Showing 3001 words to 6000 words out of 64054 words
da a
ce za ta samu dama babu dalilin da zai sa ta rama cin mutuncin da Inna ta yiwa sana'arta.
Kowa dai bai furta komai ba, dan gudun Sadiya da Ashrof kar su ji haushi, a haka aka cigaba da zana musu ƙunshi ja da baƙi
.
Inna kuwa tana fita ta nufi bayi ta yi tsarkinta ta fito ta fara
ɗ
aura alwala. Ƴan falo ana ta hira kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Hassan da Husaini kuwa Sadiya ta ajiyesu a bedroom saboda bacci suke kuma bata son hayaniya ta tashe su. Lokacin d
a Sadiya ta fita za ta jefar da gashin danya fita daga kanta da aka mata kitso, kawai ƴan falo sai ganin miciji suka yi ya fito zulululuu daga cikin
ɗ
aki, gaba
ɗ
aya aka shiga gudun famfalaƙi kowa yana neman ceton rai haba wa Inna da ke zaune tana alwala lok
acin tana wanke fuska sai ganin mutanen falo ta yi suna fitowa kamar ana korosu kowa yana kama gabansa, da mamaki ta dakata da alwalar da take tana so ta gano abin da ya sanya su wannan gudun. Sadiya da ta juyo daga wajen bola ta hango mutane kowa a ru
ɗ
e,
Ashrof da ta yi wajen bayi ce ka
ɗ
ai ta iya nuna mata hanyar falo da hannu alamar akwai wani abu tana nuna mata kwa ta yi wuff ta fa
ɗ
a bayi ji kake gararaf ta banko ƙofa, ta jingina da ƙofar daga cikin bayin.
Inna ta kasa gane dalilin da ya sa ake tseran
ta bu
ɗ
e baki za ta fara sababin nata ba sai hango miciji ta yi ba ya fito daga falo, idanu ta zaro a ki
ɗ
ime ta tashi daga kujerar da ta zauna take yin alwala, ji kake gwaraf ta bi ta kan butar alwala tana kama zaninta da ke neman fa
ɗ
uwa, mamaki take duk s
awayar da Hassan ke yi ma iyakarsa ya motsa jela ko kansa amma yau ya fito da kansa har tsakar gida, da alama farautar rai ya fito, aikuwa Inna ƙafa me na ci ban baki ba sai ta nufi hanyar kicin ko sauraren Sadiya da ke ta faman mata maganar ta kalli Hassa
n ya koma miciji ya fito bata yi ba ta fa
ɗ
a cikin kicin har tana gware da bango sosai goshin ya bugu amma babu damar murzawa haka fa daure tana neman mafaka.
Tana shiga kicin
ɗ
in ta hango ƙafar wata ta leƙo daga cikin lokar kicin
ɗ
in da nan take niyya
r shigewa, amma ganin kusan mutum biyar a ciki sun cunkusu wata ma a kan wata take sai Inna ta fara rarraba ido.
"Wannan tashin hankali da me ya yi kama ni Azumi, a ce kai kullum baka da kata
ɓ
us baka da kwanciyar hankali" Ta fa
ɗ
a a ranta hankali tashe,
hango yarinyar nan me ƙunshi Inna ta yi a bayan ƙofar kicin
ɗ
in daga ciki sai raba ido take tana ƙifƙiftawa wata harara Inna ta doka mata tana juyawa ta fara waigen mafaka, ganin danƙareriyar freezer wacce suke ajiye kayayyaki, karamin frige
ɗ
in kuma shi
ne a falo da hanzari Inna ta bu
ɗ
e freezer aikuwa ta yi sa'a babu komai a ciki ba ma a kunne take ba.
