Showing 36001 words to 39000 words out of 57925 words
gidan ita tajanyo
Da yake wayayyi
yace ta k
arshe ga iya makirci bata nunawa "yan uwanta komai ba duk da idonta yai jajir
Abu har gaban iyaye bayan suna dataga danginta sun tafi taringa masa iskanci kala kala tana boren saita bar gidan tunda har yasa hannu yadaketa ita tunda take ba,a taba marin t
aba
Abin yafi karfin UMMAH saida suka Dangana ga mai Martaba shi yayi sulhun ya bata hakuri
Sai aranar ma Sarkin yataba ganin yaron
Yaji dadin ganin Takwaran nasa jikan fari na Aure wanda yayo kamannin Yariman
Yayi masa addu,o,i tareda yi musu nasihohi
"HINDATU ina miki kallon mace me hankali baikamata ki kawo matsala afarkon tafiyar kuba tunda yanzu aka fara na ari bakin yarima nabaki hakuri sannan nadau miki alqawarin duk haihuwar da zakiyi agaba ke zaki ringa zab'a da kanki yanzun ma da ace tun farko
kafin suna nasani da sunan mahaifin naki zaisa amma tunda anyi hakan kiyi hkr kinji Surukata.
Kanta akasa tagyada kai tana fadin "ya wuce amma ayi masa kashedin kada yasake taba fuskata da nufin duka domin girmanku na gani baisa nakai maganar ga nawa iyaye
n ba ato.
Takawa yakalli yarima yace "Tunda kake kataba ganin na daki wata mace ackn matana?
Yarima ya girgiza kansa
Takawa yace "To wannan shine rana takarshe kada insake jin kamari Matarka ko zagi banyarda dashiba kutashi kuje.Suka mike suka futa
Fulan
i datake zaune agun cike da mamaki tace da Takawa "Nifa yarinyar tafara futa araina domin naga alamar batada mutunci.., D'aga mata hannu takawa yayi yace "kul kika sake kika aibata ta domin ku kuka yayota ku kuke son ta dama dan haka kuje kucigaba da hakur
i da ita ai "yar masu arxiki ce yar boko dan haka dole kubita kuso duk abinda
takeso agaba.
Fulani ta quta da takaici tace "Naji takawa amma inada wata magana me muhimmanci.
Yace "inajinki fadi.
Tagyara zama da rage murya tace "maizai hana bazaka dora Ya
rima akan karagar Mulkiba na jiran gadon don kar abar guri bakowa kafin Allah yadawo da Sarki na Biyu
Yayi murmushi yace "bankarbi shawarar ki ba Inaji ajikina yakusa dawowa don addu,a bamu dainata ba sannan garina lafiya yake ba yak'i akeyiba balle ind'or
a wanda zai zama jagoran tafiya yak'in ni na isa komai tunda inada wakilai ko ban fita fada ba.
Ta hadiyi wani yawu me daci da zafi tareda mikewa tafuce ranta ba dadi
Tana shiga Sashinta ta tarar da Yarima ya hada kai da guiwa yana ganin shigowarta yahau f
adin "
"UMMAH bazan iya doguwar tafiya na zamantakewa da Hindatu ba tunda tazama matar tashi hankali dama arashin wacce nake so na Auret
Fulani tace "kayi hakuri tukunna kasan ayanzu dole mubi abinda takeso mubarta xuwa gaba mu lallabata kafin muga
cikar burinmu ayanzu inkace zaka rabu da ita idon jama,a zai dawo kanka kaida nakeso kazamo Sarkin garin nan ai kaga baidace ace bakada Aureba.Ya gyada kai yace "hakane ya kukai da Takawan?
Tace "hhhmmmm Yarima abin babbane domin kuwa mutanen can sun gama
shanye mai martaba yaki ya amince da shawarata yace yanaji ajikinsa Lamido yakusa dawowa dan haka baxai dora kowa ba
Yarima yayi dariya yace "Ai Lamido yatafi kenan kuma ko da karfi da yaji saina zamo sarkin garin nan.
Fulani tace "nifa na fidda rai ga Tak
awan ma yakamata a kaudashi shima tunda xaizamo mana fitina shine qaluballenmu dan hakan kasan abinyi akansa
Yarima ya gyada kai yace "Nima tunani na kenan UMMAH kibani kwana biyu zan gama aiwatar da komai.
