Showing 45001 words to 48000 words out of 64054 words
baka" Cewar Inna da ta daddage tana fa
ɗ
a masa.
"Na bar muku duka halal malak" Ya fa
ɗ
a da ƙarfi har lokacin yana zabga gudu ko
waiwaye ba ya yi gudun kar a samu matsala Inna ta biyo shi ta mayar da shi
ɗ
akin miciji. Daga Inda Inna take tsaye daga ƙofar gidan da ta fito tana hango yadda ya sha wata uwar kwana a sukwane ko lanƙwasa babu.
Dariya Inna ta yi idanunta a kan motar Ab
id ta juyo ta dawo ciki tana ƙoƙarin rufe ƙofar sai gasu sun fito Imran da Abid.
"Innna har ya tafi baƙon naki?" Cewar Abid yana maida dariyarsa.
" Ya tafi mana amma dai ba baƙona bane baƙon Hassan ne kuma ya sallame su dan kuwa sun sha baƙar azaba
kwakwa dai yau an sha ta a wajen miciji" Ta fa
ɗ
a tana washe baki.
"Na gane Inna" Ya fa
ɗ
a yana daria.
"Ba dai tafiya za ka yi ba?" Cewar Inna da mamaki.
"Ba tafiya zan yi ba kaya za mu
ɗ
akko a mota kin san kayan rabawa ne gobe muka siyo"
"Ikon A
llah wato ka ji ka
ɗ
an ka ji da yawa, yanzu baƙin halin Imirana har ya kai haka, a ce zai tafi siyayyar amma ina garin nan muna gida
ɗ
aya
ɗ
aki
ɗ
aya amma ya kasa gayyata ta na raka shi sai ya je ya
ɗ
akko ka".
Wani kallo Imran ya jefa mata irin na kina kai
kan ki inda Allah bai kai ki ba, kafin ya ra
ɓ
a ta ya wuce wurin motar.
"Au Allah wato ina maganar ma ka wuce ka bar ni wato ga karya yo in ba karya ba waye ake bari yana haushi shi ka
ɗ
ai" Cewar Inna tana bin bayan Imran da harara.
"Rabu da shi Inna
ba gani ba zan tsaya mu yi hira abin mu kuma kwantar da hankalinki indai kina nan to kuwa kafin ki tafi xan kai ki yawo a mota ta mu yi siyayya ki za
ɓ
o abin da kike so in biya ku
ɗ
in" Cewar Abid yana kallon yadda fuskar Inna ta saki lokaci guda kamar an ma
ta albishir da gidan aljanna.
"Allah Abida ka ce akwai za
ɓ
ar abubuwa masu yawa to aikuwa har sa kishiya kuka da sa kishiya tagumi zan
ɗ
akko a wurin siyayyar"
Galala Abid ya yi jin furucin Inna dan shi dai ya ji ana cewa sa kishiya kuka ko tagumi m
aganin mata ne amma kuma mai Inna za ta yi da maganin mata.
"Inna sa kishiya kuka da tagumi za ki
ɗ
auka in mun je siyayya...
"Oh Abida rufani ka saya ni, dan Allah kuke bari sai mutane sun mutu kafin ku binne su.
, yo in ba fallasa auren bashi ba
har na tsaya yin maganar maganin banza da kai(Maganin mata) Magano na ce magano, to indai abin da ka yi zato to Allah tsari gatari da saran shuka, to ni ina nufin kayan ƙwalam wato
kayan ciye-ciyen ne zan
ɗ
akko sa kishiya kuka da tagumi, abubuwa ne zan
ɗ
a
kko masu da
ɗ
i wanda ba za su lalace ba har lokacin da zan gama ZAMAN WANKANA in tafi da kayana gidan Malam sai in ke
ɗ
akkowa ina ci ina jefar da takardar ko ledar yadda Tasalla da ta gani za take rafka uban tagumi da hannu bibbiyu, idan ta shige
ɗ
aki kuma
ta yi ta rusar kuka saboda baƙinciki, shi na ce zan
ɗ
akko kar ka kai ni inda Allah bai kai ni ba ka sa ni a bakin duniya" Ta kai ƙarshen maganar tana kallo Abid da ke ta faman dariyar maganar ta.
"Na gane manufarki Inna, sai Inna ta mu ta Malam bada ka
n ki a sare ki je gida ki ce ya fa
ɗ
i"
"Rass kuwa Abida ai ni ce
ɗ
aya tamkar da miliyan a wajen Malam, kuma wallahi da ka ce Inna tamu sai ka sani wata ƴar bazawarar dariya dan ka tina min da daren jiya" Cewar Inna tana ƴar dariya tana kallon Imran ta g
efen ido dama ganin ya kwaso kaya a mota ya taho ta fa
ɗ
a.
