Showing 54001 words to 57000 words out of 64639 words

Chapter 19 - Wata-Unguwa-Compelete

mai aikata aika-aika akan yarka, hakan kuma ya yi sanadiyar lalacewar budurcinta tun a wannan stage da take."

Sai ya yi shiru yana nazartar Habibu. Habibu ya zabura da ƙarfi "Kana nufin fya

ɗ

e aka yi wa 'yata Salma?"

"A'a, kusan dai haka, a

n yi amfani ne da hannu wajan lalata." Ya fa

ɗ

a murya a sanyaye.

"Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un!" Ita ce kalmar da Habibu ke yawan maimaitawa. Da kyar likitan ya tausashe shi tare da bashi baki har ya nutsu sannan ya shiga yi masa bayanin mafita.

"Yanzu zaka barta anan domin ta ci gaba da samun kyakkyawar kulawa daga likitoci, zamu

ɗ

ora ta akan magungunan da suka dace, in sha Allah zata warke garas kamar ba abin da ya faru."

"Shike nan likita na gode, amma zan iya ganinta yanzu?"

"Eh zaka

iya, amma na barta tana bacci."

Tun a hanya Habibu ke tafe yana cika da batsewa, kallo

ɗ

aya zaka masa kasan baya cikin hayyacinsa, ikon Allah ne kawai ya kai shi gidansa. A ƙofar gida ya ci birki da Babur

ɗ

insa, ya sauka tare da shiga gidan a fusace far

am-faram.

Sautin buga ƙyauren Kofar da ya yi da ƙarfi ne ya tada Biba daga baccin da ya fara samamenta, ta fito a tsorace don ganin keke faruwa.

"Sannu mara mutunci, Allah ya waddan halinki Biba, da ranki da lafiyarki kika yi sakaci har wani ya

ɓ

ata

Miki rayuwar yarki, kaicona na yi nadamar auren ballagaza." Ya fa

ɗ

a cikin

ɗ

aga murya.

"Ya isa haka Habibu, don kana aurena ba shi zai baka damar ka zage ni ko ka ci mini fuska ba, ba zan lamunci hakan ba sam. Kuma ni ba ballagaza ba ce kada ka...."

"

Idan ban kira ki ballagaza ba da limamiya zan kira ki? Ko dabba ma tana kula da ƴaƴanta, sa

ɓ

anin ke da kika kasance mutum mai halin dabbobi."

"Habibu! Wallahi zan aro hali, na kacalcala mutuncinka..."

Bata samu damar ƙarasawa ba saboda saukar gigitac

cen mari da ta ji a kuncinta."

"Ki je gida na sake ki saki

ɗ

aya...." Ya sauke yana huci.

Tana dafe da kunci ta dago fuskarta

ɗ

auke da yanayin tashin hankali ta ce "Ka ƙara sakina Habibu? Bib...biyu fa kenan yanzu?"

"Wanne shi ne hukunci mai sauki

da zan iya yi maki albarkacin Yayana, ki tattara ki bar mini gidana kafin na ƙarasa tsinka igiyar dayar data rage."

Yana gama fa

ɗ

a ya fice ya barta nan a tsaye cikin jimami da matsananciyar damuwa.

'Yanzu wai gida zan koma? Nasan Abbanmu kashe ni ne k

awai ba zai yi ba. Ba ma haka ba wane hali yata take ciki? Me ya same ta?'

Haka ta ci gaba da zancen zucinta, da kamar ba zata tafi ba, komai ta tuna Oho, kawai sai ta juya ciki ta shiga ha

ɗ

a kayanta dana jinjirinta......

Ummu inteesar ce

WATA U

NGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

19-1-2021

PAGE 26

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA

Ci

kin hanzari Sorfina ta ƙarasa wurin tare da janye Mahee daga wurin ba tare da ta ce komai ba.

Alhaji ya biyo bayansu a cikin mall

ɗ

in yana fa

ɗ

ar "Haba don Allah! Ya zaki janye ta muna magana?"

Sorfina ta yi kicin-kicin da fuska ta juyo ta fuskance shi.

