Showing 39001 words to 42000 words out of 61676 words
Asibiti ya bukaci su wuce da ita shi kuma ya na nan zuwa. Da taim
akon inna Tala suka saka Deena a mota sai dai ko da wasa Shukura ba ta yi gigin binsu ba domin ta san irin
ƙ
urar da zata tayar.
Komawa ta yi ta zauna tare da kwashewa da dariya. "Da ni kuke zancen. Ai duk jinjirin da ya hana
uwarsa bacci shi ma ba zai runt
sa ba. Deena na San aurenki da Hisham ko daga sama aka sauro shi kun rabu har abada. Na gama da wannan matsalar saura ta Munzali kai ba zan zubar da cikin nan ba zan haifesa ko don in samu malafa da zan ci gaba da cin dukiyata da tsinke. Zuwana gida ya yi
mini matukar amfani domin Mama ta nusar da ni abin da na kasa ganewa." Mi
ƙ
ewa ta yi ta shige daki.
A can asibiti kasancewar ta mahaifin Deena ce ba taba lokaci suka amshesu a hau ceto rayuwarta. Alhaji Munzali da Mommy ne suka yi wa asibitin dirar mikiya.
Mommy sai faman share hawaye take, addu'ar ta
ɗ
aya ba dai mahaifin Deena bane ya tunzurata ta je ta yi wa Hisham rashin kunyar da ya yi mata bugun mutuwa.
Ta glass
ɗ
in
ɗ
akin ya leka ya hango yadda Hisham ya canza mata kamanni. Ransa kara
ɓ
aci yayi waya ya
fiddo tare da kanga ta a kunne. "Yawwa kun kamo shi? Ku tsare min shi ko da wasa kada ku kuskura ku bayar da belinsa.
Aje wayar Dpo ya yi tare da kallon Hisham da ke ta faman latsa wayarsa. "Ka bayar da wayar hannunka da duk wani abu da ke jikinka za mu
saka ka a cell. Anya kuwa ka san laifin da ka aikata?"
Wayar ya mike tare da ci gaba da tauna cingam "Matata na buga kuma ko gobe ta maimaita abin da ta yi min nima zan sake zibgarta"
"A gaban hukuma kake ka daidaita kalaman bakinka. Sannan kai ba ma kai b
ane na taba ganin a birnin Kebbi?"
Shiru Hisham yayi domin ya gaji da wannan wasan yaran da ake masa. Kullum sai ya samu wa
ɗ
anda ke ce wa su ganshi bayan ya san shi bai taba zuwa garin ba ko a mafarki. Haka a ka tattare shi aka watsa bayan Cell. Sai dai ka
fin a saka shi ya kira Yazid ya sanar da shi halin da ake ciki.
A rikice Yazid ya nufi station din duk iyakar kokarinsa ya yi amma abu ya faskara. Dole ya nufi gidansu Hisham duk da gabansa faduwa ya ke bai san abinda zai biyo baya ba. Ya yi sa a ya iske
Alhaji a cikin falon sai dai 'yan kame-kamen da ya fara yi sune suka saka Umma ta gane babu lafiya. Fuska Alhaji ya hade domin ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta
ƙ
o
ƙ
i.
"Yazid na san ruwa baya tsami banza. Ba zaka zo gidan nan babu wani dalili ba don haka
fada mini Me ya faru?"
Shuru yayi tare da sosai keya ya sunkuyar da kansa a kasa.
"Dama.... Dama dai... Wato Abba Hisham ne suka samu matsala da Deena har ta kai ya sumar da ita domin yanzu haka maganar da nake maka. Ta na asibiti shi ne mahaifinta ya saka
aka kama Hisham, na je amma sunki bayar da belinsa Shi ne na ce ko ka saka baki tunda lamarin duk family
issue ne, bai kamata a ce ya
ƙ
ullesa shi ba."
Alhaji bai bari ya karasa maganar ba ya dora da fadar.
"Ka ga Yazid ku kiyayeni! Da mutuncina a garin na
n ba zaku zubarmin da shi ba. Maganar In je police station bata ta so BA tsuntsun da ya ja ruwa. Shi ruwa ke duka don haka babu inda zanje"
"Alhaji ai kai ka tsaya ba shi amsa. Kamata ya yi ya je ya tunkari Mahaifinsa domin ai shi ne ya hada auren. Ita da
ma rayuwar bariki me za a tsammata in banda haka, siriki ya saka a kulle masa sirikinsa Allah ka tsare mu da rayuwar bariki."
Hajiya ta karasa maganar Farida dake gefe ta amsa da amin.
