Showing 39001 words to 42000 words out of 64639 words
da wanzuwar mutane a gun ba balle ta fa
himci kallon tausayi da mamakin da suke binta da shi.
Sai da ta yi nisa sosai har ma ta fice daga unguwar Dagarman kafin ta samu gindin wata bishiyar ta zauna, tana son bawa ƙwaƙwalwarta damar yin lissafi da sanin abinda ya kamata ta yi.
Sai da ta
yi iya ƙoƙarinta kafin ta ha
ɗ
a zarrukan tunaninta da suka gama kuncewa kafin ta samu mafita.
Zumbur ta miƙe kamar an tsikare ta da allura ta nufi titi mafi kusa abun hawa ta tare, tare da shiga "Tasha zamu Malam." Shi ne ka
ɗ
ai abunda ta ce yayin da take
gyara zamanta a cikin abun hawan.
"Wace tasha yar'uwa?"
"Koma wacce." Ta amsa cikin ƙosawa.
Bai sake cewa komai ba ya ja zuwa tasha mafi kusa.
Bayan ta biya shi hakkinsa ta sauka ta ƙara nausawa cikin tashar, yan union ne suka yi mata caa! Kowa
nne yana tambayarta garin da zata je.
Rashin amsar bayarwa ya saka ta tambayi
ɗ
aya daga cikinsu, wace jihar ce tafi nisa da nan?"
"Balgori."
"Tafiyar awa nawa ce daga nan?"
"Awa takwas Hajiya, amma ki yi haƙuri zan miki katsalandan, don Allah m
e yasa meki haka na ga jikinki a farfashe."
Tsaki ta ja, a harzuƙe ta ce "Zaka sama mun mota ko na ƙara gaba, gari da yawa maye baya ci kansa ba."
Cikin
ɓ
arin baki ya ce "Afwan Hajiya mu je in kai ki gun motar garin.
*************
A
ɓ
angaren Irfa
n kuwa ya kasa jurar rashin ji daga Mahee kwana biyu, duk yanda ya so taushe zuciyarsa abun ya ci tura, dalili kenan da yasaka ya shirya da yamma cin ranar Laraba ya nufi unguwarsu, tuni ya manta da alƙawarin da ya yiwa Ma'eesh na cewa zai yi iya ƙoƙarinsa
ya ga ya manta ta, kuma zai daina kula ta na
ɗ
an lokaci.
Bai zame ko'ina ba, sai inda ya saba parking motarsa fitowa ya yi ya taka zuwa bakin ƙofar gidansu.
A haka ya karaci sallamarsa ba kowa a zauren, da alama kuma Umma dake ciki bata jiyo shi ba.
Ya fi mintuna biyar tsaye a gun ko yaron da zai aika ciki bai samu ba, dalili kenan da ya sanya bisa tilas ya juya ya nufi motarsa zuciyarsa ba da
ɗ
i, Sadiƙu da yake shirin karyo kwanar gidan nasu yana hango Irfan ya yi saurin la
ɓ
ewa, domin har ga Allah
bai shirya amsar tuhumar da Irfan
ɗ
in zai masa akan Mahee ba. Domin shi kansa har lokacin yana cikin jimami da dama sanin sanar da iyayen nasu halin da ake ciki.
Da yasan abinda zai biyo baya tabbas da bai fa
ɗ
a ba.
Ɗ
orawa....
*WATA UNGUWA*
*(L
abarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ku biya biya ku
ɗ
inku ta wannan account
ɗ
in
Account nam
e: Ruƙayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202
Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.
Ga mutanenmu na Niger masu buƙatar saye zaku biya
400F ta wannan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903
Ko da ku
ɗ
inka....
..
7 Sep, 2021
PAGE 17
BABI NA SHA BAKWAI
_RANAR WANKA BA A BOYON CIBI_
Tafiya take c
ikin ƙuncin da ra
ɗ
a
ɗ
in zuciya, tuni idanunta suka makance bata ganin kowa bata ganin komai a gabanta sai muradinta, a yanzun ta yarda da cewa bata da wanda yafi shi a rayuwarta. Tana da yaƙinin cewa idan duk duniya ta juya mata baya shi ba zai ƙyamace ta b
a balle ya guje ta, shi ka
ɗ
ai ne bangon da ya rage mata wanda zata jingina da shi ta ji sanyi a zuciyarta da garwashin wutar ƙiyayya ke ruruwa a cikinta.