"Mai kuma ya faru daren jiya Inna?" Cewar Abid yana dariyar shi ma
"Hummm kai dai bari Abida wallahi daren jiya ne abokin ka Imirana ya shiga wani hali na a zo a gani, sai ji ka yi Imirana yan
a, Innarmu, Inna ta" Ta fa
ɗ
a tana sakin dariya irin mai ƙular da mutum ganin Imran ya zo wajensu zai fice, wani irin ha
ɗ
e rai ya yi tare da wurga musu wata uwar harara. Abid kwa kawai dariya yake dan har ya hango abokinsa tabbas ya san Imran ba ƙaramar wuy
a ce za ta sa ya ce Innarsa ba.
"Hehehehe na dawo in ji
ɗ
an yawon duniya, to wallahi ban san ana yi ba kunu a maƙota, kuma ban san harara ba sai ido ya fa
ɗ
o ehe" Cewar Inna tana jefawa Imran hararar ita ma har da gatsi ne.
"Ƙyaleshi Inna" Cewar Abid
dariya har kasa magana yake.
"Yo dama ai ba biya shi zan yi ba da ina biya Imirana ai da zamana a gidan nan bai kawo yanzu ba, ni kuwa na fa
ɗ
a masa zama daram, kuma nan gani nan bari farar tunfafiya, labari kwa dole na bayar tun da ya yi abin da za a fa
ɗ
a dan labari sai ma na koma ƙauyenmu in samu abin da za mu ke maimaitawa ni da aminiyata Tsahare muna darawa yo labarin abubuwan da Imirana ya yi daga zuwana zuwa yau ai abin a bayar da labari ne, dan ba tsoronsa nake ba, bada labari kuwa farillah ne tusa
a masallaci, dan wallahi ina sane wai karuwa ta taka matar aure, dan kuwa ni na san karambanin akuya yasa ta leƙa
ɗ
akin kura" Ta kai ƙarshen maganar tana wani juya ido tare da gatsine kamar wata matashiyar budurwa.
Abid kawai dariya yake a haka ya j
e ya bu
ɗ
e motar ya
ɗ
akko wasu kayan da wata leda mai
ɗ
auke da apple mai yawa fari da kore ya miƙawa Inna, ta kar
ɓ
a tana ta godiya kamar ta ari baki, a haka suka baro zauren dan dama a can ne tun da ya same ta za ta rufe ƙofa suka tsaya suke maganar. Ko da
suka dawo ma haka ta zauna tana ta baiwa Abid labari dan haka kuwa ya zauna yana ta dariya har da riƙe ciki, amma kuwa saboda soyayya da kuma kyautatawar da Abid ke mata, Inna bata bari Abid ya ga miciji ba, dan ƙofar ma ta kulle bayan ta maida Hassan
ɗ
in
kan gadonsa dan kar Abid ya gani ya firgita dama hausawa sun ce zuciya na son mai kyautata mata.
Bayan tafiyar Abid Inna ta bu
ɗ
e jakar kayanta ta
ɗ
akko wani abu ta saka a cikin
ɗ
an tofinta (Siket da tsofaffi suke sakawa daga ciki wand ake
ɗ
inka musu har
da aljihu a jiki) Bayan ta sanya a aljihun
ɗ
an tofin nata ta cewa Sadiya za ta fita ta
ɗ
an zaga ƙafarta dan ita ta gaji da zama wuri
ɗ
aya, Sadiya kwa ta ce a dawo lafiya dan ita ma so take Innar ta fita saboda ko ka
ɗ
an in tana gidan sai an samu wani akasi
n. Baki ta ta
ɓ
e ta
ɗ
auki mayafinta ta yafa sannan ta
ɗ
auki goro guda
ɗ
aya take ci abinta ta fita. Tun da ta fito hanyar da Malam Isuhu ya bi ta nan ta bi tana yi tana kallon sawun ƙafarsa da ya yi ta sheƙa gudu
ɗ
azu dan sawun har wani nitsewa yake a cikin
ƙ
asa saboda yadda ake taka shi da ƙarfi, kalla kawai ta yi tana dariya wai mai sittin wata kan wata sai gashi ko izifi
ɗ
aya bai karanta ba a
ɗ
akin Hassan. Tafiya take abinta hankali kwance, tana cikin tafiyar, wata mota mai baƙin gilashi da wasu ke ciki su
na kallon hoto a waya
ɗ
ayan ya kalli
ɗ
ayan ya ce
"Ita ce"
Aikuwa da uban gudu motar nan ta sha gaban Inna dama wajen duk ba mutane Inna da ta tsaya kallon ikon Allah ganin mota ta sha gabanta kafin ta gama tunani sai gani ta yi an fito daga ciki a
n fisgeta an shiga da ita motar an banke ƙofa an kwasa da uban gudu...
