Showing 198001 words to 201000 words out of 363627 words
ma haka suka wuni a aikin wahalar baji ba gani ba hutu sai dare suka samu hutu,
A hankali suka fara shude kwanaki
a cikin gurin wanda babu komai sai aikin bauta da wahala,
Tinda suka shiga basu taba fitowa ba sbd babu inda zasu idanma sun fito din,
Ahankali Ummah ta shiga cikin aikin sosai sbd bata iya kallan jannah cikin wahalar datai mata yawa ita kadai,
Da
farko Jannah bata bari sai daga baya ganin Umman bata iya bari hakama ta fita iya komai sai ya zamana tare suke komai,
Ita kanta madam din dataga Ummah na aiki sosai saita dan qara musu kadan akan abinda take bawa jannah duk da ba yawa.
Duk yanda Jan
nah zatai ta hane a gane Ummah ba lafiyayya bace tana yi sbd batason kowa yayi mata kallan mara hankali ko makamancin hakan,
Tana kulawa da Ummah sosai tana kiyaye dik abinda zai tayar da ciwonta,
Bata wasa da lulurar umman ko kadan,
Itama Umman ta
nata bangaren duk dare bata iya bacci kwana takeyi kulawa da Jannah bata barin sauro ya cijeta shiyasa take kwana tana kulawa da tattalinta kamar qaramar yarinya.
Sauran abokan aikinsu basu san Ummah ba asalin mahaifiyarta bace sbd kaunar da tattalin da
take mata shiyasa suke dan respecting Umman kadan.
Tin jikinsu bai saba da wahala da yanayin gurinba har suka saba jikinsu ya sabu da wahalar sbd suna cikin wata na biyu a gurin.
Lokacin da suka shiga wata na uku a lokacin ne albashin da suka samu
yakai abinda suke nema na tafiya gida dan haka Jannah taje ta sanar da madam tafiya zasuyi.
Da farko kamar bazata barsu tafiya ba amma ganin yanda jannah din tai wata irin rama da duhu sosai ya saka tausayinta cikata sbd yarinyar tabbas tana buqatar hut
u da kwanciyar hankali koda a kauye ne indai zata samu nutsuwa.
Sallamarsu tayi ta tattara dan abinda zata basu ta basu sukai godia cikeda girmamawa suka hada kayansu akan washe gari zasu tafi.
A daren jannah bata iya bacci ba sbd bawa kanta karfin z
uciyar iyawa,
Basuda komai,
Basuda abinda zasu zaunar da kansu a birni sbd a zero suke yanzu abincin da zasuci ma basuda hanyarsa matiqar bata tafi kauyenba ta nema danginsu dad din ba ta samar masu mafakar da suna fitowa zasu je su fake su dora sabuwar
rayuwa daga can ba to tabbas suna fitowa garari da wulaqanta zasuyi dan haka ta zabi komawa kauyen ta karbe dukkanin zafi da tsangwamar da zaayiwa su Dad din kafin fitowarsu ta yanda koda zasu zo ta gama gyara alaqarta da dangin bazasu tozartasu ba idan su
kaxo.
#MAMUH
ZAFAFA BIYAR
KALBIM 500
mamuhgee
A DUNIYATA 500
Huguma
AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul
KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo
Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi
Shedan biya
09033181070
Or mtn vtu at
0903
2345899*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
97
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop
💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina
son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce ma
ce ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
*************
Da wannan ta tashi da sassafe suka shirya tin asuba sukai wanka sukaci abincin data samar musu tin dare koda karfe 7 na safe tayi sun fito bayan sunyi sallama da abokan Aikinsu.
Mota suka tara
suka shiga zuwa tasha,
Takardar hannunta ta sake budewa tana karanta sunan porthcrt da sunan wani kauyen dayake da nisa sosai a cikinsa wanda batama san ya zatai pronouncing nasa tareda sunan familyn Mahaifiyarsu Dad duka a jiki harma da sunanta ita kan
ta mahaifiyarsu dad din da hotonta danasu dad din.
