Showing 45001 words to 48000 words out of 57925 words
kace kwabo zancen nan yazaga cikin gidan sarki harma da ckn unguwar na yanda LAMIDO sarki na biyu ya tsallake rijiya da Baya
Mahaifiyarsa dataji ce masa tayi "Kaci gaba da Addu,a itace tayi tasiri ajikinka da tuni an illataka ko anga bayanka nasan ma
kiya bazasu barka kahuta ba duk kuma akan sarauta ce Wanda bata gabanka Dan haka ka kara kiyayewa domin gaba bamusan me za,ai maka na mugun Qulliba Allah yakara tsaremin kai
Yace " Amin.
MAMAH ma
addu,ar tabishi dashi
Itako Fulani da wannan labari yakai
mata tuni ta harquka ta aika Yarima yazo tace masa
"Me kake jira baka dauki mataki ba Alhalin asiri yana gab da tonuwa kasan da cewar Bincike zai tsananta akansu har wahala tasaka sufada kuma mutuncinka zai zube idon jama,a Ga Takawa yana nan kasan irin so
n da yake masa shima inyaji zai dauki mataki na umarceka daka nuna karfin ikonka na mulkin da kake dashi kabada umarnin Asake maza kafin su fadi Wanda yasakasu aikatawar
Yarima yahau gyada kai yace " tabbas UMMAH zancen ki hakkun ne yanzu kuwa zan bada wan
nan umarnin tunda nafishi karfin iko a masarautar
Yana zuwaa fada ya aika da wannan umarni na asaki fadawan nan da yawunsa
Sukuwa wadanda suke da alhalin tsaresu basu bi takan maganarba domin Dauresu sukayi ajikin bishiya abayan gari suna tsula musu bulala
dagasu sai Dan kamfe ajikinsu
Amma duk ihun da sukeyi "yan taurin kai basuda niyyar fada
Wani bafade yagarzaya ya gayowa Lamido zancen Yarima sarki na uku yace asako fadawa
Aiko Ransa ya baci sosai
Yatattaka yaje har fada yasami Yariman domin jin ba,asi
Yarima baiyi ja amaganar saba da LAMIDO yazo masa da tambayar dalilin dayasa yace asakesu
Sai Yariman yace " sbd na isa kuma sai abinda na tsara za,ayi
Ran LAMIDO ya kara baci wato yana nufin yace masa shi bai isaba kenan to kuwa zai nuna masa shima isa
shshenne
Da fadawan da suke tare da Yarima sukaga abin zaiyi tsamari sai suka tashi suka basu guri domin fadan na "yan uwane amma fa Da sauri akaje aka fadawo Liman da Waziri
Hankalinsu ya tashi jin ana hayaniya tsakanin yarima da LAMIDO abinda basu taba
jiba sun tabbata abin babbane
Koda suka zo suka tararsu suna musayar yawu sunhu sukai musu akan shi Yayi hkr ya ajiye maganar gefe ayi bincike ahankali
Yarima kuma sukace ya kauda idonsa akai su
zasui binciken
LAMIDO yafuce ransa abace yatafi ga fadawan n
an domin dakansa yakeso ya bincikesu domin yana ganin inya bari akai musu lakwa lakwa gaba ma zasu sake tafka wannan katob'arar
Yana zuwa yatararsu atuben andauresu ana zabga musu bulala sun hada zufa har ruwa aka kwara musu me sanyi ajikinsu duk ckn izaya
r amma duk da hakan basu ce kanzil ba dai
LAMIDO yana zuwa yatsaya gabansu yakare musu kallo yana mamaki na taurin Kansu duk wahalar dasukasha amma sunki fada duk sun galabaita sai zuciyarsa ta karye kadafa su sukai niyyar hakan zai takura su kuma su wahal
a sufadi Wanda bashine ba donsu tsira
Yakawar da wannan tunanin yace akwancesu
Saidai kuma wani Abu daya girgiza shi yaga wani Abu daya tuno masa baya ajikinsu
Bazai manta da tabon dake keyar wannan bawan Allah ba gakuma dayan yanada wani ciwo ahannunsa ka
mar quna Wanda shima yana rike dashi aransa alokacin daya taba miko masa abinci da suka tsareshi adaji
Haka yataba kawo masa ruwan wanka nanma yaga tabon nan
Tabbas sune sai ayau kammaninsu suka dawo masa dukda alokacin suna shafa bakin Abu a fuskarsu d
omin badda bami
Da sauri yabada umarnin amayarsu adaure niyyar da yayi na sassauci yafasa musu
Yace musu "kunsan dalilin dayasa nace amayarku?to ayau zakuji abinda Baku zata zakuji ba domin Allah yatoni asirinku Allah yaganar dani nagano kune muna fukan
da kuka aikata min ha,inci da zamba ta hanyar kaini cikin daji aka tsareni harna tsahon shekara Walh narantse da Allah saikun gayamin Wanda yasaku aikata min hakan domin ko wanene wannan bame kaunata bane shin mutum dayane duk yasaku aikata min hakan ko
k
uwa?
