Showing 60001 words to 63000 words out of 64639 words
komai ba a ransa suka gaisa ya shige
ɗ
akin Zaliha.
Daga can ciki ya ja wani m
alalacin tsaki, "mtsw! Gaskiya Zali kina da matsala, dubi
ɗ
akin nan naki sai kace makwanci Jakuna. Banda kazanta irin taki ma me ya kawo Kifi da takalmi saman gado."
"Haba Alhj Ajiye wa fa na yi kafin na zo.!"
"Allah Ya waddan naka ya lalace, da ana
gado bata hanyar ha
ɗ
a jini ba da sai na ce wannan yarinyar Habiba ke ta gado a gun ƙazanta."
A haka yata bam-baminsa, sai dai ita Inna Zali ko a kwalar rigarta, sabgogin gabanta ma take. A ranta tana fa
ɗ
ar 'Ka ji da shi ciwon ajali a
ɗ
an yatsa.'
Bai
bar gidan ba, sai ga da Magariba, bayan ya yi sallar Magariba ya dawo a nan ya tarad da Biba.
Ya kalle ta "Ke Habiba me kike jira ne da har yanzu baki koma
ɗ
akinki ba?" Nan fa ta shiga rarraba ido tamkar
ɗ
an sane a gaban jami'an tsaro sai daman sosa ƙeya
take.
Inna Jimmai ce ta kalle ta "Ai sai ki kora masa bayanin da kika koro mini."
Ya tsare ta da ido yana jiran jawabinta.
Da ta ga babu sarki sai Allah, sai ta sunkuyar da kai "Abba da ma Habibu ne ya ƙara sakina."
Dattijon ya
ɗ
ago a razane "M
e kika ce? To garin ya haka ta faru?"
Ta yi shiru tana ƙara sunkuyar da kai kamar zata yi kuka.
"Ki yi magana wane laifi kika aikata masa? Don ni na san ruwa baya tsami banza."
"Wallahi ban sani ba Baba."
"To na ji, bari zan neme shi. Ina Salam
atu? Ban ga motsinta ba tun
ɗ
azu."
"Mun tashi da ita ba lafiya shi ne ya dauke ta zuwa asibiti tun lokacin ban ƙara ganinta ba, shi ka
ɗ
ai ya dawo kuma a lokacin ya sake Ni."
"Tabbas da wata a ƙasa, Allah Ya sa ba halin ballagazancin naki ne ya janyo
wata matsalar ba."
Ta yi sum-sum ta wuce
ɗ
akin ummanta.
A nan Baba ya
ɗ
aga waya ya kira Habibu ya ce ya zo ya same shi.
Bayan ya zo gidan, a gaban iyayen Alh Sule ya zaunar da Biba da Habibu don yin sulhu.
Take a wurin Habibu ya kwashe komai da
ke faruwa tun bayan auren su kawo izuwa yanzu da abinda ya sami Salma.
Nan fa gurin ya hargitse da sallallami.
Alhaji Sule ya
ɗ
ago ya kalli Jimmala "To kin ji ko? Da ma na nasa hakan a raina da ganin yadda take ita ce bata da gaskiya. Don na fi yarda
da Habibu a kanta."
Biba da sai a lokacin ta ji abin da ya sami Yarta ta fashe da kuka "Wayyo Allahna na shiga uku ni Biba... Wannan bawan Ya cuce ni ya lalata mini rayuwar yata tilo a duniya Allah Ya...."
Bata ƙarasa rufe bakinta ba, Abba ya bige m
ata baki da hannunsa.
"Rufa mini baki ballagazar banza shashasha, ai ke ya fi dacewa a hawa Allah ya isa,
ɓ
ace mini daga nan."
Ta miƙe dafe da baki tana gunjin kuka, kafin ta ƙarasa
ɗ
akinsu ta jiyo sautin Muryar Habibu yana fa
ɗ
ar
"A gafarce Ni da ab
in da zan fa
ɗ
a Abba, amma zama tsakanina da Biba ya ƙare. Allah ya gani na
ɗ
aga mata ƙafa iya
ɗ
agawa amma bata daina abubuwan da take ba."