Ajiyar zuciya ta sake saukewa ahankali tana lumshe idanuwanta tareda maida takardar jakarta ta rufe.
Suna isa tasha babu bata lokaci akai directing nasu ga motar da zasu shiga tareda biyan kudin koma
i suka shiga suka zauna daga ita har Umman jikinsu a mace.
Basuyi zaman mintina Arbain ba motar ta cika aka rufe koina motar ta tashi ahankali ana musu Allah ya kiyaye suka fita ta lumshe idanuwanta ahankali tana kwantawa jikin Ummah wadda ta fara shafa
bayanta ahankali itama tanajin kamar tinaninta zai dawo sbd damuwa da nauyin kirjine ya rufeta sedai bata iya cewa komaiba.
Tafiya sukai sosai kafin suka fice daga abuja suka kama hanya dakyau.
Tinda suka hau hanya bata bude idanuwanta ba har sukai
tafiyarda ta dauki awanni tukuna ta bude idanuwanta da sukai jajir tana dagowa daga jikin Ummah datai shiru ta zubawa fuskan jannah din idanuwanta cikeda kulawa da tinanin da batama san tanayi ba.
Kasa kallan Umman jannah tai sai kawai ta maida kanta ta
sake kwantarwa jikinta tana godewa Allah daya kawo Ummah rayuwarta dan a yanzu batama fatan yan uwan umman su bullo takoina tana fatan Ummah ta zama tata har mutuwa.
Tafiya me tsayin gaske sukai wadda takaisu ga isa dare sosai dan haka ko bayan isarsu
a tasha suka kwana cikin baqin dake kwana tasha tinda asuba aka sakasu motar kauyen da zasu tafi me tsananin nisan gaske.
Ummah kadai ta siyawa Abinci wanda itama umman bata wani iya cinsa ba sbd sun galabaita,
Jannah jin hankalinta na tashi tsoro da f
argaban abinda zata iya tararwa na ciketa dan haka tayi shiru a sanyaye tana kallan hanya.
Sai yamma lis suka isa kauyen wanda aka ajiyesu a farkonsa,
Drivern da kansa ya hadasu da yan gari tareda fada musu gidan da zaa kaisu.
Kallansu mutane dake
gurin keyi suna mamakinsu sbd ganin yanda dukkaninsu sukai laushi sosai sukai zuru zuru musamman Jannah da bata taba tafiyar mota me tsayi ba hakama a rayuwarta bata taba xuwa kauye ba batama san rayuwa a daji shine kauyenba sai yanxu data samu kanta a da
jin Allah me nisan gaske.
Tsoro da fargaba me tsananin gaske ke shigarta tanajin kaman bazata iyaba amma kuma sbd samarwa ahalinta mafakar rufin asiri dole ta iya.
Tafiyar qasa suka fara a wahale cikin kishirwa da gajia amma hakanan suka daure suka r
inga bin wanda aka hadasu dashi yana tafiyarsa ba gajiya ko kadan sbd sabo.
Gap da magrib suka isa cikin garin qauyen wanda sai a lokacin suka ga mutane sosai da gidaje sosai kowa na harkan gabansa,
Fulanin daji ne kaf kauyen wanda kana kallansu ba tam
baya zakasan kusan kowa a garin bafulatani ne baqaqe da farare gasunan kowa harkan gabansa yake.
Kallansu akeyi cikeda mamakinsu sbd ana ganinsu anga baqin da suka taho daga nesa.
Wani gida me girma da sashe sashe suka nufa har kofar gidan matashin y
a kallesu yace
"Ga gidan nan ku shiga sai kuyi bayani"
Dagowa jannah tayi ta kallesa da idanuwanta da bakinta daya bushe qayau ta budesa tace
"Mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi"
Kallanta yayi ya washe bakinsa yana cewa
"ba damuwa ai da
ganinku na gida ne"
Sallama ya kwada a cikin gidan yana ambatar sunan abokinsa Garba dayake gidan.
Garban ne ya fito daman yana kusa zai fito kenan.