Mintuna ka
ɗ
an suka sada ta da titin unguwar wanda tsabar ru
ɗ
anin da take ciki bata ma san ta zo ba,
sai da ta ji ƙarar ababen hawa da order wasu daga ciki sa'annan ta ankara.
Tun a cikin layinsu mutane ke ƙare mata kallo ganin yadda take tafe cikin yanayin fitar hayyaci ga kuma Uniform
ɗ
inta sun lalace da jini haka
fatarta duk ta yi ru
ɗ
u-ru
ɗ
u shacin
bulala ko ina kwance a fatarta har a gefe-gefen fuskarta kasancewarta fara ya saka raunin suka bayyana ƙarara.
Haliru Maishago yana zaune ta gifta shi ta wuce, girgiza kai kawai ya yi cikin alamun tausaya duk da bai san me ya faru da ita ba.
Tare Nap
ep ta yi tare da fa
ɗ
awa ba tare da ta tsaya yin ciniki ba.
Sai da matuƙin ya tada Napep
ɗ
in sannan ya ce "Ina zamu.?"
Da ƙyar ta iya bu
ɗ
e baki kamar wacce aka yiwa dole ta ce "Dagarma." Daga haka ba ta sake furta komai ba har suka isa unguwar.
Jakar
ta ta bu
ɗ
e ta ciro ku
ɗ
in
ɗ
azu da Baba ya bata ta miƙa wa mai Napep
ɗ
in, bai ce komai ba ya cire ku
ɗ
insa ya bata canji a ƙasan zuciyarsa yana jimamin abin da ya sami wannan kyakkyawar yarinyar haka.
Cike da ƙarfin gwuiwa da saka rai ta nufi cikin gidan d
a take tunanin yanzu nan ka dai ne madogararta, ta saka kai tare da shigewa cikin gidan.
Jama'ar gidan sai ƙare mata kallo suke, wasu daga cikin karuwan suka kasa ha
ɗ
iye gulmar da ta zo masu, biyu daga cikinsu ne suka ha
ɗ
a baki gurin fa
ɗ
ar "Bariki alale
n gero idan baka iya ba sai ta kwa
ɓ
e maka."
Gayen
ɗ
azu wanda ya nunawa Sadiƙu
ɗ
akin da suke ciki ya kalle ta. Ganin yanayin da take ciki ya bushe da dariya ya ce "Duniya ta miki a tishawar jaki ne shi ya sa kika dawo nan? Ko da yake kin zo inda ya dace d
omin nan gida ne na kowa, kawai ki zo mu jone don bana tunanin wanda kika zo domin shi zai saurare ki."
Duk wannan maganganun da suke fa
ɗ
a ta ji, sai dai kalma
ɗ
aya bata yi nasarar shiga ƙwaƙwalwarta ba balle ta iya haddace ta.
Wucewa ta yi ba tare da
ta tamka musu ba ta nufi
ɗ
akinsu Jafsee.
Zaune ta same shi akan katifa yana jinyar jiki domin shaƙar da Sadiƙu ya mi shi
ɗ
azu bata wasa ba ce, har ya jiyo ƙamshin mutuwa a
ɗ
azun.
Duddoo ne zaune kusa da shi yana masa jajen abin da ya faru
ɗ
azun,
ɗ
ago
kan da zai yi ya ganta a tsaye, cikin rawar murya ya ce
"Mahee ke ce?" Sai a lokacin Ja'afar ya
ɗ
ago kai ya kalli abokin nasa sannan ya sauke dubansa akan fuskarta.
Ras ras! Ƙirjinsa ya buga da ƙarfi ganin yanayin da take ciki, da ƙyar ya ce "Mahee
me kika dawo yi a nan.?"
