Showing 36001 words to 39000 words out of 64639 words
sarari ki kira ni."
Wani ƙayataccen murmushi ta yi sannan ta masa reply na godiya, danna power wayar ta yi tare da koma kwanciya ta fa
ɗ
a kogin tunanina.
Fatant
a da duk burinta bai wuce ta samu lafiya ba da gaggawa domin ta ci gaba da sharholiyarta, Allah ya gani kwana biyun nan da bata fita ba duk a tauye take jin kanta, ga shi kwabon Kowa ya daina shigo ta, 'yar sana'ar da take ta kawar da hankalin mutane ma, k
wana biyu bata yi ba, saboda ba lafiya.
Tunanin take taya zata iya kashe wannan ku
ɗ
in da Alhaji ya turo mata ba tare da an tuhume ta a gida ba?
Washegarin ranar da misalin ƙarfe sha biyu na rana Sofi ta yo wanka, sannan ta shirya a cikin atamfa rig
a da siket da suka
ɗ
ame ta.
Ba ta yi wata doguwar kwalliya ba, hoda kawai ta shafa sai
ɗ
an man le
ɓ
e, amma fuskarta ta
ɗ
an yi ma'ana duk da cewa ba wata kyakkyawa ba ce, sannan ita ba fara ba ce, haka nan kuma ba baka ba ce, sai dai a kirata da chocolate c
olour.
Har yanzu kana iya ganin sauran mikin a gaban goshinta.
Wani yalolon ƙaramin mayafinta ta
ɗ
auko, da ganinsa kasan ya
ɗ
an kwana biyu, yana riƙe a hannunta ta fito zuwa
ɗ
akin Inna, lokacin fitar Baba kenan daga gidan, tun da dama can shi ba aikin
fari ba na baƙi, kawai yana zaman jiran na Allah ne.
Ba ko sallama ta fa
ɗ
a
ɗ
akin, Inna tana zaune akan yagaggiyar ledar
ɗ
akin da ta gama yin ƙura, akanta ta tsaya ƙerere ta ce "Inna ni zan fita."
Da mamaki Innar ta
ɗ
ago kanta ta sauke dubanta kan fus
kar Sofi "zuwa ina kuma Safiya? Shin ko kin manta baki da lafiya ne?"
Ɗ
auke kai Sofin ta yi tare da juyawa ta fara tafiya tana fa
ɗ
ar "Ni nasan inda za ni Inna, kuma karki damu da ni ai na ji sauƙi."
Innar bata kuma cewa ƙala ba, sai sake baki da ta y
i galala.
Har Sofi ta kai Ƙofa ta ci burki ba tare da ta juyo ba ta ce "Inna ki mun addu'a, Allah ya sa na dace da samun abinda zan fita nema, domin kuwa in har na rasa wannan damar akwai matsala."
Daga haka ta ƙarasa ficewa daga
ɗ
akin kana ta bar gi
dan gaba
ɗ
aya.
Tafe take tana ta famar sauri tare da addu'ar Allah ya saka ko labarinsa ta samu a gun.
Ta zo wucewa ta wajen Magama Uku ta hango Sakina tsaye akan
ɗ
aya daga cikin layuka ukun ita da wani saurayi, suna tsaye daf da juna, kai da ganin gay
en kasan irin tsagerun yarannan ne da iyayensu suka sallamawa duniya su.
Ɗ
auke kai ta yi kamar ba ta gan su ba ta bi
ɗ
ayan layin ta wuce tana girgiza kai.
Tsaki ta ja "mtssw" a ranta ta ce "Allah ya waddan naka ya lalace, dama haka duniya take matuƙar
ba zaka iya kame bakinka daga aibata wasu ba, to abun kan iya komawa kan yayanka. Nan ba zagin da Iya mai bakin Aku bata mana, ashe mai bunu a gindi ne ke kai gudunmuwar gobara."
Wani tsakin ta kuma ja tare da ƙara saurin tafiyarta.
A gida kuwa, ko d
a Hanee ta tabbatar da ficewar ƙanwar Tata, ga shi Maryam tana Makarantar boko ba kowa a
ɗ
akin sai ita ka
ɗ
ai.
