Showing 15001 words to 18000 words out of 57925 words
mata hannu yace "ya isa bana son daga murya domin zcy ta tafasa takeyi raina abace yake tambaya kawai nayi ba neman jin fitina ba ya akai hakan tafaru agayamin.
MAMAH Tace "Ranka yadade cikin nanfa tun daga turai aka sameshi domin da alamar dashi ta dawo domin YARIMAN ma da suka tafi dashi can tabaroshi baisaniba ta dawo.
Sarki Abdallah ya furgita da jin wannan maganar yace "TURAI!? ya akai har *KUYANGA* taje tura
i batareda sanina ba meyasa yarima yatafi da ita ba,a gayamin ba tabbas FULANI kece da laifi tunda kinsan da tafiyar tasu kika boyemin kinkuma san halina akan in aka munafurceni a abu
UMMAH tayi kasa da kanta
Yaci gaba da cewa "To shi yariman ne yayi mat
a cikin ko wa?
Da sauri tadago tana fadin "ba cikin yarima bane baima san ta taho ba Yace min ta dade bata gidansa tun zuwanta kasar idonta yabude take bin maza farkan natane yasata ajirgi ta taho ahalin yanzuma yarima baisan tanada cikiba
Mai Martaba y
ace "Koma dai menene laifin na yarima ne ko ba cikinsa bane to kune sila sannan Alhakin yana kanku meyasa Da hankalinki xaki hada mace da namiji suje su zauna agida daya ba matar saba bakomai ba Alhalin kinsan halayyar d'anKi munada masaniyar yana bin mata
n turawan nan acan
Maimartaba yaja ajiyar zuciya yace "Yarima baidauko halin kirki na gidan sarauta ba domin babu me munin halinsa adangina banyi fasikanci ba banyi shaye shaye ba amma gashi Allah yajarabceni da yaron dakeyi Allah nagode maka Allah kashir
ya minshi
UMMAH tahau zubda hawaye tana fadin "Amma dai kasan akwai mahassada na agun baidace karinga aibunta min Da suna gunba.,
Tsawa yadaka mata "yimin shiru fulani ko ranki yabaci banasan zancen banza wadannan abokan zaman kine ba mahassadan kiba Kuma
ki gaggauta kiran yarima awaya kigaya masa maza injini yadawo gida
Tahau gyada kai tana goge hawaye
Yace duk sutashi sutafi
Sun mike kenan zasu futa saiga Jakadiya ta shigo da sauri tadurkusa tace "Anzo da babban batu daga asibitin da aka
kwantar da *KUYA
NGA* Ana bukatar jini ackn gidannan za,a kara mata domin tana cikin wani hali.UMMAH taharari Jakadiya
Yayinda FAATU taji wani tausayin *KUYANGAR* Yashigeta tace da jakadiya "Maza Ki kiramin Ladimo A bangarensa kisanar masa yafito yaje asibitin adebi nasa.…
Mai martaba najin tafadi hakan yai mata magana "akan wane dalili zaki bashi wannan umarnin Alhalin jiya-jiya yadawo baigama hutawa ba zaki sashi wahala babu nasiyane da baxamu siyaba.?
FAATU tace "Ranka yadade dazu muna hira dashi yagama fadamin an
auna jininsa anga Group O" ne yace kuma yana son yaga yabaiwa mai bukata domin yasami lada natabbata kuma inyaji ackn gidannan ne zaije da gaggawa
Mai martaba yagyada kansa yace "To ace masa yabayar din nima na Amince tunda ladan yake nema.
Jakadiya tace "
angama zanje yanzu ko ingaya masa.
Duka suka fucedaga Turakar Sarkin
Koda jakadiya tajewa da Lamido wannan magana ta umarnin yaje yabadajini inji mahaifiyarsa bashiri yahau shiryawa zuwa Asibitin
Direbansa na gidan da aka ware masa yanema yace maza yakaish
i Asibitin da suke ganin likitansu
Zuwansu keda wuya suka tarar ana Auna jinin MAHBUB
Likitan daya gama awon jinin yadawo yatarar dasu duka azaune yace "jinin MAHBUB baiyiba damar diba shima yana bukata sannan yanada Typhoid
Nan LAMIDO yamike yace da liki
tan shi aje a debi nasa yanada tabbacin nasa zaiyi tunda group O ' Ne dashi zai iya baiwa kowa jini
Likitan daya Auna yagani yatabbatar saiyace da LAMIDO "jininka yayi saidai ba leda daya take bukata ba adebi biyun ba matsala ko adebi daya su sai dayan?
