Showing 84001 words to 87000 words out of 363627 words

Chapter 29 - KALBIM BOOK COMPLETE

Mamugee   

10 Sep 2026

137

nacin neman bayanin komai akansa wanda duka idan aka hada link daya ne

asibiti tinda shima Sayd idan har yasan Abraham a asibitin ne wanda duka kuma dai haihuwan Ummitah ce takaisu asibitin da har akai haduwar.

Nunfashi mara sauti ya sauke yan bude idanuwansa ya dauki wayarsa ya miqe yabar office din zuwa cikin gida.

Ka

i tsaye dakin Sayd din ya sake zuwa ya dubasa ya tararda ya kwanta bacci ma ya daukesa dan haka ya wuce nasa bangaren bayan ya sanarwa mama ta kwantar da hankalinta b damuwar komai bane may be ma stress ne na aiki da zaman da basu cika yiba.

Yadda mama

tayi ta dan kwantar da hankalinta sbd Sayd shima 'da ne gareta tana kaunarsa sosai da sosai.

Falaq bata gida tana school shiyasa gidan yake tsit sai data dawo hayaniyar gidan ta dawo.

Abincin rana gabaki dayansu gidan sukaci a dining kaman yanda su

ka saba

Sayd ma ya fito dashi akaci abincin sbd bayason yabar kofar da AZIZ zaisan akwai abinda bayason ya sani dan haka ya sake.

AZIZ din kuwa ganin ya sake batareda ya sanar dashi komaiba ya sakasa tabbatarda abinda yake binciken ba alkhairi bane

tinda yake kokarin boye masa.

Da daddare da kansa ya raka Falaq dakinta sai datai bacci ya fito ya wuce bedroom dinsa yana kashe wayoyinsa,

Wanka kawai yai yayi shirin bacci ya kwanta yana rufe idanuwansa batareda bacci yazo masa ba sbd abubuwa da yawa

ne a zuciyarsa da kansa wanda duk dare kafin ya kwanta kewar yar uwarsa ce take zuwar masa wadda yakewa fata da adduar tana cikin rahamar ubangiji.

**Washe gari ma basu fita aiki ba a gida suka wuni Sayd din ya sake warwarewa shima kuma hutu da kadai

ci yake so dan haka ko fitowa baiyiba abincinsa ma sedai aka kai masa palonsa aka jera masa acan yaci.

Sayd kuwa Fita yayi sbd tsananta bincikensa da ayanzu shine abinda yake tsananin buqata.

Wayar Latif Sayd ya kira wanda yake cikin yan Amanar maaik

atan AZIZ kuma duk da basa kasar haryanzu LIMBA na biyansa Albashi hakama shine drivern da duk yawon asibitin da sukai harma da ranar haihuwa shine yake yawo dasu har suka baro Nigeria shine drivernsu.

Latif dayake Shagonsa daya bude yana business dins

a yana ganin kiran ya daga cikeda girmamawa yana cewa

"Oga Sayd"

Gaisawa sukai Sayd din ya gyara zamansa yana sauke numfashi me sanyi kafin ya bude baki cikin bayyanarda Buqatan abinda zai tambaya batareda delay ba

Shima Latif din Nutsuwa yayi yana

aje abinda yake tareda wucewa kurya inda baa shiga saishi kadai ya zauna dan jin abinda Sayd din zai fada.

"Latif ka tina a ranar da Ummitah ta rasu akwai Dr da shine yayi mana bayani kuma shine ya kula damu a wannan lokacin???

Cikin nazari Latif ya

dan shiga tinani yana kokarin tinawa da lokacin sbd dashi suke tare a asibitin.

Cikin rashin tabbatarwa yace

"Eh wani black haka naji suna kiransa da kaman Dr samail ne ko yaya ma suna.....katsesa Sayd yayi da sauri da cewa

"Yes,yes yes Dr Ismail

,yes thats the name"

Jin yayi wani abu daya danne zuciyarsa ya dan fada ya sauke numfashi yana miqewa tsaye yana jin sassauci a ransa yace

"Latif inason kaje asibitin ka bincikamun Dr Ismail din,

Inason sanin bayanai akansa,

Waye shi,

Familynsa,

Aikinsa,

Yana ina yanzu?

