Showing 45001 words to 48000 words out of 64639 words
haka nan mai rabon shan du
ka ba ya jin kwa
ɓ
o sai ya sha._
Sosai maganganun Baba akan mahaifiyarta suka daki zuciyarta ko ka
ɗ
an bata ji da
ɗ
i ba, duk da ta samu labarin ƙuruciyar mahaifiyar tasu bata yi kyau ba, amma koma menene uwa uwa ce, sai dai ba bakin mayar da martani, don h
aka ta ra
ɓ
a shi zata wuce a tsorace yayin da shi kuma ya kawo mata mangara ta kauce da gudu ta ƙarasa cikin gida.
Hanee ta fito daga ban
ɗ
aki kenan suka yi arangama,goshinsu ya ha
ɗ
u da juna ƙum.
"Ahh!" Suka saka ƙara a tare.
Cikin ra
ɗ
a
ɗ
in gumuwar Han
ee ta ce "Wai me yasa kika tsane ni har haka ne Sofi?."
"Ki yi haƙuri Hanee wallahi Baba ne ya koro ni, kinsan masifarsa dai." Ta fa
ɗ
a a ki
ɗ
ime tana waiwayen bayanta.
********"****
ALLURA TA TONO GARMA.
Bayan wata biyu Hanee ta fara laulayin da a
ka rasa gane kanta, kullum da zazza
ɓ
i mai zafi take kwana ga yawan amaye-amaye, duk abin da ta saka a cikinta ba ya tsayawa sai ta haras da shi take samun salama, ba yadda
mahaifiyarta bata yi da ita akan su je asibiti ba amma fafur ta ƙi, domin tana jin t
soron kada garin bincike _Allura ta tono garma._
Sai faman shan saƙa-saƙai da ganyayen itace take tamkar 'yar mai ganye, amma duk na banza.
Ko da Baba ya ga ciwon ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai ya matsanta akan cewa sai an je asibiti.
Ganin tana munƙi-m
unƙin zuwa ya ji a ran shi cewa tana
ɓ
oye wani abin ne don haka watarana ya tasa keyarsu a gaba ita da mahaifiyarsu suka je asibitin gwamnati.
Gwajin farko aka tabbatar masu da cewa tana
ɗ
auke da juna biyu ne.
_Tashin hankali gobarar gemu_
Jin wannan
labarin ya saka Hanee ta
ɗ
ora hannu akai ta saka ihu.
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Na shiga uku ni jikar mutum hu
ɗ
u." Ina ta fa
ɗ
a tana
ɗ
ora hannu a kai tsabar firgici.
Baba Mudi kuwa tun kafin, Hanee ta rufe bakinta ya samu nasarar gwabje m
ata baki da iya ƙarfinsa har sai da Haƙorinta
ɗ
aya ya fara gyangya
ɗ
i yana fitar da jini sosai. Sai kururuwa take yi.
Likitan da ya ga haka sai ya shiga rarrashin Baba Mudi har ya samu ya kore su daga office
ɗ
in gudun kada su tara masa jama'a.
Tun a c
ikin harabar asibitin baba yake dukan Hanifah da iya ƙarfinsa yana bambamin bala'i "Shegiya karuwa, matsiyaciya wacce ta yi gadon gantali a gun uwarta, ni zaki zubarwa da mutunci a gari? Cikin shege a gidana?"
Ya ci gaba da dukanta, Inna ta matso ta shi
ga tsakani ita ma ya kai mata mangara a kumatu, dole ta kauce ba shiri.
"Habah Mudi, wannan wane irin tonon asiri ne kake mana? Don Allah ka yi haƙuri, komai zaka fa
ɗ
a ko ka aikata ka bari sai mun je gida tukunna." Cikin Muryar kuka Inna ke ba shi haƙur
i amma bai saurare ta ba.
Wasu tsirarun mutane daga cikin wa
ɗ
anda ke tsaye a gun suka matso suna ba shi baki, wani dattijo ya ce "Ka yi haƙuri bawan Allah, idan rai ya
ɓ
aci bai kamata hankali ya gushe ba."