Masu fitar min littafi ki sani haƙƙina ne, dan haka ke ma da kike karantawa haƙƙina ne kuma baki biya ni ba.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First cla
ss: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin ku
ɗ
i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt
ɗ
in Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntu
ɓ
i wannan no +22785885134
3
️
4
️
⃣
5
️
⃣
➡
️
4
️
⃣
6
️
⃣
Tun da suka saka ta a mota ta fara w
urwurga idanu, mutum hu
ɗ
u ne a cikin motar gaba
ɗ
aya suna sanye da kayan sojoji,
ɗ
aya yana jan motar shi ka
ɗ
ai ne bashi da kayan sojoji. Mutum biyu ne suka sanya Inna a tsakiya kallonsu take tana so ta ga ko ta ta
ɓ
a ganin wani, amma babu wanda ta gane, baki
ta bu
ɗ
e za ta yi magana amma
ɗ
ayan ya
ɗ
aga bindiga ya
ɗ
ora mata a kan ta hakan ne ya sanya Inna ta ja bakinta ta yi shiru dan duk abin ta bata wasa da rai da lafiyarta.
Gum ta yi da bakinta bata sake yinƙurin yin magana ba su ma kuma duk cikinsu tun da
ta shigo motar bata ji wani daga cikinsu ya yi magana ba.
Wata unguwa suka nufa da babu hayaniya sosai a ƙofar wani get suka tsaya horn aka yi mai gadi ya zo ya bu
ɗ
e ƙofar suka shiga ciki Inna kuwa sai rarraba ido take yi dan ta kasa gane dalilin
da ya sa aka
ɗ
akko ta. Tunani ta fara yi ko ƴan yankan kai ne suka
ɗ
akkota, duk da dai ta gansu da kakin soja a jikinsu amma hakan ba zai hana ta zargesu ba saboda yanzu ƴan bindiga suna kashe sojoji su
ɗ
auke kayansu suke sanyawa, dan dai ta san wancan kar
on da aka
ɗ
akko ta daga gidan masu ku
ɗ
in wannan jeji aka nufa da ita sa
ɓ
anin yau kuma da aka nufo cikin gari kuma ƙeraren gida na gani na fa
ɗ
a.
Haka dai ta daure saboda bakin bindigar da ke kanta. Suna fitowa ita ma haka ta bi ayari ta fito bisa bin uma
rnin da aka bata, tun da suka fara tafiya zuwa ainihin cikin gidan take ta kalle -kalle har suka samu nasarar shiga cikin wani falo madaidaici mai shegen kyau. Su duka wuri suka samu suka ƙame babu wanda ya nemi wurin zama Inna kuwa ganin tsayuwar ba za ta
mata ba sai ta zauna a ƙasan kafet gudun kar ta hau kujera a harbeta.
Suna nan, sai ga wata yarinya ta fito cikin wasu ƙananan kaya tana riƙe da abin wasanta, Tun da ta fito Inna ta ƙura mata ido tana mata kallon sani sai dai ta kasa tuna inda ta sa
n yarinyar tana ta kiciniya da ƙwalƙwalwarta a kan ta barta ta tuna ina ta san yarinyar amma kafin hakan sai ganin mutum ta yi ya fito daga cikin wani
ɗ
aki shi ma sanye da kaya amma ba na sojoji ba. Kallo
ɗ
aya Inna ta masa ta gane shi a take ta tuna da ind
a ta san yarinyar ma.
"Sojojo kai ne dama nan gidan ka ne ina tsohuwar matarka mai shegen tsoron nan kamar farar kura, ko da yake ma ba ita ka
ɗ
ai ce matsoraciyar ba har da...
Wata uwar tsawa da ya daka mata ita ce ta hana Inna da ta washe baki tana
ta kau
ɗ
i da kara
ɗ
i ƙarasa maganar, dan tun kan ya ƙaraso ma tsakiyar falon ta fara zuba.
