Showing 3001 words to 6000 words out of 64639 words
da za ta sada ta da layin gidan yaya Hanne(yayar mahaifiyarta) tana shigowa kan layin gidan dai dai nan w
ani Babur ya danno cikin layin zai fita, bai yi aune ba ya ka
ɗ
e ta.
Ihu ta ƙwala wanda ya gigita shi, bai tsaya ganin ko 'yar waye ba kawai ya ƙarawa babur
ɗ
insa giya ya fece ya na fa
ɗ
ar "Ku ga yarinya zata jaza mun bala'i yasin ba zan tsaya ba."
Kaw
u Sadi da ya shigo layin yanzu ya hango abun da ke faruwa sai dai kafin ya ƙaraso gun tuni mai laifin ya gudu.
Da hanzari ya ƙaraso inda take ya tada ta zaune don duba ko ta ji rauni.
Tabbas ta ji rauni, bakinta ya fashe da jini
ɗ
aya daga cikin ƙananun
hakoranta masu kama da haƙoran
ɓ
era ya fita, kanta ya fashe sakamakon ƙumuwa da kan ya yi da dutse yayin da take fa
ɗ
uwar.
Kan kace me, jama'ar layin sun cika gun an kewaye ta ana ta jimami. Wani ƙaramin yaro ne na ga ya juya da gudu ya shige wa gida a
layin, zuwa jimawa ka
ɗ
an sai ga shi ya dawo tare da Biba da yaya Hanne.
"Innalillahi wa innailaihir raji'un! Salma me ya zo dake nan?" Ta fa
ɗ
a kamar za ta fashe da kuka ta rarumi 'yar ta zuwa shagon magani mafi kusa.
Sun mata duk taimakon da ya dace
sannan ta saba 'yar ta a baya ta nufi gidanta.
A hanya ta ha
ɗ
u da Abba, yake tambayar abunda ya faru.
A nan ta gaya mata cewa fa
ɗ
uwa Salmar ta yi.
Kofar gidan ta bu
ɗ
e da maƙulli sannan ta sa kai a cikin gidan.
Zo ka ga tsakar gidan yanda ya yi k
aca-kaca tamkar makwancin Jaka.
Kwanuka ne ga su nan birjik wasu har sun bushe, sai ƙuda ke bin su buuu!
Tana giftawa zata wuce ƙuda suka tashi buuu, sai sautin kukan ƙudaje kake ji.
Wuce wa ta yi zuwa
ɗ
akinta tana fa
ɗ
ar "Don Allah ji yanda ƙudaje
suka cika gida kamar inda aka yi kashi, ni wa
ɗ
annan banzayen ƙudajen da zan samu maganin kisansu da tuni na ƙarar da su mtsw! Ta fa
ɗ
a tana jan wani uban tsaki.
Shi ma
ɗ
akin baya shaƙuwa ban da zarnin fitsari ba abunda ke tashi a
ɗ
akin.
Wani tsumma ta
Shimfi
ɗ
a ta ajiye yarinyar sannan ta fita waje tana fa
ɗ
ar "A'ah! Yau dai har yanzu ba wacce ta shigo gidan nan, ga lokaci yana tafiya ban
ɗ
ora komai ba har cikina ya fara kiran ciroma."
Can kuma ta miƙe waje tana leƙen ƙofar gida,
ɗ
aurin kirji ne a jiki
nta kanta ba ko
ɗ
ankwali.
Sadik ne ya zo wucewa nan ta sa baki ta kira shi. "Kai Sadik zo nan."
Ƙ
arasowa ya yi ta dube shi "Idan ka je gida don Allah kace ina kiran Hanee da Sofi, ina nan ina jiransu yanzu."
"Gaskiya ba gida zani ba, bari dai zan
biya na kira sun."
Murmushi ta yi har ƙazaman hakoranta suka bayyana "Yawwa ƙaninmu yi sauri
ɗ
an albarka."
Bai bi ta kanta ba ya wuce abinsa.
Da har zata juya ciki ta hango
ɓ
ullowar Nazee, ƙara maƙewa ta yi yanda ba zai hangota ba gudun kar ya gu
du.
Sai da ya zo daf da ƙofar gidanta ta dawo dai dai inda take
ɗ
azu ta ce "Nazee namu don Allah zo ka ji."
"Me zan ji ne? Yau dai haka zaki ganni ki bar ni Biba..."
"Habah! Nazee Biba ce fa, kai kasan wannan harƙallar yanda take duk cu
ɗ
e ni in cu
ɗ
e ka ne, zo ka ji don Allah." Ta fa
ɗ
a tana yashe haƙora.
Ganin bashi da mafita ya taka zuwa soron gidanta ita kuwa ta koma daga ciki "Ga ni miye?"
Ya fa
ɗ
a yana ha
ɗ
e fuska wai don kar ta ga damarsa.
Bata damu da hakan ba ta ce "Nazee don Allah
ɗ
ar
i uku zaka ba ni in yi cefane, yau haka Habibu ya fice bai ban komai ba, banda shinkafar dake ajiye."
"Mijin naki ma ya kasa baki ni me zan iya maki to?" Ya fa
ɗ
a fuskarsa ba yabo ba fallasa.