Umma baiwar Allah duk yadda hankalinta ya kai ga tashi ta kasa tsoma b
aki a cikin maganar.
"Abba da dai an duba abin da nake fada ko ba komai a duba lamarin"
"Kai fice mana daga gida kafin ina yi mummunar sa
ɓ
a maka"
Hajiya ta mike fusace tare da nuna masa hanya.
Babu yadda ya iya haka ya mike jiki a sanyaye da sauri
Umma ta bi bayansa.
"Yazid ba sai na maka dogon bayani ba kasan komai in ma Baka sani ba yanzu ka ga komai da idanunka. Da wani zai iya shiryar da wani tabbas da na saka Hisham ya koma yaron kirki da ba a ci mutumci na da nasa ba a cikin gidan nan."
"Kiyi
hakuri in Shaa Allah zan duba inga abin da za a yi amma Hisham ba zai kwana a hannunsu ba In Shaa Allah"
Gaba ya yi da sauri ganin hawaye sun ciko idanun Umma.
Ya na fita rurin da wayarsa ta fara ya saka shi tsayawa ya dauka.
Shukura ce don haka bai boye m
ata komai ba ya sanar da ita halin da ake ciki.
Suna gama wayar jifa tayi da ita saman gadon tare da zabga uban tagumi.
"Ni Munzali zai tonawa asiri. Lokaci ya yi da ya kamata ka gane mijin
ɗ
iyarka nake aure"
Wayarta ta rarumo ta nemo numbersa. Kira
ɗ
aya y
a dauka duk da yana cikin asibitin amsa mata yayi da haduwar da ta bukata.
Kai tsaye gidan gonarsa ya nufa domin da wannan damar ce zai yi amfani ya zuba mata maganin da Boka ya ba shi.
Ba a dauki dogon lokaci ba sai gata ta iso.
Ganin yadda ya ke haba-hab
a da ita ba karamin mamaki ta yi ba. Saboda ta san ba su yi rabuwar
lafiya ba.
"Alhaji ni fa ba wannan ba. Waye ka saka aka kama yau"
Mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce shi. Kada dai a ce tunanin da ya ke ne ya tabbata. Bai karasa tunanin ba maganar Shuku
ra ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula.
"Abin da baka sani ba shi ne nake yau zan fada maka. A kan Wanda ka saka aka kama wato.mijim Deena
ɗ
iyarka Mijina ne na sunnah"
Tamkar wanda ya zauna saman tsinin Mashi ba shiri ya mike tsaye.
"Wasa kike yi
amma?"
"mun ta
ɓ
a irin wannan wasan da kai. Ni ba ma wannan ba ga gaggauta kira a sakar min mijina Indai kana so amanarmu ta ci gaba da gudana"
"Shukura amma kin Shammaceni a tunanina kin jima da rabuwa da wannan yaron. Ashe shigo-shigo ba zurfi kika yi mi
n? Yanzu ya kike so in kalli diyar dana haifa wannan wace irin kazamar rayuwa ce muke yi"
"Oh! Da can baka san muna kazamar rayuwa ba sai yanzu? Ni fa ba dogayen surutai na zo muyi ba zaka saka a sake shi?"
"Ke kinsan babu abin da za ki nema ba tare da na
yi miki shi ba. Yanzu a gabanki zan saka a sake shi in dai hakan zai faranta miki."
Waya ya fiddo kai tsaye ya kira Dpo.
"Na aikata abinda kike bukata"
"Shi kenan na ji dadi. Abin da nake so in Samar da Kai Zan zubar da cikin nan domin banga amfaninsa ba t
unda baka bukatarsa"
"A'a ki barshi Indai domin ni ne ina so ki haifamin jinina"
Ba ki a sake ta ke
ƙ
are masa kallo anya kuwa ya san abin da yake fada? Ko dai mafarki ta fara daga zaune?
" Kina mamaki ko? Da gaske nake ina son
ɗ
a ko
ɗ
iyar da zaki
haifamin. Kada ki wani damu"
Mamaki ya kasa sakin Shukura ta rasa gane shin da gaske ya ke ko kuma mafarki take yi.
Ruwan lemun da ta gani gefenta ta dauka ta kurba. Wani irin dadi ta ji ya yi mata don haka kai ta
ɗ
aya ta shanye shi tass!
Dariyar mugunta A
lhaji Munzali ya saki lokacin da ya ga ta shanye ruwan lemun, tabbar burinsa ya gama cika sai dai ya jira lokaci....
