Showing 21001 words to 24000 words out of 64639 words

Chapter 8 - Wata-Unguwa-Compelete

Ta fa

ɗ

a murya na rawa.

Ha

ɗ

e girar sama da ƙasa ya yi ya ce "Saida ki zan yi, da Alama katon kankin nan zai yi ku

ɗ

i."

Ganin yanayin fushi ya dira a fuskarsa cikin ƙanƙanin lokaci, ya sa ta ha

ɗ

iyi w

ani yawu mukut ta ce "Yi haƙuri don Allah ba haka nake nufi ba, ka fahimce ni."

Dubanta ya yi har yanzu dai bai sake fuskar ba ya ce "Habah! Ai ni kin ban mamaki Babyn dama can ba ki yarda da masoyinki ba? Ke kin san ko wani na ga zai cuce ki bana bari

ba bare har ni da kaina."

Ya fa

ɗ

a cikin da

ɗ

in baki.

Wani sashe na zuciyarta na gaya mata kada ta yarda da shi domin maza ba su da tabbas, yayin da wani sashe na zuciyarta ya ƙaryata sashe na farko tare da ƙarfafa mata gwuiwa akan ta bi bayansa.

Da

ya tabbatar ya yi nasarar

ɗ

orar da ita kan yaudararsa sai ya shige ciki. Cikin

ɗ

ar-

ɗ

ar ta bi bayansa.

*Rashin sani ya fi dare duhu*

Tabbas ƙaddara ba a iya kauce mata, kuma ko wacce ƙaddara da mafarinta, da Mahee ta san irin tarin ƙalubalai da fitin

ar da zata afka mata bayan shiga wannan

ɗ

akin tabbas da ta gujewa duk wata hanyar da za ta sada ta da wannan ƙaddarar.

Bayan kamar awa biyu Maheerah ta fito daga Napep tana rangaji kamar za ta kifa da ƙasa.

Allah ya sa lokacin duhun Magriba ya fara s

auka kuma mafi yawan mutanen unguwar suna masallaci a lokacin. Hakan ya bata damar shigewa gidansu ba tare da kowa ya ganta ba.

Ko sallama bata yi ba ta fa

ɗ

a gidan tana layi irin na 'yanmaye sai ha

ɗ

a hanya take, a haka ta samu ta fa

ɗ

a

ɗ

akinta tare da zu

bewa kan katifar ta fara sharar barci cikin wani irin yanayi da bata ta

ɓ

a samun kanta a ciki ba.........

Ko da Umman ta idar da sallah sai ta fito waje tana mamakin ya aka yi har yanzu Maheerah bata dawo ba? Tana cike da fargabar kada Malam Isah ya dawo

gidan ya tarar ba ta nan ta shiga uku, domin tana sane da cewa kanta laifin zai sauka, don haka ta koma ciki ta

ɗ

auko wayarta ta komo waje tana ƙwalawa 'yar tata kira.

Ga mamakinta sai ta ji ƙarar wayar a cikin

ɗ

aki don haka ta nufi can. Tana zuwa ta t

arar Mahee na barci ko hijabin jikinta bata cire ba.

"Ikon Allah! Ni Indo yau Ina ganin abu, yaushe wannan ta dawo? Ko sallamarta ban ji ba." Ta fa

ɗ

a tare da kama ha

ɓ

a.

Nan ta shiga bubbuga jikin Maheen tana fa

ɗ

ar "Mahee ki tashi ki yi sallah, daga daw

owa sai barci.?"

"Mahee!! Wai wannan barcin lafiya ne?" Ta kuma fa

ɗ

a yayin da take girgiza jikinta a karo na barkatai amma ko gezau ba ta yi ba balle ta saka ran za ta tashi.....

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*

*YAR GANTALI*

*RIKICIN MASOYA*

*A

SANADIN KAMA*

*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*

*HALITTAR ALLAH CE*

Ku biya biya ku

ɗ

inku ta wannan account

ɗ

in

Account name: Ruƙayya Ibrahim lawal

Account number: 0431343346

Gt bank

Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202

Sa

i kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.