"Ka ga Alhaji, wannan ba irinsu ba ce ka yi haƙuri ka daina binmu a baya."

Murmushi ya yi ya ce "Haƙuri dai zaki yi 'yar budurwa, ni ina ra

ɓ

arta ne da alkhairi bai kamata ki saka kafa ki ture wannan gingimemen alkhairin dake tunkaro ku ba."

Ta saki

fuska tare da yin fari da ido "Shi kenan, mu yanzu siyayya muka zo muna sauri ne bari na baka numberta sai ku yi magana daga baya."

Har zuwa lokacin Mahee ba ta ce komai ba sai binsu take da ido.

Alhajin ya karbi number tare da fa

ɗ

ar "Wane suna zan sa

ka ne?"

"London girl." Ta fa

ɗ

a tana rage murya tare da watsa mishi wani irin kallo.

Murmushi kawai ya yi a ransa ya ce 'Wannan tana so ta

ɓ

ata mini shiri, amma bari na kwa

ɓ

ar da wasar kawai.'

Ko da ya

ɗ

ago har sun ƙara gaba suna

ɗ

ibar kayayyakin da s

uke so, bayan wani

ɗ

an lokaci suka gama siyayyar suka tura basket

ɗ

in zuwa wajen da ake biyan ku

ɗ

i.

Manyan alhazan dake wurin sai kallon Mahee suke suna ha

ɗ

iye yawu, a wurin biyan ku

ɗ

in suka sake ha

ɗ

uwa da Alhajin

ɗ

azu, ya kalli mutumin dake girka ku

ɗ

in

ya ce "Nawa ne ku

ɗ

in da suka kashe duka?"

"250,000 dubu

ɗ

ari biyu da hamsin."

Ya gya

ɗ

a kai tare da saka hannu a aljihu ya zaro Atm card

ɗ

insa ya miƙa masa, ba musu ya karb

ɓ

ya ciri ku

ɗ

insa.

"Sunana Alhaji Rabi'u ni

ɗ

an majalisar tarayya ne na nan jih

ar, na manta ban gabatar maku da kaina ba. Ke fa ya sunanki?"

Ya fa

ɗ

a yana kallon Maheerah yayin da suke tunkarar ƙofar fita daga mall

ɗ

in, da kamar ba zata yi magana ba sai can ta ce "Mahee."

'Sai dai ka fa

ɗ

a mata ita dake

ɓ

akuwa a garin, amma fa ni a

i na fi kowa saninka ni da ke da plan a kanka.' Sorfina ta fa

ɗ

a a ranta tana satar kallon shi.

A dai-dai lokacin suka zo ƙofar fita Sorfina ta kalle shi "Mun gode Alhaji ya kamata mu rabu daga nan."

Ta ja hannun Mahee suka fice da sauri.

A boot aka sa

ka masu kayansu suka shige motar Fu'ad ya fisge ta da ƙarfi ba tare da ya ce masu kanzil ba.

Bayan komawarsu gida, Sorfina ta hau zirga-zirga a

ɗ

akinta tana tunani "Inah! Ba zai yiwu ba, ba zan bari ki lalata mini buri daga shigowarki rayuwata ba, zan s

an yadda zan yi na kwa

ɓ

ar da tunaninsa daga kanki Mahee.'

Ta zauna gefen gado tana huci "Fu'ad ne ya shiga tsakani na da wannan burin, dole zan san yadda zan yi na tura shi zuwa ƙololuwa ta yadda zai yi nisan kiwo har na kammala cika burina ba tare da y

a lalata mini shiri ba."

Ta miƙe ta shiga ban

ɗ

aki ta sakarwa kanta ruwa masu

ɗ

umi, sannan ta fito tana saisaita nutsuwarta, ta sake shirya wa cikin ƙananun kaya ta fita zuwa

ɗ

akin Maheerah.

Knocking ƙofar ta yi "Shigo" Mahee ta kar

ɓ

a mata daga ciki, ta

shiga da murmushi ta zauna kusa da Maheerah a gefen gado.

"To ya kika ga garin namu?"

"Ah! gari ya yi kyau sosai, da ma ina jin labarin Babban birni yau sai gani a cikinsa."

