Showing 57001 words to 60000 words out of 64639 words

Chapter 20 - Wata-Unguwa-Compelete

ta ƙi tafiya ya ha

ɗ

a ta da duka har sai da yan uwansa suka zo suka tafi da ita.

Bayan tafiyarsu c

iwon hawan jini ya kama Malam Audu inda yake ta fama da jinya a gida ba ku

ɗ

in kwanciya a asibiti Lantai ce ma take taimaka masa da wasu abubuwan bukatun gida a cikin ku

ɗ

in sana'arta.

MUMMUNAR KADDARA....

Wata rana da misalin ƙarfe uku na daren ranar

wata Laraba, iska ake ba

ɗ

a

ɗ

awa mai tsananin gaske. Kamar yadda kowa ya sani a irin wannan lokacin na hunturu anfi komai samun matsaloli na wutar lantarki da barazanar tashin gobara.

A irin wannan yanayin ne Lantai ta manta da hita a jikin soket lokacin

da zata kwanta bacci, har ruwan ya tafasa ya gama ƙonewa. Abin tsautsayi kawai sai soket

ɗ

in ya yi bindiga ji kake

ɓ

at.

Kafin ka ce kwabo gida ya fara kamawa da wuta bababah!

Zafin wutar ya tashi ilahirin jama'ar gidan A gigice, sai kawai suka riski

kansu zagaye da wuta. Lantai da dayar matar tare da malam Audu da yake kwance a

ɗ

akinta yana jinya sai ihu suke kurma wa da iya karfinsu suna neman agaji.

Yaransu sai kuka suke suna neman taimako.

Ko da makwabta suka ji ihun suka zo don kawo masu

ɗ

auki

tuni gidan ya gama ruruwa ba ko hanyar shiga, ga ginin

ɗ

an matsattse. Ana tsaka da wannan tashin hankali

ɗ

aya daga cikin makwaftansu ya kira yan kwana-kwana.

Cikin yan dadiƙu sai gasu sun ƙaraso sai dai kash, layin na su

ɗ

an karami ne sosai, ko Babur

da ƙyar yake iya shiga layin ballantana babbar mota irin wannan.

Akan tilas aka ajiye motar daga

ɗ

an filin da yake kusa da layin aka ja tiyo zuwa gidan. Daga nan suka dakatar da jama'ar unguwa daga yunƙurin ceto rayukan da suke suka shiga aikinsu.

Su

kuwa jama'ar gidan tun ana jigo ihunsu har aka ji tsit.

Wutar da kamar ƙara izata ake, sai wuraren ƙarfe biyar da rabi na safe aka samu nasar kashe wutar, har ta fara tsallawa makwafta.

A nan fa aka kira ambulance aka shiga fito da gawawwakin mutane

n gidan. Gawa goma aka ciro dukkansu namansu ya gama gasuwa tamkar na ragunan da aka gasa. Da an ta

ɓ

a fatar sai ta su

ɓ

ale.

Banda wasu gawawwakin biyu na ƙananun yara da aka kasa shaida ko suwaye domin

ɗ

ayar gawar ma ana

ɗ

ago ta ta karye tsabar dahuwa da

suka yi.

A wannan ranar mazauna unguwar Garwa sun ga tashin hankalin da basu ta

ɓ

a riska ba, mutuwar mutum 12 a lokaci

ɗ

aya kuma halin mutum

ɗ

aya.

Bayan an kashe gobarar da Sa'a

ɗ

aya sai ga su Na'ilah da kakanninsu ha

ɗ

i da Rakiya da halima tafe suna

kuka wiwi wi.

"Allah Sarki malam Audu shi kenan ka tafi? Wayyo Allah yarana,

ɗ

a uku sun mace lokaci

ɗ

aya? Allah na gode ma." Rakiya ce mai wannan zancen cikin matsanancin kuka da tashin hankali.

Inna Halima tana gefe tana ruzgar nata.

Na'ilah kuwa s

ai ta kutsa cikin gidan da ya zama kango tana kuka sosai tana fa

ɗ

ar "Allah Sarki gidanmu ne wannan? Allah Sarki ƙannena Haidar da Kausar, Allah ka jikan babanmu...."