"Yawwa Allah ya bani mafakar
ɓ
uya, haka kawai Halima ta haifa mana jaraba shi kuma wancan mijin nata me kai tun na haihuwa ya hana a kai yaron bakin ruw
a su
ɗ
au kayansu ya bar mana shi kullum mu hankali rabe a biyu" Cewar Inna tana kiciniyar shiga freezer, sai da ta shige ta miƙo hannu za ta rufe murfin sai ganin yarinyar nan me ƙunshi ta yi tana ƙoƙarin shiga ita ma da sauri Inna ta tashi tsaye daga
ɗ
an
ɗ
osana
ɗ
uwawunta da ta yi a ciki ta tsugunna ta galla mata harara ta ce.
"Gidan uwaki za ki shiga, na ce gidan uwaki ne nan
ɗ
in za ki shiga?" Cewar Inna tana yi tana dogon wuya dan kar micijin ya zo kicin ya farmata.
"Ki bari mana mu shiga tare baki
ga na cikin lokar nan ba ma duk cunkusuwa suka yi wani kan wani, zama da ba na da
ɗ
i ba yaushe mutum zai ce baya son matsi"
"Ai wallahi ko ha
ɗ
iyeki micijin nan zai yi sai dai ya ha
ɗ
iye, ba ke taƙamarki fitsara ba to ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta
" Cewar Inna tana ture hannun yarinyar daga jikin freezer da shige tare da rufe murfin freezer.ƙwafa yarinyar ta yi ta duba mukullin freezer ta ga yana jiki, aikuwa ta kulle, ta
ɗ
auki wayar freezer ta jona a socket ta kunna ta ce .
" Ma ga yadda za ki y
i" Ta fa
ɗ
a tana komawa mafakarta ta
ɗ
azu bayan ƙofa ta ra
ɓ
e tare da
ɗ
aukan wani buhun shinkafa danya ƙare ta lullu
ɓ
a duk gudun kar miciji ya ganta.
A tsakar gida kwa Sadiya ta rasa yadda za ta yi, ta ta
ɓ
a micijin ya fi sau a irga amma yaƙi komawa mutum
kawai sai ta samu wuri ta durƙushe take rasgar kuka abinta da abin ya girmi tunaninta.
A kicin kuwa Inna da ke cikin freezer ta fara jin wani sanyi a ƙafafunta, dan babu takalmi a ƙafarta tun lokacin da ta kwaso fa gudu ta silleshi jin zai hanata wal
i wajen gudu. Jin wani sanyi yana ratsa ƙafafu da jikinta sai abin ya bata mamaki dan ta san dai da idonta ta ga wayar freezer ma bata jikin socket, amma kuma ya
ɗ
auki sanyi sai hakan ya bata tsoro sosai, jim ka
ɗ
an kawai sai ji ta yi gaba
ɗ
aga freezer ta
ɗ
a
uki mugun sanyi, a take ta fara karkarwa jin sanyi na ratsata ta ko ina.
"Habunallahu wa ni'imal wakil, kar dai shegiyar yarinyar nan ce ta rufeni a ciki" Cewar Inna lokacin da take ƙoƙarin bu
ɗ
e freezer ta ji ta a rufe gam. Jin sanyin ya yi yawa ta fara
share hawaye tana cewa.