Yana gama fadin hakan yamike ya fuce
Wani kallo
n banza Fans din LAMIDO da Takawa suka bishi dashi harda masu tsaki mitssssttt!!
Muje zuwa
Abu kamar wasa maganar B,atan Sarki na biyu ta baza koina cikin gari da wajenta harma sauran makwabtakansu sunata zuwa yiwa Takawa jaje
Takawa dauriya kawai yak
eyi domin yanajin abin ackn ransa zcyarsa kullum ckn tafasa takeyi galadima na nusarshi da rarrashinsa domin yasan lalurarsa
Akullum gani yake kamar zai dawo aranar mafarkinsa kuwa kullum sai yayi amma a yanayi mekyau yake ganinsa
Abangaren Yarima kuwa ats
akaninsa da Hindu babu wani shiri domin tun haihuwar Datayi tadaina bashi kulawa da baisaka mata sunan mahaifinta ba koda akayi musu sulhu baisa ta sake dashiba saima shariya da take masa shike kulata ma dayake mabuqacine amma ita ko ajikinta domin da tayi
arba,in ma gida taje yawon arba,in tayi sati biyu saida iyayenta suka mata dole ta dawo amma shi kusan kullum waya yake damunta dashi Wanda har mahaifiyarsa taringa masa fadan yakyaleta haka intaga dama ta dawo don yana bibiyarta da nuna mata damuwa yasa
take masa haka
Hindu ta futa aran Fulani hkr kawai take da lamarin tunda tana so Yarima yayi sarauta kuma bazasu bashiba inbaida Aure
Da Hindu ta tashi dawowa kuwa akori kura guda aka ciko da kayan gara komai buhu biyar shinkafar tuwo biyar ta dafawa ta g
wamnati biyar semovita kuwa guda goma shabiyarne dayake buhunsa karamine abubuwan da suke akwali katan katan kuwa ashirin ashirinne garwar mai kuwa ba magana harda bakin kifi
bushashshe sugar buhu biyar kai abin ba magana anyi harkar arxiki
Kayan aka jibge
asashin Fulani ita ta bada tukuici na makudan kudade
Aiko kaya sunsha rabo sai Wanda take shiri dashi taringa baiwa domin takawa yace ayi abinda yadace dasu tunda akwai finsu a store din ajiye kayan abincin gidan
Su FAATU Da MAMAH ko kiransu ganin kaya ba
tayi ba domin ta nuna musu rashin muhimmancinsu tunda tasan zasu sami labarin yawan kayan tasan batada matsala anyiwa D'anta bajinta dai yawuce gori
Ohh!agidan sarautar ma
🙄
to Allah ya sawwaqa
Saida Hindu tayi sati da dawowa sannan taje duba Takawa Yarima
ne ya matsa mata yace mata jikin Takawa ya dawo
Dakyar ta shirya ta fice amota ta tafi dubiya kin yarda tayi yakaita tace ai itama yasan tanada mota ta iya tukin
Afarkoma Haushin D'an takeji Dan ko sunansa bata boyewa Abdallah take ce masa akan hakan suns
ha fada Da Yarima shi Dole saitace masa CIROMA kamar yadda suka saka masa acan gidan sarki Fulani ce ta lak'aba masa dole shi gashi jinin sarauta D'an sarkin wataran Koda taje fisha tashiga ta dubashi ko Yaron bai daukaba ta fuce dataje gun Fulani ma bata
dadeba ko kallon sashinsu MAMAH batayiba balle su sami gaisuwarta ta wuce gurin shakatawa abinta
**********
B'acewar LAMIDO ta doshi shekara Alokacin takawa ya fidda rai da dawowar d'ansa Wanda har lokacin yana kwance ba lfy Wata ranar Lahadi Galadima yan
a kusa dashi ya gama bashi magungunan sa har yayi bacci Galadima baifutaba yasashi gaba yana kallonsa cikin tausayawa acan kasan ransa yana matuqar tausayin takawa na yanda yake jin jiki gashi akwai wani Abu dayake ran galadiman yana so yafurtashi ga takaw
an don Neman yafiya amma yakasa sbd tsoron abinda zaije yazo
Fulani ce tashigo da sallama
Galadima ya amsa mata yana fadin "Ranki ya Dade yasami bacci yanzun nan.