Washe da baki ya fito yana kallan bellon kafin ya maida kallansa kansu jannah dake tsaye a rakube.
Zuba mata idanuwansa yayi sosai yana kallanta cikeda mamaki kafin ya maida kallansa kan Ummah ya juyo gurin Bello cikin fulatanci yace
"Daga ina?
Su waye?
Waye suke nema?
Kallansu bellon yayi shima cikin fulatanci yace
"Daga binni suke nan g
idan suka taho ka shiga dasu ka kaisu gurin kawu Modibbo mana.
Garba dayaji daga binni suke da sauri yana washe baki ya kallesu yana cewa
"Barkanku da zuwa,
Bismillanku"
Juyawa yayi ciki dasu yana cewa bello ya jirasa.
Suna shiga gidan jannah
ta sake riqe hannun Umma suka nufi ciki har babbar tsakar gidan wanda kowa ya fito aka fara kallansu cikeda mamaki.
Modibbo ne babba a gidan kuma me fada a ji kuma mafadaci dan haka kowa hanyar dakin Modibbon ya kalla Garba na wucewa dasu can yana sake
musu sannu bakinsa a washe.
Modibbo ne ya fito sanye da Babbar rigarsa datake zuba qamshin ajiya maana qamshim rima da wularsa da shape dinta yafi kama da kofin silver fari tas dashi.
Yana ganinsu sake gyara zaman hularsa yayi yana kallan Ummah ita d
atake babbah sai yaga ta sauke kallanta qasa.
Jannah ya maida kallansa kanta yana cewa
"Garba su waye?
Daga ina kuma?
Sake washe baki garba yayi daidai nan kawu Isiya da kawu jibo suka iso suna kallansu jannah din dukansu baki a sake.
Garba ya
ce
"Modibbo baqi ne daga birni nan gidan suka taho"
Maida kallansa kansu yayi yace
"To baqi barkanku da zuwa,
Daga ina?
Numfashi jannah ta sauke ahankali ta bude bakinta jikinta na mutuwa gabaki daya tace
"Sunana Jannah Zadeen jikar Hajiya
Zeenah Zadeen.....
Tsit sukai gurin gabaki dayansu tareda kallan junansu cikeda mamaki a bayyane kafin Modibbo ya hade fuska yana cewa
"Kikace jikar haj zeenah??
Yar Mahmoud ko Ahmed?
Sake sunkuyar da kanta tayi ahankali ta bude baki tace
" '
yar Ahmed"
"Da wane shedan zan iya gane hakan??
Hannunta ta zira a jakarta ta ciro hoton kakarta dasu Dad ta miqa masa.
Karba yayi su kawu isiya na sake matsawa da sauri duba hoton suma cikeda mamakin abinda ya kawota gurinsu.
Zubawa hoton idan
uwansu sukai suka kafawa yar uwarsu idanuwansu sbd da mahaifin daya haifesu su ukun da haj zeenah din uwa daya uba daya suke.
Shiru sukai kafin Modibbo ya dago ya zuba mata idanuwansa yana karantar kamannin Mahmoud da Ahmed daya sani tin suna yara suka
taso tare amma tinda mahaifinsu yayi kudi ya bar qasar dasu basu sake nemansu ba haryanxu.
Cikin nutsuwa da sanyi yace
"Ina su Mahmoud da Ahmed din suke??
Dago jajayen idanuwanta tayi ahankali kai tsaye ba kwana kwana sbd batada karfin tsayawa boy
e komai sbd so take su karbeta a yanda Allah ya maidasu tace
"Daddy Mahmoud ya rasu,Mimi ta rasu,
Dad da sauran yan uwana biyu suna gidan yari sai bayan shekara guda zasu fito"
Da sauri dukkaninsu suka kalleta kawu isiya na cewa
"Mahmoud ya rasu?
?
Kasa cewa komai tayi.
Jin hakan ya saka Modibbo cewa a kaisu jannah din dakin Yakumbo su huta a basu abinci da nono me dumi su sha su huta da kyau tukuna ayi magana daga baya idan ta nutsu yanda ya kamata.