Suka kara tsorata ganin Yaganosu akaro na biyu gashi ya fusata sunsan babu abinda xaisa ayau ba,a kashe suba
LAMIDO ya zari takobin jikin daya daga ckn fadawan dasuke tsaresu ya nufesu idonsa jajir yana fadin " DA kaina zankashe Ku inbaku fadaba
Da
sukaga da gasken Gaske yake ai a take suka hada baki wajen fadin "YARIMA ne !!
LAMIDO yaja yai turus zuciyarsa na tafasa " YARIMA!? yanzu dama yarima ne duka yake hada masa wadannan kitimirmirar lallai Ashe Baiyi sa,ar Dan,uwaba tabbas biri yayi kama da
mutum wato shiyasa yashiga lamarin yazaqalqale akan maganar Dan kada ahukuntasu asirinsa yatonu Ashe shiyasa yahana a aikata musu komai na hukunci tabbas Ayau yakara jin Yatsani sarauta tunda akanta hakan keta kasancewa gareshi
Sukansu fadawan dake tsare
dasu maganar Tabigesu na wai Yarimane Ashe yasakasu
Sukayo Kansu da bugu suna fadin "Tir daku mugayen iri kisa yatabbata akanku domin bakuda amfani
LAMIDO da Jan idanu yakalli Fadawan masu tsaron yace " Kuyi musu hukunci daya dace dasu kafin inwaigo gar
esu
Kai tsaye Sashin Takawa yawuce yasameshi tare dasu waziri suna Tattauna batun da jakadiya tazo zatayi amma takasayi
Suna ganin Akwai abinda yake faruwa ackn gidan Amma tsoro yahana tafada
Ganin Yanda LAMIDO yashigo musu hankali atashe sai suka
tsorata da hakan tabbas akwai babban lamari kenan
Yana xama yazayyane musu duk abinda yafaru
Takawa ya girgiza matuqa gaya tabbas zai dauki babban mataki akan Yarima ayau
Shiko Liman karkacewa yayi yana goge gumin daya tsatso masa agoshi yana fadin "Wanna
n Abu yarikitani na Al,ajab banzaci yarima zai aikata hakan ba anya kuwa babu hannun su abacewar Maimartaba aka fice da gawar sa
alokacin?
