Showing 42001 words to 45000 words out of 64639 words

Chapter 15 - Wata-Unguwa-Compelete

kuma tun lokacin ban sake ganinta ba. Duk da cewa idan gari ƙalau ne kusan kullum sai ta zo shagon nan siyayya."

Zaro ido waje Irfan

ya yi ya ki

ɗ

ime

"Me ka ce? Don Allah fa

ɗ

a min meke faruwa da masoyiyata?."

"Nima ban sani ba sai dai ina ji a jikina ba lafiya a gidan, domin yayanta Sadiƙu mutumina ne kusan kullum sai ya zo mun gaisa mu

ɗ

an taba hira sannan ya shiga gida. Amma ya

u kimanin kwana biyu kenan ban gan shi ba, dalili kenan da ya sanya na

ɗ

iga alamar tambaya a al'amarin gidan."

Irfan ya miƙe tsaye tare da cire hular kansa cike da damuwa ya ce "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un! Meke faruwa ne?"

Ganin ba zai sami

amsar ba ya wuce ba tare da ya tsaya yi wa Haliru sallama ba, zuciyarsa ta ci gaba da tsinkayo mi shi abubuwa marasa da

ɗ

i da za su iya faruwa a gidan.

A haka ya ja motarsa ya bar unguwar bayan ya

ɗ

aukar wa zuciyarsa alƙawarin cewa sai ya binciko abin d

a ke faruwa.

Washe gari tun da sassafe ya yi wa gidansu Maheerah zobe. Yana isa ƙofar gidan Baba yana fitowa daga cikin gidan.

"Assalamu alaikum Baba ina kwana."

Irfan ya fa

ɗ

a cikin ladabi yana rusuna kai.

Baba ya miƙo masa hannu yana fa

ɗ

ar

"Wa'

alaikumus Salam, malam Irfan sannu da zuwa."

Bayan sun gaisa Baba ya kalle shi fuskarsa ba yabo ba fallasa ya ce

"Yawwa malam Irfan dama ina nemanka."

"To Baba Allah Ya Sa dai lafiya."

"Lafiya amma ba ƙalau ba, so nake na sanar da kai daga yau

ka hutar da kanka zuwa gidan nan, domin wacce kake zuwa don ita ta yi maka nisa, nisan da ba zaka iya kamo ta ba."

A razane ya dago rikitattun idanunsa muryarsa na rawa tamkar signal ta

ɗ

auke a gidan tv ya ce "Ban... Ban fahimta ba Baba."

"Ina nufin

ka cire ranka da auren Maheerah, domin babu ita a gidan nan yanzu, na gode maka da duk dawaniyar da kake damu. Haƙiƙa da ina da 'ya mace a yanzu ko wacece da na baka aurenta domin na yarda da nagartattun halayenka da tarbiyyarka. Ka je kawai Allah Ya musa

nya maka da mafi alkhairi."

Daga haka ya wuce ya bar Irfan nan tsaye ya sake baki kamar wani gaula.

Tarin tambayoyi ne cunkushe a ma'adanar tunaninsa, amma ya rasa mai kar

ɓ

a mi shi su.

Tamkar mutum-mutumi haka ya ƙame a wajen ya kasa motsa ko da y

atsansa.

Yana cikin wannan yanayin sai ga Sadiƙu ya fito daga zauren gidan suka yi kici

ɓ

is da juna.

Sadiƙu da ya ga ba shi da wata mafita tun da Irfan ya riga ya gan shi hakan ya saka ya matso kusa yana murmushin yaƙe ya ce "Aminci Allah ya tabbata a

gare ka."

Rashin sani yafi dare duhu, da Sadiƙu ya san cewa Irfan ya zurfafa a kogin tunani kuma bai lura da shi ba. Da ya yi amfani da kyakkyawar damar da ya samu gurin tserewa domin hausawa sun ce _hankali ke gani ido gulu-lu ne."

Wannan sallama

r da ya yi ita ta dawo da Irfan daga duniyar tunani zuwa duniyar da yake rayuwa a ciki.

A maimakon ya amsa masa sallamar sai cewa ya yi "Yaya Sadiƙu don Allah meke faruwa a gidan ne?"

