Showing 12001 words to 15000 words out of 57925 words

Chapter 5 - kuyanga complete

gadi inja masa kunne akan kada yagaya masa



Tayi ajiyar zcy tareda kakaro murmushi tace

"To saika dawo.



Yasa kai yafice



Kai tsaye Gidan Abinci ya wuce yasiyo mata me tsadar gaske



Kana

yashiga pharmacy yasiya mata magunguna hardana ciwon jiki dana zazzabi da ciwon kan



Sannan yawuce gidan Yarima yai sa,ar kuwa Baidawoba



Yakebe da Me gadin yabayyana masa komai tareda bashi kudi cinhanci



Me gadin musulmine dan kasar cameroon ne yanajin haus

a sosai



Yahau gyada kai yace "bazan fadaba insha Allahu domin natausaya mata yarinyar tanada kirki tun zuwanta nadaina zama da yunwa wannan Yaro bashida kirki sam, baya ganin karama ce Amma dai kaima kayi taimako Allah yabiyaka.



SAHABI yaji dadi yayi murmu

shi yace "Amin ngd.suka karayin musabiha yatafi

******

Abangare guda da YARIMA ANwar yadawo gidan bai neme inda takeba ko kusa ko alama domin cikin fushi yake da ita



Kwana yayi yana tuna yanda takasance atsakaninsu domin ta bashi haushi sosai wato don yana

jin dadi ajikinta shine tasami hanyar rainashi har tana iya musanta masa da sa,insa dashi lallai dolene yayi maganinta domin bazai zauna da *KUYANGAR* Da bata ganin darajar saba zai gyara mata zama



Abu daya yake masa yawo akwanyarsa Baiwarta da YANDA take

wajen ni,ima tabbas awannan fage yasan ta ciri tuta ba karya yarinyar tacika mace baitabajin macen daya kusanta yajita zam -zam kamar taba



Aikoda zaiyi fushi da ita na lokaci kalilan ne bazai iya rabuwa da

itaba tunda ya dan daneta yaji wani abu aransa ak

anta yazaune masa kamar super glu aransa



Yakwana yana tuno Dadin dayaji ajikin *KUYANGA*

Da Gari yawaye sai yashirya zaifuta gidan wani abokinsa zasu je wani shoping har ya futa kuma yai tunanin yacancanta yaganota tunda baiji motsin taba ko batada

lafiya



Yana kuma son dai yaganta domin shap dinta na burgeshi da cikar kirjinta

Yana shiga abin mamaki baiganta ba baikuma ji motsinta a toilet ba har lekawa yayi



Saiyaja yatsaya a tsakiyar dakin yana tambayar kansa "to shin ina wannan yarinyar taje ne?



Ya

i sauri yafuta yaleka kicin namma bata nan



Yazaga bayan gidan shine har lambu yagama zagayensa yana neme nemensa amma shiru ba bayaninta balle ma wata alamar ko tana gidan



Nan kuma jikinsa yafara sanyi kada dai guduwa tayi? Yatambayi kansa



Gabansa yafadi a

lokaci guda

Domin yasan inhar ta gudu ba iya kai kanta gida xatayiba tunda batada kudin jirgi balle wata hanya agarin da xata iya guduwa gida



Yatafi da saurinsa yatambayi me gadi yace masa shin ko yaga fitowar Zeenatun?

Me gadin yahau girgixa kai yana nuna

tu,ajjibinsa azahiri yana fadin "bangantaba tun jiya rabona da insata a ido



Yarima yace "azamanka nayau aget kamatsa na awa nawa ko minti nawa?

Me gadi yahau sosa keya yace

"Eh to dayake dai yau natashi da bacewar ciki inata shiga toilet shiyasa bana ce

ko sau nawa ma nabar get ba kuma nakan dade kafin nadawo.Yarima yadafe kai yace "Shikenan ta gudu! Nashiga uku.Me gadi yazabura yace "ta gudu? Zeenatun innalillahi wa innailaihirrajiun.

To yanzu ina za.aje aganta wata sani a kasar nan?

Yarima yahararesh

i yace "koma wata sani ko bata sanin ba ai kana da hannu aciki tunda kana wasa da aikinka baka

rufe gidan yadda yakamata.