L
AMIDO yace "Debi biyun na amince lada nake nema bawani abuba
Take yakwanta aka debi leda biyu
Saida
yahuta agadon sannan yafuta daga asibitin ko *KUYANGAR* bai nemi inda takeba don hankalinsa ba,a gunta yakeba bukatarsa dai ta biya yataimaka mata don baiw
aye taba ma.
Koda yakoma gida mahaifiyarsa taringa masa godiya da addu,a gareshi takuma bashi labarin yarinyar da abinda yafaru da ita
LAMIDO yadade yanajin ciwon abin aransa meyasa akaiwa baiwar Allah haka meyasa don anga batada gata aka danne mata hakki?
Dayake shi mutum ne mejinkai da tausan bayi sannan gashi da ilimin Addinin domin acan din dayaje karatu Islamic yakaranta yanada sani sosai
Yadago da kansa ckn Qunar rai yace da Mahaifiyarsa "Amma sam abinda yarima yakeyi baya kyautawa kodayake UMMAH ta d
aure masa gindi kuma inada tabbacin shine ma zaiyi cikin Sharri kawai za.ayi mata
FAATU tace "Muma tunanin mu kenan Amma dai koma meye ai dole asiri zai tonu tunda Inta futo daga Asibitin zata fadi ko cikin waye kuma Takawa yace agayawa yarima yadawo da ga
ggawa
LAMIDO Yace "Insha Allahu saina taimaka mata Da jikina da abin hannuna.
FAATU tayi murmushi tace "Allah yabaka iko D'an Albarka
ACAN asibiti kuwa MAHBUB ne Shida Zulaihat suka kebe yana tambayarta shin abinda yaji ackn gidan sarki gaskene?
Zulaihat
tarintse ido tana futarda kwallah tace "MAHBUB duk abinda kaji gaskiyane Likitocin sun tabbatar Zeenatu cikine da ita na Daya da satittika wanda yaso ya bare Allah baiyiba rabon dai ta wahala ne Nayi kuka sosai danaji hakan dama kuma nafara fahimtar hakan
kafin rashin lfyr tata.
MAHBUB yarintse idanuwa yana hawaye kirjinsa zafi yake masa meyasa Zeenatu taci amanarsa?meyasa Zeenatu tacanza hali? Meyasa tabiyewa sharrin Shaidan da Namiji ta Amince da wani Alhalin Sunyi Alkawarin Aure ……?
Jakadiya ce
Zaune agaban UMMAH tagama kawo mata tsegumin Matan Sarki wai da alamar sun hade mata kai sunaso asirinta yatonu agidan abata mata d'a
UMMAH ta furzar da iska abakinta kana tace "jakadiya nadade da sanin abinda suke ciki nasan basa sona dani da yarima Ku
ma walh sainayi maganinsu agidan nan daya bayan daya cikinsu
Jakadiya tace " nibakomai nakeji ba sai *KUYANGA* Kada tacewa sarki cikin na Yarima ne domin zata iya k'ak'aba masa don tagaji abin arxiki na gdn Sarauta
UMMAH ta quta kana tace "zankuwayi
maganinta domin nagama yanke shawarar abinda zansaka kiyi mata Wanda inhar kikayi zanbaki makudan kudi da zinare da gida agefen gari ckn gidajen Yarima
Jakadiya tahau murmushi tace " fadi ko meye kikeso inyi zanyishi uwar dakina "yr sarki jikar sarki me
babban daki uwar gidan Sarki Fulani uwar Yarima Wanda zaihaye karaga da yardar Allah
UMMAH tayi murmushi najin Dadin kambamawa tace " So nake dazarar ansallamo *KUYANGA* daga asibiti yazamo tadawo karkashin kulawarki koda ace ta fadi ckn Yarima ne ko bam
a nashin bane yazama tana tare dake kullum zansa ta dawo dakinki inyaso kafin ta haihu kisa mata guba a abinci ko kishaqeta da filo ta mutu kawai
Zabura jakadiya tayi kana tace "Ranki ya Dade bazai yiyu akasheta da gaggawa ba za.a fassara mu kokuma a
zo ayi nadama gara dai inta haihu inbi dare inkashe abinda ta Haifa
UMMAH tayi murmushi tace " Dakyau jakadiya kinada hangen nesa tabbas zama dake akwai riba hakan ma da kika tsara yayi don haka kizama ckn shiri
Koda jakadiya ta futa daga dakin UMMAH
saita nufi Dakin MAMAH domin kai mata tsegumin UMMAN tayi sa,a kuwa ta tarar da FAATU atare da MAMAHn suna hira
Jakadiya takai gaisuwa garesu kana ta xauna gefe bakinta na motsawa irin na munafukai sunso tsegumin
MAMAH tace "ya akai jakadiya akwai wa
ni abun ne?