"Madallah! Yanzu

ɗ

auko ledojin kayan can mu sake dubawa."

Mahee ta miƙe

ta

ɗ

auko kayan suka fara baje su akan gadon.

Sorfina ta

ɗ

auko wata

ɗ

angalalliyar riga mara hannu, wacce ta ƙoshi da adon stones ta kalli Mahee "Wow! Sis kalli wannan rigar, ba ƙaramin kyau zata miki ba idan kika saka."

Mahee ta kalli rigar sannan ta

kalli jikinta, sai ta hau ƙanƙame jiki da hannuwa.

"Me ya faru?" Ta tambaya da mamaki.

"Gaskiya sister ina ga ba zan iya saka wannan rigar ba ko alama, wa

ɗ

annan ma da suke jikina da ƙyar na iya fita da su, duk wani iri nake ji."

Sorfina ta shiga na

ɗ

e

rigar tana harha

ɗ

a sauran kayan "Ai shi kenan, sai ki haƙura da cika burinki domin ina ga ba zai ta

ɓ

a cika ba."

Cikin rawar baki ta ce "Ka...mar ya na haƙura da bu...rina? Kin san me kike fa

ɗ

a kuwa?"

Sorfina ta yi mata wani irin kallo ta ha

ɗ

e fuska

alamun ba wasa ta ce

"Eh mana, idan har ba zaki iya saka wannan kayan ba, banga dalilin da zai saka ki

ɗ

auki rayuwar bariki a matsayin hanyar cikar burinki ba."

Mahee ta kafe ta da ido kawai "Ba zancen kunya a cikin wannan harkar, idan har kina son mu

yi wannan tafiyar dake dole sai kin cire rigar kunya kin yafa mayafin rashinta, sai kin ƙulla alaƙa da

ɓ

ata garin mutane sa'annan ne zaki samu riba biyu."

Ta

ɗ

an yi shiru tana kallon Maheerah sannan ta

ɗ

ora "Riba ta farko zaki tara ku

ɗ

a

ɗ

e marasa adadi

da zaki iya cika duk wani burinki da su, riba ta biyu zaki cimma burin da ya fito dake duniya."

Maheerah ta gya

ɗ

a kai cikin gamsuwa "Na yarda dake sis, ki

ɗ

ora ni akan hanya, domin ba zan ta

ɓ

a yada wannan burin ba duk rintsi bana jin kuma akwai wanda za

i iya dakatar da ni."

"Da kyau yanzu kika

ɗ

auki hanya." Ta fa

ɗ

a fuskarta da fara'a.

************

Irfan kuwa bayan fitowarsa daga gidansu Maheerah kai tsaye office

ɗ

insa ya wuce, bayan ya zauna akan kujerarsa ya kira yi

ɗ

aya daga cikin yaransa na wur

in aiki a waya, bayan cikar minti uku sai ga shi ya turo ƙofar da sallama a bakinsa.

"Sir gani." Ya fa

ɗ

a yana gyara tsayuwarsa a gaban Irfan.

Irfan ya ciro wata 'yar takarda a aljihunsa ya miƙa masa "Salis kar

ɓ

i wannan takardar, ka je wannan address

ɗ

i

n ka bincikar mun waye Ja'afar (Jafsee), ina son sanin komai da komai game da shi hope ka fahimce ni."

Ya gya

ɗ

a kai "Yes sir, na fahimta."

"Hurry up."

"Ok sir."

Ya juya lokacin da yake saka takardar a aljihun gaban rigarsa ya fice.

Irfan ya fesar

da iska daga bakinsa tare da dafe kansa da hannu biyu, ya ba wa kujerar da yake kai amana ta hanyar jinginar da kansa a jikinta.

'Ni da kaina ya kamata na je wurin nan, amma na sani dokin zuciya zai iya fisga ta na aikata

ɗ

anyen aiki, wanda haka zai iya

sakawa baya ta haihu.'

Ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana fa

ɗ

ar

"Wannan yaron ya cuce ni, ya nisanta ƙwayar idona da kallon wacce ke sanyaya zuciyata. Idan har ta tabbata cewa yaudararta ya yi ni kaina bansan hukuncin da zan yanke masa ba."

