Showing 48001 words to 51000 words out of 61676 words
yan bori yayi a saman gadon tare da dafe kan shi da ya ke jin kamar zai tarwatse tsabar ciwo da ya ke masa.
"Nayi biyayyar aure nayi addu'a kome ma nayi a kanku. Har ta Kai wani lokacin ina ji a jikina tamkar akwai wani laifi da nayiwa Allah. Munzali me ya sa da me na rageka Ka me bani yi maka" jajayen idanunsa ya dago cikin matsananciyar damuwar da tayi masa di
rar mikiya. Rurin da wayarsa ta Fara ne ya tilasta masa fiddota daga cikin aljihun Wanda. Duk da tashin hankalin da yake ciki ganin sunan Shukara banne a screen din wayar, Bai San lokacin da murmushi ya kubce masa ba.
Abinda ta fada masa Shi ya saka Shi K
iran sunanta da karfin gaske zumbur ya Mike. Hajiya kallonsa ta yi jinya ambaci sunan Shukura. Murmushi takaico tayi tare da share hawaye dake fuskarta. Ganin zai fice ya barta cikin dakin da sauri ta sha gabansa. "Me kuke nufi dani. Ina zaku je Ku barni?"
"Ki bani Hanyar akwai damuwa domin bata shafeki na. " " Ban taba yi maka musu ba
don haka yau ce Rana ta farko da zamu Fara SAMUN sabani da kai. Munzali na rantse maka da girman Allah sai na bika duk inda zaka je" ta karasa maganar tare da gyara zaman gy
alenta. "Yau Ni kike Kira Munzali Kai tsaye ?" Murmushin Yake Wanda ya fi kuka ciwo tayi ba tare da ta ce masa uffan ba. Babu yadda ya iya haka ya dauketa a mota suka dauki Hanyar. Tunda suka Fara tafiya zuciyarsa ke innata masa abubuwa da dama musamma aka
n abinda mahaifiyar Shukura ta fada masa. KO dai cikin ya zube itaa shukurar ta Rasa rayuwarta. "In ta mutu ai ni ne na mutu. Ya Allah kasa cikin ne kadai ya zube babu abinda ya samu shukura" ya karasa tunanin zucin tare da share gumin da ya tsattsafo ma s
hi a fuska. Tunda ya Fara tunanin Momy ke kallonsa ta gefen ido, ganin ya dauki Hanyar asibiti ya saka taji gabanta ya Fadi. "To KO dai Hisham ne ya rasu, Kai aa da Hisham ya rasu da Deena ita ma ta jima da amsa Kiran mahaliccinta."
Da wannan tunanin Alhaj
i Munzali yayi parking. Kai tsaye Emergency suka nufa. Deena kuwa tun bayan Kiran da Yazid yayi Mata Kai tsaye ta nufi asibitin. Dakin da ya fada Mata nan ta fada, sai dai su UMMA suKa ganta tamkar an harbota a kibiya. "Umma ya jikin me ya same Shi. Wayyo
na shiga ukku Hisham Ka tashi in Ka tafi nima take maka Baya xanyi " Cike da mamaki mutanen dakin ke kallonta musamma UMMA kanta ya kulle yadda ta ga kamannin fuskarta sun canza duk ta sha bandeji. "Ki nutsu Deena jiki da sauki sosai ban kiraki a wurin nan
ba sai don kusan halin da ake ciki" karaf idanunta suka sauka a kan Sahla da ke gefe a sume. Mijin Ammi Wanda suka kawo Sahla ganin likita ne ya shigo dakin cikin matsananciyar damuwa. Da sauri ammin ta Mike. "MALAM lafiya, me suka fada maka" ajiyar zuciy
a ya sauke tare da kallon Sahla da ke kwance bata San Wanda ke kanta ba. "Muyi Mata addu'a. Likita ya Sanar da ni wani abu da ta ji Kota gani ya tuna Mata da rayuwarta ta Baya. A halin yanzu Abu biyu me zai faru KO dai ta farka tunaninta ya dawo KO kuma ba
zata Farka ba Rai yayi halinsa." Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Sahla ba zaki mutu ba zaki Mike har ki koma ga iyayenki" Ammi ta karasa maganar tare da rushewa da kuka. Nan fa daki yayi tsit! Bakajin motsin kowa sai sautin numfashinsu. Inna Tala da ke
rike da Manara ji yayi yarinyar na kokarin kubcewa daga rikon da tayi Mata, da sauri ta rikota amma abinda ya bata mamaki yadda Manara ta kafe majinyaciyar da taji ana Kira da Sahla da ido KO kyaftawa bata yi. Kafin ta yi wani yunkuri ji suka yi ta tsanya
re da matsanancin kuka tamkar wadda ake kwakulewa ido. Hankalin kowa kan Manara ya koma in banda Ammi da ke rike da hannun Sahla tana kuka. Kamar da wasa ji tayi ta motsa Babba Dan yatsanta da karfi. Zaburar da Ammi zata yi ita ta karasa tayar da Sahla ta
Mike zaune tamkar wadda ake sawa remote. "Ita ce wallahi ita ce, Ku bani diyata" ta karasa maganar tare da mikawa Inna Tala hannu, alamar a Miko Mata Manara da ke faman tsala kuka...