Ta gyada kai tace masa " To dama zuwan nawa biyune ai da nakama
Gabansa ne yafadi sbd yana
tsoron duk abinda xai fito daga bakin Fulani indai na shi da itane
Haka yabita zugui zugui abaya har inda suke haduwa wani sa,in
Ta dubeshi ranta abace tace masa "ya maganar mu?
Adabarce yace mata " Ta zancen da nai maka na inaso Yarima yahaye kan karaga
ta kowane hali
Yashafa gemunsa yace "Narasa yanda zanyi da Takawa yaki amincewa da zaki hakura da hakan xaifi domin yana ganin Yarima bashida nagartattun halayen daya cancanta yazamo sarkin garin TASKIRA....Tadaka masa tsawa " kai Dakata naga alamar kaima
dama ba qaunar yarima kakeba tunda har zaka iya fadin haka baka boyenba Kuma ko menene yarima yake dashi jinin Kane....
Galadima ya rintse idanu yana fadin "ya salam Fulani kidaina dawo da wannan maganar Yarima jini nane amma Dan kine tunda dole kikaimin t
un awancen lokacin kika kuma sharaddatamin kan cewar inhar kika sami ciki dani bazaki taba furta nine uban saba nakine halak malak kinga kuwa baikamata yazamo kina furtawa ba domin inhar wani yaji nashiga uku agarinnan sanin kankine akwai aminta tsakannina
da mai martaba kirufamin asiri domin na Dade da tuba da nadama
Fulani tayi murmushi tace "Galadima kenan ai babu Wanda zaisan Yarima ba D'an takawa bane insha Allahu yanda muka haqa muka binne bameji dagani saikai dinnan
Yace to yanzu meye abin yi?Ta gya
ra tsaiwa tace " Tunda yaki amincewa munyanke shawarar kasheshi
Da sauri yazaro idanu tareda dafe kirji "me?kedawa ?
Tace " Ni da Yarima da wadanda muka tanada.
Yace "inkukai hakan agari za,asaka ayar Tambaya akan Yarima za,ace ba jininsa baneTace " in
ansan dasa hannunsa kenan ?
Taci gaba "Kaine kadai zakasan meya faru kaima domin inmunzo gunsa dole zaka ganmune tunda kaike kwana dashi shiyasa nagaya maka Kuma doka da umarni zansaka maka akan kayi tsit da bakinka karka tona!karkayi ihu !!karka bayyanar
da abinda zai faru agaba!!!" inhar ka yarda ka tona to tabbas na rantse da Wanda ya busan numfashi zanyi qundunbala intona maka asiri ta hanyar yi maka sharri ince kabani maganin bacci aruwa ashekarun baya ka kwanta dani sau biyu nasamu cikin Yarima dakai
zankuma kawo manyan shedu dasuke kwararan hujjoji
Tana gama fadin hakan tayi gaba tabarshi kansa akasa yana hawaye
Wai yaushe Matar nan zata barshi yahuta ne yakamata ace ayanzu ya daina samun zunubi ta hanyar Takawa ita keja masa komai
Ya gyada kai
tareda goge zufa da hawayen yace bakomai akwai Allah
Amma fa daya koma bai iya bacciba da dare domin agaba yasaka Takawa yana kuka yana masa kallon karshe
Ita kuwa datake labe abayan wata yar Katanga taji komai atun tsayuwar Galadima da Fulani gun basu gan
taba amma taji duk bayanansu JAKADIYA ce
🤔🙆🤦
♀
Itama kwana tayi maganganunsu na yawo akwanyarta tabbas bata taba kaduwa da firgita na almara ba irin na yau Ashe dama Yarima ba jinin takawa bane?Galadima ne yaci amanar sarkin?Fulani cikin shege tayi dama
alokacin?Tabbas MAMAH zata fara gayawa domin awancan lokacin kafin Zuwan FAATU MAMAHn ce tasha wahalar Fulanin da Gori akan cikin domin MAMAH ko Bari bata taba yiba amma taga wulakanci agidan har juya akece mata duk Fulani ce sila
*********
G.Zeenatu na Zaune tana carbi da hijab ajikinta ta idar da sallar Ishsha,i tanata Zikirai da salatin Annabi da istigfari Da hailala
Bata tashi akan abin sallah aduk sallolinta harsaita gabatar da addu,oin
Zulaihat nazaune kusa da ita
Taja ajiyar numfas
hi tareda goge hawayen daya ziraro mata tunani takeyi na mijinta da ace yananan da tuni wataqila itama ta haihu
Tashare hawayen tana kallon zulaihat
Zulaihat tace mata "Amma dai kinmin Alqawarin fa kindaina kuka meyesa to?