Ya yi huci yana juyar da kai, "Ba wannan ya kamata na fi damuwa da shi ba, neman matata shi ne mataki na farko da ya kamata na bi."

Yana gama fa

ɗ

a ya kwashi key

ɗ

in motarsa da wayarsa ya zuba a aljihu ya bar office

ɗ

in cikin hanzari.

Dai-dai zai fita

suka ci karo da Ma'eesh.

Da mamaki ya kalle shi "Saurin me kake yi haka Irfan? sai ka ce wanda zai tashi sama?"

"Gidajen ya

ɗ

a labarai zani, zaka raka ni ne?"

"Me zaka yi a can?" Ma' eesh ya tambaya.

Irfan ya ci gaba da tafiya akan duga-dugansa yana f

a

ɗ

ar

"Malam ka adana tambayarka sai na dawo, ni ka ga tafiyata."

Ya ƙara saurin tafiyarsa, cikin hanzari Ma'eesh ya bi bayan shi domin yana tsoron Abin da zai je ya dawo, idan har ya bar shi ya tafi shi ka

ɗ

ai to fa sai yadda ta yiwu wai naƙuda a

ɗ

akin m

ayya.

Ummu Inteesar ce

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

29-1-2022

PAGE

27

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI

Haka malam Audu ya shiga zazzagawa Inna Halima kwandon masifa amma ita ko a kwalar rigarta. Da ma ta ga abin nasa ba na ƙare ba ne, sai ta miƙe tana ƙoƙarin barin

ɗ

akin tana yar dariya tare da fa

ɗ

ar "Idan ka gama zaka iy

a fitowa daga

ɗ

akin."

'Wato ita duk wannan kumfar bakin da nake bai dame ta ba ko? Ni na rasa gane ma wacce irin mata ce na auro haka, zuciyarta kamar

ɗ

utse, da wuya abu ya jijjigata.' da wannan zancen zucin ya fice daga

ɗ

akin.

Bayan wasu yan kwanaki

malam Audu ya je ya yi bikon Rakiya ta dawo

ɗ

akinta akan sauran igiya

ɗ

aya da ta rage musu.

Malam Audu ya maida ita ne da tunanin abubuwa za su gyaru, ya yi tunanin ko ta yi hankali ta

ɗ

auki darasi daga abubuwan da suka faru a baya. ashe fa nama ne kaw

ai ya dahu romon yana nan a

ɗ

anyensa. Kuma ma ance wai mai hali ba ya fasa halinsa. Don haka bayan dawowarta ma sai suka

ɗ

ora daga inda suka tsaya ita da Halima.

Ko da yake zaman da Rakiya ta yo a gida ashe kos

ɗ

in rikici da tsokana ta koyo, don haka ta

na dawowa ta shiga aikata shi. Yanzu abinta ya wuce kan Inna Halima har su Lantai take tsokana.

*********

Tsautsayi wanda ba a sakawa rana!

Watarana Rakiya na zaune a

ɗ

akinta Sale ƙaramin

ɗ

an Lantai ya koro kaza sai ta shigarwa Rakiya

ɗ

aki cikin r

ashin sa'a kazar ta yi kashi a

ɗ

akin.

A zafafe Rakiya ta taso daga inda take kishingi

ɗ

e ta fyalle yaron da wani gigitaccen mari har sai da ya hantsila.

Ya fasa ihu yana kururuwa "Wayyo Mama!"

Duk wannan abin akan idon Lantai ya faru, ga shi kuwa ba ab

in da Lantai ta tsana a duniyarta kamar a ta

ɓ

a mata 'ya'ya. Wannan abin ya hassala ta ta yunƙuro cikin zafin rai.

"Ke Rakiya idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, ni kinsan bana shiga shirginki haka kuma bana lamuntar a ta

ɓ

a mini 'ya'ya, ni ba yaya Hal

ima ba ce."

Rakiya ta kalle ta cike da rainin hankali "Allah ko mai 'ya'ya? To me zaki yi? Kin sani sarai ni walki ce dai dai nake da ƙugun kowa a gidan nan."

