Showing 48001 words to 51000 words out of 57925 words
amma takasa tafiya
Daya takura mata da saita futa sch saita fashe da kuka
Hankalinsa atashe ya tambayeta meke damunta saitace "to bakaine ba kacanzamin kakemin zargin na saba maganar
ka Alhalin walh bana yin komai natsarin iyali kawai daga Allah ne inhar baka yarda ba kadaukeni ka kaini asibiti a tabbatar maka
Yayi shiru yana gaskata ta aransa
Ta kama kafafunsa tace " inhar baka huce kasakar min fuskaba walh bazan iya komai ba ko naj
e sch din shiyasa bazaniba ba
Ya kama hannayenta yace "na yarda dake my hubby ba komai shirya inrakaki makarantar yawuce Ba komai na huce Allah yabamu rabo na alkairi
Sannan ne tayi murmushi ta sake
Ahakan dai sukai duk kwanakin daya rage mata akasar ata
re suna shan zumar soyayya
Ashe su basu saniba ma Allah yadubesu yabasu abinda sukeso domin G.Zeenatu dai tana dauke da ciki
Basu gane hakan ba saida suka baro Kasar ackn jirgi ta ringa kelaya masa amai ajikinsa zazzabi ya kamata cikin mintina duk yarud
e yarasa inda zaiza kansa dole suna dira kai tsaye asibiti suka wuce domin aduba abata taimakon gaggawa
LAMIDO yayi kan jakadiya asukwane ya damkota yana fadin "me kike shirin yiwa " yata ? Waya aikoki ki kasheta?
Jikinta na rawa tace "Ranka ya Dade kayi h
kr tsautsayine karufamin asiri ba kasheta zanyi ba
Ya daka mata tsawa " yimin shiru munafuka karya Zan mikine alhalin naganki da filo ahannu kina kokarin Danne fuskarta dashi
Gimbiya Zeenatu ce dataji komai ta fito arude dama toilet din a ckn bedroom din
yake
Ta Dora hannu aka tana kuka tana fadin "Nashiga uku jakadiya dama nufinki arai knn shiyasa kullum kike ajikina to ta Allah ba takiba anya ma ba ke
kika kashemin Dana acan shekarun baya ba tunda hakance takasance walh ban yarda dakeba
LAMIDO yakalli
G.Zeenatu yace da ita " kwantar da hankalinki zanje da ita atujumeta tuhuma me tsanani inma itance tayi hakan abaya Dole zata fada ai intaji wahala
Ya figota idonsa rufe Dan tsananin zugin da zcyrsa ke masa na bakin cikin data shaqa masa gudaliyar "Yar t
asa da Allah yabashi son kowa kin Wanda yarasa Ko kwana bakwai bata cikaba aduniya amma har itama ta tsare tashiga qaluballen rayuwa to meta tsare musu?
Bangaren su FAATU da MAMAH yakaita ya zayyane musu komai
Ganin yanda jakadiya tayi fiki fiki idonta ak
asa tana hawayen munafurci duk don atausaya mata
Aiko tasha zagi da d'aga murya agunsu FAATU domin MAMAH harda dungure mata kai tana ce mata Annamimiya me fuska biyu
Kai infayyace muku aranar dai Jakadiya saida tayi nadamar zuwanta duniya
Abainar Nasi aka
daureta ajikin bishiya jama,a suka baibayeta ana tir da halinta
Wasu bayi mata ke mata tuhumar domin taki fadin waye yasata aikata hakan
Ta hanyar kwara mata ruwa afuska me tsananin sanyi suke azabtar da ita ko taji wahala ta fada Dayake ana cikin hunturu
n zanyi ga yamma tayi sakaliya sanyi ya mamaye koina na Duniyar wasu dayawa agun ma rigar sanyi suka saka