Yajuya yabar Megadi da atsaye saroro

Aifa aranar yarima yarasa tsugum yanata Faman xaryar gun jami,an tsaron garin yana basu bayanin B

'atan *KUYANGA* waiko Allah zaisa aganta ahanya



Kwana biyu sukai suna checking akanta amma shiru dole yahakura yakira gida yana tambayar mahaifiyarsa



Koda UMMAH taji abinda yake faruwa daga bakinsa ta kidime tahau yi masa fada



"Yarima kodai akwai abinda ka

ke matane?ko takura mata kayi da ayyuka da fadanka?

Yarima yace "To UMMAH inma nayi mata fadan saita gudu? Banida ikon dazan matane?kawai dai yawon bude ido nakejin ta tafi tunda idonta yabude dama bakiga yanda take shigar kananan kayaba tana son tafuta ga

ri nahanata ashe dai xata shammaceni tagudu



Jin Hakan yasa UMMAH ta yarda tahau fada tana cewa "to ai da ba guduwa yakamata tayiba saita fada maka maza take bukata saika dawo da ita gida ayi mata Aure yanzu kaga hakan ai sharri zata jawo maka ace kai ka k

oreta ko cutarta kakeyi yasa ta gudu gani da mahassada ackn gida (kishiyoyi

)

Kuma dole kasan TAKAWA zaiyi fada amma kabarni dashi zansan mezan fada masa



Yarima yahau godiya yanajin dadi aransa

******

Akwana na ukunta agidan SAHABI bizarta ta samu itadashi

Suka kamo hanyar dawowa Nigeria



Dayake tasaki jikinta dashi tunda taga ba cutarta xaiyiba sai suketa hirarsu ajirgi tana ta masa godiya da nuna masa farin cikinta azahiri



Shikam bakomai yake ce mata ba sai "nikam bazan daina gaya miki ina sonkiba

kirike alkawari



Ta lumshe idanunta tabbas inda wanda zataso to abayan SAHABI yake amma ina yau data nufi kasarta ji take wata kaunar MAHBUB ta dawo mata sabuwa



Dayaga tashiga tunani saiyace mata

"Zeenatu kada fa kisawa kanki damuwa kicire komai aranki domi

n ni da Aure nake sonki kuma bazan ringa miki kallon abinda yarima yai miki ba kimance da komai yadda nima zanmanta da komai haka kuma kija bakinki kiyi tsit kada kifadawa kowa abinda yasa kika dawo ko abinda yarima ke miki kimarki zata ragu agun mutane sa

nnan za,aita yawo da maganar agidan.

Tagyada kanta tagamsu itanma ai zataso asirinta yarufu domin kada masoyinta yaji bazaiji dadiba sannan ga "yan uwanta KUYANGU abin xai iya zama abin surutu ayi mata wani kallo



Da dare suka diro kasar Nigeria bayan Ishsh

a'i



Har gidan sarki Abdallah yarima yadauki shatar mota aka kaisu amma shi bai bari anganshiba



Ita kadai aka sauke akodar gidan sarki aka tafi dashi zuwa hotel din dazai kama yakwana ingari yawaye ya wuce Daura garinsu



Kafin su rabu tun amota yabata waya

karama kirar Tecno domin yace yana son yaringa jin muryarta akoyaushe sannan in tanada Damuwa ta sanar masa zai mata maganin damuwar



Tabbas SAHABI yagama mata komai



Shigarta gidan tun daga kofa aka fara mamakin dawowarta tunda ansan da Ita da yarima suka

tafi kuma basuda labarin dawowar yariman



Kai tsaye bangarensu ta zarce bata bari kowa yagabta ba

Adakinsu mutum biyune basuyi bacci ba Zulaihat idonta biyu kawarta



Da zulaihat taganta kirji ta dafe tana fadin "wa nk gani kamar Zeenatu? Dama yau kuna tafe

amma banji sanarwar ackn gidan ba*KUYANGA* Tazauna tana fadin "wash !barni na huta tukunna zulaihat saiki watson tambayar

Zulaihat ta janyo jakar da Zeenatun tashigo da ita takaya tace "lallai kyan tafiya dawowa ina yariman ko batare kuka dawo ba?

"Idan ta

re muka dawo zaki ganmu atarene?Zulaihat Tahau murmushi tana fadin "inafa kawai dai tambayace

*KUYANGA* tace '"to batni nahuta tukunna sannan kibani labari akan MAHBUB dina.Zulaihat tayi dariya tace "MAHBUB dinki yananan qalau.