Da sauri ta bu
ɗ
e idonta tare da tashi zaune ta janyo wayarta tana murmushi cikin nisha
ɗ
i ta ce "Bari in yi amfani da wannan damar na rage zafi."
Alhaji Saminu ta dannawa kira, har kiran ya yanke bai
ɗ
aga ba, tana ƙoƙarin sake kiran shi ne kiransa ya shigo wayarta.
Fa
ɗ
a
ɗ
a murmushinta ta yi sannan ta yi gyaran murya, cikin zaƙuwa ta
ɗ
auka.
Daga can
ɓ
angaren Alhaji ne ya fara magana kamar haka
"Hanee Baby! Ya, kin saku kenan?"
Cikin wata iriyar murya mai sanyi ta ce "eh Alhajina kwana biyu, jikina da Ruhina sun raunata sosai."
Murmushi mai sauti ya yi kana ya ce "to ya jikin?"
"Ba sauƙi." Ta amsa a wasance.
"Subhanallah! Menene ya ra
unatawa Babyn Ruhi da gangar jiki?"
Ƙ
ara rage sautin muryarta ta yi sannan ta ce "Jikina ya raunata ne a dalilin ciwon da ke cinsa, amma shi Ruhina rauninsa ya samu ne a dalilin nisanta da kai, ka ga kenan ta ya zance na ji sauƙi?"
Yar dariya ya yi c
ikin nisha
ɗ
i, sai yanzu ya fahimci inda ta dosa, 'Hanee Baby ba dai Jaraba ba?'
Ya fa
ɗ
a a ransa.
Daga haka hirar ta su ta canza salo, zuwa gur
ɓ
atacciyyar hira, sun jima sosai kafin su kashe waya.
Kwanciya ta yi tana mayar da numfashi, sai murmushi tak
e faman yi ita ka
ɗ
ai "Shi ya sa nake mugun ji da kai Alhaji, ba dai iya soyayya ba, ga sake ku
ɗ
i."
A can layinsu Maheerah kuwa, Sofi ce tsaye a daidai gun da suka yi karo da gayen rannan, sai waige-waige take kamar zata gan shi.
Tunani ta hau yi, shi
n ta ina zata fara nemansa tunda ko sunansa bata sani ba?
"Ki je ki kwatantawa maishagon can sifarsa ko Allah ya sa ya san shi." Wani sashe na zuciyarta ya shawarce ta.
Bata musawa zuciyar tata babta matsa tare da tambayar Haliru Maishago, ko yasan w
ani gaye mai sifa kaza da kaza.
A take ya ce bai sani ba, bata haƙura ba, ta ci gaba da tambayar duk Namijin da ta gani, bata samu amsa ba.
Har ta gaji ta sare, ta kuma cire rai daga tunanin wannan dabarar zata fisshe ta, don haka ta yanke hukuncin
komawa gida domin ta sake sabon shirin nemansa, domin ta yiwa kanta alƙawarin duk rintsi duk wuya sai ta nemo shi, haka kuma sai ta mallake shi. (Ku ji mun jaraba daga ganin mutum rana
ɗ
aya sai ki kwallafa rai a kansa?)
Har zata juya ta tafi kamar anc
e
ɗ
ago kanki, ta hango shi yana tahowa fuskar nan a ha
ɗ
e kamar dai waccan ranar.
Murmushi ta saki a ranta ta ce "Shi dai wannan mutumin kullum fuska a tamke, kamar wanda aka aikowa saƙon mutuwa."
Tana nan tsaye tana wannan tunanin bata ankara ba har
ya zo ya gota ta.
Cikin sauri ta sha gabansa tana fa
ɗ
ar "Mun sake ha
ɗ
uwa My Man, ya kenan?"
Ƙ
anƙantar da idonsa ya yi yana kallonta, shi sai ma yanzu ya gane ta "Ke ce? Me na fa
ɗ
a miki a ranar ha
ɗ
uwarmu ta farko?" Ya fa
ɗ
a a zafafe.