Abba ya girgiza kai, "Bakomai Habibu ai ka kyauta, zama da wacce bata san ciwon kanta ba ba abinda zai kare ka da
shi sai tashin hankali da ta
ɓ
ar
ɓ
arewar iyali. Jeka Allah Ya maka albarka ya zaunar da kai lafiya da amaryarka."
Ya yi godiya ya miƙe har zai tafi Abba ya ya ce "Wace asibitin ce? Insha Allah gobe zamu shigo duba jikin Salmar."
A nan Habibu ya yi masa
bayani sannan ya masu sallama ya tafi.
Tun daga ranar da ya taka ƙafa Ya bar gidan bai sake waiwayar Biba ba.
Haka ta ci gaba da rayuwa a gidan cikin tsana da tsangwama, ƙannenta duk suka rainata.
Duk wani aikin gida Abba ya tattare ya mai da kan B
iba, wahala har wacce bata yi a farkon zamanta gida ba yanzu duk yi take yi.
Rayuwa ta yi mata atishawar tsaki. Bayan ta yaye yaronta Habibu ya zo ya kar
ɓ
e dansa ya ha
ɗ
a da Salmar ya damƙa amanarsu a hannun amaryarsa. Suka ci gaba da rayuwa ƙarƙashin kula
war amintacciyar matar uba da tafi masu mahaifiyarsu.
WATA UNGUWA
(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)
ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
AREWA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIR RAHMANI
R RAHIM
19-3-2022
PAGE 31
BABI NA TALATIN DA ƊAYA
Matashiyar budurwar ta yi murmushi ba ta ce komai ba, sai takowar da ta fara yi zuwa gaban teburinsa.
"Wai me na fa
ɗ
a miki a ranar farko ta ha
ɗ
uwarmu ko kin manta ne, na tuna miki?"
Ta w
adata fuskarta da murmushi sannan ta zauna akan kujerar dake fuskantarsa ba tare da ta
ɗ
auke ido akansa ba, ta ce
"Taya zan manta da kalmomi na farko da suka ratsa tsakanina da abin begen zuciyata?"
Kallonta kawai yake cike da takaici ganin tana bata m
asa lokaci da shirmenta ya ce "Wai meke tafe dake ne? Me kike so da ni da kike bibiyar rayuwata? Wanene ma ya nuna miki nan wajen?"
Ta ƙara yin murmushi sannan ta ce "Acikin tambayoyin da ka mun a yanzu guda biyu ne ka
ɗ
ai zan iya amsa maka a yanzu." Ta gy
ara zama tare da canza salon maganarta, cikin sauti irin na salon jan ra'ayi ta ce
"Abin da ke tafe da ni kyakkyan albishir ne zuwa gare ka, Abin da nake so da kai kuma shi ne Kai kanka."
Cikin mamaki da rashin fahimtar inda kalamanta suka dosa ya kaf
e ta da ido "Ban fahimce ki ba Malama."
"Ka kira ni da Sofi ba Malama ba." Ta
ɗ
an tsagaita sannan ta
ɗ
an girgiza kai ka
ɗ
an ta ce "Ina nufin na zo nan ne don na yi maka albishir cewa ka samu tsuntsuwar da zata maye maka gurbin wacce ka rasa. Ita wannan t
suntsuwar idan ka yi Sa'a kai ne da kanka zaka gasa namanta sannan ka cinye abinka ba tare da an samu wani tasgaro ba, sa
ɓ
anin waccen tsuntsuwar da ta hiranye maka, ka kasa kamawa."
Ya miƙe tsaye "Sofi kike kowa? Na gaji da sauraren wannan shirmen banza
n naki, idan abin da ke tafe dake kenan, zaki iya tafiya domin ba ni da lokacin batawa."
Ta sake ƙayata fuskarta da murmushi sannan ta
ɗ
ora kafa
ɗ
aya akan
ɗ
aya.
"Kada ka damu, ina gama fa
ɗ
ar abinda ya kawo Ni zan tafi, duk da cewa bana ƙosawa da kallon
ka tamkar dai yadda mage bata gajiyawa da farautar
ɓ
eraye."