Cikin
ɓ
acin rai ya ƙaraso tsakiyar falon gaba
ɗ
aya suka shiga sara masa kujera ya nema ya zauna har lokacin ransa a matuƙar
ɓ
ace yana aikawa Inna wani mugun kallo.
Ƴ
ar tasa ce ta zauna a kusa da shi tana ta ra
ɓ
ewa a jikinsa da alama dai bata manta da inda ta ga Inna ba.
"Ke inyamura ina uwaki take, yo ina so in miki magana amma na san bakya jin hausa, ina so in ce ki kira min uwaki tsohuwa mu gaisa ko yau ma tana
can tana kwalliyar tana shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa sai...
Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara yiwa Inna tsawar da ta sanya ta yi shiru sai dai yanzu tun da ta ga abokin Imran gaba yake da su, wato ogansu ne sai ta ji duk bata tsoronsu dan ta san da
i duk tsiya ba lallai su harbe ta ba.
"Oh ni Azumi Allah ya tsaga min bakina amma ku hana ni magana, na rasa ma mai yasa kuka
ɗ
akko ni duk da dai na san ruwa ba ya tsami banza amma dai da walakin goro a miya"
Babu wanda ya mata magana dan abokin Im
ran ya
ɗ
aga musu hannu alamar dakatarwa.
Kallon su ya yi cikin bada umarni ya ce
"A kai ta wannan
ɗ
akin" Da kallo Inna ta bishi tana mamakinsa amma sai ta miƙa hannunta ta ta
ɓ
o saitin aljihun
ɗ
an tofinta ta ji abin da ta ajiye yana nan hakan ya
sanya ko gardama bata musu ba suka tafi da ita. Har sun je ƙofa za su fita ta juyo ta ce
"Gobe sunan Hassan dai mutuminka ina fatan za ku je" Wani haushi ne ya rufe shi yana ayyanawa a ransa tabbas tsohuwar nan yau sai ta banbance tsakanin aya da tsaku
wa, dan sai ya tabbatar ta gane akwai banbanci tsakanin ki
ɗ
a da karatu. Ƙeyarta suka tisa har
ɗ
akin da aka bada umarni a kai ta,
ɗ
akin a can bayan gidan yake kuma a rufe yake sai da suka bu
ɗ
e
ɗ
akin suka shigar da ita ciki wani daga cikinsu wanda ya zo a ku
jerar mai zaman banza lokacin da suka taho a motar har ƙeya ya tallewa Inna, amma bata ce komai ba sai dai ta ayyana za ta rama ne.
Sai da suka gama harare -harare da wani tsawace -tswacensu sannan suka fito suka rufe Inna a cikin
ɗ
akin suka sanya mukul
li sai dai basu cire mukullin ba daga waje suka barshi a jikin ƙofar.
Sai da suka yi kamar minti goma da fita Inna ta tashi ta yi dibara ta
ɗ
an bu
ɗ
e windown sai da ta tabbatar babu kowa a kusa sannan ta bu
ɗ
e windown duka, wani dogon icce da ta samu a
ɗ
akin ta
ɗ
auka ta sanyo shi ta windown a hankali cikin dibara ta saƙala iccen a jikin ƙarfen key holder na jikin mukullin, cikin dibara ta cire mukullan daga jikin ƙofar sai dai tana ƙoƙarin shigo da iccen ta windown sai mukullin ya zame daga jikin iccen ya
fa
ɗ
i ƙasa.
A haka ta rinƙa yin dibara har dai ta ci nasarar
ɗ
akko shi a jikin iccen, daga ƙasan ta shigo da shi cikin
ɗ
akin, jijjiga kai kawai take tana dariya ta ce
" Ta yaro kyau take bata ƙarko, tabbas yaro bai san wuta ba sai ya taka, lallai
yau allura za ta tono garma, su a ganinsu sun garƙame ni, basu san na fisu wayo ba ko dan dogaye ne dan bashaushe ya ce dogo da hankali dace ne" Cewar Inna tana ta ƙoƙarin cire mukulli
ɗ
aya daga jikin key holdern dan gaba
ɗ
aya mukullan iri
ɗ
aya ne hakan ya
nuna duka na
ɗ
akin ne.
Bayan ta cire
ɗ
aya sai ta sanya a cikin aljihunta, bayan ta
ɗ
akko wata ƙaramar farar leda ƙulle da wani abu, tana gya
ɗ
a kai alamar za ku gani. Sai da ta adana mukullin da ta cira ta yi murmushi ta ce
" Mu je zuwa da ni Azumi
kuke zancen ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha"
A hankali