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'aja

bi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

9-2-2022

PAGE 28

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

Alhaji Saminu ya yi ƙwafa sannan ya juya riƙe da 'yar a hannunsa, ya fice daga gida

n a kufule, ya hau motarsa ya ta da ta da ƙarfin tsiya.

Yana tuƙi yana saƙe-saƙe a ransa 'yanzu kenan ina zan kai wannan jemammiyar yarinyar? Wane mataki zan

ɗ

auka akan Hanifah.?'

Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ƙwafa "Kina wasa da ni Hanee Baby, ko da

yake baki san waye ni ba, haka zalika baki san kirarina ba, ni ne fitilar sharri da ko ba mai nakan kai safe."

A haka ya ci gaba da karatun wasikar jaki har ya isa ƙofar gidan da ya za

ɓ

awa yarinyar don ya zama muhallinta kuma kejin da zai rufe asirinsa

daga fallasa.

Bayan doguwar gaisuwa tsakaninsa da masu kula da gidan marayun, ya nemi ganawa da shugaban gidan, ya yi masa bayanin muradinsa ya sanar da shi cewa ya tsinci yarinyar ne a gefen hanya yayin dawowarsa daga ofis. A haka ya

ɗ

ora shi akan keke

n

ɓ

era, aka bu

ɗ

e wa yarinyar file ya cike ya ƙara gaba, cike da tunanin

ɗ

aukar fansa.

Bayan kwana biyu ya gama shirya shirinsa tsaf. Tafiya ya yi unguwar Dagarma ya ha

ɗ

a kai da yan daba don aiwatar da shirinsa akan Hanee.

Wataranar Asabar da yamma

Hanee da ƙawarta Farida ne suke tafiya a cikin wani layi, Hanee tana sanye da hijabi iya gwuiwa, ta yi shigar kamala, da alama dai ta shiryu. Da ma yan magana sun ce duniya tafi Bagaruwa iya jima.

Farida sai cin-cingum take yi ƙas-ƙas, ta gyara zaman ƙa

ton glass

ɗ

in da ya kusan mamaye rabin fuskarta, ta kalli Hanee.

Ta ce "Gaskiya Mutuniyar kin ba ni kunya, kuma kin saka na ji kunya, da kika zo nemana da wannan shigar."

Hanifa ta

ɗ

ago idanunta, ta zuba mata su.

"Ban fahimci inda kalamanki suka do

sa ba."

"Sarai kin fahimta, kawai rainin hankali ne irin na sabbin ustazai zaki yi mini. Wai ke yanzu me kike nufi kin zubar da makaman yaƙinki kin daina bariki kenan?"

Hanee ta yi murmurshin yaƙe "Kusan haka, domin yanzu na

ɗ

auki darasi daga abin da

ya faru da ni a rayuwa. Sai dai abu

ɗ

aya ne zai iya dawo da ni duniyar bariki shi ne

ɗ

aukar fansa. Bana so akai ga hakan shi ya sa na zo neman taimakonki. Ina zamu je mu yi magana a sirrance?"

Farida ta yalwata fuskarta ta murmurshi ta ce "Idan sirri k

ike buƙata mu tsaya a nan kawai."

"Baki da hankali ne Reedah? Wane sirri ne zai samu akan hanya, inda kowa zai iya tsintar zancen da muke yi?"

Ta jefe ta da murmushi a karo na biyu.

"Gaskiyarki ne, kowa zai iya tsintar zancen, sai dai ba zai yi na

sarar tsintar ma'anarsa ba daga shu

ɗ

awa."

Hanee ta yi yar dariya "Shi kenan mu tsaya a nan, nama ga ba hayaniya sosai."

Bata jira cewar Reedah ba ta

ɗ

ora zancenta "Ina neman hanyar da zan koya wa Alhaji Saminu hankali ne, shi ne dalilin da ya sa ban

goge lambarsa ba. Kin ga ke bai sanki ba, ki taimake ni ki cika mini burina na ƙarshe kafin mutuwata ta riske ni."

"Sarai kin sani, Ni bana harka da ire-iren wa

ɗ

annan alhazzan, amma saboda amincin dake tsakaninmu zan yi miki. Me kike so ayi masa."