Ta ja fasali sannan ta
ɗ
ora da cewa "Ka tambaye ni dalilin da ya sa nake bibiyar rayuwarka, to Bakomai ba ne fa ce Ina sonka, kuma na yiwa kaina alƙawarin mallakarka a matsayin miji duk rintsi.
"
Ya zazzaro ido a mamakince ya ce "What? Anyah kanki
ɗ
aya kuwa? Wai ni kike so zaki aura?"
Ya shiga girgiza kai "Inah! Yarinya kin makaro, a yayin bincikenki akaina kin bar wata kafa mai matukar muhimmanci, da ace kin lalubo ta ba zaki yi gigin zuwa
nan ba." Ya
ɗ
an zagaita yana kallonta a rai ne.
"Wai shin kin kalli kanki a madubi kafin ki baro gida kuwa? Kalle ki fa da kyau sannan ki sake kallona, ai ko ba Rayuwata Mahee ke ba Ajina ba ce."
Ya sauke zancen a hasale.
Nan fa Sofi ta miƙe cike
da jin zafin kalamansa ta shiga ƙare wa suturar dake jikinta kallo, wai ko zata hango wata makusa a jikinta ko a shigarta. Sai dai da yake yan magana sun ce gwano baya jin qarfin jikinsa bata iya hango aibinta ba.
Ita ana ta ganin ta ƙule adaka domin ata
mfar sallarta ce ma ta sako, kuma sai da ta tsaya ta tsantsara kwalliya da take jin cewa ko gasar sarauniyar kyau zata je ko bata zo ata
ɗ
aya ba, zata fito a cikin uku mafiya zarra. Kowa a gari sai zuzuta kyaun shigarta yake yi. Amma shi wannan tsabar rain
in hankali ita yake fa
ɗ
awa haka?
Wannan dalilin ya saka ta
ɗ
ago ƙananun idanuwanta ta zuba mishi su tana yi masa murmushin yaƙe.
"Ban ga wani aibi a tattare da ni ba, ko ba komai nasan nafi waccen kilakin da kake taƙama da ita mutunci."
A zafafe ya
taso mata kamar zai ya galgala namanta "Ke wa kike kira da Kilaki? Ba dai matar tawa ba."
"Korarriya nake nufi, wacce labarinta ya bazu a gari, wa yasan ma ko can inda ta je tallar jikin nata ta ke a ......"
Bata samu damar ƙarasa maganar ba saboda s
aukar wani zazzafan mari da ta ji a kuncinta. Ta dafe kuncin da hannu
ɗ
aya ya matso yana huci "Ki fice ki bar mini office dina bana ƙaunar sake ganinki a rayuwa, idan kika sake kika sake nuna mini wannan mummunar fuskartaki, duk abinda ya faru kece sila."
"Ni ka mara akan wata kucaka?" Ta fa
ɗ
a tana jijjiga kai, sannan ta
ɗ
auki jikarta daga kan teburinsa ta nufi hanyar fita har ta kai ƙofa ta dakata tare da juyowa.
"Ka da ka yi tunanin wasan ta ƙare daga nan, yanzu ma aka fara, ina matuƙar sonka kuma s
ai na mallake ka duk rintsi, sai na yi nasara akan Maheerah ka ajiye wannan a ƙwaƙwalwarka."
Ta fice tare da banka ƙofar da ƙarfe har sai da ya tsorata, ko da yake ba iya shi ba dai dai da sakatariyarsa ta razana da jin wannan ƙarar.
A haka Sofi tabar
ofishin Irfan cike da ƙunar zuciya da tunanin
ɗ
aukar ƙwaƙƙwaran mataki akansa.
******"
Ta isa gida cike da
ɓ
acin rai da damuwa a dai-dai lokacin kuma ta riski mummunan labarin da ya birkita ƙwaƙwalwarta har ya saka ta Mantawa da babin rayuwar Irfan.
Bakomai ta riska a gidan ba face labarin mutuwar yayarta Hanifa wanda hakan ya dugunzuma hankalinta ainun.
"Shi kenan wai da gaske Hanee ta mutu ba zata dawo ba Maryam?" Ta fa
ɗ
a tana kallon Maryam idonta cike da hawaye.