Zuciyar Sadiƙu ta buga da ƙarfi dam! Domin da _alama wuƙa zata to

no garma_ abin da ya da

ɗ

e yana

ɓ

oyewa dole ya bayyana shi a yau.

Ya kalli Irfan da fuskar shi da yake ƙoƙarin shimfi

ɗ

a yanayin mamaki a maimakon damuwar da yake ciki ya ce "Me kake magana ne a kai?"

"Baba ne ya min wasu irin bau

ɗ

a

ɗɗ

un jawabai da na kas

a gane kansu, wai in je in manta da Mahee." Ya yi maganar a birkice.

Sadiƙu ya

ɗ

ago kai "_Ranar wanka ba a boyon cibi_ Irfan, na yi iya kokarina domin in

ɓ

oye daga ganinka ta yadda ba zaka yi tozali da ni ba bare ka tambaye ni

ɓ

oyayyen sirrin da na yi s

akacin bayyanawa har ya zama linzamin datse farin cikin gidanmu."

Ya sauke zancen a kasalance.

Irfan ya

ɗ

ago a hartsigi "Ka fito da ni duhu don Allah, na ga kana neman ƙara hargitsa min hargitsattsiyar ƙwaƙwalwata da Baba ya yi nasara kunce notikanta."

"Ka yi haƙuri Irfan Baba ya kori Maheerah daga gidan nan gaba

ɗ

aya haka ma ya cire ta daga cikin ahalinsa gaba

ɗ

aya."

Wani guf, Irfan ya ji tamkar ya kwa

ɗ

a masa guduma a tsakar kai. Take jikinsa ya hau rawa kamar an ka

ɗ

a mazari.

Sa

ɗ

iku ya wuce ji

ki a sa

ɓ

ule ya bar Irfan nan tsaye yana firfita da hular kansa. Duk da cewa kuwa har lokacin ana tsakiyar sanyi ne amma gumi ne ke tsattsafo masa ta ko wace kafar gashi dake jikinsa.

Ku biya biya ku

ɗ

inku ta wannan account

ɗ

in

Account name: Ruƙayya

Ibrahim lawal

Account number: 0431343346

Gt bank

Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202

Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.

Ga mutanenmu na Niger masu buƙatar saye zaku biya 400F ta wa

nnan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903

Ko da ku

ɗ

inka....

..

Ummu Inteesar ce

*WATA UNGUWA*

*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al

'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

8 December 2021

Page 18

BABI NA SHA TAKWAS

_NISAN KIWO_

"Hajiya ga motocin garin." Ɗan union

ɗ

in ya fa

ɗ

a yan

a nuna mata motocin dake lodi da yatsansa.

Ya kalli karen motar ya ce "kondusta ga fasinja a saka ta a motar Balgori don Allah."

"Ok ta shiga wannan motar saura mutum

ɗ

aya ta tashi." Karen motar ya fa

ɗ

a.

Maheerah ta shige motar kai tsaye ta zauna

tana ci gaba da sake sake a ranta.

Ɗ

an union

ɗ

in ya ci gaba da tsayuwa a gurin da alama yana jiran ta sallame shi, sai dai ba alamar zata

ɗ

ago ta kalle shi bare ya saka ran ta ba shi wani abu.

Girgiza kai ya yi cikin tausayawa a ransa ya ce 'Da alama

wannan budurwa tana cikin kalubalen rayuwa.'

Kondusta ya fara tattara ku

ɗ

in matafiya har ya zo kan Maheerah ya ce "Hajiya kawo baki."

Sai da ya maimaita zancen kafin ta ji ta

ɗ

ago da jajayen idanunta ta zuba masa su. "Nawa ne ku

ɗ

in?"

"Dubu hu

ɗ

u

."

"Habah dai malam dubu hu

ɗ

u ya yi yawa." Ta marairaice.

"Su ne ku

ɗ

in saboda tsadar mai, idan baki da su iya iya sauka daga motar."

Sai a lokacin ta tuna da jakar makarantar dake rataye a kafa

ɗ

arta dama abin da ya

ɗ

arsa mata tunanin barin gari. D

on haka ta sauke jakar.