Ga mutanenmu na Niger masu buƙatar saye zaku biya 400F ta wannan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903

Ko da ku

ɗ

inka....

..

Ummu inteesar ce



*WATA UNGUWA*

*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*AREWA WRITERS ASSOCIATI

ON*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

22 june 2021

Free page 11

BABI NA SHA ƊAYA

Kafin Inna ta shigo

ɗ

akin tuni ya fara tsula masu bulalar ba ji ba gani.

Nan fa suka gigice suka sake mannewa guri

ɗ

aya tare da ƙanƙame juna ƙam, sai ihu

suke don azabar ra

ɗ

a

ɗ

i.

Ko da yake abun ne ya masu yawa wai shege da hauka, ga zafin ra

ɗ

a

ɗ

in ciwon jikinsu ga kuma ra

ɗ

a

ɗ

in bulala da yake tsula masu.

Shi kuwa ko ka

ɗ

an bai damu da duk wannan iface-ifacen da suke ba, Babban burinsa shi ne ya ga ya rau

nata su, bayan raunin da yake jikinsu. Sai kumfar baki ya ke "Ba ku ga 'yan iska tijararru ba? Yau zaku ga ƙarshen ƙaryar karuwanci da iskanci, wato ku ga 'yan tasha fan

ɗ

ararru. Waya sani ma ko kun fara yan kur

ɓ

e-kur

ɓ

en nan na zamani?"

Ya daga bulalar z

ai sake tsula masu kenan, Inna ta shiga tsakaninsu tana ƙoƙarin dakatar da shi, bisa tsautsayi bulalar ta sauka kan gefen fuskarta, wutsiyar bulalar ta tsokane mata ido. A take ido ya shiga ratatar ruwa.

"Waah! Shi ke nan Malam ka kashe ni, dama can id

on ya yake bare yanzu?" Inna ta fa

ɗ

a cikin ra

ɗ

a

ɗ

in ciwo.

Ihun da Innar ta saka ne ya dawo masa da hankalinsa a muhallinsa, nan fa ya yada bulalar icen yana faman tambaya "Miye ne haka kuma Luba? Ya kike mana ihu kamar ƙaramar yarinya?"

"Malam baka ga

yanda ka shau

ɗ

a mun bulala a fuska ba? Har fa cikin idona." Ta fa

ɗ

a da alamun har yanzu tana cikin zafin ciwon.

"Ai duk laifinki ne, me ya shigo dake cikin fa

ɗ

an nan saboda Allah? Ko da yake tun can azal haka kike da shiga sharo ba shanu, dama kuma ke

ki ke

ɗ

aure masu ƙugu shi ya sa suka raina ni da yawa, yara duk sun zama fitsararru, da ai ba haka suke ba." Ya fa

ɗ

a yana huci.

A maimakon ya tsaya duba idon nata ko kuma halin da yaran suke ciki kawai sai cewa ya yi "Allah ya sawwaƙa Luba." Daga haka y

a ka

ɗ

a bujensa ya yi waje yana jin zafin yanda Luba ta shiga tsakaninsa da burinsa na lallasa yaran, ko za su gane cewar shayi ma ruwa ne kala ce ta bambanta su.

WAIWAYE

ASALINSU.

Malam Mudi

ɗ

a ne ga Alhaji Usman mijinyawa wanda ya kasance haifaff

en unguwar Garwa ne.

Mahaifinsa ya kasance mai rufin asiri sosai a zamaninsa domin shi bafatake ne, fatauci ne sana'arsa yana yawo gari-gari don kai hajarsa idan ya siyar sai ya siyo ta su ya dawo gida ya siyar.

A garin yawon fataucinsa wata rana ya is

a wani ƙauye mai nisa a cikin wata jiha mai suna Sambusa, a can ya auro wata budurwa mai suna Mari, bayan lokacin tashinsa daga garin ya zo ya je ya shaidawa iyayenta akan zai wuce da matarsa can garinsu MAMBIYA.

Sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenta

suka amince ya taho da ita. Ita ce Allah ya azurta da haifar ƴaƴa maza guda Biyar mata uku.

