Showing 18001 words to 21000 words out of 57925 words

Chapter 7 - kuyanga complete

bai yi maganaba

UMMAH Ranta yabaci sosai da jin sannan hukunci

Take Sarki yasallami kowa aka watse

Kwana biyu da faruwar hakan YARIMA yabar gidan batareda Sanin kowaba ckn da

re yagudu ko UMMAH bata saniba



Yahada kayansa yasilale cikin dare yatafi inda yafito



Da labarin yashiga ckn gidan ba karamin tashin hankali mahaifiyarsa tashiga ba Don hartahau zargin waiko Asiri akai masa dahar yabar gida



Abu kamar da wasa saida yakwana hudu labari ya isa fada



Tabbas Sarki ya guntsi bakin ciki awannan ranar yasan Yarima yanason yakun yatashine kawai tun aranar yakara tabbatarwa kansa cewar Yarima bai cancanci yaxama sarki ba



Tuni aka hadu kowa da kowa af

adar Sarki domin shi yakira taron



Inda yabayyana musu bakin cikin dayake ciki



Yace da *KUYANGA* dafarko inaso kizama me daukar kaddararki haka Allah yatsara miki naso inga yarima ya aureki domin Asirinki yarufu kedashi dinma

To gashi Allah baiba yanunan

ban isaba yawatsan kasa a ido yagudu yabar kasar



Dan haka inaso kikwantar da hankalinki da zarar kinhaihu zan karbi abinda kika Haifa hannu bibbiyu nayi miki Alqawarin baxaku wulakantaba ke dashi Dan haka wanene kike so ackn gidananna fadawa ko ckn BAY

I xan muku Aure domin inwanke miki zuciya

*KUYANGA* tayi shiru kanta nakasa



Ayayinda MAHBUB dake ckn mutane nesa da ita yadago dakanta yana kallonta gashi dai har ynzu yana sonta to amma wani Abu ma sukar ransa inya tuna ta yaudareshi duk da azaman fa

rko da akayi babushi ankawo masa Rahoton

cewa Ba da saninta komai yawakamaba Yarimane ya cuceta



Yana so yafurta kalma abakinsa ya gagara jiyayi mai martaba yayi masa kwarjini bakinsa yayi masa nauyi



Yaso yafurta shine maaoyinta na asali na gaskiya da akai

musu kutse arayuwa aka rushe musu farin ciki



Allah cikin ikonsa MAHBUB saiya kasa magana Allah yanufi LAMIDO Da maganar data furgita kowa harni

Hannu LAMIDON ya daga yana fadin "Ranka ya Dade ka Amince min Na Aureta domin inraya sunnar manzan Allah nak

uma shiryi taimaka mata kota halin kaka domin naji zuciyata ta kwanta da ita....

Kallon kallo UMMAH suka hauyi da Jakadiya hakama MAMAH takalli FAATU yayinda FAATUN takalli Mai martaba domin jiran Abinda zai yanke akai....

To muma fans da writers sai mubi

layi afada domin jiran tacewar Sarki Abdallah

AFIRGICE *KUYANGA* ta dago dakanta takai kallonta ga LAMIDO daya furta wannan kalami wanda azatonto ko karya kunnenta yajiye mata saitaga da gasken ne jin Abinda Mai martaba yace

"LAMIDO da gaske zaka Aureta

? Har zuciyarka ka Amince?

LAMIDO da fuskarsa ke cike da Murmushi da Annuri yace"Na Amince har ckn raina babu wasa ko yaudara zan Auri *KUYANGA ZEENATU* ko domin inga asirin gidannam bai buduba kuma don itama inrufa mata Asirin Amma inhar kaida mahaifiyata

kun Amince

Mai martaba yayi murmushi yace "Nidai na amince nakuma yi farin ciki kafitarni kunya domin banzamo me kyamatar talaka ba ko bawa na duk daya muke mu dasu gun ubangiji Saidai ko mahaifiyarka xamuso muji ta bakinta domin bata hakkinta.