"Malam ka ga Azuminka dai ko suna ba a yi ba amma ina kar
ɓ
ar uƙuba kala-kala daga wannan sai wannan sai ka ce wacce uwarta ta ce ki je kya gani, ko dai baka yarda da tahowata ba ZAMAN WANKAN nan ba har zuciyarka, a ce ina ganin
ƙ
alubale kamar an min baki" Ta fa
ɗ
a tana sa hannu ta bugi jikin freezer. Ƴan cikin loka da me ƙunshi da ke lullu
ɓ
e da buhu da bata gane daga inda ƙaran ya fito ba duk zatonsu miciji ne ya ƙaraso kicin
ɗ
in, ƴan ckn lokar a take suka cure a wuri
ɗ
aya kamar ƙ
arago, ta cikin buhu kuma ta tuƙunƙune gefen buhu ta cusa a bakinta gudun kar tsoro ya sa ƙara ya ku
ɓ
uce mata micijin ya ga ma
ɓ
oyarta ya farmata.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin ku
ɗ
i ne 300
Za a tura ta
wannan accaunt
ɗ
in Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntu
ɓ
i wannan no +22785885134
2
️
⃣
3
️
⃣
➡
️
2
️
⃣
4
️
⃣
"Haba jama'ar annabi ku kawo min
ɗ
auki mana, ni ba tumatur b
a ba gwanda ba amma gani a firinji sai
ɗ
aukan sanyi nake" Cewar Inna cikin
ɗ
aga murya tana jin wani kuka na taho mata. Wata atishawa ce ta taho me ha
ɗ
i da majina saboda sanyin da ya gama ratsa ƙasusuwanta, so take ta yi ihun da kowa zai ji ta, a san cewa
tana cikin na'urar bada sanyi dan ta lura duk kwakwazon da take ba wanda ya ji ta.
"Halimatus Sa'adiyya, ki bar micijin nan ki taho ki bu
ɗ
e firinji kafin in yi ƙanƙara, ko masasssara ta kamani Malam ba zai yafe muku ba, Asharofa, Asharofa, ki fito daga
bayin nan ki zo ceton rai " Cewar Inna da sanyi ya gama ratsa muryarta har ta fara shaƙewa ta fa
ɗ
a tana sakin kuka. Jin shiru babu alamar ma ana jiyo ta sai ta fara magana a ranta.
"Yau ni Azumi wannan yarinyar akwai ƴar ƙundun buhun uba, yarinya ƙaram
a cakuru kuci cikon bancin ta garƙame a cikin wurin nan firinji sai aikinsa yake ni kuma ina
ɗ
aukan sanyi, wannan ZAMAN WANKA bai ƙare ni da komai ba" Ta fa
ɗ
a tana sanya hannunta ta rufe hancinta saboda sanyin da take shaƙa kamar wanda aka jefa ƙanƙara a c
ikin hancin.
"Ƴan nepa ku taimaka ku
ɗ
auke wuta dan shi firinjin ba hankali ba gareshi bare ya san Azumi ce a ciki, ya san ba fura bace ya dakata da aiki" Cewar Azumi tana
ɗ
aga ido ta kalli
ɗ
an ƙaramin ƙwan da ke cikin freezer ya kawo haske abinsa.Hannu
ta kai ta zage ƙarfinta duk da a takura take saboda matsi amma a haka ta jimƙe hannunta ta daki jikin ƙwan tana cewa.
"Wallahi gwara na fasaka firinjin ya lalace gaba
ɗ
aya a kan ina ji ina gani in ke zaune cikin ƙanƙarar nan, ni ba me rayuwa a turai ba,
in zo in sandare in mutu a banza a
ɗ
akko ni a daskare makara ma bata kar
ɓ
eni ba dan ba tanƙwasuwa zan yi ba yadda nake a tsugunnan nan a haka zan ta zama, ko kabarin na san sai ko a gina min me zurfi a zura ni a ciki kawai, babu damar a kwantar da ni, ko
ƴan gaisuwar mutuwata suka zo, na san sai dai suke cewa ashe azumi sa'i ya yi to Allah sa tsugunno hutu ne, dan babu me cewa kwanciya hutu ce, dan a tsugunne nake ba a kwance nake ba"
Ta fa
ɗ
a lokacin da ta naushi jikin ƙwan amma ko gezau be yi ba bar
e ta sa ran zai fashe,ssi wani zafi da hannun ya
ɗ
auka. Hannu ta kai ta shafo goshinta inda ta bugu
ɗ
azu a garin gudun ceton rai, wurin ya yi ƙullutu ga zafi, tana ta
ɓ
awa wani tausayin kanta ya kamata haushi ne ya sa ta shiga bugun freezer ba ƙaƙƙautawa da
n ta san idan bata yi da gaske ba haka za ta mutu babu wanda ya sani.