Da address dinsa, No i want to know every single abu akan rayuwarsa cikin gaggawa"

Shiru Latif yayi kafin ya sauke numfashi yace

"Angama Oga Sayd sbd babu abinda bazan iya yiwa Familyn Sir AZIZ ba,

Ayau zan ziyarci asibi

tin na fara sanin Full name nasa da idan yana nan kafin sauran binciken zuwa gobe da kwana biyu zan hado maka komai"

"Thanks" sayd yace yana kashe wayarsa ya wurgar a kujera yana dafe kansa tareda lumshe idanuwansa.

Falaq data kasa gane kan daddynt

a kwana biyu damuwa ta shiga tafara dagawasu mama hankali wadda itama tane kasa gane kan AZIZ din da kuma sayd da shima duk ya kasa zama kwana biyu

Magana tai musu wanda ya saka Falaq dawo da Daddynta daidai shima sayd ganin AZIZ baice masa komaiba kuma y

asan yanda AZIZ din yake da karantar abu da ilimin gane abu atake ya sakasa dawowa daidai sbd tsaro.

********cikin kwana biyu Fahad da Latif suka duqufa da mugun bincike da bin duk wata hanyar samo bayanan da suke nema baji ba gani,

Shi kuma Sayd j

in yake kaman zai zare sbd jiransu Amma ya boye yana ayyukansa hankali kwance sbd AZIZ daya fara fita office dan haka ya dan zama busy da ayyuka da kuma handling abubuwa.

Latif ne yafara hada bincikensa dan haka ya kira Sayd din kai tsaye wanda a lokaci

nda kiran ya shigo yana gaban AZIZ LIMBA yana karanto masa bayanan Report da aka aiko musu daga Italy.

Sunan Latif ne ya bayyana Akan screen din wayar Sayd din datake ajiye a gabansu.

Hannu Sayd ya miqa ahankali ya dauki wayar tareda kashewa ya ajiye

gefensa yana cigaba da bayanin da AZIZ ke sauraronsa hankali kwance cikin nutsuwa.

Yana gama bayanansa juyawa yayi ya fice yana amsa wayar Pa din Maheer Zad data shigo wayarsa akan haduwarsu da haryanzu baa san lokacin ba..

Sayd na fita kai tsaye

ya katse wayar dayake ya nufi office dinsa yana saka kiran Latif wanda ya dauka take.

"Oga Sayd I've Send you every information daka buqata,

Cikakken Sunansa Dr Ismail Saraki,

Yana Nigeria haryanzu sedai yana jinya haka kawai aka wayi gari ya samu str

oke baya iya magana baya iya komai yana gida yana jinya tareda familynsa a Jos,

Likitan zuciya ne shima kuma bai taba aiki a kowane asibiti ba Nigeria sai zaaden sbd baa Nigeria din yake aikiba saida Zaadens suka basa babban matsayi a asibitinsu ya dawo N

igeria,

Address da duka sauran bayanin na turo maka komai"

Katsesa Sayd yayi da cewa

"Idan yana aiki a Zaadens a babban matsayi meyasa basu tsaya masa gurin neman lafiyarsa ba ya koma gida??

"Ba shine abin tambayarba Abin mamakin shine Duk wani h

anyoyin samunsa sun datse hakama komai ya rasa a qanqanin lokaci wanda kaman ana kokarin hanasa wani abun ne kokuma akwai abinda yayiwa Zaadens din nake ganin"

Ajiyar zuciya Sayd ya sauke yana cewa

"Ngd Latif zan sake nemanka sbd Zuwa jos zai kamaka"

"Ok Thank you Oga Sayd"

Yana kashe wayar ya miqe yana sauke ajiyar zuciya akai akai sbd komai ya fara fito masa sedai tsoron qarasa bincikawan yake ma dan abinda zai binciko kada ya kashe AZIZ.

Sai yamma suka dawo gida suna isowa AZIZ kai tsaye b

angarensa ya nufa yai wanka ya shiryo ya fito suka zauna cin abinci a dining falaq nata masa labarai kala kala wadda a duniya ita kadaice take ajiyesa tayita basa labarai da surutai kala kala ya bata kunnuwansa yana saurara batareda yace komaiba.

Suna g

amawa suka wuce sallah

Saida sukai ishai suka dawo,

Motarsu na shigowa harabar gidan motar Fahad na shigowa bayansu dan haka a tare sukai parking.

Fahad dinne ya rigasu fitowa sanye cikin three quarter da farar sweatshirt ya nufo motarsu ya budewa

AZIZ motar yana masa barka da dawowa.

