Showing 27001 words to 30000 words out of 57925 words
ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy
Yace "Amin
Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO
tace "To.
Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta
Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira
Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata
FAATU ta amsa ta
reda zama kusada MAMAH
Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi
Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto
UMMAH taga shigowar Jakadi
ya hankali atashe
Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji
Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi
Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zans
o ace Yarima ne zaizama sarkinmu
UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE
Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH
Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa ara
nsa akwai abinda yake
ayyanawa akansu
Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona
Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka
Yace "Hhhmmm adane kike son
a amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani
Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daid
ai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance
Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu n
a Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO
Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai
Waye ya kawo miki wannan labarin?
Tace "JAK
ADIYA CE
yace "shikenan.
Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take
Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa
Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta
hakan
Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan !
Jiki na tsuma ta karba
Tace "na menene wannan?
Yace "Nakine aiki zansaki
Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina
Yace "Yanda kika zama makisiya shine nake
so ki kashemin wani nima
Ta zabura "Baxan iya ba walh
Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye?
Tace "waxan kashe?
Kaitsaye yace mata "LAMIDO!!
taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe
LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba
Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki
Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wanna
n lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!!
Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami
Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin
******
Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'
ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA*
Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan
Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa
Itako dama
ranta baiso ba
Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar yariman ta tafi
Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin
Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadas
hi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na mintina a Airport
Hindu "Yar Minister ce
a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo
"Yar boko ce
gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan asalin saba tashi guda
Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima tar
inga kanainaya da kissa don yasota takuma yi sa,a
Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi
Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta
Saida s
uka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ?Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan
Takuma gaya masa asalinta da matsayin data taka na aiki domin tana aiki da Ministry of Health itace Director
asashen kula da Asibitocin Shiyyar Su
Ya jinjina kai yace " Ina sonki zaki Aureni?
Da zakuwa tace "Kwarai kuwa inhar da Gaske kake na amince maka amma kada ka yaudareni bani da dadi
Yayi dariya yace " nima ba Dadin gareniba.
Tayi dariya kawai
Aranar ta t
ayashi kwana agidan sunyi romance amma basu zarta nan ba don ya ayyana aransa ita zai aura takwanta masa
Aranar sun tsaida magana zaizo nanda sati biyu Kaduna yagaida iyayanta zai kuma tura magabatansa
Tunda suka tsaida magana da Hindu shikenan soyayya ta
dinke atsakaninsu akullum suna tare awaya ba dare ba rana Shaquwa sukai sosai in basuji muryar juna ba basajin dadi
Tana daga Kaduna amma kowa nata yasan da Fara soyayyarta da yarima
Iyayanta harsun San da sunansa domin ta gaya musu tuni
Dama ita kada
i suka Haifa itace shalele sunaji da ita basa son bacin ranta
Yarima yakasa sakat tuni yahado kayansa sai Nigeria
Amaimakon yadiro Kano saiya zarce Kaduna
Kai
tsaye yabi kwatancen d tayi masa
Ta aika da mota aka daukoshi aka kaishi gidan
Yaji Dadin tar
bar da tayi masa da yan gidan
Yai mamakin ganin shankwamen gidansu kamar gidan Gwamna ga tarin motoci kamar ana saidasu
Akaita kawo masa gaisuwa ma,aikatan gidan aka cika gabansa da kayan ciye ciye A main falour aka saukeshi
Mahaifiyarta taje taku
ma yaba da zabin diyar tata
Saida yajira mahaifinta Alh baffanyo yadawo suka gaisa ckn mutunci
Dayake mutumne wayyaye tuni yace yabashi ita yakuma bashi sati yaturo magabatansa
Yarima yai na,am
Sunyi soyayya kafin yatafi da yamma yai mata sallama yabi
jirgi yataho Kano
Yaringajin kamar karsu rabu tamkar Wanda tayi masa asiri yaringaji
Ransa Dari qal yasami Matar Aure yasan yanzu dole maimartaba zai sauko inyaji zaiyi Aure
Da Isar yarima gida kai tsaye gun mahaifiyarsa ya nufa
Tayi mamakin zuwansa bai
sanar mata ba
Yana murmushi yace "UMMAH dawowar gaggawace tasameni adalilin Matar Aure dana gamu da ita
UMMAH da mamaki tace " Matar Aure kuma yarima ?a INA?