"Ka san me ta yi ne?" Ya fa
ɗ
a a kufule yana
kallon tsohon, sai huci yake tamkar kumurci.
"Koma me ta yi ai ka yi mata uzuri ku je gida, kuma ban da abinka ai _ice tun yana
ɗ
anye ake tanƙwarashi_
_Da ƙyar da sidin goshi_ suka ƙwace ta a hannu Baba Mudi suka tare masu Napep ita da Inna suka shig
a, shi kuma ya hawo mashin
ɗ
in hanya.
**********
"Ina take matsiyaciyar, ƙaramar karuwa? Yau ko ni Ko ke a gidan nan." Da wannan furucin ya shigo a maimakon sallama.
Jin sautin muryarsa ya ƙara ki
ɗ
imar da Hanee har ta ji ta yi nadamar dawowa gidan
.
"Shi kenan na shiganga
ɗ
i, yau na san sai nafi gya
ɗ
a marka
ɗ
uwa ka cuce ni......."
Wane tasku Hanifah zata fuskanta a rayuwarta bayan faruwar wannan mummunar ƙaddarar?
Shin Alhaji Saminu zai saurare ta?
Ku biyo ni don jin ƙarashen labarin.
Ummu Inteesar ce
WATA UNGUWA
RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
23 DECEMBER 2021
PAGE 20
BABI NA ASHIRIN
_IDAN ANA CIN ƘASA..._
A motarsu da ake yiwa kirari da shiga ba biya fita da Allah Ya isa suka jefa ta sauran 'y
an sandan suka
ɗ
are cikin hanzari. Direbansu wanda shi ma yake sanye da kakin yan sanda ya tada motar, Maman Fa'ee sai ihu take tana dakatar da su amma ina ko saurarenta ba su yi ba.
Bayan motar ta wuce sauran mazauna gidan na bargaja suka juya ciki, wa
su na dariya wasu kuma suna jajanta mata faruwar lamarin.
A gurin ta ci gaba da tsayuwa cikin tashin hankali a bayyane ta ce "Yanzu ina zan same ta kenan? wace hukumar zasu kai ta?"
Wani matashi na unguwar dake tsaye a bayanta ya girgiza kai, cikin t
ausaya wa ya tako zuwa gabanta ya ce "Mama ki yi haƙuri da abin da ya faru. Amma ni na san inda zasu tun da ga sunan station
ɗ
insu a jikin motar."
"Yaro taimaka ka fa
ɗ
a mini sunan gurin." Ta fa
ɗ
a tana share hawayenta.
"Guza Station dake unguwar Samin
aka a can zaki same su." Cikin tausayawa.
"To yaro na gode, amma ƙarin alfarma
ɗ
aya don Allah ka jira ni na shiga gida na fito sai na tare abin hawa ka kwatanta masa gurin."
Lokacin ana gab da sallar magariba ta juya ciki, bayan 'yan mintoci ta fito
ta sami yaron yana jiranta, tana fitowa ya tare masu abin hawa suka shiga. Ba su zame ko'ina ba sai Guza station. Yana nuna mata ƙofar shiga
ɗ
in ta biya mai Napep ku
ɗ
in duka ya juya da saurayin cikin gari ita kuwa ta bazama ciki tana rarraba ido.
Tun da
take a rayuwa bata ta
ɓ
a taka sawayenta a cikin station ba sai yau.
'Yan sanda ne ke ta kai-kawo daga haraba zuwa ciki.
A bakin kanta ta tsaya kopur Adamu ya ce "Meke tafe dake?" "Yata kuka kame shi ya sa na biyo sahu.
"Ya sunan 'yar taki, kuma me k
ike so yanzu?" Ya tambaya a tsattsaye.
"Sunanta Fa'iza kuma na biyo sawu ne don jin abin da ya saka kuka je har gida kuka kama ta " ta amsa cike da tsiwa.
Ɗ
ayan
ɗ
an sandan dake tahowa daga nesa ya ƙaraso yana tambayar Kopur Adamu abin da ke faruwa.
Adamu ya masa bayani.
Ya gya
ɗ
a kai "Ok, Hajiya an kawo mana ƙarar 'yarki ne akan yunƙurin kisan kai da ta yi."