Murmushi ta sak
ar masa tare da cewa "Kamar cewa ka yi kar na sake mu sake ha
ɗ
uwa domin......
Ko da yake na manta sauran idan na tuna na fa
ɗ
a maka."
'Kut lallai wannan ta kai yar rainin wayo wallahi.' ya fa
ɗ
a a ransa.
A zahiri kuwa ƙara ha
ɗ
e fuska ya yi ya ce "Kauc
e mun daga hanya."
"Saboda me?" Ta tambaya.
'Lallai wannan ta cika neman magana, da gani ba natsattsiya ba ce' ya kuma fa
ɗ
a a ransa.
A zahiri kuma cewa ya yi "Saboda bana son ganinki."
Daga haka ya matsa ta gefenta ya wuce yana huci, domin ta ƙ
ara rura masa wutar da ke ci a ransa. Bata bar shi da zafin cin fuskar da masoyiyarsa ta masa ba, tana neman ƙarasa shi. Shin ita wacece?
Da wannan tunanin ya shige motarsa ya fige ta da ƙarfi.
Tana ganin wucewarsa, cikin hanzari ta ƙarasa gun Haliru
Maishago ta ce "Malam ai ka ga wanda mu ka gama magana da shi yanzu ko? To shi nake tambayarka, ka san shi?."
Ta inda ya bi ya wuce Haliru ya bi da kallo kafin ya mai da dubansa kanta ya ce "Me yasa kike tambaya a kansa?"
Ba kunya ta ce "Ka sani ko
ina son shi ne?"
Murmushin takaici ya yi sannan ya ce "Yarinya dama kin haƙura da wannan zancen domin......."
Ko me Haliru maishago zai sanarwa Sofi?
Ku tara da ni a shafi na gaba.
Ku biya biya ku
ɗ
inku ta wannan account
ɗ
in
Account name
: Ruƙayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202
Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.
Ga mutanenmu na Niger masu buƙatar saye zaku biya 4
00F ta wannan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903
Ko da ku
ɗ
inka....
..
Ummu inteesar ce
*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wata
hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
7 Sep, 2021
PAGE 17
BABI NA SHA BAKWAI
Tafiya take cikin ƙuncin
da ra
ɗ
a
ɗ
in zuciya, tuni idanunta suka makance bata ganin kowa bata ganin komai a gabanta sai muradinta, a yanzun ta
yarda da cewa bata da wanda yafi shi a rayuwarta, tana da yaƙinin cewa idan duk duniya ta juya mata baya shi ba zai ƙyamace ta ba balle ya g
uje ta, shi ka
ɗ
ai ne bangon da ya rage mata wanda zata jingina da shi ta ji sanyi a zuciyarta da garwashin wutar kiyayya ke ruruwa a cikinta.
Mintuna ka
ɗ
an suka sada ta da titin unguwar wanda tsabar ru
ɗ
anin da take ciki bata ma san ta zo ba, sai da ta j
i ƙarar ababen hawa da order wasu daga ciki sa'annan ta ankara.
Tun a cikin layinsu mutane ke ƙare mata kallo ganin yanda take tafe cikin yanayin fitar hayyaci ga kuma Uniform
ɗ
inta sun lalace da jini haka fatarta duk ta yi ru
ɗ
u-ru
ɗ
u shacin bulala ko in
a kwance a fatarta har a gefe gefen fuskarta kasancewarta fara ya saka raunin suka bayyana ƙarara.
Haliru Maishago yana zaune ta gifta shi ta wuce, girgiza kai kawai ya yi cikin alamun tausaya duk da bai san me ya faru da ita ba.
Tare Napep ta yi tar
e da fa
ɗ
awa ba tare da ta tsaya yin ciniki ba.
Sai da matukin ya tada Napep
ɗ
in sannan ya ce "Ina zamu.?"
Daƙyar ta iya bu
ɗ
e baki kamar wacce aka yiwa dole ta ce "Dagarma." Daga haka ba ta sake furta komai ba har suka isa unguwar.