Ƴan cikin loka ƙaran bugujn freezer da Inna take sai suka
ɗ
auka micijin ne ya ƙaraso jikin lokarsu yake bugawa hakan ya sanya kowacce ta tsure, wata ƴar gidan ƙanwar Mama da yake
ƴ
ar siririya ce ita ce daga ƙasa sai wata bazawara ƙatuwa ƴar uwar Imran a kan ta tsabar yadda bazawarar ke da nauyi kuma a kan siririyar budurwar take dakyar take jan numfashi dan gaba
ɗ
aya ta danne mata har wajen kanta amma saboda tsoro sai bata ce komai
ba, wannnan ƙaran da ya sanya suka firgita sai ƙatuwar ta
ɗ
an muskuta
ɗ
uwawunta aikuwa tsabar tsurewa ta saki wata uwar tusa da ta gama ratsa hancin siririyar ji ta yi kamar an saka hancinta a cikin kashi, tsabar wari har wani
ɗ
aci-
ɗ
aci ta ji a maƙoshinta.
Kai ta shiga girgizawa, tsabar. Inna da bata san wainar da ake toyawa ba tana ta ƙoƙarin a zo a ceceta dan ta san har ƙwara na cikin lokar sau dubu a kan
ita da ke ciki duk ta fara sandarewa dan da wani zai ta
ɓ
a jikinta yanzu sai ya ji kamar ƙanƙara ya t
a
ɓ
a. Wani uban zabura ƙatuwar matar ta yi aikuwa kanta da ke dab da saman lokar ta ciki ya bada wani gum, gumewar da ta yi a kanta sai kuwa ta sake sakin tusar, gaba
ɗ
aya lokar ta ha
ɗ
e da wari su duka a takure suke, ba dan micijin nan ba da babu wanda zai
iya shaƙar numfashi saboda
ɗ
oyi amma tsoro ya sa ba za su fito ba, siririyar nan jin an ƙara sakar mata tusa haushi da takaici ya sa ta
ɗ
an gota kanta daga saitin
ɗ
uwawun matar dan hancinta ma a wajen maraba biyu yake ta tsagar
ɗ
uwawun matar aikuwa cikin f
usata ta bu
ɗ
e bakinta ta gantsara mata cizo a
ɗ
uwawun wani azababban zafi ne ya ratsa matar da ta manta da cewar a
ɓ
oye suke ta hangame baki ta saki wani uban ƙaran ta ce.
"Wayyo ya gantsara min cizo a
ɗ
uwawu" Duk ta ru
ɗ
e da zafin cizo sai ta zata micij
in ne ya shigo ya cijeta dan ƙuncin da suke ciki ko ƙasa baka iya kallo duka a wuri
ɗ
aya suke a cure. Yarinyar nan me ƙunshi jin an ce an yi cizo a
ɗ
uwawu sai ta fara karkarwa dan ta san ita ma micijin dole ya ganta tunda ya ga na cikin loka ma bare ita ai
kuwa ta saki wani kuka, ga buhun da ta tuƙunƙuna ta saka a bakinta sai sautin kukan ya bada wani wuuuuu kamar wata jiniya. Inna da ke cikin freezer jin ihun da kuma ambaton da aka yi na an yi cizo sai ta ce.
"Wallahi gwara ku a kaina duk tsiya ai inda s
auran kwananku za a sa muku maganin dafin miciji ku warke, idan kuma kuka mutu ai zaku kwanta a kabarinku a kan ni da sai dai ake Allah sa Azumi tsugunno hutu ne" Ta fa
ɗ
a tana sakin kuka tana da na sanin zuwa ZAMAN WANKAN ma gaba
ɗ
aya.