"To masha Allahu.

Gari na wa

yewa aka aiko kiran *KUYANGA* labari yakaiwa UMMAH anga Zeenatu ta dawo gdn da daddare



Saida UMMAH ta tabbatar da lallai Zeenatun ce tunda tazo da gaggawa kiran tadurkusa agabanta



UMMAH tace "Meya dawo dake Gida yarima baisaniba?



Gaban *KUYANGA* Yafadi tak

e dabara tazo mata



"Fita nayi don ganin gari shine na bace har wasu suka tsinceni suka tambayeni inda nake nikuma namanta inda zance musu bansan kwatancen mazaunin yarima shiyasa dasukace zasu dawo dani Nigeria ban musa musuba



UMMAH nagama ji tace "kodai y

awon iskanci kika tafi Allah yakamaki aka dawo dake gidan?.

Da sauri tahau girgixa kai tana hawaye tabudi baki tace "walh ba haka bane waccen maganar danayi ce gaskiya.



UMMAH Tace ta tashi tabata guri tayiwa kanta rayuwar jin dadi wasu ma nema suke

Tana fu

ta UMMAH takira Yarima tagaya masa komai

Yarima yasha mamakin dahar ta iya dawowa ita kadai yacewa UMMAN yana tunanin akwai wanda yataimaka mata ta gudo zaiyi bincikeUMMAH Tace "nidai kawai kadawo Yarima domin nafi son zamanka akusa da mahaifinka don inyan

a ganinka akusa dashi zaifi shakuwa dakai sannan Hakan ne zaisa sarauta ta dawo hannunka ta sauki tunda wancen Sahoramin yatafi Sudan karatu bazai dawo yanzuba

Yarima yace "Nima bana jin Zandawo Yanzun UMMAH saikamar nanda wata guda.Tace "To kayi kokarin k

adawo awata gudan kada ka kara fa.

Yace "angama UMMAH Na baxan karaba.



Sukai sallama



Saida Labari yakai kunnan sarki wai *KUYANGA*



Dasuka tafi Turai da Yarima ta gudo itakadai



Mamaki ya ishi sarki

domin baisan anyi tafiya da mace ba da bazai bariba

balle har ya yarda yabar yarima yatafi da mace



Aranar yasaka UMMAH agaba yace ban kanki in aske



Yaita mata fada harsaida tayi hawaye



Tana fadin "Ayi hkr Takawa ai anrigada anyi kure dahar aka tafi ba.a gaya makanba baza.a karaba



Ita kuwa *KUYANGA* tasake a

ckn "yan'uwanta Bayi bata nuna wata damuwa ba ko Wani abun



Haka suma basu gano komai ba saima yabon canxawarta dasuke tayi wai tayi kyau fatarta tayi kyau acan



Shiko MAHBUB kallonta yai tayi yana fara,a dajin dadi yana fadin '" kincanza dayawa Zeenah kinyi

matuqar kyau fatarki sai sheki takeyi lallai kin huta acan kinbarmu ckn aikin wahal



Inafa Hutu tambayemu kasha labarin komai tayi fari

🙄

tace kaima ka kara kyau anya kayi kewata kamar yadda nayi taka kuwa?



Yace "sosai kuwa ko nan gurin damuke xama

zaishedi hakan dafatan dai soyayyata batayi gibi ba tananan yanda nasanta da yawa?



Gibi kai

😉😄

Amma injini ita cewa tayi



"Saima karuwa tayi ai aduk inda nake dana tafi ina tare da sonka da kaunarka



Yace "naji dadi soaai.