Maman Fa'ee ta zaro ido ta daki ƙirji "Kisa? Na shiga uku ni 'yarsu jikar Mado."
Asp Ashiru ya gya
ɗ
a kai "Ƙwarai kuwa, wata mata ce 'yar
unguwar ku ta shigar da ƙarar cewa 'yarki na yunƙurin kashe 'yarta."
Ta shiga girgiza kai, "Ba gaskiya ba ne yalla
ɓ
ai, duk zuciya irin ta Fa'ee na san ba zata yi yunƙurin kisa ba. Wace mata ce wannan?"
"Sunanta Iya Suwaiba, 'yarta kuma Sakina. Zaki
iya zuwa ki ga 'yarki tana Cell." Yana gama fa
ɗ
a ya juya ya fice daga station
ɗ
in, don yin alwala.
Ta ƙarasa ciki da hanzari lokacin ana ta kiraye-kirayen magariba.
Fa'ee na ganinta ta rusa kuka tana fa
ɗ
ar "Kin ji ko Mama za'a dabaibaye ni da igiyar s
harri, daga
ɗ
an fa
ɗ
an nan na
ɗ
azu da muka yi." Hawaye ya fara sauka kan kumatunta, bata ta
ɓ
a rayuwa ko da ta minti biyar ba ce a tsare kafin yanzu.
"Shi ya sa na ce miki ka da ki kula su, kinsan Iya mai bakin aku ta fi kowa iya Gulma da kutunguila a ung
uwar, _Fitilar sharri kenan_." Maman ta fa
ɗ
a tana kallonta cikin tausayawa.
Fa'ee ta share hawayenta "Mama ai na tauna tsakuwa ne don aya ta ji tsoro."
"Ga shi garin saka aya a fargaba kin rasa haƙoran tauna wata tsakuwar ba." ta fa
ɗ
a tana share hawa
ye sannan ta ce "karki damu zan je in samu iya in ji dalilinta na kulla miki sharri."
Ta juya ta bar Fa'ee tsaye a Cell
ɗ
in, lokacin da ta dawo gurin kanta an riga an sallame Sallar magariba, a nan ta tarar da Iya mai bakin aku.
Ta harare ta sannan t
a matso, ta ce "Iya me 'yata ta miki kika sa aka kamata?" Iya ta yi 'yar dariya daga inda take zaune shirim kamar rumfa, ta ce "ki tambaye ta ki ji, ko da yake ba buƙata tun da a gabanki ta shaƙe min Ya tana yunƙurin kashe ta baki yi magana ba, sai yanzu."
Sakina ta birtsono baki, "Wallahi Iya tana
ɗ
aki lokacin, kuma ina da yaƙinin ta ji komai amma bata yi yunƙurin raba mu ba, Shamsiyya ma shaida ce."
"To ta Allah ba taku ba, kuma in sha Allah sai Fa'ee ta fita daga wannan tarkon da kuka
ɗ
ana mata da
izininS..."
Bata ƙarasa maganar ba saboda shigowar Atika da mijinta wurin Atika ta matsa gaban kantar ta tsaya. Kopur Adamu ya ce "Me ke tafe dake?"
ta ce "Ni ma na zo shigar da ƙarar Fa'ee ne saboda ta fasa mini kai."
Ta nuna wurin da aka mata
ɗ
in
ki a kai "Yalla
ɓ
ai ka ga wurin, wannan yarinyar 'yar ta'adda ce kowa yana da ƙurjinta a gidan."
"_Atika idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri kuma ki iya bakinki a nan wajen, ko ki kwashi kashinki a hannu yanzun nan_ don na yi fa
ɗ
a da ke
ɗ
azu ba shi zai
baki damar yi wa 'yata sharri ba, ke ki fa
ɗ
i abin da kika yi mana manah. Nan fa suka hau cacar baki, kamar zasu buga ganin haka ya saka 'yan sandan dake wajen suka yi waje dasu tare da masu gargadin cewa Su kula station ba.....
UMMU I
NTEESAR CE
WATA UNGUWA
(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)
ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)
AREWA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
25 Disamba 2021
PAGE 21
BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA
DAWOWA DAGA LABARI.