Dakin yakumbo aka kaisu matan gidan da
yara na musu sannu da zuwa cikeda mutuntawa da farin cikin ganin jikar zeenah ce yau a gidan.
Kasa cin komai jannah tayi wanka tayi da ruwan sanyi a bandakin da baida rufi take sanyi da zazzabi suka rufeta.
Daqyar yakumbo ta sakata shan sabuwar madar
a me dumi wadda ta dan taimaka mata amma sallah kawai tayi ta dunqule guri daya tana rawar sanyi idanuwanta na tsiyayo da hawaye masu dumi.
Ummah ma taci abinci tayi wankan amma itama zazzabin ne ya kwantar da ita.
Washe gari duk yanda ake tinanin ci
won yabar jannah kasa barinta yayi dan haka tsoro ya kama su Modibbo kawu isiya yace karta mutu su tattarata su sallemeta yakumba tace aa.
Ummah ta warware ita dan haka tafara kulawa da jannah din wadda ta rafke lokaci daya ta sake komawa kalar tausayi.
Satinta daya ana jinyarta anata maganin hausa kafin tafara warwarewa ta dawo daidai.
Sai a lokacin hankalinsu kawu ya fara kwantawa harma suka zauna da ita ta fada musu komai sedai ta boye cewan da sanin iyayenta akai komai tadai sanar dasu zuciyar
da aka kawo musu ashe ta kisa ce bata hanyar gaskia bane batareda saninsu ba wanda hakan ne ya saka rufesu shekara daya.
Su kawu Modibbo dasu kawu isiya da kukansu da komai na tausayin yan uwansu wanda kukansu kadai ita jannah tsoro ma ya ringa bata sbd
tamkar kukan yayan aljanun dare haka suka ringa matso hawayen suna darzar idanuwa kaman masu gasar kuka sbd ta gani idan su Dad din suka fito ta fada musu da waye da waye sukai kuka sbd su samu rabo me tsoka sbd basu yadda da kakaf komai aka kwace musu ba
dan kamar bame yiyuwa bane dan haka zasu kula da ita kamar kwai har su Dad din su fito su samu suma su lasa arziki.
Bangaren Asalin kakansu na gidan daya dade da mutuwa Modibbo yace samarin gidan su saka karfi suyi aikin qasa su gyara daki biyu ne da b
andaki sai madafa a gyarawa su Dad din kafin su fito.
Su Garba da fodio da Idris sune matasa samarin gidan masu ji da lokaci tini suka fara aikin kowa da abokinsa ake aikin sbd kowa da kudirinsa na shirin dawowan su Dad din rayuwa a cikinsu da santaleli
yar buturiyar 'yarsu data zama tamkar bayyanar Zinariya a kauyen.
A cikin gida kuwa kamar jannah bazata iya rayuwar kauyenba sai kuma tafara sabawa sbd kauna da kulawa datake samu tako ina a gidan harma da wajen gidan wanda ya saka mata farin jini.
A
cikin gidan akwai budurwa tsararta 'yar kawu isiya wadda mijinta ya rasu ta dawo gida da yarinyarta 'daya itace tafara zama abokiyar hirarta.
Fatma itace tafara fita da ita garin da gurare daban daban tin tana tsoron mutane harta saba tana shiga cikins
u sosai,
A gidan kowa ta kansa yakeyi dan haka tana ganin lokaci yafara ja ta fara koyan sanaar saqa da siyarwan da Fatma keyi itama tafara ita kuma Ummah tana taya matan su Kawu harkan nono da manshanun da sukeyi dan haka itada Ummah sai ya zamana suna
dan samun abinda suke kulawa da kansu basu bari sun zamarwa kowa lalura me gajiya ba.