Shehu shi ne Babba sai Iliya, Mariya wacce suke kira yaya Kande sai shi Muddasiru da suke kira Mudi, Ali(Baba ƙarami) sai kuma Dije Sannan Ummaru(

ɗ

an lami) sanna

n Auta A'i.

Gidan Alhaji Mijinyawa gida ne na jama'a gida ne da aka inganta gininsa cike da soyayya da ƙaunar juna, yaransa sun taso da ha

ɗ

in kai fiye da zaton mai zato.

Hakan nan da baƙo da na gida kowa nasa ne, ko da yake yawon fataucinsa ba ya bar

i ya share tsawon lokaci tare da iyalinsa, amma hakan bai saka yaransa sun taso cikin wani mummunan yanayi mai kama da yunwa ko ƙishi ba.

Gidansa ƙaton gida ne da yake

ɗ

auke da wani makeken fili bayan bangaren da iyalansa ke zaune. Duk lokacin da ya ta

shi aurar da

ɗ

aya daga cikin

yaransa sai dai ya yankawa

ɗ

an fili shi kuma ya yi gini iya wanda ya ishe shi.

A haka duk ya aurar da ƴaƴansa maza banda Iliya da Ummaru da suka rasu tun kafin su kai munzalin aure, sai kuma Mudi da ya jima bai yi aure ba, d

omin kuwa har ƙaninsa Baba ƙarami sai da ya yi aure, shi yana zaune shiru.

A wancan lokaci bayan wasu yan shekaru ga

ɓ

o

ɓ

in Alhaji mijinyawa suka sake, ga curuta ga yanayi na tsufa bisa ga tilas ya daina fita fatauci tunda har Allah ya masa gya

ɗ

ar dogo ci

won bai kwantar da shi ba sai a gaban iyalansa.

Lokacin ne kuma komai ya fara ja baya, yanayin walwala ya fara bankwana da gidan.

Abun duniya ya taru ya ishi Inna Mari, ga ciwon tsohon mijinta ga nata yanayin ita ma na mayyanta. A

ɓ

angare

ɗ

aya kuma g

a Mudi da lamarinsa ya shige masu duhu.

Wasu irin

ɗ

abi'u da halaye ya aro wanda sam ba su ha

ɗ

a hanya da

ɗ

abi'un ahalinsu ba.

Ya fara 'yan

ɗ

auke-

ɗ

auke cikin ruwan sanyi, tun abun bai bayyana ba har ya kai kowa ya shedi wannan halin Ɓeran nasa a unguwar.

Suna nan a haka, damuwa ta fara samun matsugunni a zuciyar iyayensa sai kuma suka ji labarin ya fara tsiro da wata sabuwar

ɗ

abi'a ta damfara. Wannan labari Kusan a'iya cewa shi ne mafi munin labari da ya yi silar jijjiga ahalinsu har ma ya yi silar

ɗ

auke

musu tsohonsu da ya kasance Babban jigo a rayuwarsu. Domin kuwa Alhaji mijinyawa ya kasa jurar wannan baƙin ciki na yawan

ɗ

ebo masu rigima da Mudi ke yi. Ga shi a kwance yana jinya amma a rana sai a masa sallama sau goma duk akan wannan sana'ar banzar da

ɗ

ansa ya fara. Wata rana da safe misalin ƙarfe goma Alhaji mijinyawa yace ga garinku bayan ya gama kar

ɓ

ar ƙarar Mudi da aka kawo da mintuna talatin, kuma da wannan tabon ya tafi a ransa.

Koda Inna Mari ta ga Mudi na neman

ɗ

auko masu dala ba gammo kawai s

ai ta yi kurum a ranta ta ce 'yaro inka san wata ai baka san wata ba.'

Da yake su mutanen wancan zamani haka suke yi, idan yaro ya

ɗ

auko wata

ɗ

abi'ar lalaci ba barararsa ake ba, cikin ruwan sanyi suke maganin matsalar ta hanyar nemarwa yaronsu taimako g

un malamai in kuma sata yake a

ɗ

aure hannunsa ta yanda ko miliyan nawa zaka ajiye su kwana a gabansa ba zai

ɗ

auka ba.