Jakarta ta bu
ɗ
e ta
ciro ku
ɗ
in
ɗ
azu da Baba ya bata ta miƙawa mai Napep
ɗ
in, bai ce komai ba ya cire ku
ɗ
insa ya bata canji a ƙasan zuciyarsa yana jimamin abunda ya samu wannan kyakkyawar yarinyar haka.
Cike da ƙarfin gwuiwa da saka rai ta nufi cikin gidan da take tunanin
yanzu nan ka dai ne madogararta, ta saka kai tare da shigewa cikin gidan.
Jama'ar gidan sai ƙare mata kallo suke, wasu daga cikin karuwan suka ƙasa hadiye gulmar da ta zo masu, biyu daga cikinsu ne suka ha
ɗ
a baki gurin fa
ɗ
ar "Bariki alalen gero idan bak
a iya ba sai ta kwa
ɓ
e maka."
Gayen
ɗ
azu wanda ya nunawa Sadiƙu
ɗ
akin da suke ciki ya kalle ta. Ganin yanayin da take ciki ya bushe da dariya ya ce "Duniya ta miki a tishawar jaki ne shi ya sa kika dawo nan? Ko da yake kin zo inda ya dace domin nan gida n
e na kowa, kawai ki zo mu jone don bana tunanin wanda kika zo domin shi zai saurare ki."
Duk wannan maganganun da suke fa
ɗ
a ta ji, sai dai kalma
ɗ
aya bata yi nasarar shiga ƙwaƙwalwarta ba balle ta iya haddace ta.
Wucewa ta yi ba tare da ta tamka musu
ba ta nufi
ɗ
akinsu Jafsee.
Zaune ta same shi akan katifa yana jinyar jiki domin shaƙar da Sadiƙu ya mi shi
ɗ
azu bata wasa ba ce, har ya jiyo ƙamshin mutuwa a dazun.
Duddoo ne zaune kusa dashi yana masa jajen abunda ya faru
ɗ
azun,
ɗ
ago kan da zai yi ya
ganta a tsaye, cikin rawar murya ya ce "Mahee ke ce?" Sai a lokacin Ja'afar ya
ɗ
ago kai ya kalli abokinsa sannan ya sauke dubansa akan fuskarta.
Ras ras! Kirjinsa ya buga da ƙarfi ganin yanayin da take ciki, da ƙyar ya ce "Mahee me kika dawo yi a nan.?"
Wani busasshen murmushi ta masa sa'annan ta zauna a saman carpet na
ɗ
akin tare da fa
ɗ
ar "Ina mai maka albishir cewa na dawo ne domin mu rayu tare har ƙarshen rayuwa."
Kallon baki da hankali ya yi mata tare da hangame baki.
Sarai ta fahimci ƙarin ba
yani yake nema don haka ta koma yin murmushi ta ce "Na dawo nan ne domin mu yi aure, wallahi ko a nan gidan ka ajiye ni zan zauna, yanzu ba ni da kowa daga Allah sai kai."
Kallonta kawai yake, kallon da ba zaka iya fahimtar ma'anarsa kai tsaye ba 'Lalla
i wannan bata da hankali, a yanda suka farfasa mata jikin nan a matsayinta na jininsu, kenan ni me zai faru da ni idan suka kama ni karo na biyu?' ya fa
ɗ
a a ransa.
A fili kuwa miƙewa tsaye yayi idonsa ƙyar a kanta yana fa
ɗ
ar
"Mahee ki rufa min asiri
ki tashi ki koma gida, ko so kike wannan mahaukacin yayan naki ya kashe ni ne?"
Hawayen da suka ƙafe mata tun
ɗ
azu ne suka yi nasarar sake
ɓ
allewa ta ce "Abba ya kore ni daga gidansa da ma rayuwarsa da ta iyalansa ga baki
ɗ
aya, yanzu ba ni da kowa sai
kai, kai ka
ɗ
ai ne na yi imani zaka zauna da ni cikin kowanne hali saboda soyayyar dake tsakaninmu."