Amsawa yayi yana kallansa a taqaice ya nufu hanyar studyroom dinsa suka nufi bayansa.

Yana shiga zaunawa yayi tareda ajiye wayarsa gefensa ya dago a natse ya kalli Sayd wanda yake kallan Fahad kafin ya maida kal

lansa kan Fahad din ya bude bakinsa yace

"Yes,the dets???

Kallansa Sayd yayi da sauri yana matsowa zaiyi magana AZIZ din ya dago manyan fararen idanuwansa yai masa kallo daya take ta dakata yana komawa baya ya saukar da kansa zuciyarsa na tsananin na

uyi da tashin hankalin abinda fahad ya samo akan binciken.

Fahad da shima yake a natse sbd a gaban AZIZ din suke ipad dinsa ya daga ya fara budo bayanan yana cewa

"Babu Alaqar kowane business dake tsakanin Zaadens da dr Abraham saina likitanci wanda

kaman yanda muka zarga akwai me ciwon Zuciya a familyn sunanta ZEYNAB ZAD sedai kuma ta rasu da dadewa,

Bayan rasuwarta Zadeens sun sake samun mace a familyn wadda duniya ta sheda yanda suke tsananin sonta amma kuma tana tsaka da karatu kawai aka nemeta

aka rasa baa sake samun labarinta ba tsawon shekaru sun boyeta batareda an sake taba ganintaba wanda babu wanda yasan dalilin hakan amma kuma a yanzu tana wannan qasar tana karatu sedai ta koma gida a yanzu batanan,

A familyn kowa mun samu bayanin cika

kkiyar lafiyarsu banda JANNAH ZAD wadda babu wanda a iya binciken danai babu likitan daya taba ganinta bayan Dr Abraham......"

Dan shiru yayi yana tinani da shakkar abinda zai fada kafin ya dago ya kalli sayd wanda shima shi yake kalla da dukkanin imani

nsa kafin ya juyo ya saci kallan AZIZ da yayi shiru yana sauraronsa da dan sassauta murya yace

"A yanda na tabbatar sbd bamu san health status din JANNAH ZAD ba a cikin familyn kuma dr Abraham ne kadai likitanta kuma Shi din likitan zuciya ne Tabbas ita

ce takeda matsalan Zuciyar datake cikin zaadens,

Dr Abraham ya samu zomowa babban likitan dayake cikin manyan doctors na duniya tareda tarin dukiya me yawan gaske daya zamo babba sbd zaadens da suka tsaya masa,

Jannah Zad itace rai da Zad sukafi so f

iyeda komai da suka mallaka a duniya...

Dago idanuwansa yayi Ahankali ya saukesu akan Sayd sbd a duka bayanin baiji wani abin daya shafesu ba bayan maganar ciwon zuciyar datai kama data tasa 'yar dan haka ya zubawa sayd idanuwansa yana jiran bayaninsa w

anda bayani kawai yakeso gamsashe batareda wani kwana ko daya ba.

#MAMUH

#BEST REVENGE

#BEST LOVE

#CRAZY LOVERS

#SELFMADE BILLIONAIRE

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500

mamuhgee

A DUNIYATA 500

Huguma

AJIYA A DUHU 500

Billyn Abdul

KIRJIN ME

HANKALI 500

Miss xoxo

Pay at

0022419171 AccessBank

Maryam sani gummi

Shedan biya

09033181070

Or mtn vtu at

09032345899*_Arewabooks@Mamuhgee_*

41

*KALPANAH COLLECTION*

08105064494

Shin ke daliba ce ko kuma uwa wadda har yanzu bata daina

rokon urgent 2k a wurin yan uwa da kawaye ba,tou nesa tazo kusa domin kuwa na kawo miki maganin matsalarki,domin kuwa *Kalphanah Collection* ta shirya tsaf domin taimaka wa duk wani dan kasuwa ko kuma wanda yake son fara kasuwanci.A *Kalphanah Collection*

muna saida kaya kama daga Jaka,Takalmi,Atamfa,Laces,Kayan yara da kuma kayan kitchen.Wani abun mamakin ma muna saida kayan mu ga masu siyen daya ko kuma sari,ga waenda basuda jari ma mun tanadar masu hanyoyi daban daban da zasu fara neman na kansu.Hajiya

kina gida kwace zaki dinga jin saukar kudi a asusun bankin ki.Ga musu fuskantar qalubale a kasuwancin su kuma an kawo muku sauqi domin kuwa an bude muku group dinku da zaku dinga tattauna matsalolin ku.