G.Zeenatu tace " Zulaihat kiyimi
n uzuri bazaki gane yanda nakejin mijinaba zulaihat inama ace inmutu kawai domin samun saukin zcyta inama saida muka haihu dashi aka hadamu tare aka sace mu akashe mu tare Kinga ai munbar me mana addu a walh saibayan Mijina baya tare dani nakara kaunarsa j
i nake kamar nahadiyi zuciya inmutu kawai
Tafashe da kuka
😭😭😭
Zulaihat tajata ajikinta tana fadin "yi shiru yar uwata damuwarki tawace walh INA mk uzuri tunda wani zubinma sai hawayen yazubo akejin saukin zcy kici gaba da addu,a Allah baya bacci yana ku
ma sane da komai wannan jarabtar kuce kiyita daurewa lokacin kadan saikiga waraka Allah yabayyana manashi
" to sai yaushe Zulaihat?shekara guda fa Ni walh bakaina nafi tausayiba Tsohon can ina kaunar Takawa to amma gashi shima yashiga wani hali adalilin wa
nnan lamarin yanada ciwon zuciya tsorona Kada ya mutu yabarmu da Alhini dayawa
Zulaihat tace "Allah zai tashi kafadunsa mudai muci gaba da Addu,a kawai.
G.Zeenatu tace " To.
*******
Awani Dare wasu fadawa Suka biyo wannan Daren Sadaf sadaf suka shiga Turak
ar Domin aiwatar da Aikin da akasakasu
Galadima yana bacci amma saida suka Fesa masa hodar da tasashi jin nauyin jikinsa yakasa motsawa balle yagansu mintina abin zaiyi yasakeshi
Suka Fesawa Takawa wani Ruwa dayasashi Jan Numfashi sau daya baisake motsiba
FANS KUSANI WANNAN RUWA BANA MUTUWA BANE
Suna Futa Suka isa inda aka basu umarni dama Yarima yana sashin mahaifiyarsa
Amma dayaji komai ya kammalu saiya taho zuwa turakar takawa
Yayita sallama Dayaga shiru saiyanufi Galadima yatasheshi afurgice yafarka y
ana mika jin yanda jikinsa yayi yana daddaure yakejinsa
Galadima yace "Yarima lafiya naganka adaren nan.?