Lantai ta matso kusa ta fallawa Rakiya fallelen mari a kuncinta ta

ɗ

aga yaronta ta bar gun.

Rakiya ta tsaya kiƙam ta dafe kunce tana fa

ɗ

ar "Kai! Kika mare ni? Ashe yau za'a yi ruwan rikici a gidan nan." Tana gaba fa

ɗ

a ta sunkuya ta kamo

kazar nan ta jefa a rijiyar dake tsakar gidan na su. A zatonta ko

ɗ

aya daga cikin kajin da Lantai take kiwo

ne tana siyarwa.

Inna Halima na ganin haka ta fito a hanzarce tana fa

ɗ

ar "Cab! Kazata kika jefa rijiya tsabar neman fitina Rakiya? Ai kuwa yau zaki ga haukar da tafi taki."

Rufe bakinta ya yi dai dai da shigowar Haidar

ɗ

an Rakiya na kusa da ƙarshe,

dawowarsa kenan daga makaranta yana riƙe da allonsa, da ma tana tsaye a hanyar ƙofar gidan, don haka ba tare da wani nazari ba ta sunkuce shi, sai ji kake tsundum, ta jefa shi cikin rijiyar.

"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Rakiya da Lantai suka fa

ɗ

a a tare cikin

ɓ

arin baki. Kowaccensu ta

ɗ

ora hannu a kai ta zare ƙwala-ƙwalan idanunta.

"Yaya Halima kanki

ɗ

aya kuwa? Haidar fa kika jefa a rijiya a madadin kaza!" Lantai ta fa

ɗ

a cikin tashin hankali.

"Haidar

ɗ

in fa, rai ya fi rai ne? Ko ita kazar

ba numfashi take shaƙa ba?." Inna Halima ta mayar da amsa a zafafe.

Rakiya ta yi kukan kura ta rarumo Kausar (yar Inna hakima yar shekara 7) ta kunduma ta cikin rijiyar sai tsumbul suka ji sautin fadawar yarinyar a rijiyar.

A wannan lokacin Lantai ka

sa magana ta yi sai fashewa ta yi da kuka, da ma iya sune a gidan, sauran yara suna makaranta. Dayar matar gidan kuma ta fita.

Inna Halima da ƙwalla wani ƙwalelen ihu cikin ƙwalelen sauti tare da

ɗ

ora hannu akai ta ce "Shi kenan Rakiya, kin cuce ni yar

budurwar tawa kika hallaka mini?" Ta ƙarashe zancen cikin kuka.

Rakiya ta yi murmushin yaƙe d yafi kuka ciwo cikin zafin rai ta ce "Annafu bin nafsi, yadda kika shaƙe numfashin

ɗ

ana haka na tauye hancin yarki daga shaƙar iskar duniya."

Daga nan suka

hau dambe kaka-kaka kiki-kiki. Lantai da ta ga lamarin sai godiyar Ubangiji kawai sai ta shiga

ɗ

akinta ta

ɗ

auko makulli da hijabi ta, ta sulale zuwa ƙofar gida sannan ta garƙame gidan da kwa

ɗ

o gudun kada sauran yaran su dawo su shiga gidan suma mahaukatan

iyayen nasu su salwantar da rayukansu.

A haka ta bazama cikin unguwa tana ihun neman agaji, bayan ta samo mataimaka ta bu

ɗ

e gidan, da ƙyar aka raba fadan don har Rakiya ta cijgewa Inna halima rabin kunne da haƙoranta masu kaifi kamar zarto.

Ita kuma

Inna Halima ta samu nasarar bigewa ragiya idon dama har sai da ya tsiyaye. A taƙaice dai ko da aka raba fa

ɗ

an sun yi kare jini biri jini.

Malam Audu da ya dawo daga aikinsa ya tarar da wannan mummunan labari kawai sai ya yanki jiki ya fa

ɗ

i.

Sai da y

a yi jinyar sati

ɗ

aya a asibiti kafin aka samo kansa.

Bayan dawowarsa ya ƙara sakin Rakiya a karo na Uku, ita ma Halima ya sake ta a karo na barkatai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login