Yagyara zama yazayyane mata komai
Tahau gyada kai tana jin farin ciki aranta domin jin yarinya
r yar masu dashine kuma hakan yayi mata arai tafiso shima yariman yayi Aure kamar yadda LAMIDO zaiyi domin Aure yana karawa mutum martaba da kima a idon Al,umma abin tinkahon tane ace tayi suruka Yar babban gida ba "yar Bayi ba dama
Tasawa abin
albarka tareda karfafa masa guiwa " na amince maka kayi Aure adaidai wannan lokaci Yarima domin makiya suji kunyar abinda ake shirin maka tunda nasan duk don abakanta maka aka shiryi Auren su balle anga kafito da maitarka karara ka watsar dasu zuwa gab
a mushirya kutunguila akansu inhar Aka nada LAMIDO sarautar
domin baxamu barsuba
Ya gyada kai yace "Nima akwai shirin Dana shirya akan LAMIDON, UMMAH saidai zan ajiye komai agefe sai bayan nayi Auren tukunna amma kiyi kokari Takawa ya karbi abin da muhim
manci ahada ayi tareda na LAMIDON domin iyayan yarinyar da Gaske suke asatinnan zasu Zuba idon ganina
UMMAH tace " kada kaji komai Aure fa kamar anyi Angama
******
Koda UMMAH tajewa da Mai martaba wannan zance Murna ma yayi domin yasan yin Auren Yarim
an kamar wata hanyace zatazo masa ta shiriya don haka saiya nuna amincewarsa da gaggawa tareda tsayar mata da maganar zai tura aje akai kudin Aure tareda tsaida musu rana daidai Dana LAMIDO
Taji dadi tayi masa godiya takoma yiwa Yariman Albishir
Da fari
n ciki yakwana jin antsaida masa ranar Aure sati uku masu zuwa
Yaiwa Amarya Hindu albishir
Ai ihu taringayi Dan dadi da farin cikin data tsinci kanta aciki
Tuni ta gayawa iyayanta tamkar suma sungaji da itan saigashi suma suna murnar
Ackn Satin kuwa
Mai martaba ya Aiko batun nan Aure
Galadima ne da Liman Amintattun Sarki sukaje kai kudin Aure Dubu Dari biyar
Da kwatance suka sami gidan domin mahaifin Hindu fitaccene babu Wanda baisan Gidan Minista ba a A T/wada Kaduna
Anbasu an amince musu nanda sat
i ukun Dayake kanin mahaifinsa ne da Yayan mahaifin nata da Amininsa suka karbesu agidan Ministan
Anbasu tukuici me tsoka tareda karramawa domin da tsaraba aka rakosu da zasu koma
Kaji da cake da lemuka da turarika da shaddoji haka aka zubasu a but di
n motarsu
Koda suka koma suka rattabasa sarki abinda suka gano cewar iyayan yarintafa Sunada mutumci da Halin girma
Sarki yaji dadi yasawa abin Albarka
Zancen Auren yarima da LAMIDO yazagaya gari anata irgen kwanakin dasuka rage sbd irin shagulgulan da a
ka shiryi
yi sbd nad'in da za,aiwa LAMIDO na zama sarki da zaiyi
Lefe ma yarima A England yatafi yahado
Shiko LAMIDO dayaje gun *KUYANGA* tambayarta yayi
"Gimbiya!