A yan kwanakin nan Biba ta fara laulayi da alama tana
ɗ
auke da ƙarami ciki. Habibu da ya kasa gane kan ciwonta ya
ɗ
auke ta zuwa Asibiti a gwajin farko aka gano tana
ɗ
auke da cikin wata uku. Murna a gu
n Habibu abin ba ya faduwa yake tamkar ya taka kan jariri. Nan fa ya shiga bata kulawa ta musamman domin ya rage cika dare a kasuwa sai ya dawo tun kafin magariba. Hakan ya damu Biba sosai duk jinta take a tauye, shi ya sa ta matsu ya daina dawowa da wuri
domin duk ya takura mata ga shi ƙazantarta ta da
ɗ
u tun da ta fara laulayi, shi kuma ya tsani ƙazanta yana da matuƙar tsafta da son ƙamshi shi ya sa kullum yake fa
ɗ
a da Biba.
Watarana ya dawo gida wuraren 6pm ya tarar da gidan a kazance kamar bolar cikin
gari. Tun daga ƙofa ya fara ƙwala mata kira.
"Nona! Biba! Habiba!!" Da ƙarfi kamar zai fasa bangon gidan.
Ta fito a tsorace tana maida numfashi "Haba maigida, wannan kiran kamar zaka fasa min dodon kunne? Duk ma ka tsorata ni wallahi."
Ya hararet
a, ta numfasa ta ce "Ba don Ni ba ko don yaronka dake ciki ai ka sassauta kasan ba a son mai ciki tana tsorata zai iya shafar lafiyar yaron dake jiki."
Kalamanta sun sanyayar masa jiki domin Allah ya jarabce shi da son yara, ga shi tun daga kan Salmah
yau shekara biyar kenan ba su kuma samun haihuwa ba sai yanzu da suke saka rai, don haka ya wuce ta zuwa daki ba tare da yace komai ba.
Ta same shi a cikin
ɗ
akin ta zauna tana murmushi "Ka yi haƙuri ban fa
ɗ
a don na bata maka rai ba."
"Ya wuce." Ya fa
ɗ
a a tsaitsaye.
Ta ƙara wadata fuskarta da murmushi "Ka dan yi murmushi mana."
A maimakon ya bi umurninta sai ya ƙara yanke fuska ya ce "Don Allah Biba sai yaushe zaki gyara ki daina ƙazanta? Da can lokacin da muka yi aure ai ba haka kike ba, me ya c
anza ki?"
Cikin yanayin damuwa ta ce "Ka yi haƙuri ayyukan ne ke mun yawa, ga kula da yarinya ga aikin gida da girki shi ya sa, da can kuwa ban da kowa. Amma Insha Allah zan gyara."
Sai a yanzu ya sake fuskarsa ya ce "Ko kefa, ki tuna Habiba yar gayu
n dana sani ada ina so ki dawo ita."
Ta masa murmushin yaƙe a ranta ta ce 'Masifafe, Allah Ya nuna min randa zaka daina dawowa da wuri.'
A fili kuwa cewa ta yi "Am maigida wai yanzu babu customers ne da yawa kamar da?"
"Me kika gani?" Ya waigo yan
a dubanta.
"Na ga ne ka daina kaiwa dare kamar da."
Ya fadada murmushinsa ya ce "Akwai customers sosai fiye da da, ina dawowa da wuri ne don baki kulawa ta musamman saboda wannan." Ya nuna cikinta.
"Kai ai kuwa na gode, amma duk da haka, ya kamata
ka dinga tsayawa har 9 ko 9:30 don na lura cinikin daren ya fi tafiya, Ni zan aika gida ƙanwata ta zo ta dinga taya ni ayyuka ka ga shi kenan." Ta fa
ɗ
a tana murmushin yake.
Ya amsa mata da "To zan duba, bani abincina."
Ta tashi ta miƙo masa abincins
a ya janyo Salmah kusa da shi suka ci tare.
Bayan wani
ɗ
an lokaci Habibu ya ci gaba da jimawa a kasuwa, Biba kuma ta ci gaba da Sabgoginta na yawace-yawace.