https://chat.whatsapp.com/IyDlSVdw1rDIlCNNQMel68

Kedai idan kin shirya ki dannan link din nan na kasa domin shiga group dinmu ki ganewa idonki kunsan ance gani ya kore JI

Karki yadda ki wuce bakiyi joining group din nan ba domin kuwa yanzu sallah tana qaratowa ko bakiyi kasuwanci ba zaki siya domin a

mfanin ki na yau da kullun kuma ko baku buqata yanzu nan gaba zaku iya neman ta.

Siyen na gari maida kudi gida.

08105064494

************

Sayd daya cikin tsananin shock da mamaki da sauri ya karbi ipad din ya zubawa hoton Jannah idanuwansa wadda she

karunta suke kusan daya dana Ummitah..

Hannuwansa na rawa ya ciro wayarsa cikin jikinsa ya saka kiran Latif wanda a cikin bayaninsa yace masa a ranar da akai aikin Ummitah doctors din hudu ne ba uku ba kuma yaga dayan bayan ya fice daga gurin yana cire

facemask kuma yaji nurse data biyo bayansa ta kirasa da Dr Zad sedai baiga fuskansa ba.

Cikin sauri yacewa fahad

"Turawa Latif hotunan familyn Zaadens gava dayansu yanzu"

Daukan wayar Latif yayi take sayd yace masa

"Duba ga sako nan fahad ya tu

ro mata kaga idan akwai dr Zad din ranar haihuwan Ummitah"

Kalman data saka AZIZ rufe idanuwansa kenan yana hadiye shirunsa gaba daya tareda wani irin ciwo da radadi suka gama shigewa cikinsa ya bude baki da fushi yace

"Meyake faruwa nake tambaya ana

n"

Bude baki Sayd yayi zaiyi magana Latif ya kira AZIZ yace ya ajiye wayar ya saka handsfree.

Cikin tabbatarwa Latif yace

"Tabbas naji an ambaci dr Zad amma wlh banga fuskanba sedai koma waye a cikinsu ne sbd su kadaine Zad"

Kashe wayar sayd ya

yi yana jin kaman zai fasa wayar hannunsa sbd rashin samun tabbacin ganin fuskan.

Cikin wani irin matsanancin ciwo da radadin zuciya ya dago ya kalli AZIZ AY LIMBA ya bude baki da tsananin rauni yace

"A ranar da Ummitah ta rasu gurin wankanta akwai d

inki a kirjinta setin zuciyarta sabo wanda a ranar ta samesa sbd koda muka kaita asibiti nine nai shirinta na tabbatarda babu wannan dinkin a kirjinta,

A cikin likitocin da sukai mata aikin haihuwan babu gynecology doc ko daya a cikinsu,

Babu aikin hai

huwa a cikinta wanda shima na bincika idan har babu aiki a ciki to tabbas da kanta ta haihu ba aiki akai mata ba,to amma bayyanar aiki a kirjinta shine abinda nakeson sani,

A asibitin zadeens akai mata a aikin,

Likitocinsu ne,

A familyn a akwai me ciw

on zuciyar da bamu san waye ba,

Meyesa suka dauki nauyin kai mata gawarta kyauta har gida?

Meya hada haihuwanta da likitocin zuciya?????..........

Tsit gurin ya dauka sbd mutuwar tsayen da fahad yayi da fahimtar inda zancen ya dosa,

AY din kuwa aji

yan zuciya ya sauke me sanyi kansa na kwakwalwansa na kasa daukan me Sayd din ke kokarin fada sbd bame yiyiwa bane har abada hakan sedai kuma baya wasa ko kadan da abinda aka ambaci sunan Ummitah a cikinsa koda kuwa bata raye dan haka ya kallesa a natse ya

ce

"Ina dayan dr din da kake maganar?

"Yana jos"

"A shirya tickets zamu kai masa ziyara lokaci yayi da zansan a hannun waye UMMITAH ta cika da time data rasu" ya fada kai tsaye yana miqewa yabar dakin kirjinsa na wani irin riqewa amma kuma lokaci

yayi da fuskanci abinda yaketa gujewa shekara da shekaru musamman a yanzu da wannan unbelievable lamarin yake shigowa a lamarin.