Takalleshi da murmushi kan fuskarta tana murza zoben hannunta da MAHBUB yabata kafin yara
su
Tace ahankali
" Harna zama gimbiyar ?ai naga Gimbiya Matar Sarkice wacce yakeso kuma
Yayi murmushi dama shidin ma,abocin murmushine yace "Zeenatu kenan ai kamar kinzamane Tunda saura kwanaki daga lokacin da Aka daura mana Aure nima naxama Sarki Kema ki
nzama Gimbiya tunda aranar za,ai Nadi Ta gyada kai tanajin annashuwa aranta da kuma sonshi ackn zcyrta
s
hima hakan yakeji aransa agame da itan
Yakatse shirun nata dacewa " Awace kasa kikeso ahado miki lefe?
Takama baki "Ni na isa? Wacece ni tab ahad
o anan
Yasha mur! Yace " keko kika isa kuma ke me matsayice da kima don haka daga yau kidaina ma daukar kanki maqasqanciya agidannan domin kintashi daga *KUYANGA* kindawo *GIMBIYA ZEENATU*
Tayi murmushi ita kanta sunan yayi mata dadi
Yaci gaba da fad
in"kinaji ko zamuje Sudan ko Dubai inhado miki komai acan nida Abokina Safwan tare mukai karatu dashi acan mahaifinsa ne liman na gidannan tare TAKAWA ya biya mana zaizo kugaisa
Takawa yana sonki Zeenatu ki godewa Allah jarabtar da Allah yayi mk arayu
wa tazame miki riba da ci gaba domin ayau yakirani yakaramin kudi akan Wanda yabamu na siyayya nida yarima yace ke tadabance inyi miki siyayya mekyau
Yakarasa maganar yana kallon kyakykyawar fuskarta yana murmushi
Itama murmushin takeyi tana fadin "Na
ji dadi nagode ayiwa takawa godiya
Yace " To ni zankoma
Tayi masa yar rakiya da baifi taku biyar ba ta koma tana waigensa
LAMIDO ya burgeta tabbas yanada aji ga iya magana da kalami duk macen dayace yanaso dole ta amsa domin shi din abin sone
Tana
sh
iga Daki tafada akan gado tana fara,a
Zulaihat tabita da kallo tana fadin "Yarinya tashiga kogin soyayya tafito
Dafatan kinyo iyo kinkamo kifi?
*KUYANGA* tayi murmushi tareda tashi tazauna tana fadin "Zulaihat kifaye ma nakamo ba kifiba tabbas LAMIDO
yatafi dani kamar yadda nima natafi dashi
Allah nake godewa da yabani wannan baiwar ta zama matarsa gashi Yace Takawa yana sona yakara masa kudi akan Wanda yabasu da yarima na soyayyar lefe Mahaifiyarsa kawai nakeji bansaniba ko itama tana sona kamar
yadda Sarkin ke sona?
Zulaihat tace "Hhhhmm Zeenatu kenan aike abar soce itama banajin zataki sonki tunda ta tako har gidannan tazo miki barka da gaisuwa Dan haka kigodewa Allah kawai
" Allah nagode maka.cewar *KUYANGA*Zulaihat tace "Ga magunguna can i
nji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno
*KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun?
Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki
Sosai
" Hhhmmm Allah dai yasa ba daci
Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa
*KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha
******
Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba
Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama kana da nambata kamance dani
Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayi
min amma yanzu na huce Dan haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata
SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya
Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin nakama
Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni arank
a SAHABI
SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar diyar kanin mahaifina ce ita ke sona
Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa zaka dauko musu banza me sakaran
ra,ayi
Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura?
Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England
SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai
Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi
"Nima bawai kinta nakeba
tunda yar 'uwa tace Ina Zeenatu naji ance abinda ta Haifa yarasu
Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO...SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi?Nan yarima yazayyane masa komai
SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni
Allah yasanya Alheri
Yarima baikulaba yai masa sallama
Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa
Anata shirye shiryen biki akowane bangaren
Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada atakura masa
shida amaryarsa
Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha gyara babbane dama ba kowa ciki
Aka zuba komai na alfarma agidan
Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu
Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin sunhadu sunburge kowa
Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu s
uka dauka bayan Su MAMAH DA
FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA
Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina
Shiko Yarima karya