Dayake wayar da yarima yabata Boy

eta tayi sam bazata bari MAHBUB yagani ba balle yayi mata fassara gara Zulaihat ta nuna mata amma tace kada tafada wa kowa



Zulaihat hartana tsokanart dacewa "Toko dai SAHABIN nan zaki Aurane komai kice SAHABI mudai kada kiyi mana sakiyar daba ruwa*KUYANG

A* tace "Banga abinda zaisa nabar MAHBUB ba kima bar wannan maganar SAHABI abokin shawara ne abokan taka ce atsakaninmu

Dariya kawai Zulaihat tayi tare dajan bakinta tayi gum

*****

Watan *KUYANGA* D'aya da dawowa yanayinta yacanxa domin wani laulayi tarin

gayi ga yawan Zazzabin dare Da ciwon Ciki da bacci da kasala da kwadayi da take yawan yi



Zulaihat itace tajikinta ita tasan matsalarta na rashin lfyr

saita samo mata magunguna taita bata na gargajiya tana jikawa tana bata tana sha



Kwana biyu tayi ak

wance MAHBUB yatada hankalinsa ganin ciwo yaki lafawa Kullum cikin Aikawa da Rubutu yake



Aranar data gama shanye jikon da Zulaihat tayi mata aranar tayita malelekuwa atsakar daki mararta na ciwo kamar ta mutu



Tana ihu tana kiran sunan Alla



Jini ne yaring

a xuba ajikinta ta kasanta me yawa



Zulaihat ta tsorata ainun

Da gudu tagayowa manyansu tsoffin Bayin gidan



Da sukazo kanta sukaga ikon Allah abin yafi karfinsu sai suka baxama cikin gidan gun matan Sarki aka gayo musu



Mamah ta tsakiya da Amaryar Sarki Faat

u mahaifiyar Lamido sune suka fara zuwa gunta kafin UMMAH Tazo

Likitansu na ckn gidan aka kira macece *DOCTOR HALIMA WASAI* da kayan aikinta tazo taxaci abin karamine



Saida tazo taganta tace musu ai bari zatayi da alamar cikine da ita maza atafi da ita

asibiti don inya bare ayo mata wankin cikin

Hankalin kowa na gidan yatashi ba,a bari sarki yajiba

UMMAH taringa fadin "shegiyar yarinya Me sifar munafukai ashe abinda tayo akasar ta gudo kenan lallai asirinki yatonu Yarima bashida Alhaki shiyasa baima sani

ba ta munafurceshi.

MAMAH tace "ai irin wannan ba,a aibunta mutum kuma bamu tabbatar ba likitanma zato takeyi dan haka muyi mata fatan Alkairi tunda D'a nakowane



UMMAH ta harari MAMAH dama haushinta takeji ganin ta rungumi FAATU sunhade mata kai



UMMAH ta

watsowa MAMAH magana me zafi dan taji haushi tace "TO IN D'A NAKOWANE WANI MA YAYI D'AN MANA NAZACI TUN ZUWANKI GIDANNAN KATON KASHI KAWAI KIKEYI KOKIN TABA YIN BARIN MA?

MAMAH jarumar mace me tawakkali tayi murmushi tace "Bantabayi ba Amma nagodewa Allah

yabani Taqwa da Sanin yakamta kuma ina dada gode masa nasn kuma bai manta daniba, na tabbatar kuma inhar yabani agaba inda yawan rai xanfiki iya yiwa yara tarbiyya....FAATU ce taja hannun MAMAH tana fadin "kibar maganar haka kiyi shiru ga mutane fa bayinku

agun baikamata ba.

MAMAH da FAATU suka bar gurin

Ita UMMAH Data gwaba me zafi aka mayar mata tafi MAMAHn jin xafin maganar ma



Yawwa ai gara hakan dama inbaki yafadi son rai aibaisan me za,a mayar masa ba.

*Muje zuwa dai Auntyn Sayyadah da Shahidah*

AC

AN Asibiti Likitoci sunata iya bakin kokarinsu domin Suga jinin dake zuba daga jikinta yatsaya don tafuta ahayyacinta



Saida Allah yataimaka jinin yatsaya kana sukai mata allurar bacci sannan aka nemi "yan uwanta domin suzo adebi jininsu akara mata

m

Likitoc

in kansu sunyi zaton cikin dake jikinta yazube to ajiyar Allah baifita ba sai wuya datasha

i

ya Yabi wata tsohuwa cikin wadanda suka kawota tace musu su taimaka su karasa fitar da cikin ba Aurene da itaba Abin kunya taja musuDr Halima tace mata

"Gaskiya bam

a zubda ciki domin inmunyi hakan tamkar munyiwa ubangiji shishshigine domin bamusan nufinsa dayasa tasamu cikin ba alokacin da bai dace tasamu ba

