Showing 24001 words to 27000 words out of 61676 words

Chapter 9 - MANARAH COMPLETE

zabga mata ta saka ta fara zunduma ihu.

Duk abin da ya tari gabanta dauka ta rika yi ta na jifarsa da shi

. Ihun da Shukura ta jiyo shi ya tada ta daga bacci. A rikice ta fito falon. Ganin irin katakkar da ake sha ya saka ta sakin murmushin farin ciki. Kamar zata koma falon wata zuciya ta ce tayi sauri ta ceceta don ya na iya yi mata illa.

Shiga tsakiya da ta

yi ta rike Bulalar shi ya ba Deena damar aiko masa da munanen maganganu.

Inna Tala da ke tsaye rike da Manarah jikinta sanyi yayi.

"Wannan wane irin gida ne Allah ya jefoni. Rayuwa suke tamkar rayuwar bariki, kai jama'a "

Ta karasa zancen zucin ta na kallo

n Manarah in ba gizo idonta ke mata ba kamar dariya ta ga tana yi.

Da gaske ne domin har bude baki take yi.

Wurgar da belt din Hisham yayi ya fice a matukar fusace.

Cike da gadara Shukura ta juya ta na kallon Deena.

"Me rabon shan duka baya jin kwana

sai ya sha. Deena ko a haka aka tsaya ya kamata ki gane irin tazarar da ke tsakaninmu da ke. Har na gama rayuwar bariki da Hisham ko yatsa bai taba

ɗ

aya muni ba, ke kuwa sau tari ya sha hada miki na jaki ga shi har bayan ya aureki ba ki daina dakuwa ba"

Ta

karasa maganar ta na dariya.

"Wannan ba komai ba ne face sharri ki. Kin ga yadda kika shigo gidan nan sai na zama sanadiyyar barinki a cikinsa. "

"Haba Deena! Ke kinga na miki kama da kalar matan da za ki iya fitarwa a gidan miji ko da ba miji

ɗ

aya muke

aure ba? Ko da ya ke ke baki san ko ni wacece ba amma ki tambayi Alhaji Munzali zai fada miki wace ce Shukurah"

Ta na karasa maganar ta juya cikin taku

ɗ

ai

ɗ

ai ta shige

ɗ

aki.

Deena dake tsaye tamkar icce da gudu ta fada

ɗ

akinta. Bata bata lokaci ba ta dau

ki wayarta cikin sa a kira

ɗ

aya mahaifiyarta ta

ɗ

aga.

Mommy da ke zaune a falo duk tunanin duniya ya isheta, karar wayarta da ta ji ce ta sakata

mikewa. Ganin sunan Deena ya sakata kara wayar a kunnenta.

Kukan da ta ji ta fashe da shi ne ya tabbatar mata

da babu lafiya.

"Ki daina kuka ki fada mini me ya faru ko baki lafiya?"

"Ki dawo gida fa kika ce Deena? Kin manta gidan wanda kike? Hisham fa ne. Maganar ya auri wata ba tare da kin sani ba kuma hakuri za kiyi. Ni kai na hakuri nake a gidan mahaifinki in k

uma kin ce auren za ki kaso ki zo gidan ki zauna to ba zan hana ki ba. Wata kila lokacin mutuwa ta ne ya karaso ke da Mahaifinki kune za ku zama ajalina."

Ƙ

itt Mommy ta kashe wayar! Wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska.

Wannan shi ake kira

rana zafi inuwa

ƙ

una! "Ubangiji na gode da wannan jarabawar. Allah ka bani ikon cinyeta"

Ta karasa maganar tare da share hawayen fuskarta.

Kai tsaye Hisham gidansu ya nufa.

Duk da ganin Hajiya da ya yi a cikin falo gaisuwa bata hada su ba ya shige dakin m

ahaifiyarsa.

Auta ce ta fara magana cike da masifa.