FAATU tayi

murmushi tace "Tunda har ka amince TAKAWA ainima dole in amince akullum Allah nakewa

Godiya akan yanda mukai dace da samun D'a nagari wanda akullum burinsa shine yaga ya kyautata mana ya kuma bi sahun masu bin tafarkin ubangiji burinsa akullum yasami lada

arayuwarsa kaga dole muzamo masu bashi goyon baya Allah yasa hakan yazamo Alkairi arayuwarsa

*"AMINNNN*"Kaf Al,ummar gurin suka furta banda mutum biyu



MAHBUB da xcyrsa ta cika da kishi



Da kuma UMMAH da hakan bai mata dadiba

Mai martaba yadubi

*KUYANGA* yace mata "Dazarar kin haihu za,a daura muku Aure da LAMIDO kigodewa Allah sannan duk abinda kika haifa mace ko namiji zamu karba da hannu bibbiyu Zansoshi kamar yadda nake son iyalaina tunda jinina ne za.a bashi kulawa sosai bakuma nafatan yatas

o cikin tsangwama ko bayan raina dan hakan ki Kizama me mika lamuranki ga Allah

*KUYANGA* Ta ckn ladabi ta Amsa tana godiya

Sarki yadubi LAMIDO yace "Asakamakon Wannan farantawar da kaimin ina me yi maka Albishir da cewa kaine zaka haye kan karagar Sarau

ta idan nayi murabus nan ba da dadewa ba Halayanka sunnuna kaine zaka iya rike masarautar nan ko bayan raina kacancnta babu haufi kaine adalin Mutumin da akullum ake nunamin amafarki wanda zai zamo sarkin garinnan Kadauko halayen kwarai na iyaye da kakanni

nmu kwarai ina godiya da Allah daya bani kai amatsayin D'a

Yadubi Tarin jama.ar da suka cika fadar maza da mata na gidan yaci gaba dacewa "Inaso kusheda daga yau LAMIDO Shine wanda zaizama jagoranku nan bada dadewa ba LAMIDO shine xai xama sarkin gobe da

yardar Allah.Take Gurin yahautsine da sowa da murna fadawa Suka hau Kabbara

Bayi mata tsoffin da manyan suka gau guda



Yayinda MAMAH ta rafka guda tareda cewa sarki "TAKAWA Allah

Yaja da ranka muna taya LAMIDO murna kuma muna tayashi yin Godiya da wannan ky

auta



Maimartaba yagyada kai yana murmushi



Dayake anyi tsit ana sauraren maganr MAMAH

Saijin kukan UMMAH Akayi ta dora hannu aka tana fadin "Shikenan burinku yacika kun raba D'ana da gidan ubansa kunyi kutunguilar da D'anku zai zama sarki kuma walh baku is

aba



Sarki yadaka mata tsawa

Amaimakon tayi shiru saita mike tana fadin "walh baza,a dakeni ahanani kukaba. Tafuce fuuu tana kukan bakin ciki

LAMIDON da kansa yanuna godiyarsa ga sarki



Maimartaba yahau shafa kan LAMIDON yana fadin "Kacancnci hakan LAMIDO

fatana harkullum Abinda kayi min na Farantawa to ubangiji Allah yafaranta maka kaima

LAMIDO ya amsa da "Amin, Aminn Saida Sarki yabada umarnin tafiya sannan kowa yatashi yayi nasa guri



Jakadiya har sashin FAATU tabisu tana Rangada guda



Tareda fara yi mas

a kirari na sarakai

Saida tafaranta musu rai



Da kalamanta garesu masu dadin saurare sannan tafuta



Jakadiya

Tana barin Bangaren FAATU ta wuce sashin UMMAH Domin tayata Jimami da Alhini tunda tafi kowa sanin yanda UMMAH take da burin taga Yariman

yazamo sarki



Ta tarar UMMAH tana waya da Yarima tana bashi labarin komai daya faru sannan Tabashi ixinin akan yadawo Gida maza maza akwai abinda take shirya masa akai



Yarima ya amsa da to zaidawo nanda kwana uku ko

Biyu



Kai UMMAH ta hada da guiwa tareda d

ayin shiru na minti Talatin



Jakadiya na gefe taa jiran tafara kawo gulma da soki burutsin karya Data saba donta sami fada agun Fulanin



UMMAH tadago takalleta tace mata

"Jakadiya jeki kya dawo anjima ayanzu baxan iya maganaba ina ckn wani hali banda loka

cin zanta wata magana kibari nahutawa bakin cikin dana dauko afada

Sum sum jakadiya ta tashi tafuce guiwa asage

Itako *KUYANGA* Kwana tayi ba ci basha Sai dakyar Akwana na biyu da Yin abun sannan Zulaihat data matsa mata taci abinci kadan duk tasaka da

muwa ackn ranta

Zulaihat tace mata "walh kigodewa Allah ma ayanzu ji nake dama nice ke kuma nasan bani kadai ke wannan tunanin ackn bayin gidan nanba domin kin xama "yar baiwa tunda gashi Allah yakusa "yantaki

Zaki zamo matar sarki Surukar Sarki.……

"Uwar

Shege ko Shegiya kuma ba.