Intakaice muku Masu karatu jakadiya ba wasu fa shekaru take dasu dayawa ba balle wasunku su tausaya mata suce ana wahalar da tsohuwa bazata wuce arba
,inba tun tana shekara 30 da mijinta yarasu agidan lamarinta ya canza da mutuniyar kirkice daga baya tazama me bakin hali dama bata taba haihuwa ba
Kuma duk bakar wahalar nan datake Sha batayi nadama ba tunda gashi nan batada niyyar fadin komai akan wada
nda suka sata tsoronta daya inta fada Fulani zata tsangwame ta tunanin yanda ta kasance abaya kawai takeyi
dama ai
GOGAL bokanyarku ta fada miki jakadiya lallai yau ga ranar taxo Gareki Jakadiya
Da labarin yakai kunnen Fulani burus tayi da zancen ta nuna
ma ko a jikinta domin inta nuna damuwa ko kuma inzata zaqe ackn maganar saita kwana da ita tunda bata manta yanda akai abaya ba da Yarima yayi Abu ya dawo masa makamancin hakan da asirin wanda yasa aikin ya tonu yasa bakin asakesu daga tsaresun da akayi a
i dashi ta kwana tunda Allura ta tono garma anata goma biyar bata gyaruba karshe hakan yai sanadin barinsa gidan sukuma fadawan da suke masa mugun qulli na aikin nasa gidan zasuyi rayuwar dindindin agidan Yari
To itama hakan take tsoro kada taje saka ba
ki amaganar Asirinta ya tonu duka duk da sunyi da jakadiya duk tsananin bazata fada ba inhar Abu ya b'aci
Abangaren Takawa kuwa da maganar taje masa ransa ya dugunzuma hankalinsa ya tashi wai agidansa za,a ringa samun wadannan matsaltsalun na kisan kai ! L
allai yakamata yadau mataki da kansa kodon a daina tunda anyiyyi abaya baiyi maganaba
Yayi mamakin ace wai jakadiya ce ke shirin kisan kai kisan ma na abinda yanzu yafiso aransa Jikarsa Khaleesat tabbas bazai kyale ba saiya dau mataki
Da kansa yataka har
inda ake ganawa Jakadiya azaba
Mutanen gidan sunyi cuncurundo anata kallonta
Takawa yasa aka kunceta fada yahauyi agun yana cewa meyasa ake mata hakan mace ce fa baikamata abata irin wannan horon ba ga izaya nan kala Kala ayi mata mana idan ta kamu da
babbar cuta ta wannan hanyar fa!?
Wadanda suke bata horon suka dukar dakai suna bada hkr daya tace masa "Tuba muke Ranka ya Dade za,a canza mata horo munyi hakanne domin bin umarnin Adalin Sarkin mu bisa yanda yace a azabtar da ita a idon jama,a sbd wasu s
ugani suji tsoron kwatantawa agaba amma agarcemu bamuda laifi
Sarki Abdallah ya
gyada kansa yace " Akwantota akawomin ita inyi mata tambayoyi yanzun nan
Sukace "angama
Jakadiya kasa daga idanu tayi takalli Takawa sbd kunya gashi agalabaice take gabanta na
ta faduwa domin tasan itanma karshenta yazo agidan
Takawa yasaka aka kira masa kaf matansa da manyan Gidan irin su liman da Waziri da sarkin fada,zagi, dadai wadanda ke da mukami ackn gidan Sarautar
Aka hadu asashinsa harda LAMIDO kowa na Zaune tsit ana
jiran tacewar Takawan
Mai martaba Sarki Abdallah yayi Gyaran murya tareda kallon jakadiya da kanta ke kasa yace mata " Jakadiya kin zama me cin amanar gidan Sarauta sannan kinzama me fuska biyu tunda kina nuna koina kina sonsu Alhalin son kowanne baikai