Da sauri Waziri yace " kada kayi wannan zargin Yarima bazai aikata hakan akan Dan,uwanSa ba wannan dai daya aikata ya
yi katobara Allah yashiryashi
Yayi hakanne don kada Allura ta tono garma
Takawa yace da LAMIDO "Kayi hkr nasanka dama kai din me hakurinne inaso ka kara akai daga yau kuma inaso inhar na isa dakai ka koma kan matsayinka na Sarkin Garin TASKIRA domin Dole
yarima Yasauka dama nazuba idone kawai domin naga gudun ruwansa Tunda kuwa yawuce makadi da rawa aishikenan yaiwa kansa kuma hukunci na akansa na abinda yai maka bani bashi dole ya nesanta da gidana bazan zauna da mugunya agidanaba sbd gaba bansan mezai ai
kata makaba
LAMIDO yana kaunar mahaifinsa bakuma ya iya musu dashi adole yasa hkr aransa zaikoma kan karaga ba Dan yasoba
*******
Hukuncin da Takawa yadauka akan yarima ya qona ran Fulani amma tana shakkun Takawa bata isa ta tankaba
Saita. saka yarima ga
ba tana Tausar shi " Kayi hakuri Yarima Haka Allah yakaddara maka tunda yace kanesanta da gidan katafi kafin zuciyarsa ta huce nasan nanda wasu lokuta zai nemeka da kanka tunda bazan bariba dole zanyi wani Abu akai
Yarima yaja ajiyar zuciya yace "Zantafi
turai dama inaso Dana yayi karatunsa kaf acan nima kuma zanhuta da bakin cikin da nake ciki na rashin qauna da mahaifina kemin
" kadaina fadin hakan yana sonka akwai abinda akai muku Dan ahadaku nasan ba haka siddan ba ansaka masa tsanarka ne sbd Yafi so
n nasu amma kabani lokaci
Yace "shikenan nan da zuwa jibi zamu D'aga
Tace " wace qasa zakaje kenan ?tunda kasan dai gidan Takwa England Zeenatu tana can tana Zaune kuma bazai yiwu Ku zauna tare ba
Ya lumshe idanu tuno yanda yakejin
ZEENATU aransa yace "A
kasar zan zauna Nafi sabo da kasar inada abokai acan gara can din inyaso sai innemi mazauni nesa da gidan
Ta gyada gidan tace " Allah yatsareka yasa kafi haka.
๐๐คฃ๐คฃ
Tsiya zaifi hakan
๐
Muje zuwa*GIMBIYA ZEENATU*
๐ฟ
Cigaban KUYANGA
๐ฟ
Tunda Yarima
Yazowa da Hindu maganar barin kasar taji Dadin maganar domin dama tana son tafita abroad ta huta ta Dade bata budi ido ba
Ckn rage murya tace dashi "kai!Amma fa Dadyn ciroma naji dadi matuqa Amma dai zamu Dade ko? Domin inaso in zauna acan insha Iskar
can inkoshi sannan yarona yayi karatun primary da secondary acan
Yarima yayi murmushi yace mata " keta jin Dadin rayuwa kikeyi Hindu amma Allah yagani adole zanbar gida domin kowa yabar gida gida yabarshi Inason zama cikin masarautar mu Dan babu yadda za
nyine kawai
Ita dai bata bi takan maganar sa ba ta hau shiri abinta
*******
Tun barin Yarima gidan Jakadiya tarasa hanyar da zatabi domin Tona asirin Fulani da waziri najin wai Ashe sune suka haifi Yarima
Ta rasa yanda zata billowa lamarin akullum gulmar
ciyota takeyi sai tayi kamar ta fadawa su FAATU saikuma taji tsoro ta fasa ammafa taci alwashin ko ba Dade ko ba jima saita fallasa kowa yaji
Shiko Sarki na biyu LAMIDO yaci gaba da gudanar da Mulkinsa na garin TASKIRA yaci gaba da aiwatar da duk abubuwan
da yakewa talakawansa na adalci Wanda akullum suke fahari das
Kullu yaumin iyayansa ckn Yi masa addu,a sukeyi sbd yanda yake musu biyayya da gudanar da Adalcinsa ackn Addu,a
Shiyasa akullum yake kasancewa ckn ci gaba da walwala
Baya ckn qunci da bakin ci
ki sai kewar matarsa data cikashi
Akullum suna yin waya yakai biyar
yanajin lfyrta da yanda take karatunta ckn kwanciyar hankali
Ita kanta takan fito fili ta bayyana masa irin kewarsa da tayi kullum magiyarta yaushe zai zo taganshi?