Wani busasshen murmushi ta masa sa'annan ta zauna a saman carpet na
ɗ
akin tare da fa
ɗ
ar "Ina mai maka albishir cewa na dawo ne domin mu rayu tare har ƙarshen rayuwa."
Kallon baki da hankali ya yi mata tare da hangame baki.
S
arai ta fahimci ƙarin bayani yake nema don haka ta koma yin murmushi ta ce "Na dawo nan ne domin mu yi aure, wallahi ko a nan gidan ka ajiye ni zan zauna, yanzu ba ni da kowa daga Allah sai kai."
Kallonta kawai yake, kallon da ba zaka iya fahimtar ma'an
arsa kai tsaye ba 'Lallai wannan bata da hankali, a yadda suka farfasa mata jikin nan a
matsayinta na jininsu, kenan ni me zai faru da ni idan suka kama ni karo na biyu?' ya fa
ɗ
a a ransa.
A fili kuwa miƙewa tsaye yayi idonsa ƙyar a kanta yana fa
ɗ
ar
"Mahee ki rufa min asiri ki tashi ki koma gida, ko so kike wannan mahaukacin yayan naki ya kashe ni ne?"
Hawayen da suka ƙafe mata tun
ɗ
azu ne suka yi nasarar sake
ɓ
allewa ta ce "Abba ya kore ni daga gidansa da ma rayuwarsa da ta iyalansa ga baki
ɗ
aya,
yanzu ba ni da kowa sai kai, kai ka
ɗ
ai ne na yi imani zaka zauna da ni cikin kowanne hali saboda soyayyar dake tsakaninmu."
Kallon sakarya yake binta da shi yayin da ya ji maganar tata ta zo masa a banbarakwai. Dariya ya sheƙe da ita sannan ya tsuke fus
ka kamar bai ta
ɓ
a dariya ba ya ce
"Sakaryar ina ce ke Mahee? Iyayenki ma suka guje ki balle ni? Shin wai ke har a cikin zuciyarki baki ta
ɓ
a zargin yaudararki zan yi ba? Lallai zuciyarki gafalalliya ce kuma ta shagala da duniya da yawa."
A ru
ɗ
e take bi
nsa da wani irin kallo mai nuni da tsantsar mamaki. Tarjamar kalamansa ta shiga yi a ƙwaƙwalwarta kafin ta iya bu
ɗ
e baki da ƙyar ta ce "Ban fahimce ka ba, kana nufin baka sona, ba zaka aure ni ba?"
Jinjina mata kai ya yi alamun tabbatarwa kana ya ce "Id
an kika zaci ni Ja'afar zan aure ki to kin yaudari zuciyarki, ba zan ta
ɓ
a auren gafalalliyar yarinya irinki ba wacce zuciyarta ta fi ƙarfinta, iyayena suna kyautata min zato ba zan saka masu da auren wacce ta zubar da ƙimarta a waje ba."
Yanzu kam lissa
finta ya gama ƙwacewa, fatan take yi ta bu
ɗ
e ido daga cewar a mafarki wannan abin ke faruwa, amma sai dai da alama wannan zahiri ne ya zo a cikin littafin ƙaddarar rayuwarta.
Tana kuka ta tsugunna a gabansa tana roƙon ya rufa mata asiri ya aure ta, fa
ɗ
a
r take "Ka min rai masoyina, kai ne silar gur
ɓ
acewar rayuwata, ka yi sanadin raba ni da ahalina da mutuncina, shin idan ka kore ni ina na nufa?"
Sosai tausayinta yake ratsa jijiyoyin jikin Duddoo duk da kasancewar shi
ɗ
an iska amma ya tausayawa rayuwart
a.
Duban Ja'afar ya yi cikin sanyin murya ya ce "Jafsee ka tausaya wannan rayuwa da take cike da ƙunci a yau, don Allah ka zauna da ita ko da ba zaka aure ta ba."
A zafafe ya juyo da dubansa ga Duddoo "Ashe fa kai baka da hankali ko? So kake wannan m
ahaukacin yayan nata ya kashe ni, ko so kake banzan mahaifinta ya je ya tonan asiri a gun mahaifana?"