"Hajiya wai yaushe Alhaji zai sallami yaron nan su yi rabuwa ta har abada a tsakaninsu? Ni fa na gaji da ganinsa, tsorona daya kada karuwan da ya aura su zo su haifi namiji kin ga sabon lissafi ya tashi k

o da a ce kin kawar da Hisham"

"Haba Auta ai Hisham ba zai ta

ɓ

a haihuwa ba, wannan garanti ne ma samu daga wurin boka. Ku dai ku zuba ido kuyi kallon yadda za mu kare. Shiri muke ba na kadan ba"

Ce war Hajiya.

"Ni Hajiya so nake ma ki bar mu mu je gidan

mu koyawa matansa hankali ta yadda zasu fahimci su waye mu"

Farida ta fada.

"Yau ya kamata mu je gidan ni fa tunda aka ce wannan

ƙ

aruwar tasa ce ya aura na ji na kara tsanarsu"

"In Banda abinku wa ya isa ya hanani zuwa gidansa. Ai ko don su gane matsayink

u ya kamata Ku

je gidan. Ina suka nuna su na son kawu maku wargi ku na

ɗ

a masu kashin tsiya ni na sakaku"

"An gama Hajiya"

Auta ta karasa maganar tare da tafawa ita da Farida.

Tunda Hisham ya shiga dakin gaban Umma ke faduwa. Addu'ar ta daya Ubangiji ya s

a kada Alhaji ya shigo gidan ya tarar da shi.

"

Ɗ

a da Mahaifinsa amma sun zama kamar wasu abokan gaba. Ubangiji ka nuna min iyakar wannan al'amari."

Bayan tafiyar Hisham Hajiya da su Auta sun shirya Driver ya kwashesu. Wurin Boka aka aje Hajiya su kuma su A

uta kai tsaye gidan Hisham aka dosa da su.

Yadda Hajiya ta nutsu a gaban Bokan zaka iya ce wa ba ita ba ce. Ya jima ya na bincike kafin ya

ɗ

ago kai ya dubeta.

"Bukatarki

ɗ

aya zata biya

ɗ

aya kuma ba zata biya ba. Domin bakin alkalami ya jima da bushewa.

Ɗ

i

yar robar da kika bari aka fita da ita duk wani aiki ya rushe.

Mafita

ɗ

aya ce sai dai cikin biyu ki zabi daya. A kashe miki Hisham ko kuma Manarah."

"Boka ni Manarah bata a gabana Hisham

ɗ

in dai nake so a kawar min da shi a wannan duniyar. In aka

aiwatar mini da haka an biyani"

Tuntsurewa da dariya Boka yayi, ya jima ya na yi kafin ya hade girar sama da ta

ƙ

asa tamkar wanda aka aikosa da sakon mutuwa.

"Wohoho! Wato ba ki san mutuwar yarinyar sai ta fi zama rufi asirinki bisa ga a ce Hisham ne ya m

utu. Wannan yarinyar da kike gani in Ina hango abubuwa da dama a kanta amma na rasa ta yadda zan gano wacece ita, duk in na yi yunkurin aiwatar da wani abu a kanta asarar kayan tsafina nake yi. Amma ki sani zata iya zama sanadiyyar tonuwar asirinki, ina fa

tan baki manta da abin da zai biyo baya ba in asirinki ya tonu?"

Wasu yawu masu

ɗ

aci Hajiya ta ha

ɗ

iye.

"Ban manta ba shi ya sa zan iya yin komai domin asirina ya rufu. Zan kauda koma me ye ya ke son tona mini asiri"

"Aikin ki ba zai ta

ɓ

a tabbatuwa ba sai k

in kawo abubuwan da kika saba bayarwa. In kuma kudi za

ki bada a siyo to, bance miki yarinyar zata mutu ba amma in kika yi kuskure ga aikin da zan sakaki hakika

ɗ

aya daga cikin 'ya'yanki zata rasa rayuwarsa"

Rass! Gaban Hajiya ya yi wata irin mummunar fad

uwa.

"Rasa yarana kuma Boka?"