Jakadiya tahau shafa hab'a tana fadin 'Dama wani Abu najiyo dayake damuna tunda naji nakasa fada muku
FAATU tace 'ikon Allah mene wannan Abu fadi muji shi
Jakadiya tayi kasa da murya tace " Ranki ya Dade Gimbiya FAATU zancen ma dai akan
d'an kine domin FULANI tananan tana hakon tayi masa mugun Abu domin kada yagaji sarautar mahaifinsa kada ma yaji yanaso aransa sannan inada tabbacin Yarima ne yayiwa *KUYANGA* cikin nan amma naga tanaso adanne mata hakkinta don haka yakamata kuyi wani
Abu akai
MAMAH Da FAATU suka kama baki suna mamaki domin kuwa basu zataba duk da sun Dora zarginsu akai
MAMAH tace "lallai jakadiya mungode munyarda ke me kaunarmuce don haka munbaki izini akan kiringa bibiyar lamarin don kar hakanta yacimma ruwa
J
akadiya tace " Angama ranki ya Dade Amaryar Sarki Dangwale shalele agun maimartaba Uwar Lamido me jiran gado
Koda jakadiya tafuta sai FAATU tacewa MAMAH "Nifa shiyasa bantabajin inason LAMIDO yahau kankaragar
nan ba in maimartaba yayi murabus haka shima
LAMIDON bashida ra,ayi Sam mulkin baya gabansa balle yadorawa ransa
MAAMAH tace " to duk da hakan dai saiki tashi tsaye kiringa addu.a ba dare ba rana kirage bacci kigayawa Allah akan yakawo muku agaji kada aje a cutar miki dashi
Nan dai MAMAH
tayita bata addu,o,in na kariya domin sunfurgita da zancen da sukaji abakin Jakadiya
**********
A can Asibiti kuwa anbaiwa *KUYANGA* kulawa daidai gwargwado harta samu kanta
Zulaihat CE agunta kafin arubuta musu sallama
Domin sai data kwana daya a asibit
in kana aka bata sallama
Suka dawo gida Zulai ita ta gaya mata duk abinda yafaru da ita tunda a sume aka debeta xuwa asibiti batasan me akai mata ba tundaga Karin jini da daukar jininta aka auna aka gano tanada shigar cikin
Hannu ta Dora aka taringa kuka
tana fadin "Nashiga uku na cuci kaina da tun farko na aminta dakai ban bujire makaba.biyayya batayimin ranaba wayyo Rayuwata ta gurbata Allah kadauki Raina kona hu.... Zulaihat tayi saurin toshe mata baki
" kada kice haka Zeenatu Allah yajarabceki da hakan babu tsimi babu dabara sannan Ni bana zarginki sai tausayinki
"Inke bakya zargina Zulaihat MAHBUB fa ? Nasan kome zance baxai yardaba Allah ne kadai zaifutar ni ko a gidannan.
Zulaihat tace " Waye
yayi miki cikin?