Meenat A 'Yandoma
08133562798
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RA
MA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bar
e ma oga ko saurayinki da kansa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karsh
e indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA
ππ»
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara
Saloon
Kunshi
na salatap Dana zane
Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba
ππ»ππ»
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA
π―
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
PG 53&54
NA KUDI NE DOMIN BIYAN KUDIN LITTAFIN 500 TA WANNAN ACCOUNT DIN 8133562798 OPAY AMINA ABUBAKAR
...Da mamaki kowa ke kallo Sahla, musamma Inna Tala
da sai a lokacin ta Kara ganin ainahin kamannin dake tsakanin Manara da Sahla. "Alhaji ta farka. Alhamdulillah!" Ammi ta fada tare da
rirrike Sahla tamkar za kwance Mata ita. Umma jinin jikinta ta Kara sha saboda ta ga abin da take tunani zai tabbata. Domi
n tun sa'in da Sahla ta Yankee jiki ta hango tsantsar kamannin da ke a tsakaninsu da Manara. Muryar Sahla ce ta daki dodon kunnen duk Wanda ke cikin dakin.
"Ammi a bani diyata wallahi ita ce, an rabani da ita tun lokacin da na haifeta. Banji dumin jikinta
ba haka ita ma bata ji nawa ba." Ta karasa maganar tare da rushewa da kuka. Hankalin Ammi taShi ya karayi. Kada a ce Sahlarsu ta farka da tabin hankali. Abin da basu sani ba Shi ne tun farkarwar Sahla Shi ma Hisham ya farka. Shuru ya yi tare da share gunt
un hawaye da ke fuskarsa. Ba su yi aune ba sai gani suka yi ya Mike tsam ya tunkari Inna Tala da ke ta faman rirriga Manara da ke faman tsala kuka. Amsarta ya yiya na kokarin tunkarar gadon da Sahla take. Da sauri UMMA ta sha gabansa. "Aa Hisham. Kada Ka b
ata ita, kana da tabbacin abin da ta fada? KO kuma Ka Santa ne?" Girgiza Kai yayi tare da dago jajayen idanunsa ya kalli Umma. "Ba ta yi karya ba. Domin na Santa kamar yadda na San yunwar cikina. Don Allah Ku barni in sauke wasu daga cikin nauyin da ke kai
na ta Hanyar sada Manara da mahaifiyarta" Jin abin da ya fada kowa sake tsunduma ya yi a duniyar tunani musamma Deena da ke tsaye kikam ta na kallonsu tamkar a mafarki. Shan gaban Hisham ta yi "ba zaka matsa daga inda kake ba sai Ka fada mini wace ce ita"
kallon Daya watsa Mata ba shiri ta ba Shi hanya wani sabon tsoronsa ya darsu a zuciyarta.
Mikawa Sahla Manara yayi kamar daukewar ruwa yarinya ta yi tsit! Tare da kwantawa a kafadar Sahla ta na mayar da ajiyar zuciya. Cikin kuka Sahla ta Fara magana. "Ash
e dama zan sake ganinka, Ashe kaddara Kai ta damkawa diyarka. Innalillahi wa inna ilahi rajiun! Ubangiji in mafarkin da na sabane na rokeka da Kada in farka in ta yin mafarkin nan har karshen rayuwata. Zubewa ya yi a saman gwiwowinsa cikin karfin zuciya ya
Fara magana. "Hakika ni Mai laifi ne a wuriki amma Allah ya fini sanin halin da na tsinci kaina tun bayan rabuwarmu. Ashe ke ce Mahaifiyar Manara. Allah na gode maka Kai ne kayi mini kyauta sannan Ka Kara mini. Ya Ubangiji KO yanzu Ka dauki Raina Ka biyan
i"
Alhaji da UMMA hada harda Deena. Kuka Deena ta fashe da shi tare da cin kwalar Hisham da ke durkushe. "Ka cuceni Ka cuci rayuwata. Har zuwa yau she ne zaka daina Tara matan banza, jikina ya jima ya na bani Kai ne mahaifin Manara, ta ya ma zamu yarda da
kazo mana da diya da ranar Allah sannan Ka ce ba taka na ce. Ka koreta daga kusa da Kai KO kuma inyi abin da ba zai yiwa kowa dadi ba domin Zan Fara kashe 'yar sannan in kashe mahaifiyar in kasheka sannan nima in kashe Kaina. Bahagon Marin da Hisham ya ts
inkata da Shi sai da komai ya tsaya Mata cak! Kafin ta tsinkayo muryar Hisham cikin kakkausar murya. "Matar tawa kike Kira da karuwa. Gudan jini na zaki Kira da shegiya. Ba shakka lokaci ya yi da Zan nuna maki ainahin kalata. Ke har kin ISA ki kalli wannan
ki ce Mata karuwa? Asali, nasaba, da tarbiyya kome ta fiki" ya karasa maganar a matukar fusace ya na kokari sake tsinketa da wani Marin.