Ita ma Inna Mari ta wannan hanyar ta

ɓ

ullowa lamarin Mudi, da kanta ta saka ƙawarta Kande ta rakata gidan Malam na gangare suka kar

ɓ

o m

asa taimakon.

A cikin abincinsa ta dinga zuba masa yana cinyewa ba tare da ya sani ba.

A hankali maganin ya bi jikinsa kawai watarana sai ya wayi gari ya riski kansa da kasa ta

ɓ

uka komai a cikin sana'arsa ta damfara, duk wata basirarsa a harkar ya neme

ta ya rasa tamkar an zare ruhi daga gangar jiki.

Kwatsam watarana sai ga shi ya zowa inna Mari da zancen aure. Zuwa lokacin kuwa ya kai kusan shekaru talatin a rayuwarsa bai ta

ɓ

a zancen aure ba.

Hamdallah Innan ta yi tana ƙara yiwa Allah godiya da y

a shiryar mata da shi. A nan ta ba shi dama ya nemo duk yarinyar da ta masa a fa

ɗ

in garin, ita kuwa insha'allah in abun bai fi ƙarfinta ba zata aurar da shi.

ANA WATA GA WATA.....

Bayan sati

ɗ

aya sai ga Mudi ya zowa Inna da albishirin cewa ya samu wa

cce ta masa har ta amince da zancen aurensa.

Inna ta yi murna sosai, anan take tambayarsa wace yarinya ce?

Ya ce "sunanta Luba Inna, 'yar kauyen Shabaka ce a nan garin."

"Shi ke nan kada ka ji komai zan saka ayo mana bincike akan yarinyar." Inna ta

fa

ɗ

a da fara'arta.

Innan da kanta ta je ta samu wasu amintattun mijinta a unguwar suka je har ƙauyen Shabaka don yin bincike.

Bayan wani

ɗ

an lokaci suka dawo gare ta bayan kammala binciken.

Bayan doguwar gaisuwa da suka yi ta masu sannu da dawowa

sannan ta kasa kunne don jin sakamakon bincike.

Alhaji Bashiru(aminin Alhaji mijinyawa) shi ne shugaban tawagar 'yan binciken don haka ya gyara zamansa yana ƙara jinjina lamarin da tunanin ta ina zai fara bata wannan labarin.

"Kun yi shiru lafiya dai

Alhaji?" Innan ta tambaya da 'yar damuwa.

Alhaji Bashiru ya yi gyaran murya ya

ɗ

ora da cewa "Uhmm! Babu komai hajja Mari, da farko dai abunda nake son na fara cewa shi ne mu yi haƙuri da ƙaddara duk yanda ta zo mana mu saka hannu biyu mu runguma domin

fa ba zamu iya canzawa ƙaddararmu muhalli ba, kuma shi lamari na aure dama haka ya gada. Kowaye mutum kuwa in aka ce za'ayi bincike akansa ba a rasa kama shi da kuskure ba ko yaya ne, sai dai in za'a yi ayi kawai."

Jin wa

ɗ

annan kalaman ya sanya jikin I

nnan ya yi laushi, ta ji a ranta cewa yarinyar bata kirki ba ce sai dai koma miye ya kamata ta ji sakamakon binciken don ta san irin zaman da zata yi da yarinyar in ƙaddarar ta

ɗ

auro da ƙulluwar auren.

Don haka ta kalle su "Bincike abu ne mai kyau a yay

in aure, kuma ba baƙon abu ba ne, ku taimaka ku gaya mun gaskiya tunda yake har na amince da ku na

ɗ

ora muku amanata da ta yarona bai kamata ku mun rufa-rufa ba."

Jin wannan zancen nata ya sanya bisa tilas suka fe

ɗ

e mata biri har wutsiya.



A nan suka

tabbatar mata da cewa Luba dai ba yarinyar arziƙi ba ce domin kaf garin ba wanda bai shede ta da yawon banza ba, duk wani gida na

'yanbariki dake garin nasu ba wanda Luba bata sheda cikinsa da bansa ba domin nan ne mafakarta. Iyayenta da kansu sun gaji da

fa

ɗ

an sun zurawa sarautar Allah ido.