Sayd da babu abinda yakeso din kaman ya gansu a Nigeria din daman sbd ya fuskanci Dr ismail da kansa take ya kalli Fahad yac

e

"Ayi clearing gaba daya appointments na AY din da schedules nasa na satin gaba daya har zuwa wani satin"

Yes" fahad ya fada yana juyawa shima ya fice,

Sayd din kuwa take ya kira ya saka akai musu booking ticket din tafiya ba bata lokaci.

Ma

ma batasan da tafiyarsu ba sai washe gari kawai kai tsaye taji tafiya AZIZ din zaiyi Nigeria da bayason zuwa tinda Ummitah ta rasu dan haka tasan koma menene zai kaisa yanada matiqar mahimmancin gaske wanda kilama ya shafi Ummitah ko falaq ne dan sune kada

i zasu sakashi zuwa Nigeria lokaci daya.

Cikin kwana biyu aka gama komai jirginsu ya saika Nigeria.

A lagos suka sauka kuma anan zasu zauna dan bayajin zai iya zuwa abuja dan haka lafiyayyan Lodge ya sauka wanda securities dinsa kadai da tsaron gur

in zakasan ko masu kudin sai wainda suke amfani da dollars ne ke suke gurin.

Koda suka iso lagos din a daren shima latif jirginsa ya sauka a lagos daga abuja dan haka bai samu ganin AZIZ dinba sedai Sayd sai washe gari Sayd ya shiga dashi inda AZIZ din

yake ya gaidasa cikeda farin cikin ganinsa da tsananin girmamawa da kaunar dayake masa.

Abinda ya kawosu shi Sayd yake dan haka kwanansu daya a lagos ya nufi jos tareda Latif daman tin kafin su iso Nigeria Latif yaje jos din yayi confirming address di

n Dr ismail ya kuma gansa ya tabbatar da shi dinne dan haka koda suka isa jos lafiyayyan masauki su sauka sai washe gari suka isa gidansa inda suka tarar dashi zaune daure a kujera baya iya komai.

Dayake ansan ana zuwa dubasa duk da ya dauki shekaru a h

akan shiyasa kai tsaye suna fadar gurinsa suka taho dubasa aka shigo dasu har palonsa yana zaune abin tausayi kan kujera an dauresa da belt sbd fadowa dayake.

Sayd ne a gaba sai Latif yana bayansa suka shigo da sallama....

Idanuwansa dake rufe ya bud

e ya saukar dasu akan Sayd wanda ya sauya gabaki daya sedai kuma kamanninsa basu sauya daga Idanuwansa ba sbd dasu yake kwana a ransa dasu yake tashi sbd sanadin komai da akai musu yake tamkar matacce yanzu rai ne kadai banbancinsa da matacce dan shima mut

uwar yake fada tafi masa akan azabar dayake ciki.

Wasu zafafan hawayene masu tafe da radadin dayake zuciyarsa da danasanin da batada amfani suka gangaro gefen Idanuwansa yana kasa kallan fuskan Sayd din wanda shi kuma hawayen dr ismail din da kallan day

a kasa masa ya saka zuciyarsa fara karyewa dan abinda yake shirin tabbata...

Zaunawa sukai suna mai masa sannu da fatan samun lafiya sedai kwata kwata Dr ismail din ya kasa kallan Sayd sai hawaye yake zubarwa.

Shiru sukai babu wanda ya iya cewa komai

saida matarsa ta shigo Sayd din ya kalleta yana mata tambayoyi akan yanayin jikin nasa tana masa bayanin babu kowane irin cigaba daga yanayinsa.

Nunfashi Sayd din ya sauke ahankali yace

"Zamu dauki nauyin nema masa lafiya tin daga Nigeria har zuwa

qasashen da sukeda manyan likitoci idan hakan zai muku"

Ya qarasa maganar yana kallan Dr ismail din wanda ya fashe da kuka yana rintse idanuwansa baki a juye ba damar magana.

Matarsa saurin kallansa tayi kafin ta dawo da kallanta kan Sayd din wanda

yake kallansu cikeda yanayi na buqatan amincewansu.

Numfashi ta sauke tana jin farin cikin hakan sbd lura da Dr ismail din ya gane koma su din su waye sedai kukansa daya sakata jin jikinta na mutuwa.

Godia tayi musu cikin tsananin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login