Kallon Sakarya yake binta da shi yayin da ya ji maganar tata ta zo masa a banbarakwai. Dariya ya sheƙe da ita sannan ya tsuke fuska kamar bai ta
ɓ
a dariya
ba ya ce "Sakaryar ina ce ke Mahee? Iyayenki ma suka guje ki balle ni? Shin wai ke har a cikin zuciyarki baki ta
ɓ
a zargin yaudararki zan yi ba? Lallai zuciyarki gafalalliya ce kuma ta shagala da duniya da yawa."
A ru
ɗ
e take binsa da wani irin kallo mai
nuni da tsantsar mamaki, tarjamar kalamansa ta shiga yi a ƙwaƙwalwarta kafin ta iya bu
ɗ
e baki da ƙyar ta ce "Ban fahimce ka ba, kana nufin baka sona ba zaka aure ni ba?"
Jinjina mata kai ya yi alamun tabbatarwa kana ya ce "Idan kika zaci ni Ja'afar zan
aure ki to kin yaudari zuciyarki, ba zan ta
ɓ
a auren gafalalliyar yarinya irinki ba wacce zuciyarta ta fi ƙarfinta, iyayena suna kyautata mun zato ba zan saka masu da auren wacce ta zubar da ƙimarta a waje ba."
Yanzu kam lissafinta ya gama ƙwacewa, fata
n take yi ta bu
ɗ
e ido daga cewar a mafarki wannan abun ke faruwa, amma sai dai da alama wannan zahiri ne ya zo a cikin littafin ƙaddarar rayuwarta.
Tana kuka ta tsugunna a gabansa tana roƙon ya rufa mata asiri ya aure ta, fa
ɗ
ar take "Kamun rai Masoyina,
kai ne silar gur
ɓ
acewar rayuwata, ka yi sanadin raba ni da ahalina da mutuncina, shin idan ka kore ni ina na nufa?"
Sosai tausayinta yake ratsa jijiyoyin jikin Duddoo duk da kasancewar shi
ɗ
an iska amma ya tausaya rayuwarta.
Duban Ja'afar ya yi ciki
n sanyin murya ya ce "Jafsee ka tausaya wannan rayuwa da take cike da ƙunci a yau, don Allah ka zauna da ita ko da ba zaka aure ta ba."
A zafafe ya juyo da dubansa ga Duddoo "Ashe fa kai baka da hankali ko? So kake wannan mahaukacin yayan nata ya kashe
ni, ko so kake banzan mahaifinta ya je ya tonan asiri a gun mahaifana?"
Duddoo zai sake yin magana kenan ya daga masa hannu da cewa "Bana son jin komai daga gare ka, ka sani sabo da kaza bai hana a yankata, idan tausayinta kake kai ka aure tan mana, dam
a can ni ba ita nake so ba jikinta nake so kuma na samu, me ya rage?"
Wani wahalallen kuka ne ya kufce mata da gudu ta tashi tana gyara zaman hijabinta da jakarta ta bar
ɗ
akin domin ba zata juri sauraren wa
ɗ
annan kalaman ba.
Duddoo ya so ya biyta ya
lallashe ta ko ta ji sassauci a zuciyarta na wannan yaudarar da ta zo mata kwatsam daga inda bata yi tsammani ba, sai dai babu Wadataccin kalmomi a bakinsa da zai iya amfani dasu, da yanada yanda zai yi da ya taimake ta, amma inah....
A waje ta wuce Gay
en
ɗ
azu ya yi ƙoƙarin dakatar da ita da cewa "Dama na gaya miki, kawai ki dawo mu jone haka bariki ta gada." Ko saurarensa bata yi ba ta bar gidan cike da ƙuncin zuciya.
Takawa kawai take amma bata san inda ƙafarta ke sauka ba, kamar yanda bata san inda
ta nufa ba, duniyar ta mata duhu gabaki
ɗ
aya, jinta da ganinta sun yi nisa ta yadda bata iya hange ko jin abunda ke faruwa a kusa da ita ba.
Haka ta ci gaba da nausawa layukan unguwar kamar ta
ɓ
a
ɓɓ
iya, bata ma san