Kaunar datake tsakaninta da Ummanta ya wuce dukkanin tinanin da mutanen gidan dana waje keyi akansu sbd Ummah babu abinda takeyi a rayuwarta yanzu bayan duk abinda za
ta kula ta tattala rayuwar Ummijan dinta,
Duk aikin wahalar datakeyi a gidan sbd jannah ne hakama duk daren Allah kwana takeyi kulawa da jannah dinta harta saba bata iya bacci sauro bin jannah,bata iya bacci idan jannah na cikin damuwa bata iya komai said
a jannah dinta.
#MAMUH*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
98
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop
💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7
Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable
price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu
shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.
**********
A bangaren jannah a yanzu data samu kwanciyar hankali da nutsuwar datake jin babuta sai a kauye da babu tashin hankali sai rayuwar rufin asiri,
Ummah ce hasken idaniyarta da zuciy
arta,ummah ce karfinta,Ummah kuzarinta,duk abinda takeyi tana yinsa ne sbd Ummah dan haka a ranta takejin Ummah uwartace da bazata iya rabuwa da itaba har abada dan haka ma ta yanke shawaran hada ahali da Ummah daga ranar da Dad dinta ya fito.
Angama gy
ara dakunan da zasu zauna dan haka itada Ummah suka fara komawa da Fatma wadda take takure a rabe dakin yadikkonta.
******lokaci yafara tafiya sosai sbd shekara ta kusa cikewa dan haka lissafin su kawu sai ninkuwa yakeyi shi kawu isiya har batan lissa
fin abubuwan da zaiyi yakeyi,
Shikuwa Modibbo bature yakeda niyar binsu ya zama duk inda zasu kafarsu kafarsa shima.
Su garba kuwa shirin sosai sukeyi na yanda zasu tarbi ahalinda zasu iya zama sirikansu dan kuwa dadi da wuya zasu tsaya bazaa bar kauye
n da jannah ba sai waninsu ya aureta ko zaa tafi kasar wajen dasu suma.
Rayuwa tayiwa jannah da Ummah daidai babu me damuwar komai a cikinsu saita kewan nasu idan ta taso musu,
Ciwon Ummah yana dadewa bai tashiba idanma ya tashi jannah rungumeta take
yi duk dukan dazai mata bata iya saketa haka zata ringa hadiyewa cikim azaba harda rauni da komai bata iya rabuwa da ita har saita dena ta fara kuka shine zata rungumeta susha kukansu tare su gama batareda wani yasan halinda suke ciki ba.
Jannah Zad
kaman yanda rayuwarta ta sauya ita kanta ta sauya tako ina,
Rama da quncin data fito a cikinsa ya tafi,
Jikinta ya dawo daidai bame qiba ba ba kuma ramammiya ba,
Halaye da dabiunta da yawa rayuwa ta sauya mata su,
Kaman yanda komai nata ya sauya hatta
sunanta ya sauya sbd a yanzu kaf garin ba jannah suka santa ba da sunan da Ummanta ke kiranta aka santa dashi wato UmmiJan,
Rayuwa ta koyar da ita darasi,
Rayuwa a cikin mutane daban daban ya koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa tareda sanin meye rayu
war a yanzu.
Ahalin Modibbo sun kaunace ta a lokacinda batada kowa batada komai,
Sun karbeta hannu bibbbiyu batareda gudunta ba sbd iyayenta sun gujesu dan haka har cikin ranta a yanzu take kaunarsu sbd a yanzu ne ta gane me dangi da yawa suke nufi,
A kauye suke suke rayuwa a cikin dajin da babu wuta babu ruwa amma a hakan tasamu nutsuwar da bata samu ba a can inda daular take dan haka take rokon Allah ya bawa ahalinta ikon iya rayuwar da zasu taho su tarar anan din.
Babbar muguwar halin da gida
n suke dashi shine tsananin son abin duniya wanda a tsakanin kawunnin nata bata san wanne yafi wanne kwadayi da son abin duniya ba.
********BAYAN SHEKARA GUDA
Ayau itace ranar datafi kowace rana a rayuwar UMMIJAN sbd itace ranar da zata isa abuja dan h
aduwa da mutanen da sune rayuwarta sune rabin jikinta