A gefe
ɗ
aya takan aiki Salmah gidan Baba mai itace sayen wani abu irinsu daddawa, Maggi da sa
uransu. Inda shi kuma Baba mai itace ya yi amfani da damar ya ci gaba da lalata mata yarinya ba tare da ta sani ba. Duk lokacin da Salmar ta yi yunƙurin sanar da ita, sai ta kwatse ta bata bari ta yi magana.
Bayan watanni Shida Biba ta haifi
ɗ
anta kyakk
yawa, murna wurin Habibu ba a magana yau dai ya samu Magaji Namiji.
Ranar suna yaro ya ci sunan Salman, a gidan yaya Hanne aka yi shagulgulan suna kasancewar ita gidanta ba ya da girma sosai.
A haka Biba ta ci gaba da renon yaronta cikin kulawa da taim
akon matar babanta har zuwa lokacin da ta yi arba'in. Bayan wasu watanni Habibu ya bijiro da zancen ƙara aure. Nan fa Biba ta tuma tara bata ta
ɓ
a ƙasa ba, ta ƙeƙashe ido kan cewa bai isa ba.
Watarana ta same shi zaune a falo yana rungume da Salim ta tsa
ya a kan shi ƙiƙam.
"Habibu ni fa ban fahimcin wannan abun ba? Duka duka yaushe ne muka yi auren da zaka tsiro wata maganar banza? Me ka rasa a rayuwar aurenka da
ni da har wannan tunanin ya shige ka?" Ta fa
ɗ
a tana ta huci kamar macijiya.
Bai tari nu
mfashinta ba, sai da ya bari ta gama sauka sannan ya ce "Na rasa tsafta a gidana, ba kya kulawa da yarana yadda ya kamata ni kaina bana samun kyakkyawar kulawa da ta dace, me yasa ba zan yi tunanin ƙarin aure ba?" Ya kalle ta a
ɗ
age.
"Haka kace?"
"E
h haka na ce." Ya mayar mata.
Ta juya tana jan tsaki tare da fa
ɗ
ar "Ayi mu gani idan tusa zata hura huta."
"Zata hura kuwa har ma ayi sanwa akwashe a ci." Ta tsinto muryarsa yana fa
ɗ
a yayin da ta je kofar shiga uwar
ɗ
aka.
Tun daga lokacin ne kuma
kwanciyar hankali ya ƙauracewa gidan, Biba ta daina kula Habibu sam, ko abinci ta yi bata ajiye mishi sai dai ya dafa nasa ya ci. Da ya gano cewa da gayya take yi masa wannan abubuwan sai ya dinga ciko cikinsa daga kasuwa. Da ya shigo sai dai ya kwanta ya
tashi, shi ma kwanan gidan bisa tilas yake yinsa domin ji yake tamkar a ƙaya yake saboda kazantar matar tasa ta ninku, har kayan miya take ajiye wa akan gado in ta ga dama.
Sai dai duk da hakan Habibu bai fasa shirinsa ba, bai kuma sake fa
ɗ
a mata komai
ba, sai ana gobe za'a daura auren da dare ya same ta a
ɗ
aki, ya jefa mata invitation card a jiki.
"Gobe za'a
ɗ
aura mini aure da yar shilar amaryata yar gayu, idan kin ga dama ki gyara gidan in baki gani ba kuma matsalar ki, domin ke za'a zaga ba ni ba."
Yana gama fa
ɗ
a ya fice daga
ɗ
akin zuwa ban
ɗ
akin dake tsakar gida.
Nan ta saki baki galala, ta bi shi da kallo har ya
ɓ
ulle. Sai ga shi hadarin da ya gangamo daga idanunta ya fara zubar da ruwan ƙwalla.
Tana jin motsintsa ta yi saurin share fuskarta
tare da gayyato jarumta a zuciyarta ta ce "A'ina zaka ajiye matar? Ko a gidansu zaku tare?" Tana yar dariya irin ta takaicin nan.
"Wannan ba matsalarki ba ne, ko da yake akwai haƙƙin maƙwaftaka bari na fa
ɗ
a miki." Ya yi murmushi sannan ya ƙulla zancensa