Dubu hu

ɗ

u ta ƙirgo ta bashi sannan ta cilla duniyar tunani.

"Mahee Baby ga wannan ku

ɗ

in dubu 20 ne ki ajiye mana su a wajenki, na yin kodumo ne a watannan, kin sani dole zamu shayu sosai."

Maganar Ja'afar ta safiyar yau ta

dinga dawo mata a kunne tamkar yanzu yake furtata.

Murmushi mai ciwo ta yi ta ce a ranta 'Ku

ɗ

inka ne zasu min jagora zuwa inda zan yi shirin tarwatsa rayuwarka. Shi kuma Babana zai ga ribar sallama jini wa duniya na yi maku wannan alƙawarin.'

A daida

i lokacin motar ta shiga direban ya cilla hancin motarsa ya fice daga tashar, sai fatan a sauka lafiya.

******"*"*****

Zumbur ya mike tsaye bayan shafe tsayin daƙiƙu yana mayad da numfashi tamkar wanda ya yi tseren gudu. Cikin hanzari ya fice daga

ɗ

a

kin yana dube-dube.

Duddoo dai bai ce masa uffan ba sai binsa yake da ido. Can bayan daƙiƙa biyar sai ga shi ya dawo

ɗ

akin ya tsaya tare da

ɗ

ora hannu

ɗ

aya a kai yana hargiza gashinsa.

"Me ya faru ne Jafsee?"

Iska ya fesar daga bakinsa sannan ya

ce "Wannan macijiyar ta gudar mini da ku

ɗ

i."

Ɗ

an murmushi Duddoo ya yi sannan ya ce "Har nawa ne ku

ɗ

in?"

"Dubu ashirin ne fa, gaskiya ta jiƙa min aiki." Ya fa

ɗ

a yana jan tsaki tamkar jikan ja

ɓ

a, sannan ya ce "Da na san inda ta je ba shakka da na bita

na kar

ɓ

o ku

ɗ

ina amma ba komai gobe ma rana ce."

****. ******

Ana cewa dare mahutar bawa, domin a lokacin ne ruhuka kan sami nutsuwar hutawa. Duk da ƙwarewar bacci da shahararsa a bangaren sata a ranar bai yi gigin satar Irfan ba. Domin kuwa yadda y

a ga safiya haka ya ga dare. Ya

ɓ

ata muhimman sa'o'in shi na hutawa gurin tunanin mafita a matsalar da ta Kunno masa kai a rayuwa.

Washegari tun da sassafe ya fice daga gidan ko ƙaryata bai yi ba. Ko da hajiyarsa ta zo kiransa su ci abinci sai ta tarad

da sashensa a rufe.

Sosai ta yi mamaki don haka ta je ta sanar da alhajinsa ba bata lokaci suka kira shi a waya.

"Wai Ina kaje ne da safe haka Irfan?" Alhajinsa ya tambaya.

"Am! Alhaji ina wurin aiki ne, da akwai wani aikin da ban kammala ba jiya sh

i ta sa na yi sakko yau." Ya fa

ɗ

a a hargitse sannan ya datse kiran gudun kada Babansa ya kuma jefo masa wata tambayar da zai kasa amsawa.

Bayan fitarsa gida bai zame ko'ina ba sai gidansu Mahee don yana son ya samu Baba ko Sadiƙu a gida don duk da bai t

abbacin Baban zai saurare shi.

Yana zuwa ya ja ya tsaya a ƙofar gidan tamkar

ɗ

an dokar da aka bawa aikin kama mai laifi. Sadiƙu ne ya fara fitowa daga gidan riƙe da buta yana shirin wanke fuskarsa, da alama tashinsa kenan daga barci.

"A'ah! Irfan kai

ne tun da sassafe haka?" Ya fa

ɗ

a cike da mamaki duk da bai kamata ya yi mamakin ba. Domin a dai yadda Irfan ke matuƙar son Maheerah zai iya yin abin da yafi haka a kanta.

"Ni ne ina kwana yayanmu?" Murmushin yaƙe Sadiƙu ya yi.

"Lafiya ƙalau malam Ir

fan, meke tafe da kai? Ina ce jiya na maka bayanin komai bai kamata ka dawo nan ba."

