Showing 60001 words to 61676 words out of 61676 words
yiwuwar in lokacin haihuwarta ta yayi abu ne Mai matukar wahala ta iya haihuwa da kanta. Sannan sanadiyyar magungunan zubar da cikin da tasha Dan dake cikinta ya samu matsala Abu me matukar wahala a haifesa da cikakkiy
ar lafiya. Haka ita ma uwar da zarar mun Ciro Dan za a cire Mata mahaifa." Salati da sallallami Mana ta hau yi cikin kuka. "Likita kana ganin Dan da ke cikinta zai iya ci gaba da rayuwa KO kuma za Ku fito da Shi ne a sakamon Shi cikin kwalba. Likita in Dan
nan ya mutu nima mutuwa xanyi" Alhaji Munzali ya karasa maganar cikin tashin hankali.
"In Shaa Allah zai rayu domin maganin bai bigeshi da yawa ba, sai dai ita zata iya mutuwa a KO wane lokaci muddun ta Kara gigin Shan maganin zubar da ciki." "Zanyi maga
nin abin bada jimawa ba." Ya na karasa maganar ya fice daga office din a matukar fusace. "Likita Ka fadamin diyata zata rayu? Idan Shukura ta mutu asirina ya tonu na Gama wulakanta a wannan duniyar" "Hajiya ki Kula da ita sosai ta yadda ba zata Kara gigin
zubar da cikin na. Saboda muddun ta Kara ciki fa ba zai zube ba amma ita da abinda ke cikinta za su bar wannan duniyar."
Jin abin da ya fada da kukanta ta fice daga dakin. Kai tsaye dakin da Shukura take ta nufa. Alhaji Munzali ta iske tsaye a kanta tamka
r zai Kai Mata duka. Cikin kakkausar murya ta ji ya na Fadar.
"KO da wasa kika Bari cikin nan ya zube sai na sanadiyyar mutuwarki ke da wannan kwadayayyar uwar taki. Na Yankee shawarma daga asibitin nan gidana zamu wuce da ke domin na fuskanci in kina tar
e da wannan uwar taki komai zai iya faruwa." Rass! Gaban Shukura ya Yankee ya Fadi. "Mama da gaske cikin nan Bai zube ba?" Ta karasa maganar tamkar zata fashe da kuka. "Shukura ciki ya na nan zaune kamar duniya. Ki rufa mana asiri ki haifi cikin nan Kada k
i janyo mana bala'i." Kuka Shukura ta fashe da shi. "Kun cuceni kun lalata mini rayuwata kun janyo mini bakin tabon da har in bar duniya ba zai goguba. Ina amfanin kudin da muka Tara? Hisham ya fiye mini komai na wannan duniyar hatta cikin nan da ke jikina
tsaf Zan zubar da Shi in sai Hisham zai dawo gareni." Kyakkyawan Marin da Alhaji Munzali ya wanke ta da Shi ne ya sakata dafe kunci tare da fashewa da kuka. "na tsani Hisham na tsani duk wani Abu da ya dangance Shi. Saboda ya sanadinsa ne na Rasa tilon 'y
ata komai nawa ya lalace ne saboda Shi. Shukura mafi mini kiskuren da za kiyi a rayuwarki Shi ne ki zubar da cikin da ke jikinki sai na Koya Miki hankalin da har duniya ta nade ba zaki manta da Shi ba. Sannan na Gama magana daga nan gidana zaku wuce KO bab
u aure sai kin Haifa mini cikina " ya na kaiwa nan ya fice a fusace...
Can gidansu Umma kuwa lokacin tafiyarsu yayi amma Alhaji ya kafe Kai da fata CE war kaninsa bazai koma wancen garin ba domin a Baya ma sharrin Rahila ne ya Raba su. Babu yadda ya iya h
aka ya hakura da zummar zai je yayi bankwana da sauran makwaftansa. Abdallah kuwa Basu jima da zuwa garin ba ya samu matar aure an saka ranar biki nan da wata Daya. Hisham da Sahla ma a saka ranar tarewarsu da bikin Abdallah. Farin cikin Umma ya dawo a lok
acin da bata taba tsammani ba. A yanzu kan Sahla ta yafewa Hisham amma fa ya sha bakar wahala.
Hajiya Rahila kuwa duniya ta juya Mata Baya domin cikin danginta ta koma Wanda a lokacin da take da Hali bata taimaka masu b, tsakaninta da su sai cin mutumci d
a wulakance. Gawani irin ciwo da ya kamata bata iya daga koda Dan yatsanta komai sai anyi Mata. Haka za tayi kashi su barta a ciki har ya bushe Mata in sunga dama haka zasu saka tsintsiyar kwakwa SU wanke Mata Shi. Nadama mara amfani ta aureta. Ta bangaren
mahaifiyar Deena kullum cikin kuka take tare da rokawa tilon diyarta gafarar Ubangiji. Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba Jin tsohon mijinta ya dauko Shukara ya maido gidansa. Sai dai ta tuna wanene Munzali bata yi mamaki ba. Rana bata karya sai dai uwa
r Diya ta ji kunya. A yau ne aka shaida daurin Auren Abdallah da amaryarsa Salima sai Yazid Shi ma da tashi amaryarsa Zaliha Hisham kuwa Baki ya ki ruhuwa ganin yau Shi ne zai tare da farin cikin ransa. Tuni Umma ta amshe Manara domin yanzu ta Fara tafiya.