Iya tace "Amma dai da kuntaimaka sbd idan labarin yaje kunnan sarki baxataji ta dadiba dan korarta ma zaiyi ag

idan kuma gashi bamusan cikin wayeba gata marainiy



Dr halima tace "koma dai meye ne iya saidai kuyi hkr mufa bama Abotion a asibitinnan sannan kusani wannan ciki bame futa bane inhar kuma kukayi kokarin yi masa dole to

tabbas zaku iya rasa ranta

awajen zubarwa



Iya Yabi ta tsorata matuqa gaya jiki na rawa tace "to abar maganar Allah yabata lfy yarufa Asiri



Acan gida Da labarin neman jini yazowa kowa sai akaita nokewa MAHBUB kuwa da rawar jiki yanufi asibitin sbd yabada jininsa ga masoyiyarsa

Shi a

tunaninsa ko wata lalaurar ce tadaban take wahalar da ita

*********

Dayake aranar LAMIDO yadawo yanufi daga SUDAN yagama karatunsa wanda yayi na shekara 5

Rangadi suka futa shida maimartaba domin Sarki yana son LAMIDO kwarai. can bayan gari yajashi wai

suyi hirar yaushe gamo anitse kada atakura musu

LAMIDO yaji dadin wannan zaman da mahaifin nasa domin sunsa hira tun da sukazo wajen sha daya nasafe sai yamma suka fara haramar komawa gida dayake dirar sassafe yayi Nigeriyar



Jakadiya tana gaban UMMAH tana fadin "Ranki yadade naje cikin azama fada domi

n insanarwa sarki labarin irin abin kunyar da *KUYANGA* ta hada mana ayau sainatarar bayanan natambayi Dogari wai yafuta shida LAMIDO dakuma fadawa Rangadi



Lallai nayarda Sarki yana son LAMIDO domin namanta rabon dana ganshi yafuta ran gadi balle bai tab

a zuwa da YARIMA ba anya kuwa ranki yadade ba asiri Matar can tayiwa Sarki da Yarima ba kuwa?

UMMAH ta hau gyada kai ckn takaici tana fadin "Ai walh jakadiya matar can burinta ackn gidan nan baxai taba cikaba domin D'ana shine sarkin gobe da yardar Allah

kuma Duk me binsa Da sharri sai nayi maganinsa muxuba mugani



Har dare da Sarki yadawo shida LAMIDO labari baije kunnan saba



Sai da Sassafe Jakadiya ta bazama taje takai gaisuwa tagurfana agabansa don takware a munafurci da gulma



Saida tagama banbadan cin

ta dayi

masa kirari kana ta zayyano masa komai duk abinda tasani daya faru



Sarki yayi Shiru kirjinsa na dukan uku uku dan fargaba



Yanzu cikin KUYANGUNsa akaiwa 1 ciki?me hankalin ciki da yasanta farin sani sbd yawan Ayyukanta ackn gidanba da ladabinta



Yada

fe kai yai tsahon minti biyar ahakan kana yadago ya kalli jakadiya yace



"maza kije ki kira min matan gidannan su ukun



Su UMMAH Da FAATU Da MAMAH yake nufi



Dakin fulani tafara isa tagaya mata kana tawuce dakin MAMAH

Bayan tasanarta kiran sarki saita wu

ce Dakin FAATU Tana shiga ta tararta da LAMIDO Suna hira tadurkusa takai gaisuwarta garesu kana ta isar da sako tafuta



Koda suka hadu gaban Sarki UMMAH tafisu faduwar gaba sbd tasan kaf dinsu itace me laifi tunda itace silar samuwar cikin *KUYANGA* dan dab

ata turata kasar wajeba da yarimanba da batasa samuba

Bayan Shiru na wasu mintina Sarki yayi gyaran murya kana yakallesu d'aya bayan d'aya yace "Kunada masaniyar Abinda yake faruwa agidannan

?

Suka hau gyada kai



Yace "to ya akai har hakan tafaru ?ya akai *K

UYANGA* Tasami ciki a ina akai hakan meyasa kukai wannan saken...?



MAMAH ta budi baki ahankali ckn ladabi tace "Ranka yadade Takawa banida laifi ciki



FATUU ma tace "Nima dai banida laifi…



UMMAH ckn jin haushinsu tace "to tunda bakuda laifi ciki saiku gaya

masa me laifin naga alamar dai so kuke kununa masa karara nice da laifi ack



Mai martaba yadaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login