Sauran ƴan cikin lok
ar kuwa sai tsoro ya ƙara shigarsu ji micijin har ya shigo lokar ya yi cizo banda wacce ta yi cizon da ta san ita ce ta yi cizon ba miciji ba, hakan ya sanya
ɗ
aya kama jikin
ɗ
aya ta damƙe da hannu biyu aikuwa wacce aka damƙa ta wage baki ta saki ihu ta ce.
"Wayyo an damƙe min nono, wayyo ni Allah na, ni ba a min ƙunshi ba amma za a min lahani" Ta fa
ɗ
a cikin kuka da azabar da ta ji a jikinta, da yake yarinya ce ba wata babba ba irin ƙirgen dangin nan ne ta fara wanda ko
ɗ
an bigewa ka yi a jiki sai ka ji a
zaba. Ita kuwa wacce ta damƙi yarinyar bata ma san abin da ta yi ba, jin wai an ce ta damƙi nono da sauri ta saka dan ita bata ma san ina ta kama ba ta dai ji fitsarin yarinyar na gangara a kan ƙafafunta.
"Wayyo Allah wallahi da a ta
ɓ
a min wurin nonona,
ko da kuwa da
ɗ
an yatsa ne gwara in bada kyautar naira dubu saboda azabar ciwo amma kin zo kin damƙa kamar kin samu ƙanzo" Ta fa
ɗ
a cikin kuka, babu wanda ya ce wani abu dan yanzu ta kai- ta kai ake.
"Gwara ke nono aka damƙa, wayyo
ɗ
uwawuna za a cire mi
n fatar" Ta fa
ɗ
a jin an ƙara cafka da haƙori dan tana sakin tusa ita kuma ta ƙasanta ke gatsara mata cizo.
Inna da ke cikin freezer ta ƙyalƙyale da dariya duk da halin da take ciki, amma jin ana damƙe-damƙen
ɗ
uwawu da nono sai abin ya bata dariya ta
ce a zuciyarta
"Yau dai ana dara ga kuma dare ya yi, Hassan duk ya rabawa kowa aikin wahala"
Me ƙunshi ma kukan da take ne ya ha
ɗ
e da dariya a ranta ta ce.
"Ta
ɓɗ
i yau da a ce ba a halin ƙaƙanikayi nake ba dariyar da zan yi sai cikina ya yi ciwo,
dan ko ni lokacin da na fara ƙirgen dangi ko wanka na zo sai dai in zuba musu ruwa in
ɗ
auraye su, ba na yarda in sa soso in wanke saboda azaba" Ta fa
ɗ
a tana dariyar da ta kusa fitowa fili saboda yadda dariyar ke cinta.
"Inna! Inna!! Inna!!!" Inna ta jiy
o muryar Sadiya tana ƙwala mata kira tun ƙarfi.
"Inna dan Allah ki fito ki tayani mu dawo da Hassan gashi can ya kama hanyar ƙofar gida zai fice kuma ƙofar ba a rufe take ba, ni ka
ɗ
ai ba zan iya ba dan ya ƙi tsayawa ko
ɗ
aukansa zanyi zulalewa yake" Cew
ar Sadiya tana kuka ta rasa yadda za ta yi hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, bata so
ɗ
an nata ya fice duk da kasancewarsa a siffar muciji tana ƙaunarsa, Allah sarki uwa!
"Mtssss" Inna ta ja wani dogon tsaki ta ce.
"Banza ta kori wofi ma kenan y
o Allah na tuba da ba a cikin firinjin nan nake ba ma babu abin da zai sa na zo wallahi, da kaina zan ka
ɗ
ashi ya tafi, gwara ma ya je ya fice abinsa wataƙila ma wahalarki ce ta yanke, yo Allah na tuba zama da wannan abu a gida ai jafa'i ne, ya je can daji
ya samu ruwa ƴan ruwa su ja abinsu mu huta, ga Husaini nan ya isa" Ta fa
ɗ
a tana
ɗ
a
ɗɗ
aga kai take kallon saman freezer.
"Dan Allah