Duddoo zai sake yin magana kenan ya daga masa hannu da cewa "Bana son jin komai daga gare ka, ka sani sabo da kaza bai hana a yanka ta, idan tausayinta
kake ji kai ka aure tan mana, dama can ni ba ita nake so ba jikinta nake so kuma na samu, me ya rage?"
Wani wahalallen kuka ne ya kufce mata da gudu ta tashi tana gyara zaman hijabinta da jakarta ta bar
ɗ
akin domin ba zata juri sauraren wa
ɗ
annan kalama
n ba.
Duddoo ya so ya bi ta ya lallashe ta ko ta ji sassauci a zuciyarta na wannan yaudarar da ta zo mata kwatsam daga inda bata yi tsammani ba, sai dai babu Wadataccin kalmomi a bakinsa da zai iya amfani da su, da yana da yadda zai yi da ya taimake ta,
amma inah....
A waje ta wuce Gayen
ɗ
azu ya yi ƙoƙarin dakatar da ita da cewa "Dama na fa
ɗ
a miki, kawai ki dawo mu jone haka bariki ta gada." Ko saurarensa bata yi ba ta bar gidan cike da ƙuncin zuciya.
Takawa kawai take amma bata san inda ƙafarta ke
sauka ba, kamar yadda bata san inda ta nufa ba, duniyar ta mata duhu ga baki
ɗ
aya, jinta da ganinta sun yi nisa ta yadda bata iya hange ko jin abin da ke faruwa a kusa da ita ba.
Haka ta ci gaba da nausawa cikin layukan unguwar kamar ta
ɓ
a
ɓɓ
iya, bata ma
san da wanzuwar mutane a gun ba balle ta fahimci kallon tausayi da mamakin da suke binta da shi.
Sai da ta yi nisa sosai har ma ta fice daga unguwar Dagarman kafin ta samu gindin wata bishiyar ta zauna, tana son bawa ƙwaƙwalwarta damar yin lissafi da
sanin abin da ya kamata ta yi.
Sai da ta yi iya ƙoƙarinta kafin ta ha
ɗ
a zarrukan tunaninta da suka gama kuncewa kafin ta samu mafita.
Zumbur ta miƙe kamar an tsikare ta da allura ta nufi titi mafi kusa abin hawa ta tare, tare da shiga "Tasha zamu Ma
lam." Shi ne ka
ɗ
ai abin da ta ce yayin da take gyara zamanta a cikin abin hawan.
"Wace tasha yar'uwa?"
"Koma wacce." Ta amsa cikin ƙosawa.
Bai sake cewa komai ba ya ja zuwa tasha mafi kusa.
Bayan ta biya shi hakkinsa ta sauka ta ƙara nausawa ciki
n tashar, 'yan union ne suka yi mata caa! Kowanne yana tambayarta garin da zata je.
Rashin amsar bayarwa ya saka ta tambayi
ɗ
aya daga cikinsu, wace jihar ce tafi nisa da nan?"
"Balgori."
"Tafiyar awa nawa ce daga nan?"
"Awa goma Hajiya, amma k
i yi haƙuri zan miki katsalandan, don Allah me ya same ki haka? na ga jikinki a farfashe."
Wani malalacin tsaki ta ja, a harzuƙe ta ce "Zaka sama min mota ko na ƙara gaba? Gari da yawa maye baya ci kansa ba."
Cikin
ɓ
arin baki ya ce "Afwan Hajiya mu j
e in kai ki gun motar garin.
*************
A
ɓ
angaren Irfan kuwa ya kasa jurar rashin ji daga Mahee kwana biyu, duk yadda ya so taushe zuciyarsa abin ya ci tura, dalili kenan da ya saka ya shirya da yammacin ranar Laraba ya nufi unguwarsu. Tuni ya mant
a da alƙawarin da ya yi wa Ma'eesh na cewa zai yi iya ƙoƙarinsa ya ga ya manta ta, kuma zai daina kula ta na
ɗ
an lokaci.