Cewar Zeenatun tana matsar kwallah



Zulaihat tace "kibar fadin hakan domin inma shegene ko shegiya duk kafin yafito duniya ne ko tafito duniya domin Kinji ta bakin Sarki yakarba kuma za,a bashi kulawa zai zamo tamkar d'a ko "ya me

"yanci to balle LAMIDO natare dake kinyi matsayin da bakowacce zata iya takashiba ackn mu *KUYANGIN* Gidan kema kinsan hakan

Zeenatu tace "hhhmmm ke kike ta wannan tunanin ni tunani na yatafi ga masoyina MAHBUN tausayinsa nakeji yanzu shikenan ……

Zulaihat

ta daga mata hannu "saurara niarki dameni da xancensa domin banga yayi hobbasa yanuna soyayyar da yake mikiba agun dan da,a ce sonda yake miki har zucine da kafin LAMIDO yace wani abu akai tuni shizaice

Dan Allah kicireshi aranki tunda yanzu bake kadai ba

ce ba,bafa ason me ciki da shiga damuwa balle kuma abinda zaki haifa me matsayine agidan



Zeeatu tace "Zulaihat da alama bakisan radadin soyayya a zuciba Ni LAMIDO baya

gabana Mulkin gidannan baya gabana ko arzikinsu kawai Matsayina nake tunawa ayanzu



Zulai

hat tace "ke nifa Allah nagodewa da bai nufi MAHBUB da magana akan kiba agun natabbata da tuni LAMIDO baice komai b.……

Sallamar Wata yar matashiyar yarinya ce cikin bayi tashigo dakin nasu takatseta tashigo musu da ladabi tagaidasu

Zulaihat tace

"Laminde ya akai akwai wani abune?

Laminde tace "Ustaz ne yace Zeenatu taje yana waje.



Da sauri Zeenatun tace mata "kije maza kice masa ina zuwa

Ta xira hijab tabi bayan Laminde data futa da mintina uku

Yau ya canxa gurin tsayuwa can gefen hanya yaja tung

a yatsaya yana jiranta



Tun daga nesa yakura mata idanu yana kallonta tayi haske fuskarta taxamo yar kuyas tayi kyau saidaita rame



Takasara gareshi da sallama tagaidashi

Ya amsa yana kallon yana fadin "ZEENAH ina sonki amma dole inbarki, yanzu kinmin nisa k

infi karfina.……takatseshi dacewa "kadaina fadin haka komai nufin Allah ne matar mutum kabarinsa saikaga muna tamune Allah na nasa zai iya kuma canza lamarin aduk sanda yaso bamu zataba kaifa malamine kasan hakan kazama me tawakkali mana kana fa da Sani..

..

Yace "Duk na susuce Zeenatu ayanxune akwanakin nan biyu da faruwar lamarin naji kaunarki ta karu araina tamkar ana kara rura wutarta ma



Kokinsan YARIMA yadawo Gida adaren jiya labarin yakarade gidan nan. Sarki ko kallonsa baiyiba haryanzu yayi fushi das

hi kuma duk akan ne "yar baiwa



Duk da gabanta yafadi jin ya ambaci sunan yarima sai bata nunaba a fuska ta dake tareda kawar da maganar ma tace masa