ba azcyrki
Me yasaka kika aikata hakan ko waye yasaka ki aikata hakan ?ko dole akai miki?tunda abaya kin taba zuwar min da zance amma kika kasa fada to ayau INA son ki fadi ko meke faruwa agidan ta bangaren ki Wanda ke a ranki kike boyewa
Yayi shiru Jim
kadan yana kallonta yaci gaba da maganar Dayaga batada niyyar batu
"Wato yin shirunki shizai cuceki fadin gaskiyarki kuma shizai kubutarki muna saurarenki inkuma kika bata lokaci ko kikai min karya zaki tinzirani insa ayi miki azabar datafi wacce akai mik
i
Jakadiya ta dago kanta ahankali aiko sai ackn idon Fulani
Gaban KOWACCE saida yafadi
Fulani na addu,ar Allah yasa kada inta tashi fada tasakota wai yauda ta cuceta kuwa
Itako jakadiya tunani take na yanda yau zatayi bankada amma Allah yasa kada ta kwan
a aciki ita kadai
Ahankali ta bude baki tace " ina Neman arangwanta min domin duk abubuwan Dana aikata sakani akai kuma ba kowane yasaniba illa FULANI…
Zabura Fulanin tayi ta daka tsalle gefe guda dafe da kirji ido waje tace "ke makira
munafuka maza sake
maganarki bansan zancen ba
Takawa yadaka mata tsawa akan ta zauna takuma nutsu bai bata izinin magantuwa ba
Ta zauna jiki na bari zuciya na bugawa
Kowa dai agun kallonta yake amatsayin Mara gaskiya
Takawa yakalli jakadiya yace " wato abinda nafahimta an
an duka kisan da akai na baya na gidan kece kikayi ma knn tundaga kan Bawa MAHBUB da Jaririn da Zeenatu ta Haifa abaya dasa hannunku knn?
Jakadiya tace da sauri " Dani aciki amma Wani dasa hannun Yarima akirashi aji...Kowa agun yahau sallallami ana mamaki
n zancen
Ita kuwa Fulani bata San lokacin datayi kan Jakadiya ba ta shaqota tana duka tana fadin "Munafuka zakiyi Yarima sharri Dan Kinga baya gurin ta Allah ba takiba walh bazan barki ki bata min d'a ba
Jakadiya sai kakari takeyi taji bakar wahala ahannun
Fulani
Takawa ya buga mata tsawa ya nunata da hannun
" Fulani zaki fuskanci hukunci yanzun nan idan har baki shiga taitayinkiba maza ki koma gurin ki ki zauna kikuma bani hankalinki domin na fuskanci baki da gaskiya
A salube takoma ta zauna tana raba idan
u
Takawa Yakalli jakadiya yace mata "kin tabbatar maganar ki gaskiya ne akwai sa hannun Yarima ack zaki fada koda agaban sane ?
Ta gyada kai kawai sbd jikinta ke nukurkusar ta gashi taci wahala ahannun Fulani Wanda akan hakan taci alwashin yau saitayi tono
n sililin da fulanin bata zataba
Takawa yakalli LAMIDO yace masa " Kiramin Yarima awayarka
LAMIDO kunna wayarsa dake hannunsa yai dialing nambar Yarima 3 missed call bai dagaba dayake yasan nambarsa
Dama a hands free yasa wayar kowa yaji ring ba,a dagaba
Takawa yace "kyaleshi
Yakalli waziri yace " waziri kiraminshi kai tunda yaki daukar ta dan,uwansa
Waziri da rawar jiki ya kira nambar
Yariman shima ahandsfree yasaka tayi ring tana gab da katsewa ya daga "Assalamu Alaikum !