Shiko banda lallabata
da yi mata Alqawarin yana hanya kullum ba abinda yakeyi
Ita kuwa batada wata Matsala a yanzun duk wata tanajin alard na uban kudade shiyasa fatarta ke kara sheki da haske ta canza ckn watan ni tazama big girl kai bakace KUYANGA CE adaba
Ta bangaren karat
unta bata samun matsala komai ckn sauki yake zuwar mata inma assignment aka bata kanta yakulle takan kirashi ta tambayeshi yagaya mata shikenan
Saida Tayi shekara guda kana LAMIDO yazo mata aiko dai yasha mita agunta
Yaita bata hkr yana rarrashi
hardai ya wanke laifinsa don ce mata yayi yaki zuwane sbd yabata damar yin karatu anitse yanzunma Dan tace masa suna hutu ne
Kuma daya tashi zuwar matan ma bai sanar taba kwatsam taganshi
Ranar wata Juma,a da yammaci tana sanye da mini skert da body hug w
anda suka kamata tsam sun mata matuqar kyau kanta ba Dan kwali ta zubo gashinta gadon baya dayasha gyara yana sheqi da tashin kamshi na mayukan kitso
Tana falo tana kallon Tashar labarawa tana shan tea a cup tana ckn nishadi yau haka kawai takejin wani an
nashuwa na shigarta
Akullum dama kafin ta kwanta saitasha tea kaidane da rana abinci dayawa take kaiwa me gadin domin bata na dare
Kawai taji budewar kofa anshigo
Tazubawa kofa idanu don taga kowaye haka adarennan ya baqunceta
Ai take idanunta ya gano
mata mijinta abin alfaharinta LAMIDO
Tuni ta mike aguje ta nufeshi da sassarfa ta rumgumeshi tana masa sannu da zuwa
Yahau shinshinar gashinta yana murmushi
Ya mannata da jikinsa sosai yana ajiyar zcy
Ta dago takalleshi da rage murya tace "Amma dai Ka sham
maceni zuwa ba sanarwa ?.
Yace " Ayi hkr nasan saikin tuhumeni
kewar kice ta isheni yasa nataso ba shiri
Taja hannunsa tana fadin "to naji na hkr muje ka watsa ruwa kahuta
Bayan ya fito daga toilet ya bude Dan akwatin dayaxo dashi ya Ciro singlet da gajera
n wando yasanya kana yafito falon inda yatararta harta dire masa kunun aya datayi tun dazu ta ajiye a firji dama kusan kullum sai tayi tasha
Meat 5 ta dire a dining din tana kallonsa tana murmushi tace " zauna kayi maleji da wannan naso inama kafadamin z
uwanka Dana shirya maka deliciou
m
Yahau dry "wannan ma is OK kadan ma zanci domin cikina a cushe yake naci abinci a jirgi
Ya zauna ya fara tsiyayar kunun ayar a cup
Ya lumshe idonsa jin sanyin ya ratsa masa makoshi ga wani kafirin gardi daya mamaye masa b
aki
Ya bude idanunsa tar akanta yace " wannan dame dame aka hadane najishi ba damane
Ta lumshe ido ta bude tana murmushi tace "kunun aya ai kayan hadinsa bawani yawan kuzo mugani bane kawai dai iyawane kuma wasu basayi da kauri amma dayake ni nashanane
ni kadai kullum zanyi dabkaurinsa nakeyi
Ya gyada kai yana fadin " lallai kice kinmin tanadi gara da Allah ya kawoni tunda nasan kunun aya yataru ko?
Taji kunyar maganar lallai maza sai abarsu ya akai yasan da kunun aya nasaka ni,imar mace ta karu tab Ya
u takara yarda da LAMIDO yasan wasu sirrrikan mata toko yankar duro yayi ne?ta tambayi zuciyarta
Yakatseta da cewa "Yakamata abani baby ayau
Tayi murmushi tace " karoka Allah yabaka mana
Yace "Zan roka amma kema kitayani roka plz
Ta rausayar da kanta t
ace "Nikam yanzu banaso nasami ciki Ranka ya Dade sbd karatuna yafara nisa Nafison saina gama Dan Allah ka amince min inje insaka inplan mana saboda kar.......