"Ka dai gutsira min bayani, amma baka ba ni cikakkiyar hujjar da ta saka Baba ya korar min mata ba." Ya fa

ɗ

a a sanyaye.

Janyo hannunsa Sadiƙu ya yi suka shige zauren g

idan, ya tura ƙofar

ɗ

akinsa dake zauren suka shiga sannan ya sake hannunsa.

"Yawwa zauna nan mu yi magana a sirrance." Sadiƙu ya fa

ɗ

a yana nuna masa gefen katifarsa.

"Wane irin laifi Mahee ta aikata wa Baba har ya kore ta daga cikin rayuwar ahalinsa?"

Irfan ya tambaya tare da kafe Sadiƙu da manyan idanuwansa.

Sadiƙu ya yi da ajiyar zuciya Hmmm sannan ya ce "Ranar wanka ba a boyon cibi, duk yadda na so da son rufe maka gaskiya watarana zata bayyana ne, har gara ka ji da bakina. Mahee jinina ce amma ta

yi abin da ko dabbar dake rayuwa a gidanmu bata yi ba." Ya

ɗ

an tsagaita yana karantar yanayin Irfan.

"Har yanzu ban ji laifin da ta yi ba ai."

"Me kake ci na baka na zuba? Yanzu zan kaika filin sukuwar, inda zaka hau dokin da zai tabbatar maka da ab

in da kake son ji."

Irfan bai sake cewa komai ba ya dai yi masa ƙuri da ido, tamkar ya ga baƙuwar halitta.

Sadiƙu ya ci gaba "Mahee ta

ɓ

ata kanta ne da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, daga ƙarshe ta biye wa wancan lalataccen yaron na unguwar

Dagarma s

hi ne ya

ɗ

ora ta a wannan turbar kuma ya lalata mata rayuwa daga nagartacciyar yarinya zuwa mazinaciya."

Tun da Sadiƙu ya fara magana Irfan ya yi suman zaune tuni ya daskare a gurin, kalmar Sadiƙu ta ƙarshe akan Maheensa ita tafi cakar masa zuciya 'Mazi

naciya? Wal iyazu billah.'

Cikin barin baki ya ce "Habah! Yayanmu na yi tunanin idan kowa zai kama ra

ɗ

a ko jita-jitar magulmata kai ba zaka kama ba. Shi kuma Baba kawai sai ya yanke hukunci ba tare da bincike ba?"

Murmushi mai ciwo Sadiƙu ya yi kafin

ya girgiza kai ya ce "Ka yi tunanin wani ne ya fa

ɗ

a mana?

"Eh mana, nasan bai wuce sharrin mahassada."

"To ba wani ba ne ya fa

ɗ

a dubunta ce ta cika, an da

ɗ

e ana ruwa ƙasa na shanyewa, ranar da asirinta ya tonu da kaina na bi ta a baya bayan ta fita

da shirin makaranta. A nan na gane wa idanuna abin da har gobe ya kasa gogewa a ma

ɗ

aukar hoton idanuna."

Irfan ya jijjiga matuƙa lokacin da yake sauraren wannan labarin da ya kasance mafi muni da ya ta

ɓ

a ratsa masarafar sautinsa. Ya dafe saitin ƙirjins

a tsawon daƙiƙu bai ce komai ba kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ya ce "Yayanmu yanzu ina kake tunanin zan same ta?"

"Na yi fatar ace na sani Irfan, da na riga ka zuwa, na yi nadamar bayyanar da wannan sirrin ga mahaifanmu. Da na san

haka zata faru da na binne wannan sirrin a raina sannan na samowa ƙanwata mafita." Ya fa

ɗ

a yayin da yake ƙoƙarin shanye ruwan hawayen da ya taru a idonsa.

"Ka ban address

ɗ

in mayaudarin saurayin nata, mai yiwuwa zan samu wata fitilar da zata haska min i

nda zan sami matata.

Ya miƙe, ya kar

ɓ

i address

ɗ

in sannan ya fice.