*KUYANGA* Tace "wakuwa zaimin inba Yarima ba cikin sane bantaba sanin wani namiji ba inba shiba harta dole yakemin....nan tahau baiwa zulaihat labarin yanda rayuwarta ta gudana a Turai tareda Yarima bata rage mata komai ba har taimakon
ta Da SAHABI yayi
Zulaihat
tashare hawayen tausayin zeenatu tace " Zeenatu Yarima yacuce ki domin ayanda nafuskanci MAHBUB yaji ciwon abun yakuma zaci ko kinyi cikinne abisa sonki har kuka yayi yace yayi nadamar fara kaunarki yace kincuceshi yayi kuka s
osai a asibiti
Kuka takara fashewa dashi jin yanda MAHBUB yadauki lamarin
Shikenan tafaru ta kare tasan ko a agidan bakowa zai yarda ba sai Wanda yasan halayyar Yariman
Zulaihat ita tayi ta dannarta tana bata baki Dan kwantar mata da zcy
Kwana tayi kuka
duk tafuta hayyacinta ta rame
Ko futa dainawa tayi saidai Zulaihat ta karbo mata abincinta in an gama abangaren nasu dayake dakinsu daya da zulaihat din
Tayi zaton ko MAHBUB zaizo yadubata amma saitajishi shiru na wasu kwanaki baizoba
Sannan takara tabba
tarwa lallai yadau zafi da ita
Sati Daya da maganar cikin da *KUYANGA* Tazo dashi daga turai YARIMA yadawo
Magana ta yada ko ina na cikin gidan sarki
Wasu suna yarda na yarimane wasu kuma suna ganin bazai zama nashiba tunda ance yawonta take da maza data
je turan
KARSHEN TIKA TIKI TIK!!
Dawowar yYarima yasa kowa agidan yashiga murna domin ansan tunda yadawo kasar za,a samo matsaya akan cikin *KUYANGA*
Tana Zaune adaki tana tunanin data sabayi Zulaihat ta shigo da Sauri tace mata "Zeenatu yi sauri kidauko
hijabi muje an aiko sanarwa daga Fada Sarki nabukatarki agun Yarima yana can fadar da Kaf Ahalin Gidan za,ayi Zubeben kwarya...
Gabantane yafadi tareda dafe kirji take hawaye suka hau zarya akuncinta
Zulaihat tajata jiki tace mata "daina kuka kwantar da
hankalinki me gaskiya yana tare da Allah Abinda kika Sani shi zaki fada kada kiji tsoro kada kuma kirage komai
*KUYANGA* Tahau gyada kanta taredajin karfin guiwa ajikinta
Zulaihat tace " muje inrakaki fadar......
CARBI ne ahannun *KUYANGA* datake ja
ackn burmemen hijabin dayake jikinta Addua kawai takeyi Akan Allah yabata Nasara yashige mata gaba yakuma dorata akan maimartaba
Gaban tane yafadi ganin yanda fada ta cika da ahalin gidan daga matansa da yaransa YARIMA da LAMIDO da kuma fadawa da Galadim
a da sauran masu mukaman gidan Bayi ne kawai basa gurin
Kowa ita yake kallo itako kanta akasa tasami guri anesa dasu tazauna Zulaihat ma ta xauna kusa da ita
Maimartaba yana ganin shigowarta yayi Gyaran murya ganin tazauna nesa da mutane duk aka nuts
u ana kallonsa
Yace " *KUYANGA ZEENATU* Ke muke jira kuma adalilinki muka taru anan Dan haka kidawo tsakiyar mutane kizauna domin ki amsa tambayoyi daga bakina
Tayi saurin tashi tabi umarni takoma tsakiyarsu inda fadawa suka bata guri akusa da Yarima da
yake kusada Sarki LAMIDO na gefen yariman Wanda tunshigowar *KUYANGA* Yazuba mata idanu yana kare mata kallo
Bayan ta zauna Mai martaba yawatso mata tambayar data rikita mata kwanya
"Dawa kike tarayyar fasikanci a kasar waje ???Ahankali tace " Bakowa
,Yace "To waye yayi miki ciki?