"Kwarai kuwa. Ruwan magani ne zan ba ki jika tare da saka shi cikin inda zai yi sanyi na tsawon kwanaki uku. Sharadin amfani da shi shi e ko da wasa kada ki ce wa kowa kinyi ajiyar kada a taba ko kuma kada wani ya sha. In kika

sake ki ka gargadi yaranki a kan kada su taba ko su sha, ki sani ke zaki haukace. Za ki bar maganin ya yi mako

ɗ

aya kafin ki ba yarinyar ruwan ta sha. Da ta sha magana ta

ƙ

are sai dai wata ba ita ba. Ki sani in aka yi rashin sa a daya daga cikin 'ya'yanki

ta sha ruwan nan minti biyar ba zata kara a duniya ba"

Wata irin zabura Hajiya tayi tare da dafe

ƙ

irjinta da take jin tamkar zuciyarta zata faso kirjin ta fa

ɗ

o.

Jiki na kyarma ta fara magana...

A SHIGA NAN DOMIN SAMUN SAURAN PAHES

Ɗ

IN

👇👇👇👇

PG 29&30

NA KUDI NE DOMIN BIYAN KUDIN LITTAFIN 500 TA WANNAN ACCOUNT DIN 8133562798 OPAY AMINA ABUBAKAR.

..."Boka wannan ita ka

ɗ

ai ce hanyar da za a bi. A rangwanta mini"

Sake kecewa da dariya ya yi

"Babu wata hanya, don haka dole ki amshe shi

Bakin alkalami ya bushe"

Ya karasa maganar tare da miko mata ruwan da ke daure cikin leda.

Lallai yau kam tana cikin tashin hankali. A tarihin rayuwarta yau ce rana ta farko da ta fara

gamuwa da irin wannan tashin hankalin.

Jiki a sanyaye ta tabaro

wurin zuciyarta cike da sake-sa

ƙ

en abubuwa da dama.

Su Farida da Auta kuwa babu sallama haka suka fa

ɗ

a falon. Inna Tala da ke zaune da sauri ta mi

ƙ

e ta na masu sannu da zuwa domin ta shaida fuskokinsu.

"Dallah dakata! Ina matan gidan suke? Ko da ya ke wan

nan sai dai a kira su

ƙ

war

ƙ

warori"

Auta ta

ƙ

arasa Maganar tana me zama a bisa

ɗ

aya daga cikin kujerun falon.

Jiki na kyarma Inna Tala ta nufi dakin Shukura.

Tsaye take bakin kofa ta rasa ta inda zata fara. Tsoronta

ɗ

aya kada a ce bacci take ta tayar da ita

ta ha

ɗ

u da

ɓ

acin rai.

Shahada ta yi ta tafka sallama ta na me Kiran sunan Hajiya. Shukura da fitowarta daga wanka kenan ta ji ana kwalamata kira. Amsa wa ta yi amma bata le

ƙ

o ba sai da ta gama shiryawa.

Ganin Inna Tala tsaye a bakin kofar ta shi ta bata

mamaki.

"Hajiya da ma ba

ƙ

i ne kuka yi suna falo suna jira"

"Ba

ƙ

i kuma? Daga ina"

"Daga gidansu mai gidan,

ƙ

annensa ne"

Inna Tala ta fada tare da rirriga Manarah da ta fara mutsirniya.

"Ok! Ki ce ga mu nan zuwa"

Jiki a sanyaye ta juya ta nufi falon.

"Ta ce

gata nan zuwa"

Ta karasa maganar ta na kokarin juyawa.

"Ina kuma za ki je? Zuwa za kiyi ki fito mana da

ɗ

ayar munafukar. Kika wani kwashi jiki sumi-sumi da wata yar iskar

ɗ

iya da ke bayanki za ki wani shiga daki"

Farida ta karasa maganar tare da daka mata

tsawa.

Babu yadda ta iya haka ta nufi dakin Deena.

Deena da ke kwance ta na faman kuka tun bayan fitar Hisham da sauri ta mike.