Meenat A 'Yandoma
08133562798
MASU BUKATAR SAURAN PAGES
Ɗ
IN SU SHIGA NAN
👇👇👇👇
PG 45&46
NA KUDI NE DOMIN BIYAN KUDIN LITTAFIN 500 TA W
ANNAN ACCOUNT DIN 8133562798 OPAY AMINA ABUBAKAR
TALLAH
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MA
TA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason ji
kinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take k
i tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA
👇🏻
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara
Saloon
Kunshi na salatap Dana zane
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a
ko Ina ba tare da wata matsala ba
🙏🏻🙏🏻
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA
💯
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu.
...Wani tsam! Ta ji ilahirin tsikar jikinta ta tashi. Ajiye kofin tayi ta na
jin bakon yanayi a tattare da ita. "Amma me ya sa ka ce ka hakura? Bayan da farko ce wa kayi a zubar."
Dariyar da bata kai zuci ba yayi ya dora da fadar. "A kowane lokaci dan adam cikin canza shawara ya ke saboda haka nima shawara na canza zan amsa duk abi
nda kika haifa. Wa ma ya sani ko namiji ne za ki haifa mini"
Ya karasa maganar cikin sigar kwararriyar yaudara. Mi
ƙ
ewa ta yi tunda bukata ta biya ya kamata ta koma gida kafin Hisham ya dawo. Bai hanata tafiya ba saboda shi ma kwanciyar hankalinsa ce ta je
gidan kafin maganin da ta sha ya fara aiki. Farin ciki sosai ya tsinci kansa bayan ta fitar ta. Kai tsaye asibitin ya nufa. Deena da ke kwance ce ta fara motsa hannu, da sauri Afra ta matso kusa da ita.
"Mommy ta farka"
Mommy da karasa gama sallar ta
kenan da sauri ta mike. Jiki a sanyaye ta
ɗ
aya hannunta dake dauke da kalula ta shafa kanta, bandeji da ta ji ne ya sakata tunawa da abin da ya faru. Yunkurin mi
ƙ
ewa ya take yi da sauri Afra ta dakatar da ita.
"Kada ki mike jikinki babu kwari kiyi hakuri k
i kwanta."
Ba don ta so ba haka ta koma ta kwanta. "Mommy ina Daddy ya je. Da gaske Hisham ne ya yi mini haka?"
"To dama me kike tsammani a wurin Hisham in Banda haka? Ai wallahi Deena ka
ɗ
an ma kika gani in dai ba zaki kashe wannan
ƙ
addararren auren ba kin
a tare da wahala domin in ba ayi sa a ba Hisham Shi zai zama ajalinki. Sannan Daddy da kike tambaya ya na can ya saka an daure dan gwal
ɗ
in naki" Afra ta karasa maganar cike da jin haushin Deena.
A zabure Deena ta mi
ƙ
e. "Afra ban fahimta ba. Me kike son fa
da muku wane Hisham
ɗ
in aka kama?"
"Hmm! Hisham Nawa kika sani ko bayan naki Hisham
ɗ
in akwai wani ne?"
"Mommy ke na san ba za ki boyemin komai ba don Allah ki taimaka min"
Ajiyar zuciya Mommy ta sake. "Abin da Afra ta fa
ɗ
a gaskiya ne. Yanzu haka Hisham y
a na a hannun hukuma sakamakon dukan da yayi miki. Amma Deena komai kika ga ya faru ke kika jawa
kanki. Zuwan da kika yi gida ba irin jan hankalinki da banyi ba akan kiyi hakuri kowa da kika gani hakuri ya ke a gidan miji. Hatta ni hakuri nake a gidan Maha
ifinki, amma saboda ba kya jin maganar da nake miki kika je Mahaifinki ya rika zugaki kika kika hayewa mijikin yanzu wa gari ya waya?"
Kuka Deena ta fashe da shi jin abin da mahaifiyarta ta fada.
"Wallahi bance ya kama Hisham ba ko kasheni ya yi mijina ne
. Yanzu Hisham
ɗ
in ne aka saka cell aka kulle. Daddy baka kyauta mini ba"
Afra da ke gefe tsabar bakin ciki ji tayi tamkar ta sha
ƙ
e Deena. "Amma ke kuwa kinyi asara. Mommy da wahala In ba asiri yayiwa Deena ba. Ina ba haka ba ta ya mutum na neman makasarki
amma ki zauna kina fadar kada a kulle shi. Kai ni ba zan iya kwasar wannan bakin cikin ba yanzu xan tafi daga asibitin nan"
Murmushin takaici Mommy ta yi. "Ai Deena kin baro shiri tun rani. Domin yanzu haka Mahaifinki ya hana a bada belin mijinki sai da k
i sakawa ranki hakuri tun wuri. Da baki biyewa zugarsa ba da yanzu da lafiyarki sannan mijinki ma kuna tare. Amma yanzu ki duba yadda jikinki ya koma "
"Ni Mommy ba damuwa ta jikina ba. Ina wayata take in Kira Daddy"
"Wallahi karya kike ba za ki kirashi ba
"
Afra ta karasa maganar tare da fizge wayar.