Haka a Ka Kai kowace amarya gidan mijinta cike da so da kaunar juna. Anti Maryama kuwa bayan an Gama biki wurin mahaifiyarta ta nufa ganin irin mugun yanayin da take ciki ba karamin tayar Mata da
hankali yayi ba. Rayuwa Kenan yanzu GA mutanen data wulakan
ta ta cuta ta so ganin bayansu suna can cikin rufin asiri da kwanciyar hankali ita kuma ga yadda karshenta ya kasance. Hayaniyar da Anti Maryama ta ji ce ta sakata yin zumbur ta Mike. Kanwar Hajiya Rahila kancewar ita CE gidan iyayensu tun bayan da Mata Au
ren ya mutu. "Maryama mun shiga uku! Fito ki gani kamar gawar Farida ce" a guje suka karasa fitowa. Bakin fuska Maza guda biyu ta gani tsaye GA kuwa motar asibiti da ke faman Kara wiwi. " Ke CE yayar Farida? " A hanzarce ta amsa. "Gawarta muka tsinta a cik
in mugun yanayi an debi wasu daga cikin sassan jikinta, mun kaiwa mahaifinku gawar amma fur ya ce ba zai amsa ba a kawo ma mahaifiyarta gawar. Da kyar muka iya gane gidan nan, dan haka yanzu zamu shigo maku da gawar." Kafin Ka ce me tuni mutane sun cika gi
dan. Gawar Farida tayi munin da Maryama na ganinta ta Yankee jiki ta fadi. Ba ita ta farfado ba sai da aka dawo daga rufeta har lokacin Sam nahaifinsu ya ki ya zo inda suke. Hajiya kuwa ba a vari ta ga gawar ba amma duk da haka da kyar take Jan mumfashi. G
a baki a rufe tana so ta yi magana ta kasa.haka aka karasa zaman makoki Maryama ta koma gidan mijinta tare da barmasu kudin da zasu ci gaba da kuka da mahaifiyarta. Sai dai tana bada Baya suka hau bushasha da kudin ba tare da sun bata wAta kulawa ba zata i
ya yini ta Kwana ba su bata abinci ba.
Shukura kuwa tun bayan da suka koma gidan Munzali yake gasa mata Aya a hannu. Kwamacala Kam ana yinta domin Munzali ya mar da ita tamkar matarsa har cikinta yashiga watan haihuwa. Ranar da nakuda ta zo Mata ba su rin
tsinta ba haka suka nufi asibiti. Anyi nasarar Ciro Mata da namiji sai dai Bai da kafa Daya hannu Shi ma babu Daya. Farin cikin Alhaji Munzali komawa ciki yayi ganinirin halittar da Shukura ta Haifa masa. Haka aka cire Mata mahaifa suka koma gida. Alhaji M
unzali ya kori mahaifiyarta ta koma gida haka ya rage daga Shukura sai Shi danginsa kuwa KO da suka samu labari tuni suka warwatse da Shi kowa ya kama hanyarsa. Sai dai abin da Shukura bata sani ba Shi ne. Boka ya ba Munzali umarnin ya yanka Dan ya sha jin
insa muddun ya na so dukiyarsa ta ci gaba da habaka. Domin yanzu Shukura ita da babu duk Daya ne. Shukura kuwa wani irin kaunar yaron take har cikin zuciyarta. Yana da mako uku ta na bacci zata juya Kenan ta bude ido babu da babu dalilinta. A firgice ta Mi
ke ta nufi zashen Munzali domin in ba Shi ba wa zai dauki dan abin da ta gani ne ya sakata kurma ihu. Munzali rike da gawar jinjirin ya yanka Shi Yana zugar jininsa. Duk da alamar shigowar mutum da ya ji Bai damu ba saboda ya San lokacin haukacewarta ne ya
yi. Tunda ta Yankee jiki ta fadi ya tattara ta ya mayarwa da mahaifiyarta, tambayar duniya tayi masa akan abinda ya sameta sannan ina dan ya ke. Sai ce Mata yayi Dan sa ne sannan yayi abinda ya dace da Shi. Bayan farkarwar Shukura dariya ta rika babbakawa
tana Fadar " ya yanka Shi ya Shanye jinin mama kema haka Zan Miki in yanka ki in Shanye jinin" kuka Mama ta hau yi shikenan ya haukata Mata Diya. A daren ranar Mama na bacci Shukara ta yi Mata yankan rago ta gudu tana hauka tuburan. Sai sai wayar gari aka
yi da wannan mummunan labari. Alhaji Munzali kuwa dukiya ta Kara bunkasa. Yanzu haka a kan hanyarshi ta zuwa wurin wani mashahurin boka yake. Suna cikin tafiya motarsa ta kwacewa direba ta nufi jeji wani icce ta nufa lokaci Daya ta kama da wuta... Haka ta
ci ta cinye kurmus ko gawar Shi a ba fidda ba. Danginsa sunyi farin ciki haka suka dawo gidansa ana zaman makoki da murnar uwar dukiyar da ya bar masu. Ranar da akayi sadakar uku a ranar duk wasu gidaje da dukiyar da suka mallaka suka kama
da wuta. Suka ci
suka cinye kurmus..
KO da Hisham ya samu labari Bai tausaya masa ba domin ya ji kaf labarin abinda ya faru. A yanzu Hisham ya shiryu rayuwarsa yake yi cikin Kamala da mutumci. Tamkar ba Hisham din da ya sha fama da rashin ji ba, sai dai mu yi fatan Ubang
iji ya tsare my da mummunar kaddara.
Halin da Hajiya Rahila take ciki yayi muni fiye da lissafi. Wani sashen jikinta ya ru
ɓ
e, har ya fara tsutsa amma sunki kaita asibiti kudin da aka bata ma haka suka cinye su tass! SSI wayar gari akayita mutu.
ALHAMDULI
LLAH ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI ABIN DA MUKA FADA DAIDAI UBANGIJI YA BA MU LADAR WANDA MUKA YI KUSKURE ALLAH YA GAFARTA MANA