Wannan labari bai yiwa Inna Mari da

ɗ

in sauraro ba sam. Don haka bayan tafiyarsu ta kira Mudi ta zaunar da shi akan cewa ya canza mata, ya nemo duk wacce ta masa banda wannan domin bincike ya tabbatar da ba nagartacc

iya ba ce.

Take a gurin Mudi ya ƙeƙashe ido ya daki ƙasa ya kuma ba

ɗ

awa idonsa toka akan cewa Lallai shi in dai ba Luba ba to ya haƙura da aure a wannan rayuwar ita ka

ɗ

ai ya ji zai iya aura.

Ba yanda Inna bata yi da shi ba akan ya haƙura ya nemawa ƴa

ƴ

ansa uwa ta gari amma ya saka hannu ya toshe kunnuwansa.

A haka ta zura mi shi ido kuma ta amince da auren ba don ta so ba, aka daura auren Mudi da Luba.

Sai dai shi ba kamar sauran yaran ba ya ƙi amincewa da zama a gidan mahaifinsa kamar sauran yar

a bisa ga hu

ɗ

ubar Amaryarsa Luba, ya zo ya tada rigima sai da aka raba gado aka ba shi na shi, sai ya kasance ya gadi

ɗ

aya daga cikin madaidaitan gida ukun da Babbansu ya mallaka bayan wannan.

A can Amarya ta tare Inna kuwa tana nan gidan da mijinta ya

mutu ya barta a ciki. A lokacin ne kuma Babbar 'yarta mace (Mariya) ta rasu a can garin da take aure.

Sai dai me? Amarya bata ganin kan kowa da gashi, haka bata da ragowa ko ka

ɗ

an komai tsufan tsoho in ya takata ta iya ramawa bata shayin kowa, Innar ma

bata bari ba balle duk wanda ya saura.

A haka rayuwa ta ci gaba da gangarawa har zuwa lokacin da Luba ta haifi

ɗ

anta na fari Suleman (Mankas) bayan shekaru hu

ɗ

u ta haifi Usman (Abba) nan ma sai bayan shekaru hu

ɗ

u ta kuma haihuwa inda ta santalo 'yarta

mace baƙa Hanifa bayan shekara biyu ta Haifi Safiya ta yi Maryam sai Hanif sai Hafiz sai Abubakar Sadik da auta Basma.

Yaran sun taso ƙarƙashin kulawar mace marar kirki da rashin kula duk wasu

ɗ

abi'u da halayarta ita ce yaran suke koya.

Ita bata cik

a damuwa da sakawa ƴaƴanta ido ta ga abunda suke ba, balle har ta kwa

ɓ

e su. Hasalima wani abun ita ke ƙara saka su yin shi. Dalilin kenan da yasa yaran suka taso cikin irin wannan mummunar rayuwa.

Ko da tafiya ta fara tafiya Innan ta shiryu ba don Allah

ba, sai don ganin an tara zuri'a kuma tana son ganin ƴaƴanta sun zama shiryayyu, amma inah! An bar kyau tun ranar wanka, kuma da yake shi ice tun yana

ɗ

anye ake tanƙwarashi idan ya riga ya bushe to fa sai dai a haƙura kawai, domin kuwa ba zai tanƙwaru ba

sai dai a karya shi.

Ɓ

angaren Baba Mudi kuwa baya sakewa yaran fuska ko ka

ɗ

an ga duka, abu ka

ɗ

an ya ishi ya hau masifa yana jibgar yaro, dukan kuwa bana wasa ba irin wanda zai lahantasu yake masu.

Daga baya da ƙarfinsa ya fara ƙarewa shi ne yake sa

ka

ɗ

an'uwansa Baba

ɗ

anlami yana jibgarsu da zaran sun yi laifi.

Wannan shi ne ya yi silar ƙara fan

ɗ

arewar yaran, duk da har yanzu suna tsoronsa......

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*

*YAR GANTALI*

*RIKICIN MASOYA*

*A SANADIN KAMA*

*RASHIN GATA (G

AJEREN LABARI*

*HALITTAR ALLAH CE*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login