Da sauri Waziri ya mikawa taka
wa
Mai martaba yakarba yana amsawa tareda cewa " Yarima aduk inda kake kataho nan da gobe domin akwai gagarumar magana....yarima yace "Ranka yadade ai gamu agab da gida ma ina hanyar zuwa nida iyalina tunda naji anyomin waya ance Matar LAMIDO ta haihu nac
i Alwashin dawowa domin ayi suna muna gidan
kaji makiri hhhhmmm andaiyi walkiya
Takawa ya lumshe idanu yaji Dadin hakan kenan komai zaizo ma da sauki
" saikun shigo , yafada tareda kashe wayar
Shi Yarima dama yayi nufin zuwane domin samun soyayyar takawan
shiyasa yafadi hakan domin yafaranta masa ko zai huce da fushin da yayi dashi tunda yasan yafison LAMIDO akansa
Alokacin da aka kirashin ma tuki yakeyi yana cikin kanon sun kusa gidansa saiya karya akalar motar zuwa gidansu tunda ance masa gagarumar magana fatansa Allah yasa dai maganar tasace shida takawa domin shikam so yake yashirya da mahaifinsa
Hindu takallesh
i ranta bace tace "Amma dai daga yo maka waya sai wani ce gakanan zuwa ina laifin kabari muje gida muhuta zuwa safe saikaje haba haba Daddyn Ciroma
Yarima yabata rai " ke kinsan kuwa banaso in saba maganar Mahaifina nikam yanzu neman shiri nake dashi bana
so na saba masa ko musu dashi nashiryi kyautata masa don haka babu ruwanki ciki
Ta tabe baki bata kara cewa uffan ba
Ciroma yana kan cinyarta baccinsa yakeyi abinsa Yaron yayi wayo
Suna isa gidan kai tsaye sashin Takawa suka nufa
Hindu na rungume da Ciro
ma tana bin bayan Yarima da tunda yashigo gidan yaji gabansa na faduwa
Ai bakaramin kaduwa yayiba daya shiga Dakin takawar yaga taron mutanen gidan kaf ga iyayansa da manyan gari Sallamar dake bakinsu ma makale masa tayi yatsaya cak!
Mai martaba yakalleshi
yace "Ku shigo Ku zauna Ku kawai dama muke jira
Asanyaye yashige ciki yanemi guri yazauna kusada mahaifiyarsa yanayin UMMAN tasa yabashi tabbacin ba lfy ba
Hindu ta zauna gefe guda itama tana mamakin wannan taron da akayi
Takawa yakalli Yarima yace " N
asan zakayi mamakin ganin munhadu kaf dinmu anan to wata babbar matsalace ta taramu Wanda kuma Jakadiya da mahaifiyarka sune suka haddasa sannan kaima kazama sila tunda mungano dasa hannunka ciki
Yarima ya firgita yace "Kamar yaya meye nawa ack?.
Takawa ya
kwashe komai yagaya masa
Ai bakin cikin da yarima ya qunsa na yanda Jakadiya tasakoshi ack yasa shikuma yayi kokarin fitar da kansa ya kuma kara dilmiyata ack yace " bansan zancen maganar kisan Bawa MAHBUB ba asalima ni bansan ya akai aka kashe shiba nad
aiji ance ya mutu amma banbi ba,asin ta hanyar daya mutun ba
Jakadiya tace "karya kake munafuki kaine kasaka fadawan da ka saka suka sawa LAMIDO guba a gwaiba suka kashe MAHBUB kabiyasu walh jin kunne na naji kuma kaima kasan najin inkuma ba hakaba aje ata
ho dasu su zasu fada ai
Takawa yace " Yarima kayarda aje ataho dasu din?Yarima yayi shiru kansa akasa
Takawa yafara fahimtar da qamshin gaskiya
Sai yace "Waziri maza aje ataho da fadawan nan suzo nan muji ta bakinsu inhar sun fadi gaskiya to nasahale musu
zaman kurkukun…
Waziri yayi farat yace " Ranka ya Dade kada abiyewa wannan makirar nafahimci zata wargaza maka gida ne nidai shawarata tunda maganar ta Dade da wucewa to abarta zaifi da aita tone tone ayi mata hukuncinta daidai ita yafi
Jakadiya ta dago
ahasale takalli Waziri ranta na mata quna ta bude baki tace da Takawa "Ranka ya Dade shima
Wazirin inkaji irin Abinda yayi maka bazakaso kazauna dashiba balle har yazamo me baka shawara sbd yafini cin amanarka shima fuska biyu ce dashi atare dakai