Yarima yace '" Tafiya tasameni Sassafe shine nazo inyi sallama da mahaifina naga kuma yana bacci so nake yatashi muyi sallama
Galadima yatashi dakyar
yaje yahau tashin takawa ahankali
Abu kamar wasa yaga Takawa baya motsi yabata kirjinsa yaji baya bugawa yatabbatar dai ba rai saiya fashe da kuka
Arikice Yarima yatambayeshi ko lfy
Galadima yace "Takawa babu rai ya mutu
Kuka yarima yafashe dashi
Aitake
suka fuce waje suna kuka kamar yara Take gida kowa yafarka ana jiyo ihunsu
Aka taru agun takawa ana ta koke koken Mai martaba ya mutu
Gida kowa ya farka har bangaren bayi anata kuka
G.Zeenatu hannu tasaka aka tana fadin sun shiga uku
Matansa KOWACCE kuka
takeyi Amma Fulani tafisu kunzumawa ita nan uwar gida Matar fari
Wajen Ukun dare anyi cirko cirko abangaren Takawa sai Waziri da Liman sukace kowa yatafi sashinsa abarshi in anyi sallar asuba sai afito ayi addu,a asallaceshi akaishi makwanci Dan haka kow
a ya watse har dasu domin gidajensu ba tazara
Galadima ne dai yana tare dashi da yarima
Abin mamaki Galadima saijin jikinsa yakara daurewa yayi yana Zaune yakasa motsawa ga wani bacci dayai a won gaba dashi Wanda yakasa yakarshi
Ashe abinda fadawa suka fe
sa masane baigama sakinsaba tuni yarima maganin hakan yagarzaya yaje ga fadawan dasukai masa aikin sukazo sukai Dabara iya dabara suka dauke gawar takawa suka fuce dabita ta wata sirrintacciyar hanyar da zata bulle dasu bayan gari Wanda yariman ne yasama m
usu hannayr amma saida suka yiwa fadawan gem surkulle domin tanan zasu dawo duk suma bacci akasakasu
Saida sukai tafiya ta awa guda ckn wani daji aka shigar da Takawa cikin wani gida
Acan gidan Sarkin kuwa Galadima baifarkaba sai da asuba sanyin asuba yaf
arkarsa
Abin mamaki sai yaga wayam babu yarima adakin babu Takawa
Wani ihu yakurma yafito waje yana kuka me amsa kuwwa
Kowa na gidan yabazamo jin abinda ya faru wai babu Gawar Takawa ta bace kowa mamakin yaringayi
Yarima daya dawo yana kuka yana yiwa gala
dima fada kan cewa me yakeyi har aka sace gawar Takawa to tabbas sai yayi furzin domin da laifinsa
Galadima yana kuka yana fadin "walh bansan ya akai ba saijin nayi inata bacci me nauyi Wanda bansan dalilinba bantaba irin saba da alamar Wanda sukazo saces
hi sunmin wani abun.
Waziri yagyada kai yace " kudakata maganar Galadima akwai kamshim gaskiya domin kuwa acan get ma naji masu tsaron get suna mamakin wai sunyi baccin da basu taba yin irinsaba ayau daya dace kada ayi shi na yanda muka tashi da rasuwar Sa
rkin mu Sannan yama za,aiyi ashigo har ckn garinmu asace gawa gawarma ta Maimartaba me hakan ke nufi tabbas akwai wani lamari akwance akasa Wanda bazamu kyaleba sai mungano ko waye
Liman yashare hawaye yace "dole mushigar da hukuma ayanzu kuwa Ck tunda
zamuso muga gawar sa musallaceta kamar kowace gawa ra musulmi Dan haka muyi maza mukira hukuma
Yarima yace " Bari nakira inspector yazo da yaransa danna tabbatar duk inda gawar nan take ba,ayi nisa da itaba
Gida fa yashiga ckn rashin lfy na rashin Takawa j
ikin kowa asanyaye atsorace kowa yake aranar anshiga bincike hankalin kowa atashe yake ....
Daga MAMAH har FAATU suma Rudanin suka shiga domin sunkasa fahimtar Zulaihat din
Saida zulaihat ta daidaita Numfashinta tadawo nutsuwarta kana ta bude baki a
hankali tace "Ranku ya Dade Sarki na biyu nake nufi Allah ya dawo mana dashi…
Kabbara suka hau yi G.Zeenatu kuwa ji take kamar ta futa aguje ta taro shi kafin yashigo musu amma kunyar surukanta takeji hawayen farin ciki kawai take gogewa
Suma kasa jiransa
sukai suka fuce
Aiko sai ganin sa sukayi yataho Sashin nasu fadawa na take masa baya
Sukai turus suna kallonsa duk ya rame amma bai canza kala ba alamu basu nuna awahala yake ba
Yakaraso da sauri garesu ya rungume iyayansa kowacce yana xubda hawayen Da
di
Matarsa kuwa kasa rumgumeta yayi suma dansun manyantane yatsura mata idanu yana kallonta yanajin wani kafirin dadi na ganin ta
Ta rame kamar yadda ya rame ita damuwar sace shikuwa Tunanin rashinsune yasa ya rame
Duka suka juya suka shiga gurin FAATU
n
Koda suka zazzauna dafe kansa yayi yana fadin "wash!..
MAMAH tace " sannu kaji Mun Auna Arxiki da Allah yasaka