"wasa ya wuce wasa Afra a kan Hisham zan iya tsinka miki rashin mutumcin da ba za ki taba tantancewa ba"
A fusace Afra ta matsa a kusa da ita. "Deena ni? Ni za ki tsinkawa rashin mutumci a kan wancan bazan mij
in baki?"
Ta karasa maganar tare da nuna kanta da yatsa. "Kurkuren da za ki yi a Rayuwarki shi ne ki
ƙ
ara kiran Hisham da banza. Ba
ƙ
awance ba Afra ko tare muka zo duniya sai kin gane baki da wayo"
Murmushin takaici Afra ta yi har zata yi magana sai kuma
ta girgiza kai tayi gaba. "Amma dai Deena in da zan fada miki kiji abinda kika yiwa Afra sam-sam bai dace ba. Kawarki fa ce wadda kuka taso cikin aminci a kan namiji za ki bari ku rabu?"
"Mommy ba za ki gane bane Hisham rayuwata ne ba zan iya rabuwa da
shi ba. Ni babbar damuwata ita ce Daddy ya gama wulakantani, wa ma ya sani ko Hisham ya sake ni shi kenan na mutu"
Ta karasa maganar tare da
ɗ
ora hannuwa a ka ta fashe da kuka. "Ban wulakantaki ba in dai Hisham ne ki saka a ranki ki bar gidansa kamar yadda
kika baro cikin uwarki"
Daddy da shigowarsa Kenan ya karasa maganar a fusace.
"Daddy ban fahimta ba. Hisham ne ya sake ni wayyo Allah na na shiga uku" "baki shiga uku ba Uwata. Domin Hisham bai sake ki ba. Amma ki sani Indai Ni na haifeki ba zaki koma gid
ansa ba
tunda ke baki san inda ke miki ciwo ba ni na san ciwonki saboda ke daya na mallaka a wannan duniyar"
"Daddy kada ka yi min haka na rokeku. Hisham shi ya kamata ya yi fushi da mu inta kama ma ya dauki mummunan mataki. Amma bai dauka ba, ka saka an k
ulleshi a matsayinsa na sirikinka ko zan mutu ba zan rabu da Hisham ba. Daddy Wa ya hana ka yin alaka da Shukura Daddy na fa San komai."
Falau. Ya tsinketa da gigitaccen mari. Ganin za ayi abin kunya Mommy ta shiga a tsakiya ta na salati.
"Alhaji kai ne ya
u da dukan yar gaban goshinka abin da ba
ɗ
abi'arki ba ko da a ce lafiyarta lau. Bare kuma yau da take a bisa gadon jinya. Abun da mamaki gaskiya kun kulle mini kai ku fada mini wacece shukura"?"
Tambayar da Hajiya ta jefa masa ita ta karasa rikita sauran n
utsuwar da ta rage masa. "Shi ke nan Deena ta ballo masa ruwa" ya furta a cikin zuciyarsa ya na ji tamkar ya sha
ƙ
e.
"Alhaji magana nake, ku fitar da ni a duhu wacece Shukura?"
Tamkar ba zai yi magana ba sai kuma ya juyo a fusace. "Babu ke ba gidan Hisham.
Na gama magana" ya fice ba tare da ya juyo ya kalli inda Monmy take ba. Ilahirin jikinta ya yi sanyi ta rasa me ke mata dadi. Abin da take zargi kada dai ya zama gaskiya. "Wallahi sai na koma sai dai in Daddy ya kashe ni ba zan zauna ba. Shukura ba kowa ba
ce face karuwa wadda ta lalata min farin ciki kafin aurena da kuma bayan aure na. Ko da ya ke ba rayuwa kadai ta lalata ba Mommy hada taki rayuwar saboda tare suke da Daddy." Numfashin Mommy tsayawa yayi na wucin gadi! Da kyar ta samu ta zauna a gefen kuj
erar da ke gefen gadon. Dafe kirjinta tayi da take ji tamkar zai tsare zuciyarta ta yi tsalle ta fado...
Bayan fitowar Hisham daga Cell Kai tsaye gidansa ya nufa shi da Yazid. Sai dai abin da ya bashi mamaki bai wuce yadda ya iske Inna Tala kadai ba. Da y
a