Sadiƙu ya girgiza kai yana jinjina irin girman soyayyar da Irfan ke yi wa Maheerah, duk da wannan

ɓ

arnar da ta aikata har yanzu baya ganin laifinta kuma bai janye ƙudirinsa na aurenta b

a.

***** ***** ******

Zaune take a cikin mota yayin da motar ke ta cin hanya ta zuba tagumi da dukkan hannayenta guda biyu, hawaye ne ke tsere a kumatunta. Bata damu da share su ba, sosai ta zurfafa a kogin tunanin rayuwar da zata fuskanta bayan rabu

warta da ahalinta.

"Baiwar Allah meke damunki?" Wata siririyar murya ta ratsa masarafar jinta.

Ta dago tare da share hawayenta ta ce "Ba fa.........

Ummu Inteesar

*WATA UNGUWA*

*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abub

uwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

19 December 2021

Page 19

BABI NA SHA TARA

_MAI RABON SHAN DUKA BAYA JIN KWAƁO...._

"Yarinya dama

kin haƙura da wannan zancen don kuwa wannan yaron ya miki nisa." Haliru ya fa

ɗ

a

Sofi ta yi murmushi "Me yasa kace haka

ɗ

an'uwa?"

"Saboda zuciyarsa a kulle take kirif, ma'ana dai wata ta miki shigar sauri ta riga ki kafa tutarta a birnin zuciyarsa."

Wani murmushin ta sake jifarsa da shi kana ta ce "Ba daga nan take ba, na tabbatar da cewa zan iya rikito da tutar tata ƙasa har ma na yi galaba a kanta, shi kenan dai Nagode."

Daga haka ta juya ta bar gun tare da kama hanyar gida. Tana tafe tana murmus

hi ita ka

ɗ

ai ƙwaƙwalwarta na hasko mata yanayin zaman soyayyar da zasu yi da tauraron zuciyarta.

Bata yi aune ba ta ji an dafa kafa

ɗ

arta ana fa

ɗ

ar "Shegiyar gari, daga ina kuma haka?"

Waigowa ta yi ta kai dubanta ga mai maganar ta wadata fuskarta da

murmushi "Ka ga _dakalin majina a hauka a zame ka hau mutum ka zauna daidai._ _Duddoo ƙanin iblis idan baya kusa kai ne

ɗ

an aikensa._"

Ya yi dariya sosai "Zancenki dutse 'yar hannu, amma fa yanzu na fara laushi."

Ita ma dariyar ta sheƙe da ita kana

ta ce "_Kowa ya tuba don wuya ba lada,_ yanzu dai me ka zo yi a unguwarmu?"

"Wallahi na zo duba wani abokin Babanmu ne ba shi da lafiya, a nan layin yake so har ma na fito zan juya gida ne yanzu."

"Nima dai gida zani yanzu, sai mun jame wurin Partyn

Billy Lukency." Ta daga masa hannu sannan ta juya.

"Ok bye." Yana daga mata hannu.

Kowa ya kama hanyarsa.

*****

A ƙofar gida ta tarar da Baba, yana hangota ya ha

ɗ

e girar sama da ƙasa.

Jikinta ne ya hau

ɓ

ari kamar an ka

ɗ

a mazari ƙafafunta suka sh

iga har

ɗ

ewa jin take kamar ace mata ƙyat ta ruga. Amma ta kwana da sanin cewa _Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne_ dalili kenan da yasa ta matsa bakinta na motsi.

"Baba Barka da hutawa."

Ya zuba mata harara da ta saka yan cikinta suka hautsine.

"Daga gidan uban wa kike da ranar nan." Ya ƙara tamke fuska.

"Am! Baba, dama-dama na je...." ta kasa ƙarasa zancen.

"Dama kin je gidan ubanwa ne? Ko dai daga wurin yawon karuwancin naki kika dawo? Ko da yake komai kuka yi _baku yas ba kan gado kuk

a

ɗ

auko_ mahaifiyarku nan ba yawon ta zubar

ɗ

in da bata yi ba har Kajara take zuwa can ne kuwa ƙarshen matattarar 'yan tasha, ba yadda mahaifiyata bata yi da ni ba na ƙi ji dama' yan magana sun ce _kowa yaƙi ji ba ya ƙi gani ba._

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login