Cikin kuka Maryam ta ce "Sai
haƙuri yaya Sofi, kowa lokaci yake jira, mutuwa rigar kowa ce idan baka saka ta a yau ba zaka saka ta watarana."
Nan fa Sofi ta shiga zubar da ƙwalla tana sambatu kala-kala.
"Yanzu ba ni da abokiyar fa
ɗ
a kenan? Da nasan da zuwan wannan ranar dana roƙi
gafarki kafin ƙasa ta rufe idonki yayata. Ki yafe mini, Allah ya gafarta Miki zunubanki."
Duk mutanen dake zaune a gidan makokin sun tausayawa Safiya ganin halin da ta shiga har suna yi mata fatan shiryuwa a zuƙatansu.
Dai dai da Mankas ya nutsu a w
annan ranar, har da shi da abokansa a yan zaman makoki, duk sun sha jallabiya kamar yaran arziƙi....
Inna da Baba Mudi kuwa a ranar ba a cewa komai a yanayinsu sai godiyar Allah (mutuwa mai wa'azi.)
Ummu Inteesar ce
WATA UNGUWA
(Labarin game
da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)
ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
AREWA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
25-3-2022
PAGE 32
BABI NA TALATIN DA BIYU
Bayan ficewar Sofi daga of
fice
ɗ
in da kamar sa'a biyu, wanda Irfan ya tura don yo masa bincike akan Jafsee ya dawo.
Bayan sun gaisa ya ce
"Ranka Ya da
ɗ
e na samo wasu muhimman bayanai dangane da wannan yaron Ja'afar.
Ainahinsa ba mazauni wannan unguwar ba ne, gidan iyayensa
yana unguwar Bashal. bariki ce ta zaunar da shi a unguwar Dagarman, wani Gaye na samu a cikin abokanan shiriritar tasa shi ne ya yi mini bayanin komai, har ma ya nuna mini hoton Ja'afar
ɗ
in.
A taƙaice dai ranka ya da
ɗ
e na zauna a ƙofar wannan gidan
har zuwa lokacin da Jafsee ya fito don zuwa gidansu kuma na bi bayansa na gano har gidan nasu."
Irfan ya
ɗ
aga hannu cikin alamun jinjinawa ya ce
"Well done, ka yi ƙoƙari sosai. Yanzu ka zo mu je ka nuna mini gidan iyayensa da kuma shi yaron."
Ya
yi saurin
ɗ
aga kai ya kalli Irfan kamar zai yi magana kuma ya yi shiru.
Irfan ya gya
ɗ
a masa kai tare da fa
ɗ
ar
"Ƙwarai can za mu je kuma yanzun nan, ai ba a bori da sanyin jiki. Baka ji 'yan magana sun ce da zafi-zafi akan daki ƙarfe ba?"
Mutumin
ya yi murmushi, bisa ga tilas ya bi bayan ogan nasa ya kai shi inda ya buƙata.
Koda suka ƙarasa ƙofar gidan ana kiraye-kirayen sallar azahar. Kafin Irfan ya gama daidaita tsayuwar ƙafafun motarsa ya ga fitowar wani Dattijo daga gidan yana sauri.
Daga
damshin ruwan da ya gano a fuska da hannuwan dattijon ya fahimci Masallaci ya nufa. Don haka cikin hanzari ya fito daga motar ya ƙarasa wurinsa suka gaisa.
"Baba idan ba damuwa ina son yin magana da kai."
"Shi kenan yaro bari na fito daga masalla
ci." A tare suka ƙarasa masallacin su Uku. Bayan sun idar da sallah ne suka dawo ƙofar gidan tare da tsayawa.
Cike da fara'a malam Rabe ya ce "Yaro ina saurarenka."
Irfan ya yi murmushi yana kallon dattijon mai cikar kamala.
"Don Allah Baba kai ne M
ahaifin Jafsee?"
Dattijon ya masa wani irin kallo alamun rashin fahimta a take ya
ɗ
ago kuskurensa
"Am! Ja'afar nake nufi Baba."
Dattijon ya Ƙawata fuskarsa da murmushi.
"Ƙwarai kuwa Jafaru
ɗ
ana ne da nake ji har tsakiyar rai saboda tarbiyyarsa."