"Ko awane hali nake bazan manta dakaiba bakuma zan daina son kaba kaine kadai wanda naso a afarko da ka

rshe ackn Duniyar nan ……

Adaidai lokacin da *KUYANGA* Ke furtawa MAHBUB wannan daddad'an kalma ar daidai lokacinne Allah yakawo yarima yazo xai girfta ta gun yahangosu yabiyo ta jikin katangar da suke tsaye kunnansa yadebo masa wannan kalami da muryarta ya

watso akunnansa

Yaja da sauri yatsaya baya so su ganshi domin dan ita kawai yabiyo ta gurin



Rintse idanunsa yayi wani abu yaji yana masa yawo akirjinsa

Tabbas yau yakara aminta da zargin dayake mata na soyayya da MAHBUB duk da ta taba tabbatar masa amma

kalaminta na yau yakara bashi haske



Ya dafe kansa domin Wani hali yashiga Akanta yadawo adalilinta tun daya hada kayansa yabr kasr yakoma turai yakas sakat Allah yajarabceahi da azababbiyar kaunarta dayaji batun da mahaifiyarsa ta gaya masa na LAMIDO z

ai Aureta bakaramin tashin hankali yashiga ba domin yasan shirinsa yagama baci

Nemanta yakeyi ido arufe ruwa ajallo Donsu keb'e yanuna mata nadamarsa ya amshi cikin nasa domin ta yarda dashi yakuma roki alfarmar tarakashi gun Sarki Ta tayashi neman yafiya

Yasan ita din me hkr ce da biyayya bazaisha wahalar taba



Waishin ma tawace hanyar zaisamu hakan? Anya bai makaro ba kuwa hhhhhh fans kufito ku gaya masa

😆😅😂🤣

A SANYAYE Yarima yajuya da baya don gara yakoma kada wani cikinsu yaganshi su rainashi

Yakoma sashen mahaifiyarsa ya tararta tana Safa da marwa atsakar dakinta tana buga hannunta daya cikin daya tana kwafa da alamar har yanzun ranta abace yake

tana

kuma ckn halin damuwaTana ganinsa tahau fadin "Ya Akai yarima kasame tane?

Yazauna akan kushin yana fadin "Bansami ganawa da itaba UMMAH natarta ne da wani Kazamin bawa da take so..,UMMAH Takatse shi da sauri

"Au dama ackn gidan nanma akwai wanda take so

yayya dashi ? Ashe haka tazama yarinyar to da alama ma cikin agida tayishi kenan

Yarima yadago da sauri yadubi mahaifiyarsa da jajayen ido yace "A,a UMMAH tunjiya Dana dawo nagaya miki cewar Wannan cikin fa nawa ne kada ki kakabawa wani makaskanci mana j

ini na karba.... " Dakata!



Ta dakatar dashi da daga murya ranta abace



"Wai bazaka daina kiran cikin jikin *KUYANGA* da sunan mallakin kaba,walh inkai ka karba to ni ban karb'aba domin bazan yarda da shege ace shine jikanaba jikanma ajikin baiwa Allah yaki

yaye dama ajikin wata baturiyar ne ko " yar sarauta da sauki



Yarima yace " Amma ai u UMMAH shi .mahaifin



yakarba ballantana ke da kike mace kikafi sona.



Tace "Dan babanka yakarba be dameniba domin yakarbane da wata manufa aransa tunda bayason azageshi

bakuma yaso Dan daza,a haifa yatashi yarasa madafa amma nasan ba har zuci yakarba

" kidaina fadar haka UMMAH.

"Saina fada din kaida bakasan inda yake mk ciwo ba baka



ma damu da kyautar kujerar sarauta da Aka baiwa LAMIDO ba



Yarima yace "Ni wannan kam b

aya gabana fatana dai ayanzu *KUYANGA* zeenatu ta Amince da abinda nazo dashi sbd Allah yajabceni da kaunarta UMMAH kitaimaka kiyi wani Abun walh sonta nakeyi sosai har cikin raina

UMMAH ta maka masa wata harara tace "Shima LAMIDOn daya Amsa yana so

nta zai Auretan nasan badan Allah yayiba a to.



Yarima ya shiga tunani

Kai Yadafe don kan nasa ke bugawa dolene yasamo mafita akan MAHBUB Domin irin kalamin dayaji tana watsa masa na soyayya tabbas su yake muradin yaji wataran tagaya masa



Toshin ta wace

hanyar? Ta Yaya?