"Uban me kika shigo yi mini cikin

ɗ

aki? Ko kinzo ne ki

ƙ

ara ja mini wani sharrin?"

Ta karasa maganar tare da mikewa ta na mai

nunata da yatsa.

"Wallahi ba abin da ya kawo ni ba kenan. Baki ku ka yi,

ƙ

annen mai gidan ne su ne suka ce ina kira masu ku"

"

Ƙ

anan Hisham kuma? To fitar muni daga

ɗ

aki ga ni nan zuwa"

Da sauri ta fice ta bar Deena a tsaye.

Duk da tsoron shiga

Toilet

ɗ

in da take yi a gaggauta ta shiga ta wanke fuskarta ta fito.

Lokacin da ta karasa cikin dakin ita ma Shukura fitowarta kenan.

Ku jera suka samu suka zauna.

A maimakon su Auta su hau gaishesu sai ma suka fara aika masu da kallon wulakanci.

"Sannunk

u ya su Hajiya, kun zo lafiya"

Deena ta fada fuska a

ɗ

an sake.

Caraf Auta ta amshe zancen.

"Ke kike da sannu! Domin na ga kamar kin fi bu

ƙ

atar a miki sannu! Wai Allah! Kai bariki ba riba. Duk da lakataccen auren da aka yi amma rayuwar barikin dai ta na nan

. Jiki duk sawun bulala, sannu kinji"

Ta karasa maganar Farida ta kalla suka kwashe da dariya.

Deena ta so ta

ɓ

oye

ɓ

aci ranta amma ina. Bata san lokacin da ta mi

ƙ

e ba.

"Ke kuma da kika kafe mu da ido gida ba a koya miki yadda ake girmama

ƙ

annen miji ba ne

? Ko da ya ke wanda ya saba da bariki ai ba shi da wata manner"

Farida ta karasa maganar tare da yi wa Shukura kallon up and down.

Murmushi Shukura ta yi ita ma ta mi

ƙ

e tsaye ta na kallonsu.

"To wai da ku ka yi mana tsaye a ka tamkar zakaru. Lafiya ko kum

a dukanmu za ku yi?"

"Kun ga ku fice daga gidan nan tun kafin in aikata abin da zuciyata ta ke ayyana mini"

Deena ta karasa maganar tare da nuna masu hanya fita.

"Eyee! Lallai kuwa kin kai! Ke har kin isa ki nuna mana hanyar fita? Ko da ya ke za ki iya ai

kata komai domin wadda kika baro gida ita ma haka kika ga ta na yi"

Auta ta karasa maganar tare da mi

ƙ

ewa.

Lafiyayyan marin da Deena ta wanke ta da shi ba shiri ta ji tayi zaman 'yan bori a kasa.

Kafin Farida ta samu zarafin magana Shukura ta fara magana a

cikin kakkausar murya.

"Ku kwashi ru

ɓ

a

ɓ

un kafafuwanku ku fita daga gidan nan kafin mu saka me gadi ya fita da ku ta karfin tsiya. Ku har wata tarbiyya ce da ku daga ku har tsohuwar uwar ta ku ba ku wuci In ba ku tarbiyya ba. Ku In Banda na yi sanyi da

kuma gudun

ɓ

acin ran me gidan nan yau da sai na saka an kulle mini ku a cell!"

"Karya kike

ɗ

iyar matsiyata. Wacece ke in Banda karuwa wadda ta gama tamba

ɗ

ewarta a titi. In 'ya'yan halak na magana shegu shuru suke yi da bakinsu"

Rufe bakin Farida yayi daida

i da tsinketa da mari da Shukura ta yi. A zafafe ita ma Faridar ta

ɗ

aya hannu da nufin ramawa

Caraf! Shukura ta ri

ƙ

e hannun

"Kika bari hannunki ya sauka a jikina sai na raba hannun da gangar jikinki"

Kafin ka ce me dambe ya kacame a tsakaninsu.