Ha

nee ta yi ƙayataccen murmurshi tare da fa

ɗ

ar "Nagode ƙawata, zan baki lambar wayarsa da muhimman bayanai a kansa. Ina so ki ƙuntata rayuwarsa, ya zamana cewa naman dake cikin ruwan mai akan wuta ya fishi walwala. Ina so ki saka shi a masifa sa'annan ki fal

lasa asirinsa a idanun da suke

ganin darajarsa sosai. Da son samu ne ma, ki yi duk yadda zaki yi ki shafa masa wannan cutar ta zamani."

Dariya sosai Reedah ta yi ta ce "Ta kwana gidan sauƙi, indan wannan ne ki kwantar da hankalinki tamkar kina cikin jir

gin sama mai ya ƙare. Na yi miki alƙawarin cewa daga kanki Allah Saminu ya ƙare yaudara."

Suka tafa cike da nisha

ɗ

i, suka ci gaba da tafiya. Sun zo dai-dai titi suka yi sallama Reedah ta juya ta fara tafiya.

Gif! Wani sauti mai ƙarfi ya ratsa kunnen

ta ta juyo a ki

ɗ

ime.

"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un!!"

"Ku bi shi, ku dakatar da shi."

Wadannan sautukan ne ke kawowa kunnuwanta ziyara, idanunta suka fara disashewa. Idan har ba ƙarya idanunta suka fa

ɗ

a

mata ba, kamar Hanifah take gani kwance a cikin jini tana kokawa da numfashinta.

A da gudu ta ƙarasa wurin, a lokacin har an fara kewaye Hanifar da take famar

ɗ

aukar rai. Mai motar da ya buge ta kuwa ya gudu, kamar da gayya ya aikata wannan aikin.

T

a tallabo kan Hanifar tana fa

ɗ

ar "Hanee Baby ki tashi, kada ki mutu pls. Wani ya taimaka a Kaita asibiti don Allah."

Hanifah sai kallonta take tana yunƙurin yin magana, dakyar ta amayar da kalmomin da ta na

ɗ

o a harshenta ta ce "Ki cika alƙawarinki."

Ummu Inteesar ce

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

6-3-2022

PAGE 29

BABI

NA ASHIRIN DA TARA

Bayan fitar Irfan a mota bai zame ko'ina ba sai kafar ya

ɗ

a labarai mafi kusa da shi, ya gabatar musu da shaƙuwarsa. A nan suka nemi ya ba su hotunan ita yarinyar da bayanai akanta domin su fara ya

ɗ

awa.

Irfan ya yi wiƙi-wiƙi da ido t

amkar mara gaskiya, sannan ya ce "Am! Gaskiya ba ni da hotonta a yanzu, amma..."

"Ranka ya da

ɗ

e taya za'a rasa nono a ruga? Matarka ce fa, ya za'a yi ka ce baka da hotonta?" Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya fa

ɗ

a fuskarsa na bayyanar da mamaki.

Ma'eesh y

a yi saurin tarar numfashin mai maganar "Ba fa matarsa ba ce ja'irar, wacce ya ƙalafa a rai ce yake burin aura."

"Dakata Ma'eesh! Ban gayyato ka nan don ka ci zarafin masoyiyata ba, idan wannan ne ya kawo ka don Allah ka tafi tun muna shaida juna."

M

a'eesh Ya kalle shi da mamaki "Akan waccen ja'irar yarinyar zaka yarfa ni a gaban jama'a? Yarinyar da ma ko ƙaunarka bata yi?"

Irfan ya miƙe "Eh

ɗ

in na ji, ta ƙaunace ni ko akasin haka duk wannan ni ta shafa, kuma ina ƙaunarta a haka. Ma'eesh kafi kowa

sanin cewa ni mai sauƙin kai ne, amma akan al'amarin Matata Maheerah ni mai zafi ne tamkar Borkono. Ka tafi kawai."

Jin wannan zancen ya sa Ma'eesh ya fice a fusace. Irfan ya juya yana huci ka

ɗ

an.

Ya ba su bayanan da suke nema sannan ya masu alƙawari

n nan da gobe zai kawo masu hotunanta.