Irfan ya yi busasshen murmushi a ransa ya ce
_'Da alama ya gama yaudare zuciyar salihan iyayensa sun kasa fahimtar cewa kura ce lullube da fatar akuya.'_
"Ina jinka yaro, kai abokin Jafaru ne?"
'Allah ya tsari gatarina da saran shuka.' Irfa
n ya fa
ɗ
a a zuciyarsa. A zahiri kuwa cewa ya yi
"Am, wata magana ce tafe da ni wacce zaka iya jinta tamkar almara, sai dai kuma ba almarar ba ce. Ja'afar ya yi mana wani gagarumin laifin da za mu iya maka shi a kotu idan mun so, amma kamalarka da ƙimark
a da na duba shi ne na fara zuwa gare ka don a yiwa tufkar hanci."
Malam Rabe ya
ɗ
an razana ka
ɗ
an
"Me kake nufi yaro? Shi Jafarun?"
Ya shiga girgiza kai yana fa
ɗ
ar
"Ina! Sai dai ko in
ɓ
atan kai ka yi."
"Ba
ɓ
atan kai ba ne Baba, Ja'afar
ɗ
inka wato Jafsee shi ne wanda ya lalata rayuwar ƙanwata, kuma matar da nake burin aura, yanzu haka ba mu san inda za a same ta ba, kuma shi nake zargi da sace ta."
Shuu! Wutar lantarki dake aiki a jikin malam Rabe ta
ɗ
auke na wucin gadi, ya ƙame tamka
r mutum-mutumi kafin daga bisani ya samu damar motsa harshensa.
"Yaro ina yi maka kallon mai kamala duba da shigar da ke jikinka da kuma nutsuwarka ashe dai kai motsattse ne?, wannan abin da kake fa
ɗ
a abin da ba zai yiwu ba ne auren mage da
ɓ
era."
Yana gama rufe bakinsa ya hango tahowar Ja'afar riƙe da baƙar leda a hannu da alama cefane ya yo.
Dattijon ya yi murmushi "Ai shi kenan inda ba ƙasa ake gardamar kokowa, ga Jafarun nan zuwa, zaka tabbatar da cewa ka yi
ɓ
atan kai ne."
Irfan ya yi
saurin juyawa ya kalli bayansa ya hango mai tahowar, a take ya ji wani ƙololon baƙinciki ya tokare masa maƙoshi.
'Wai wannan abun ma shi ne Jafsee? Wannan ƙazamiyar halittar ce Mahee ta guje ni saboda ita? To me ta gani a nan? Wannan gajeren hanc
in ko kuwa ƙaramin kan nan nasa mai kama da na jinjirin jaki?'.
ya fara nisa a duniyar tunani ya tsinto muryar Ja'afar
ɗ
in yana fa
ɗ
ar
"Barka da rana Abba, Ɓaki sannunku da zuwa."
Abban nasa ya fa
ɗ
a
ɗ
a murmurshinsa "yawwa
ɗ
an albarka da ma a k
anka muke magana da yake kai
ɗ
an halas ne sai ga ka."
Ya juya ga Irfan "Ɗan samari maimaita tuhumarka ya ji."
Jafsee ya tsaya yana rarraba ido "Tuhuma kuma Abba? Ni Jafaru me na yi musu kuwa?"
Abban nasa ya ce "Wannan ne ya ce ka lalata masa
rayuwar ƙanwa kuma yana tuhumarka da sace ta."
Dam! dam!! ƙirjinsa ya buga a zuciyarsa ya ce
'Wata sabuwa inji 'yan caca, wannan kuma yayan wace jakar ne a cikin Jakunan...'
kafin ya ƙarasa zancen zucinsa ya jiyo sautin matashin yana cewa.
"Ƙanwata Maheerah wacce ka yaudare ta a watannin baya, ka koya mata shaye-shaye kuma ka raba ta da mutuncinta, kuma kai nake zargi da
ɓ
oye ta ko ince sace ta."
"Daram dam!" Sautin bugawar ƙirjin Ja'afar kenan, A take 'yan hanjinsa suka shiga ƙadawa tare