A

rikice Inna Tala ta fito sai dai ta rasa ta yadda zata raba wannan fa

ɗ

an. Dole ta koma gefe ta na bada hakuri amma ina babu me saurarenta.

Su Auta sunji a jikinsu domin ba zaka hada da su Shukura wadanda suka ga jiya suka ga yau ba.

A guje Inna Tala ta fit

a kiran me gadi kada ayi kisan kai.

Ta na fita motar Hisham na kunno kai a cikin gida.

Tun kafin ya fito a mota ta ruga da gudu ta na haki.

Shi kuwa a rikice ya fito domin a tunaninsa wani abu ne ya faru da Manarah da ke goye a bayanta.

"Alhaji ka taimaka

mana kada ayi kisan kai"

Maganar ta datsewa ta yi ta na huttai.

"Me ya faru sanar da ni abin da ke faruwa"

"

Ƙ

annenka ne sun kama Matana da kokawa"

"

Ƙ

annena! "

Ya hau nanata maganar. A fusace ya tunkari falon.

Shukura kuwa jin karar motar Hisham ya sakata

ta yi shirya. Takun

ƙ

afarsa da ta ji ne ya sakata faduwa kasa tana kurma ihu.

"Ka cecemu!

Ƙ

annenka za su kashe mu. Ashe dama su da uwarsu ba su

ƙ

aunarmu ta aiko su su kashe mu. Me muka yi maku haka?"

Jin abin da Shukura ke fa

ɗ

a cike da tsabar mamaki Auta

da Farida suka kalli juna. Hisham kuwa a matukar fusace ya fada dakinsa.

A zafafe Auta ta fara magana

"Makira annamimiya. Duk bariki da Jan sharrinki sai dai kiyiwa waccan " Auta ta karasa maganar tare da nuna Deena.

Dariya Shukura ta kwashe da ita.

"Ku k

ananun 'yan iska ne. Ba ku kunce zaku ja da ni ba? Ku jira fitowarsa."

Rufe bakin ta ke da wuya sai ga Hisham ya fita da belt a hannu. Ba su Farida kadai ba, hatta Deena sai da ta ji hantar cikinta ta ka

ɗ

a.

Shukura kuwa ko a jikinta domin ta san ba su zai

daka ba.

Hanyar guduwa su Auta suka fara nema amma ina jibgarsu ya ke tamkar Allah ya aikosa. Ihu suke su na neman taimako babu wanda ya bi ta kansu.

Ganin dukan ya yi yawa ya saka Inna Tala Shiga tsakiya.

"Kayi wa girman Allah ka barsu haka. Baka

gudun abin da zai biyo baya? Ka san fa halin Mahaifiyarsu. Umman ka zaka ha

ɗ

awa wani tashin hankalin"

Su Farida da suka fahimci in suka tsaya zai iya kashe su a guje suka bar gidan. Suna fita suka yi sa'ar samun napep sai gida.

Napep na sauke su a guje su

ka shige gidan.

A falo suka zube suna zabga ihu ha

ɗ

e da kiran Hajiya.

Ta na

ɗ

aki abin duniya duk ya isheta ta rasa mafita game da wannan

ƙ

addararren ruwa data amso. Ji ta yi kamar muryarsu Auta. Sake kiranta da akayi ne ya saka ta mikewa da sauri ta yo fal

on.

Hango su da ta yi baje a cikin falon ya saka ta yi kansu ta na salati....

Meenat A 'Yandoma

08133562798

MASU BUKAR WASU PAGES

Ɗ

IN DU SHIGA NAN

👇👇👇

LADY'S BEAUTY PALACE

SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE?

KINA SO KIYI HIP

S HAJIYATA KIYI KYAU?

KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI?

KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA?

Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa,

Shin kinason ko koma yar d

agwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?ko kina neman inda za,a gyara maki Kai ne wato saloon

To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san

inganci da gaskiyarsane,

MAZA KI ZIYARCI LADYS BEAUTY PALACE ko ta waya ko ta asalin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login