Da sauri Alhaji ya rukoshi. "Hisham maimata abinda Ka fada in ji. Kamar matarka na ji Ka ce, a yaushe kuka yi Auren w
aya daura maku auren. Ita wannan yarinyar kana nufin jininka ce jikata ce? Hisham Ka fiddo mu daga duhun Daren da Ka sakamu" Umma ce ta amshe zancen.
"Ku fada mana gaskiya a ina kuka San Juna har kuka yi Auren har ma da rabo a tsakaninsu amma mu mahaifank
u ba mu sani ba. In Baka manta ba babu tambayar duniyar da ban maka ba akan wannan diyar taka ce domin tun a lokacin na hango tsantsar kamannin da ke a tsakaninku"
"Ba karya ya yi ba kamar yadda ya fada maku ba shegiya ba ce da Ubanta. Hisham Ka lalata ko
mai Ka haddasamin bala'in da har yau cikin masifa nake. Me ya sa zaka gujeni a lokacin da na Gama sakankancewa da Kai? Na rokeku mu je wurin mahaifina Hisham ya warware komai da bakinsa har yau mahaifina fushi ya ke dani ya rabani da dangina ya fitar da ni
a cikin ahalinsa." Kukan da ya ci karfinta ne ya tilasta Mata yin shuru. Daki yayi tsit! Anyi jugum jugum kowa da abin da ya ke sakawa. Musamma wadan da suka tsinci Sahla hankalinsu ya fi na kowa tashi.
Alhaji Munzali kuwa tun bayan da suka shiga dakin d
a Shukura take ya kasa magana jikinsa yayi matukar sanyi ganin irin kallon da take aika masa. Mamanta ce ta katse shuru ta Hanyar Fara magana.
"Jikina ya bani Kai ne Ka bata maganin zubar da ciki. Me ya sa? Gashi nan Ka lalata komai Alhaji Baka
kyauta mana ba. "
Rass! Gaban Mommy ya Fadi. "Baiwar Allah wane ciki kike magana?" A wulakance Shukura ta kalleta da fuskarta ta Gama hadewa da hawaye da majina.
"Ciki na haihuwa Wanda mijinki ya yi mini. Abin da Baki sani ba nice abokiyar zaman
diyarki kuma wannan dake tare da ke tare muke tun kafin inyi aure haka ma bayan nayi. Yanzu haka cikin da ke jikina nasa ne. Sai ki shirya amsar danku."
Kafafun Mommy kasa daukarta sukayi dole ta dafe kujerar da ke kusa da ita lokaci Daya duniyar ta Fara
juya Mata.
Cikin karaji Shukura ta ci gaba da magana. "Munzali. Umma wallahi kun cuceni GA Shi nan kun
rabani da Wanda na fi kauna fite da kowa a wannan duniyar. Yanzu haka ban San halin da ya ke ciki ba wama ya sani KO mutuwa yayi Yazid ya boye mini" ta
karasa maganar tare da dirowa daga saman gadon a Gigice ta yi waje da gudu. A guje su duka suka take Mata Baya. Bata bata lokaci ba ta fada dakin da Hisham ya ke. Sai ganinta su suka yi tamkar an jefisu. Ilahirin annurin da ke a fuskar Hisham daukewa yayi.
Da mamaki UMMA ke kallon mutanen sai kuma ta tuna dama Yazid ya ce Mata Shukura na asibitin nan bata lafiya. Sai dai tsawar da ya dakawa Shukura ita ta saka kowa fadawa duniyar tunanin me kuma ya hadasu?