Yakasa samo amsar tambayar domin kansa yakulle Dole saiya nutsu

UMMAH bacin ran abinda Yarima yaxo mata dashi baisa tasami nutsuwa ckn rantaba tabbas dolene tasami mafita akai rana zafi inuwa quna knn domin wannan shine ana wata ga wata

can Hukuncin da sarki ya yanke nabaiwa LAMIDO sarauta nacinta arai saigashi Yarima yazo mata da wani batu wai yana son *KUYANGA* to tawace hanyar ma zaisameta Alhalin LAMIDO yakarba kowa yashaida hakan lokaci kawai ake jira



Yarima yadago dakansa yaga ma

haifiyarsa ta hada kai da guiwa

.yasauko kasa Yakama kafafunta yana fadin



"UMMAH kitaimaka mini kije ga mai martaba kinemamin yafiya sannan kifada masa batuna na karbar cikin *KUYANGA* da zanyi kice nayi nadama sharrin shaidanne inasonta yadaina

fushi dani



Wani dunqulelen abune yatsayewa UMMAH a maqoshi na takaici da bakin ciki



Taki jinin jin Kalmar nan dayake furtawa na son *KUYANGA* dayake fada mata yanayi domin ita ji takeyi tana kara tsanarta ma tunda itace tazamo silar rushewar Burinta ayau,

tayi nadamar amincewa da tayi tun farko daya yatafi da ita kasar waje tasan da bata yarda sun tafin ba da tuni hakan bata faruba tunda gashi akan Yariman yak'ita yaki cikin ne LAMIDO yashirya manaqisa yakarba don abashi sarauta kuma anbashin kamar yadd

a sukeso kuma bazata

taba bari suji Dadin yin mulkinba indai daranta saita zame musu masifa a ckn gidan



Wannan tunanin tane

UMMAH dai taga Yarima da Gaske yakeyi domin shirin kuka yake mata akan bukatarsa



Dabara ce tafado mata tace masa "kwantar da han

kalinka shalele zansan abinyi agun Takawa



Yace " to agun ZEENATUN fa?



Tahade rai

Yamarairaice mata Taga dai da Gaske ne lamarin nasa saitahau tunanin anya kuwa ba Wani abun akaiwa D'an nataba mutumin dayaqi Abu futuk kuma cikin "yan kwanaki saiya haukace

akai



Lamarin Allah nefa UMMAH

😃

Allah yakara inji fans



Takama hannayensa itama ckn marairaita tace masa "YARIMA kai D'ane D'an fari abin so aduk wani gidan sarauta baikamata ka lanjare a son BAIWA ba kafi karfin Auren *KUYANGA* ajinka da kimarka da izza

rka na Dan sarki zai ragu inhar ka Auri *KUYANGA* inaso kayi hakuri kabarta ni dakaina zansamo maka ko ackn gidan sarautar mune akwai mata masu kyau adangina mahaifina kafin ya mutu yayi sarki yanzu babban yayana shine sarkin garinmu kasan da haka Babbar

masarautace datafi wannan munada mata kyawawa yan boko wayayyu sai wacce kazaba babu me kinka walh kanada cikar da namiji kaidin gwarzone me tattare da mazan taka gaka kyakkyawa kafi LAMIDO kyau da kwarjini Meye naka na damuwa da Baiwa Alhalin kafi karfi

nta shi din dayace abashi ita ya Aura kabarsu dama da ita yadace

Yarima yakyabe fuska yace " UMMAH bazaki ganebane



Tace "tayakuwa zangane kaki amsar batuna



Dayaga da Gaske takeyi baxata sakkoba saiya rushe mata da kuka yasan lagontane bata son damuwarsa

balle ganin hawayensa



Nan take kuwa ta rude tace masa yayi shiru zata duba lamarin yaje zuwa gobe kafin tasan abiny

i

Yana

Fita ta aika aka nemo mata jakadiya



Jakadiya na zuwa tagurfana gabanta

" gaisuwa nakeyi Uwar dakina barka da warhaka gani ckn

ladabi mezan miki ?nasan bukatace babba tasa kk kirani



UMMAH tagyada kai tace "tabbas kuwa jakadiya domin Yarima yaxo min da banzan zance wai yanzu shi *KUYANGA* yakeso kuma ya amince da cikin jikinta nasane



Jakadiya tadafe kirji tace " wannan Abu bai Da

din jiba kamar Wanda akai masa surkulle



UMMAH TACE "Maza kije kishirya kije min gurin GOGAL matsafiya kice inaso acire masa son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login