"Taimako dai zaka yi irin wanda ka saba, in na dafa ma zan
ajiye maka yasin."
Ganin dai Biba ba zata ta
ɓ
a sake masa kurwa ba in dai ba bata ya yi ba, hakan ya saka ya ciro N200 a aljihunsa ya miƙa mata "iya wannan zaki samu a gurina, kuma Allah ya tsare ni da cin ƙazamin abincinki." Ya juya.
Yana jinsa sanda
ta ke cewa "Shege na ji dai je ka ba dai ka bada ba."
Komawa ciki ta yi tana fa
ɗ
ar "aha! Ka ga yanzu na samu ƙari sai na yi cefane da wannan, 500
ɗ
in da Habibu ya bada ta cefane kuma in sa a bankina, gwanda na tara ku
ɗ
in ankon nan da wuri, shi mai zurf
in ido daga nesa yake fara kuka. Allah ya kawo mun Hanee na san zan samu ƙari a gunta." Murmushi kawai take ita ta ci banza.
Bayan mintuna talatin sai ga Sofi ta shigo gidan.
"Yawwa Sofinmu zo ki ji."
Me zan miki kuma?" Ta tambaya a gadarance.
don
Allah kwanukan nan zaki wanke mun, girki zan
ɗ
ora yanzu ga shi ba kwano ko
ɗ
aya a gidannan nan duk sun yi datti."
"Tab ai ni ba jakar gidanku ba ce da zan ci wannan uban wanke-wanken ni ka
ɗ
ai." Ta fa
ɗ
a tana ƙoƙarin zama kan tsumman tabarmar dake shimfi
ɗ
e a tsakar gidan.
"Habah Sofi ki yi haƙuri, yasin zan saka abincin da ke, ki ci sai kin ƙoshi don na san ko kin je gida ma ba samu zaki yi ba." A haka ta ci gaba da lalla
ɓ
a Sofi har ta shawo kanta ta amince za ta mata.
Nan Sofi ta shiga ha
ɗ
a kwanuka
n yayin da ita kuma ta fice zuwa cefane. Bayan wani lokaci sai gata ta shigo gidan tana fa
ɗ
ar "A'ah! Wai ni kam har yanzu Hanifa bata shigo ba? Wai me take yi ne haka?"
Ta
ɓ
e baki Sofi ta yi ta ce "Tana can tana kitson kan wata mata, baki ga kan ba kamar
an ci goriba da wuƙa, shi yasa ni ba ko wanne kai nake kitsawa ba."
Dariya sosai Biba ta yi yayin da take ƙoƙarin ha
ɗ
a wuta "Gaskiya Sofi baki da kirki."
A taƙaice sai da Sofi ta kwashe kusan awa hu
ɗ
u a gidan kafin ta tafi gida bayan ta cika cikinta
.
Lokacin ne tana shiga gida ta tarar da ruwa a ƙofar ban
ɗ
aki ba tare da sanin ko na waye ba ta sunkuci bokitin ta yi ciki a ranta tana fa
ɗ
ar "Rikici ba gado ba kowa ya kwana lafiya shi ya so, in na fito koma ruwan waye sai ayi wacce za'a yi."
Shine
fa wannan rikicin ya barke dama ita fitina barci take yi kuma Allah ya laanci mai tashe ta.
Da misalin ƙarfe tara na dare Habibu ya nufo gida tun daga bakin titin unguwar wani ya tare shi ya bashi labarin abun da ya faru da 'yarsa.
Hankali a tashe y
a nufo gida, kafin ya ƙaraso gida ya ci karo da wasu mutum uku wa
ɗ
anda suka tarbe shi da labarin sai dai kowa yanda ya ƙaddara masa aukuwar lamarin dabam.
"Assalamu alaikum." Ya shiga gidan da sallamarsa, sai da ya sallama sau uku ba a kar
ɓ
a mishi ba am
ma yana jiyo sautin dariyarsu sai ƙyaƙyatawa suke, dariyar Matarsa tafi ta kowa tashi.
Hakan ya sosa masa rai don haka ya fa
ɗ
a
ɗ
akin ba tare da sallama ba. Tsawa ya yi cak kamar an dasashi a gurin, ya sake baki yana bin falon da kallo kai daganin yanda
ya yi kasan ya ga wani abun da ya matuƙar bashi mamaki ne.
Ba komai ya gani ba face Nura(yaron maƙotansu kuma
ɗ
an uwansa) zabgegen saurayi ne don zai kai shekaru ashirin da uku a duniya kwance yake kan kujera shi da Sagira (yarinyar layin) sun yi kai da
ƙafafu ma'ana dai kansa na gurin ƙafafunta itama kanta na gun ƙafafunsa suna fuskantar juna , kanta bako
ɗ
ankwali.
Sauran 'yan mata biyu suna kwance a ƙasa yayin da Biba ke zaune a tsakiyarsu da
ɗ
aurin ƙirji, sai su
ɓ
alewa zanin yake tana kamawa.