"Na datse duk wata alar da ke a tsakaninmu me kum
a ya dawo dake kusa Dani. Shi ne zaki zo mini hada wancan kwarton a kusa Dani?" Ya karasa maganar tare da nuna Mahaifin Deena. A fusace mahaifinsa ya daka masa mahaukaciyar tsawa.
"Ba Kada hankali ne? KO kuma kwaya kasha. Mahaifin matarka Wanda siriki ne
a wurinka Shi kake Kira da kwarto?"
"Daddy wannan ya fi kwarto illa. Domin wani kwarton sau Daya take bin mace ya kwaketa amma wannan nashi yayi muni, tare ya ke da Shukura tun kafin in aureta haka bayan na aureta yanzu haka cikinsa na jikin Shukura na ts
awon watanmu uku" Ilahirin Wanda ke cikin dakin a kidime suke kallon Alhaji Munzali. Deena kuwa wata irin bugawa zuciyarta tayi, ja da Baya ta Hanyar saka hannayenta biyu ta dafe kirjinta. Ja da Baya ta Fara yi har sai da ta hade da mahaifiyarta da ke fama
n rusa kuka har muryarta ta shake.
" Mommy Kada ki ce min da gaske ne, hawaye da na gani a fuskarki sun Kara karyar min da zuciya. Da gaske Shukara kishiyata wadda muka auri miji daya dauke take da cikin Mahaifina, mommy inta haihu Kenan abokiyar zaman ta
Haifa mini kane? Mommy ki fada mini gaskiya" ta karshe maganar tare da girgiza Mommy dake faman cizgar kuka tamkar ranta zai fita. "Da gaske ne Deena. Munzali ya Gama kashe mu da rayuwarmu, mum Zama gawa Deena" wani irin tari ne ya sarke Deena lokaci Daya
ta dafe gefen zuciyarta. Karfin Hali ya saka ta rarrafa kusa da kafar Hisham. "Lokacin tafiya ya yayi. Hisham kunyar kallon fuskarka nake bare ta kaini ga rokon yafiyarka. Laifin da Ka sani da Wanda Baka sani ba in kaga zaka iya yafe min Hisham ban tilast
a Ka ba. Na so in yi doguwar rayuwa da Kai Allah me shaida a wannan kwanciyar da nayi asibiti na yi niyyar canzawa daga Deenar da Ka sani. Ashe waadi na ne ya Matso Hisham sai wata rana lokacina ya yi Hisham. Daddy Ka cuce ni Ka cuci rayuwata da..." Magana
rta ce ta sarke sakamakon tarin da ya kwareta. Wuyanta ta rike gam tana madodowa a kasa, jinin da ya fara biyo Mata ta Baki da hanci Shi ya saka Hisham fita a guje ya na Kiran likita. Mommy kuwa kuka take tana girgiza Deena dake kokarin furta magana amma b
akin ya Gaza. "Ka ga aikinKa Munzali. Ga sakamakon da Ka Fara gani tun a duniya. Deena ba ke ya kamata ki tafi ba ki bari mu tafi tare" lokaci Daya jinin
dake fita a hancinta da bakinta ya karu, wata irin kara tayi ta Fara girgiza tare da rirrike mahaifiya
rta. Ji kake tsit komai ya lafa idanuwanta sun kakkafe. Mahaukaciyar kururuwa Mommy Ta kwala tare da Kiran sunanta Deena ta na girgizata ....
Masu BUKATAR link GA Shi nan
πππππ
LADY'S BEAUTY PALACE
SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BR
EAST DINKI NE?
KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU?
KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?
KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?
Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da ka
nsa,
Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu
sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S BEAUTY PALACE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA
KIKE SO KAMAR HAKA
ππ»
Zumar kiba
Zumar breast
Zumar hips
Zumar infection
Zumar sliming
Zumar sabon budurci
Back to virgin
Abayas
Atamfa
Lace
Hijabs
Supplements
Kayan yara
Saloon
Kunshi na salatap Dana zane
Kitchen items and more Muna maraba da
masu siyan Daya ko
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba
ππ»ππ»
SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA
π―
Whatsapp or call 08169307477
Tiktok Hajara Rabiu (lady's
beauty palace)
Instagram Hajara Rabiu
PG 55&56
NA KUDI NE DOMIN BIYAN KUDIN LITTAFIN 500 TA WANNAN ACCOUNT DIN 8133562798 OPAY AMINA ABUBAKAR
...A daidai lokacin Hisham yashigo da Likita. Bai bata lokaci ba aka shigar masa da ita dakin da Zainaba take,
Mommy ta kasa daina kuka. Alhaji Munzali kuwa wani irin gumi ne ya shiga wanke ilahirin jikinsa, jinshiya ke