Ya katseta da cewa " ban amince ba Wato kinfison karatunki akan inkaru dake ko ?to walh inhar n
aga kin kara wasu watanninma baki sami cikin ba tona tabbatar Kinyi wani abun ban saniba
G.Zeenatu tayi narai narai da fuska tace "Haba Ranka ya Dade ya za,ai naje nayi wani Abu abayan idonka bazan taba yiba insha Allah Da ixininka zanyi komai tunda ko ba
ka son nayin na hakura Allah ubangiji yabamu karuwa
Yasaki fuskar yana fadin " Amin.
To awannan dare angurji soyayya ba karaba saida idon Zeenatu ya raina fata dakyar tasha Ahannun LAMIDO domin sai gab da asuba yakyaleta tun dare ana guda aranar takara kiy
aya da gwarzon mijinta
Ckn hutun sch da takeyi na wata gudan tare sukayishi da LAMIDO Wanda yaringa yawo da ita da dare domin ta bude idon ta
Ana gobe zai barta yadawo Nigeria ne sunje shopping wani babban store sukai kicibus da Yarima da Hindu da
Dansu dayayi wayo sun gama lodar kaya sunzo gurin biyan kudi sukuma suna shirin shiga
Da sauri LAMIDO ya isa gareshi yana murnar ganin Dan,uwa yai masa sallama ya mika masa hannu
Amma abin mamaki sai yarima takalleshi yakauda kansa domin yarikeshi sosai a
rai
Itako Hindu kallon banza tabi G.Zeenatu tayi gaba
G.Zeenatu taji ba dadi aranta Wanda bata San akan me sukai hakan ba
Ta tausayawa LAMIDO domin ya nuna damuwarsa karara afili sbd shi mutum ne meson zumunci gashi baida riko ko
abinda yafaru ma yamanta y
asa maganar agefe kuma shi yariman yaiwa laifi ai amma kawai saiyakauda abin yabasar sbd Zeenatun
Yasan batada labarin komai saina baya baya
Yanda bata tambayeshi daliliba hakan shima bai gaya mata komai akai ba
Ammafa kwana yayi da damuwa aransa gashi ba
isan mazaunin yariman ba dayaje yanemi shiri kawai tunda baida kamar sa aduniya bayaga mahaifansa
*******
Tafiyarsa batayiwa G. Zeenatun dadi ba sbd yabar mata kewarsa saidai babu yanda zatayi tunda karatune yatsaidata data bishi
Sauranta kuma
shekara biyu agaba tunda yanzun daya tayi kuma yace bazata zo Nigeria ba yafison shi yazo inta gama ta taho baki daya kawai
Cikin kwanciyar hankali take karatunta akasar batada kawa ko kadan tabi maganar mijinta da mace guda take ma,amala makwabciyarta ita
ma SBD taji bahaushiyace Yar Nigeria ce iyayanta a katsina suke ita mijinta ta biyo aiki yakawoshi kasar
Aliya ba wata babba bace shekara kadan zata baiwa G.Zeenatu tanada Kirki matuqa gashi tasu tazo daya suna zumuncinsu bata taba aihuwa ba itama shekarar
su biyar da Aure itada mijinta
Idan suna hirar haihuwa takan nunawa G.zeenatu cewar Haihuwa ai ta Allah ce bata taba damuwa ba haka mijinta ma tunda an aunasu a kasar anga duk lfyrzu lau kawai daga Allah ne
To Itama Zeenatu alokacin ji take inama ta sami
cikin bata so ta kwarari shekaru batare da ta samu cikin ba
Aiko wani ikon Allah har tazo year dinta ta gama karatu Allah bai kawo cikin ba kuma duk wata biyar LAMIDO ke zuwar mata inyaji tasami Hutu
Ana saura wata guda su kammala da sch din suna tsaka d
a Exam din karshe Yadiro mata gidan
Tayi murna da zuwansa amma kuma da yazo mata da wata fuska sai hankalinta yai matuqar tashi bai taba nuna mata bacin rai ba sai wannan lokacin wai shikam bai yarda da itaba yana
zargin ko planning tayi tayi watsi da mag
anarsa ta baya
Kwana yayi bai kula taba yanata fushi
Aranar tanada exam