?wannan karan dai kindade rabonki da gida kinbiye Ogah yana boye mana ke



Dariya Aliya tayi tace "walh inason zuwa nasaka ranar zuwa amma tund

a yaga ina rashin lfy atsatstsaye wai saiyace gara ma incire son zuwa Nigeria a raina domin jikinsa na bashi cikine dani kada intafi inbarar masa ajirgi ko wahala tasa yazube idan nazo nikuma nace masa yama daina wannan tunanin shekarunmu fin 20 bamu sami

cikiba sai yanzu da girma yazo mana Wanda da ace munhaihu abaya da tuni muna shirin Aurarwa..…

GIMBIYA ZEENATU takatseta da cewa "bar fadin haka Kawata ba,a Tara Sani da Allah kuma karki fidda rai saikiga ko cikinne kuma Wanda suka shekara 30 ma zasu iya

samu balle Ku kimayi Addu,ar Allah yabiye bakinsa kawai



Aliya tace " To Amin,kema Allah yakawo mk don kinyi mana nusau dayawa khaleesat tayi bakin baya Dariya G.See tayi tace "lallai kam Niko harna hkr ba shima Ogan tun yana jira harya mika lamarin sa ga

Allah nike tausar sama tunda Allah yabamu dayarma ai abin agode masane wasuma neman dayarfa suke



Aliya tace " aiko dai tunda muma hakan take ina diyata Khaleesat "Yar daru " Yar shagwaba?

G.Zebra tace "Hhhmmm sunfita da Abbanta zaimata Registration na sch

din dazata fara high institutions ita tafison Sch of Nursing shikuma yafiso tayi FCE don so yake ta shekara biyu ko uku tagama ya Aurarta dazu suka

gama fada tanata fushi dashi suka fita to dayake Takawa yafison Abinda takeso bansan dai ya suka kareba k

o zaibi maganar Takawan ko kuma zai lallab'a takawar ne ya hkr ayi nashin oho



Aliya tace " ho!Khaleesat "Yar Lele lallai inason inkara ganinta gani biyu nayi mata aduniya amma ina kaunarta araina



G.ZEENATU tace " Hhhmmm kusan kullum zancenta Aunty Aliya da

ace Abbanta me ra,ayin tayi karatu a wajene da tuni kinganta tadawo gidanki da zama don nan tayi zabin zata zauna dama

Suna cikin wayar saiga Khaleesat tashigo aguje tana kiran "Momy!Momy na dawo kina ina...

Tadafe cinyar ZEENATU tana fadin nadawo



Ba

shiri zeenatu tace mata " Khaleesat kada ki karyani mana



"Sorry Momy murna nakeyi Abbana yabarni a FCE



Dariya G.ZEENATU tayi tace " to natayaki murna ga Auntyn ki awaya kugaisa



Khaleesat ta karbi wayar ahannun momynta da doki takanga akunnenta tafara da s

allama da gaisar da ita



Aliya ta amsa tareda tayata murnar shiga high institutions da tayi domin fara karatu



Khaleesat tayi mata godiya sukai sallama



Bayan sungama waya da Aliyar sai Khaleesat tace da Momyn nata "Momy yunwa nakeji me zan samu akicin?



G.Ze

enatu tace mata " Khaleesat kenan kin manta yau ba ranar cin abinci na bace agun ki yau ranar MAMAH ce gobe kuma Ta Kakarki ko?



Khaleesat tace "Amma kuma ai da kin Dan Ajiyemin delicious din danaga kinyuwa Abbana dazu yawuna fa yatsinke Momy



Dariya tayi ma

ta sosai tace " aina gaya mk indai kina so inringa sammiki duk wani abin kwadayi na snacks to tabbas saidai ki ajiye lalaci da son jiki kiringa zuwa kina tayani domin ki koya inko ba haka ba kya ringa jin kamshi



Khaleesat tahau shagwaba tana buga kafa akas

a



"Haba Momy nifa Autace wai meyasa kikemin rowar abincinki me dadi ne?bakuma kya Jana ajikin ki walh banajin dadi plz in wani laifin nayi

mk kiyi hkr kicanzamin plz karasa fada tana hada hannu alamun ban hkr idonta yaciko da kwalla

Murmushi tayi mata ta

ce " Khaleesat ina sonki ke "Yar fari ce baikama in ringa nuna tsagwaron sonki akoina ba ina tare da surukaina zasuga rashin kunyata kuma ba Dan komai nake miki hakaba sai Dan kiyi hankalin kanki domin kada ki sangarce ki gagaremu nunawa yara tsagwaron so

yakan bada gudummawar tabarbarewar tarbiyyar yaro nagani da idona kuma abin bai karge musu da dadiba Dan haka kada ki fassara yimiki hakan da wata manufa



Sai zancen girki inaso ki koya kima fini iyawa Khaleesat domin girki shine diya mace ayanzu HK mahai

finki baya taba cin abincin kowa awaje kai koda na iyayansa matane baya iyaci sai nawa inkinga yai looz na girkina to tabbatar baya kasar



Khaleesat tahau gyada kanta tana murmushi tace " kumafa hakane Momy na gamsu nima kuma inaso afara koyamin latest din

foods



Tace mata "to kifara karatun naki tukunna inyaso saimu fara a nitse muma saimu ware rana muringayi nima ai zanso inga kin kware akomai kafin a Aurar dake



Wata zabura tayi ta hade rai tafara shagwabar tata tace " wa za,a Aurar?tab ta zobaro baki tac

i gaba da cewa "walh ina tare daku bazanyi Aure ba nikam



Gimbiya Zeenatu ta zaro idanu tace " ke!adalilin me zakice haka ?kada inkaraji kin fada



Khaleesat tace "to Momy ainaga babu Wanda nake so ne shikuma Aure saikana so ana sonka zakayishi



G.Zeenatu t

ayi dry tace " Zaki samu insha Allahu.



Khaleesat ta mike tsaye ta nufi kicin tana fadin "nikam dai bari naje kwadayi tukunyar Momy na



Da kallo tabita tana murmusawa lallai taga alamar saitayi da gaske akan Khaleesat..…



Muje zuwa akwai wata cakwakiyar fa fa

ns film bai kareba

Auntyn Sayyada Da Shahidah ce

*NABILA ALIYU T/WADA* NAKE _AMINCI RADIO_*GIMBIYA ZEENATU*

Khaleesat Yarinya kyakkyawa tanada hankali da nutsuwa gata da aji tanada yanga gata Yar kwalisat tanada magana batada shiru shiru tanada dan sa

urin mgn harma hakan kesa wasu suna ganin tanada tsiwa

Yanda kakanninta keji da ita ko iyayanta basa nuna mata tsagwaron SO ta taso da kaifin basira idan tana turanci saika zaci ko a turai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login