*********

Babban Birnin Balgori

Superior Hotel

9:30pm

Tafe take tana tauna cingum ƙas-ƙas-ƙas, tana sanye da wasu

ɗ

amammun English wears a dirararren jikinta. Ƙafafunta sanye da takalmi, Doguwa ce ba can ba

, tana da manyan fararen idanu tamkar madara.

A gefenta Alhaji Rabi'u ne suke tattakin a tare da shi. Sun zo dai-dai corridorn da zai sadaka da harabar hotel

ɗ

in wayarta ta hau burari.

Cike da iyayi irin na matan bariki ta

ɗ

auka. "Hello dear Sis!"

A

can bangaren aka yi dariya tare da fa

ɗ

ar "Ashe fa yanzu kan mage ya waye kin zama yar hannu."

Ta yi 'yar dariya "Abin da ya wajaba akaina kenan tun da har na fantsamo duniya. To fa ba gudu ba ja da baya, sai na ga abin da zai ture na

ɗ

in Buzu."

Daga can



ɓ

angaren aka sake yin dariya "Ashe za'a jima ana iyo a tafkin zunubai don jiran zuwan wannan ranar da daidai yake da neman jaki mai ƙaho."

Suka saka dariya a tare "Baki da dama Sis."

Sorfina ta tsagaita dariyar tana fa

ɗ

ar "Wai ina kika shige ne yau?

Duk na damu kin san baki ta

ɓ

a kwana ba a nan gidan ba."

Mahee ta juya ta kalli Alhaji tare da kashe masa ido

ɗ

aya, sannan ta mayar da hankalinta akan wayar.

"Ina tare da Alhaji Sunusi ne a Superior Hotel, amma yanzun nan zaki ganni don ina hanya ne ma

."

Daga haka suka yi sallama, Alhaji Rabi'u ya kalle ta, "Amma baki da dama Lady Mahee, me ya saka baki fa

ɗ

a mata gaskiyar cewa kina tare da ni ba ne?"

Dai dai lokacin ne suka zo inda ta yi fakin motarta, don haka ta danna malatsin motar.

Kafin ta s

higa ta kalli cikin idonsa tana wani irin fari "Ai na ga take-takenta ne fa tun a ranar farko, ka san wai yan magana sun ce idan ka ga kare yana sansana takalmi to

ɗ

auka zai yi. Ni kuma ba zan yi sake a yi mini sakiyar da ba ruwa ba."

Ta murmusa, ya may

ar mata da martani murmurshi "Kina da gaskiya Lady Mahee, ai ko a rayuwar bariki wanda duk ya same ki ya gama kula wasu matan, domin ba za su burge shi ba."

Ta fa

ɗ

a

ɗ

a murmurshinta sannan ta yi blowing kiss a hannunta ta hura masa iskar ta shige motarta

tare da yi mata key tana fa

ɗ

ar "Sai gani na biyu Honey."

Ya tsaya a gun yana bin motar da ido 'Lallai kin shigo bariki da ƙafar dama, amma da sannu zan fanshe duka dukiyata da kike ci sannan daga ƙarshe na cimma manufata a kanki.' ya yi wani shu'umin mu

rmurshin da shi ka

ɗ

ai ya san ma'anarsa

**** Haka kwanaki suka ci gaba da turawa al'amarin Maheerah sai da

ɗ

a ta'azzara yake yi. Har ta kai matsayin da bata jin shakka ko tsoron wani ya san sana'arta. Bata shakkar taka masu mulki da dukiya, zuwa wannan lo

kacin har gidaje guda biyu take da, wanda alhazawan da take tarawa suka gina mata. Ita da gidan London girl sai idan ta kai mata ziyara.

Daga nan ƙyashi da hassada suka fara ziyartar zuciyar Sorfina don ta ga Maheerah na neman shiga gabanta a kowanne al

'amari, ga shi tana neman wargaza mata plan dinta akan Alhaji Rabi'u, wanda ta ci alwashin sai ta janyo shi ƙasa.

Tun lokacin da ta fara harkar bariki kawo yanzu bata ta

ɓ

a samun wanda ya fita da ita ƙasar waje ba.