Hawaye na zuba a idonta tace " cikin jikina bana kowa bane illah na YARIMA!
f
adawa suka hau salati
Yayinda Sarki ya rintse idanu jin yasami jika Dan gaba da fatiha a ckn gida
Suko matan kirji suka dafe alamun mamaki
Yarima ku
wa fuskar sace ta nuna bacin rai tsababa ji yake tamkar yashaqeta ta mutu akan wannan tonon sililin datayi masa
LAMIDO kuwa girgiza kai kawai yk yi na al,ajab sannan yana mamakin yayan nasa da wannan hali
UMMAH mahaifiyar Yarima Ta dakawa
*KUYANGA* Tsawa "karya takeyi munafuka saikin nemo Wanda yayi miki inma ackn turawan da kika barosu kika gudo
Sarki ne yatsawatar mata akan tayi shiru
Yajuya kan Yarima yace masa " YARIMA ya abin yake? kanada tabbacin naka ne ko ba nakaba
?
Yarima yaji
sassanyar Tambaya sai yahau gyada kai yana fadin "Ranka ya Dade bansan da maganar ba baninayi mata cikiba
Sarki yace " to wanene?Yarima yayi shiru
Jin yayi masa shiru yasa yaci gaba da tambayarsa
"Sau nawa kataba Kusantar ta?
Nan ma yayi shiru kansa akas
a yahau fidda xufa
Ganin haka sarki yace " tun anan alamu sun nuna cikin kane Dan haka bazaka wulakanta Rayuwar yarinya kaci riba ita ta wulakantaba Dolene ka Aureta....
"bazai yiyuba!Cewar UMMAH tafada ranta abace
" don ci baya sai D'ana ya Auri KUYA
NGA gaskiya da sake
Mai marmataba yanunata da yatsa "kishiga taitayinki Fulani idan Dan kine nima nawane nama fiki iko dashi danhaka magana dole abita in anason zaman lfy dani
YARIMA yadukar dakansa yana magana ahankali " Ina Neman Alfarma ayimin rai
walh bana sonta akwai wacce nakeso mun mayi alkawarin yin Aure atsakaninmu ayimin kowanne irin hukunci amma banda wannan
Galadima yayi Gyaran murya yace "kwantar da hankalinka Yarima Munanan ma baza.ai hakaba kaidai katsaya da gaskiyarka inhar bakai kayi cikin nan ba Ai
jini zai nuna dazarar ta haihu za a auna jininka da abinda ta haifan agani
Galadima yadubi *KUYANGA* du
k don yakamata da laifi sbd yana goyon bayan Yarima yace mata
" Ke Wanene shaidarki akan wannan lamari?
Tadago dakai ahankali tana tace "SAHABI shine Shaidata domin shine yadawo dani daga kasar waje
YARIMA yazaro idanu yana mamakin lafazinta wato Ash
e SAHABI munafukin Sane?Galadima yace mata " wanene kuma SAHABI?
Tace "Abokin Yarima tun acan yasan wasu abubuwan
Nan tahau bada labari tiryan tiryan Har takai karshe tana fidda kwalla a idonta
Kowa agun yaji labarin KUYANGA me taba zuciya Wanda masu taus
ayi agun harda hawayensu irinsu MAMAH da FAATU
Haka LAMIDO yacika da tausayinta zufa taringaa karyo masa agoshi yana gogewa
Sarki yakalli Yarima daya sunkui dakai alamun rashin gaskiya yace masa "Maza kira SAHABI awayarka kasaka handsfree kowa
Jiki asan
yaye yakira wayar SAHABI yabarta a bude sunajin tana ring
Saida takusa katsewa kana Sahabin yadaga
Sarkine dakansa yahau masa magana
SAhABI yanutsu awaya jin martabane dakansa
Duk yanda ake ciki dai da mai martaba yazayyane masa kana yakara da koro masa
Tambaya
SAHABI yakadu dajin hakan tabbas yasan abin babbane
Nan yagyara zama yafede masa biri hr wutsiya bai rage masa komai ba na abinda yasani duk domin yaga yafutar da *KUYANGA*
Yarima yaita mamakin SAHABI nayanda yake zayyano bayanai
Da sarki yagama
ji yaiwa SAHABI godiya yakashe wayar
Ran sarki yagama baci akan musantawar da Yarima keyi
Yarima yahau sose sosen kai jin Sarki yace masa " kaji abinda abokinka yace anyi hakan?
Yagyada kansa
Sarki yace "Kasan da saninka Inta haihu zan daura muku Aure d
a ita sannan ayanzu Alhakin kulawarta yadawo kanta sbd abinda ke jikinta
YARIMA