Bai zame ko'ina ba, sai inda ya saba parking motarsa fitowa ya yi ya taka zuwa bakin ƙofar gidansu.
A haka ya ƙaraci sallamarsa b
a kowa a zauren, da alama kuma Umma dake ciki bata jiyo shi ba.
Ya fi mintuna biyar tsaye a gun ko yaron da zai aika ciki bai samu ba, dalili kenan da ya sanya bisa tilas ya juya ya nufi motarsa zuciyarsa ba da
ɗ
i. Sadiƙu da yake shirin karyo kwanar gida
n nasu yana hango Irfan ya yi saurin la
ɓ
ewa, domin har ga Allah bai shirya amsar tuhumar da Irfan
ɗ
in zai masa akan Mahee ba. Domin shi kansa har lokacin yana cikin jimami da danasanin sanar da iyayen nasu halin da ake ciki.
Da ya san abinda zai biyo ba
ya kenan tabbas da bai fa
ɗ
a ba.
Irfan ya ci gaba da tafiya jiki a sa
ɓ
ule yayin da ƙwaƙwalwarsa ke cunkushe da tunani iri-iri. Ya zo daf da shagon Haliru kenan kamar daga sama ya jiyo ance "Irfan!"
Cikin hanzari ya waiga inda ya jiyo sautin don gani
n mahaluƙin da ya kira shi.
Bai iya ganin kowa ba sai maishagon dake zaune a ƙofar shagonsa, don haka yake kyautata zaton shi
ɗ
in ne ya kira shi. Dalili kenan da ya sanya ya ƙura masa ido.
Ya lura cewa da magana a bakin mutumin ganin yadda bakinsa ke m
otsi tamkar mai lazimi, amma kuma sai ya kawar da kansa gefe.
Hakan ya saka Irfan ya ci gaba da taka sawayensa kai tsaye zuwa inda maishagon yake zaune.
Da isarsa ya miƙa mishi hannu suka yi musabaha sannan ya zauna kan teburin da maishagon ke zaune.
"Ɗan'uwa ka kira ni kuma baka ce komai ba, da alama akwai magana a bakinka."
Irfan ya fa
ɗ
a.
Haliru ya kalle shi, sai ya yi kamar zai ce wani abu kuma sai ya yi shiru.
Can ya ce "Gaskiya ina son na fa
ɗ
a maka wani abu amma ina tsoron abin da zai
je ya dawo, ka san ance _baki shi ke yanka wuya._"
"Karka damu ka fa
ɗ
a min koma miye Insha Allah a nan gurin zamu yi wa zancen ƙabari mu binne shi ba mai ji."
Ya yi mi shi murmushi.
Haliru ya gya
ɗ
a kai alamun gamsuwa ya gyara zama ya ce "ka yi mamak
in kama sunanka da na yi ko?"
Irfan ya gya
ɗ
a kai ba tare da ya yi magana ba domin zuciyarsa ta zaƙu da son jin me bawan Allah nan zai gaya mi shi.
"Ko ba kai ba ne Irfan saurayin Maheerah ta gidan malam Isa?"
Nan ma sake daga kai ya yi bai yi maga
na ba, tamkar dai wanda cutar kurumta ta kama shi.
Haliru ya
ɗ
ora zancensa da fa
ɗ
ar "Ina tunanin daga gidan kake yanzu, kuma da dukkan alama baka samu wacce ka je nema ba."
"Eh haka ne, na yi sallama amma gidan kamar ba kowa shi ya sa na juyo ko wani
abin ya faru ne?" Ya tambaya da yar damuwa a fuskarsa.
"Gaskiya ina ji a jikina ba lafiya a gidan, domin kwana biyu da suka shu
ɗ
e ina zaune a nan na ga wucewar Mahee cikin wani irin yanayi, jikinta duk ya yi ru
ɗ
u-ru
ɗ
u da shacin bulala, ga dukkan alamu
dukanta aka yi bana raba
ɗ
ayan biyu ba, ko dai a makaranta aka dake ta ko kuma a gida domin da uniform a jikinta ta wuce