Amma abin mamaki wai agwa-gwa da ƙin

ruwa, sai ga shi Maheerar da ko shekara bata rufa ba a harkar, kusan ko da yaushe tana yawatawa a ƙasashen duniya.

Wannan ya saka duk yawan ƙaunar da Sorfina take yi wa Mahee bai hana mata jin ƙyashinta ba, duk da cewa bata yi wani yunƙuri na dakatar d

a Maheerar daga fantamawa a duniyar daular da take ciki ba.

******

GARIN MAMBIYA

Irfan ya faka motarsa cike da zafin rai ya shiga ma'aikatar ta su. Kai tsaye office

ɗ

insa ya shige sannan ya cire cort

ɗ

in da yake sanye da ita ya saƙale a abin saƙale

kaya da ke kafe a gefe cikin office

ɗ

in.

Ya rage daga shi sai rigar ciki. Ya ƙure masuburbu

ɗ

ar sanyin da take sanyaya ofishin.

Duk da haka zafi yake ji, kuma zufa bata daina tsattsafowa daga kafofin gashin jikinsa ba. Bako tantama zafin dake zuciyarsa

ne yake taimakawa wurin rura wutar zafin da yake ji a ga

ɓɓ

an jikinsa.

"Meyasa Masoyiya? Why? Me yasa zaki horar da ni ta wannan

ɓ

angaren, ba zan iya jurewa ba."

Ya sauke doguwar ajiyar zuciya sannan ya shige ban

ɗ

akin ofishin ya watso ruwa ya fito.

Zamansa da knocking

ɗ

in ƙofar duk ba yi minti biyu ba.

"Yes, shigo"

Sakatariyarsa ta shigo ta

ɗ

an rusuna ta gaida shi cikin girmamawa.

Ya amsa yana kallonta ba walwala "Meya faru kika shigo mini a wannan lokacin da na fi sha'awar ka

ɗ

aici?"

"Sir w

ata matashiya ce ta zo nemanka."

"Me ya kawo ta?"

"Ba ni da masaniya Sir sai dai ta nuna mini tsananin buƙatarta da ganin naka, shi ya sa ma..."

"Je ki fa

ɗ

a mata ba yanzu ba, ta dawo wani lokacin."

Zata sake yin magana ya zare mata ido.

"Ki je kaw

ai ki cika aikinki."

Ya koma ya zauna tare da sunkuyar da kansa kan teburin ya fara karatun wasiƙar jaki.

Ta fice jiki a sanyaye, cikin abin da bai fi minti

ɗ

aya ba ya ji an mur

ɗ

a handle

ɗ

in ƙofar alamar bu

ɗ

ewa.

Ya yi saurin

ɗ

agowa a fusace a zatons

a ko sakatariyar ce ta dawo.

Ya zazzaro ido tare da miƙewa a hanzarce "Ke! Ke ce a nan? Me ya dawo dake a cikin rayuwata a dai-dai wannan ga

ɓ

ar?"

Ummu Inteesar ce

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan

al'ajabi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

11-3-2022

PAGE 30

BABI NA TALATIN

A cikin yanayin jimami da rashin makama, Biba ta gama tattare yan tsumokaranta tsaf

, ta ja akwatinta ta fita tana karatun wasiƙar Jaki.

'Yanzu ina na nufa? Zuwa gidan yaya Hanne dai kamar tsautsayi ne, zuwa gidan Baba kuwa ƙaddara ce da rabon wahala.'

A haka ta nufi hanyar titi a ranta tana fa

ɗ

ar 'Shi tsautsayi idan ya tashi zuwa b

a a san taya zai zo ba, amma ƙaddara bata da makawa, wahala kuwa ta

ɗ

an lokaci ce, koma miye na san dai dole Abbanmu ya bar ni da numfashina.'

Da wannan zancen zucin ta ƙarasa titi ta tare abin hawa sai unguwarsu.

Ko da ta je gidan ta yi Sa'a Abbansu

baya nan, shi ya sa ma har ta samu sararin zama ta huta ba tare da wani tashin hankali ko damuwa sun biyo baya ba.

Bayan dawowar Abban nasu da ya tarad da ita gida, bai kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login