Waziri
ya harzuka yana nunata da hannu " ni zakiyi sharri to menayi na fuska biyun fadi ko meye munafuka yaudai karyarki ta kare
Hhhhhh
🤣🤣
waziri da kasan abinda zai biyo baya da bakace hakanba koda yake bakasan Jakadiya Nada Sirrin ka bane
Fulani tasha jinin jikinta sai gabanta yahau dukan uku uku
Takawa yace da jakadiya "Na baki izinin kifadi abinda kike son fada Wanda yake boye akan wazi
rin inko kikayi masa karya saina hukuntaki
Jakadiya tace " Ranka ya Dade ashekaru dayawa da suka shude tun farko farkon zamana agidan nan ina yawan ganin Fulani da Waziri awata mahada suna maganganu to ina yawan bin bayan su in labe
Alokacin rikici nake y
awan jin sunayi na tirkar tirkar rashin amincewar Waziri na abinda tasakashi yaki amincewa yayi
To Allah ckn ikonsa ashekarun nan na kusa sai Allah yakaini gurin Dana ga sun saba haduwa Dana hangosu saina labe abayan wata "Yar Katanga da suke tsaye jikint
a duk don inji kome suke qullawa
Aiko dai abinda naji ya matuqar firgita ni kwana nayi banyi bacci ba na yanda naji akunne na wai Fulani nabashi umarnin ya kasheka ta hanyar baka guba shikuma yaki shine tace masa to zasu kasheka su itada yarima zakuma susa
ka asace gawarka don haka kada yasake yatona asiri koda yagani tunda shine ke kwana dakai yana baka magungunan ka SBD bakada lfy alokacin bakasan inda kanka yakeba
Duk saboda sugaji sarautar suke shirya hakan
Ta gindaya masa sharudda da gargadi ciki hard
a ce masa idan yasake ya tona musu asiri to itama saita tona masa asiri na yanda
suka munafurceka suka Aikata zina suka sami cikin yarima.....
Ana wata ga wata
*ALLURA TA TONO GARMA...*
MUJE ZUWA FANS
Hannu Fulani ta Dora akanta tana kurma ihu wai yau tas
higa uku jakadiya tayi mata kazafi
Shiko Waziri suma yayi azaune domin bai zaci abinda zaifito knn daga bakin jakadiya ba domin da ace yasan da wannan rana da jakadiya zatayi masa hakan gara ace yasa ankasheta
Yarima kuwa hankalinsa ne yai matuqar tashi t
saye ya mike yana nuna jakadiya yana rawar murya yakasa furta abinda yayi niyya "ke...me…
Shiko Takawa wata zazzafar zufa ce ta keto masa hankali tashe yahau sharceta
Kowa agun saida ya mike tsaye banda takawa da jikinsa yai masa nauyi
Ba abinda
kakeji sai salllami da ihun Fulani agun
Hatta Hindu kanta kwancewa yayi ta dafe kirji tana kallon jakadiya tana addu,ar Allah yasa wannan zancen ba gaskiya bane domin inya kasance gaske tabbas batayi sa,ar uban D'a ba
FAATU da MAMAH hankalinsu ya tashi mat
uqa tabbas wannan shi ake kiran RANAR WANKA…
liman kuwa cika yayi da tu,ajjibi yana ta nazari aransa domin shi kansa ansha gaya masa anga Fulani da Waziri amma bai taba kawo komai aransa ba
Takawa ya rarrashi zcyrsa domin gani yake zancen kamar a mafarki s
aidai kuma ba abin mamaki bane sbd mutum mugun icene
Yabaiwa kowa na gun umarnin azazzauna zaiyi magana
Kowa ya zauna yana ta rarrabi arai
Jakadiya kuwa Yar iya ko dar batajiba aranta domin da ace ta kwana aciki gara sun kwana aciki su duka tunda ta fuskan
ci daga waziri Fulani yarima kowa Neman Dora mata laifi yake suna son ita tarasa rayuwarta alhalin sun fita gingimemen laifi agidan
Takawa yayi Gyaran murya cikin Nutsuwarsa
yahau magana ahankali
"Hankalina yatashi dajin wannan zance matuqa da jakadiya ta
fada Wanda nake fatan ya kasance ba gaskiya ba domin bazan taba murna da farin cikin inada shege agidaba shegenma Matar farina ce tayiminshi tareda amintaccena inko abin yakasance gaskiya baxanji dadiba domin wannan babbar cin