Dag
a can gefe kuwa yarsa Salma ce a yashe kan ledar
ɗ
akin ba ko shimfi
ɗ
a ga filasta a goshinta sai barci take abunta, sai dai kallo
ɗ
aya za ka mata ka fuskanci bata jin da
ɗ
in barcin domin sai mutsu-mutsu take ta yi zufa sharkaf, duk da cewa akwai fankar cha
ji a
ɗ
akin kuma aiki take, sai dai iskanta baya isa gunta.
Ko da suka lura da wanzuwarsa a
ɗ
akin sai suka miƙe kowa ta ja hijabinta sumi-sumi suka bar
ɗ
akin.
Nura ne ya zo ficewa sadda kai ƙasa ya yi yana Fa
ɗ
ar "Sannu da zuwa yaya.."
Har yasa kai zai
fice daga
ɗ
akin Habibu ya riƙo hannunsa ya na Fa
ɗ
ar "Dakata!"
Kallo
ɗ
aya zaka yiwa fuskar Habibun ka tabbatar cewa ransa ya kai ƙololuwa gun
ɓ
aci, zai iya aikata komai a wannan lokacin.......
Ku biya biya ku
ɗ
inku ta wannan account
ɗ
in
Account
name: Ruƙayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202
Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.
*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da w
ata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
*AND NOW*
*WATA UNGUWA*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
3 june 2021
Free p3
BABI NA UKU
Wani kyakkyawan saurayi ne durƙushe akan gwuiwoyinsa ya ha
ɗ
e hannayensa biyu alamar roƙo ya na fuskantar wata 'yar k
yakkyawar budurwa cakulet "Don girman Allah Mahee ki taimakawa rayuwata, ban zo nan don na yaudare
ki ba,tsananin so da ƙaunarki ne suka mun jagora zuwa gurinki duk da kina wulaƙanta ni, na kasa barinki ki jure ki sama mun matsugunni a zuciyar ki komai ƙan
ƙ
antarsa in fake."
Wani mugun kallo ta bi shi da shi tare da jan wani siririn tsaki "Gaskiya wannan ganyen ka yada zuciyarka kare ya
ɗ
auka, sau nawa zan gayama ka fita harkata, amma ka ƙi ji?"
"Ki dai ƙara haƙuri sahibar zuciyata ina matuƙar ƙaunarki
ne shi ya sa..."
"Don Allah dakata malam!
Ta fa
ɗ
a cikin tsawa tare da
ɗ
aga masa hannu. "Irfan kake kowa? Ka saurare ni da kyau, don Allah ka fita harkata domin ina da wanda nake ƙauna, dukiyarka ba ita ce a gabana ba. Ni ba zaka iya siye ni ba kamar y
anda ka siye mahaifana, don haka ka je Allah ya ha
ɗ
a ka da rabon ka....."
Har ya bude baki zai sake cewa wani abu, ta ja wani uban tsaki ta wuce fuu abunta ta bar shi nan
ɗ
urkushe a cikin zauren.
Duk da cewa yana tsananin ƙaunarta duk irin cin kashin d
a take masa baya damuwa amma wannan karon ya ji ciwon abun da ta masa sosai.
Miƙewa tsaye ya yi tare da juyawa ya bar soron gidan zuciyarsa ba da
ɗ
i. Tabbas da ba don Maheerah ba ce ko wace yarinya ce ta masa kwatankwacin haka zai bar ta barin mantuwa.
Am
ma abun mamakin shi ne ko ka
ɗ
an bai ji son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Hakika so makaho ne baya iya ganin matsugunnin da ya dace da shi, da ba don haka ba kyakkyawan saurayi kuma
ɗ
an gata me zai yi da Maheerah 'yar talakawa?
Tafiya ya fara yi ya
na nufar inda ya faka motarsa domin mota bata iya shigowa layin na su, bai yi aune ba sai ji ya yi ya ci karo da mutum. A take ya ji ransa ya ƙara
ɓ
aci.
Cikin hanzari ya
ɗ
ago kansa da niyyar ya sauke zafin akan koma waye.
Daidai lokacin ita ma ta
ɗ
ago ka
nta da nufin ta amayar masa da ruwan masifar dake cikinta sai dai me?
Suna ha
ɗ
a ido ta yi saurin soke kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.
‘’ke wace irin jaka ce? Ko ke makauniya ce da zaki hada ƙazamin jikinki da ni’’ ya fada cikin daga murya yayin
da yake binta da kallon tsana.
So take ta dago kanta ko don ta ƙare masa zagi, amma ko ka
ɗ
an zuciyarta ta kasa amincewa da wannan tunanin nata.
Ganin bata da niyyar magana kuma har yanzu bata kauce daga gabansa ba ya saka shi ratsawa ta gefenta ya wuce y
a na fa
ɗ
ar "Ka da ki sake ha
ɗ
uwarmu ta gaba ta kasance haka domin komai zai iya faruwa.’’
Bayan tafiyarsa Sofi ta juyo baya tana kallonsa a ranta ta ce "Gaskiya kyakkyawa ne ajin farko, da yana masifar ma sai ya ƙara kyau.’’ Tana zuwa nan a zancen zucint
a murmushi ya ƙwace mata.
Tsayawa ta yi tana kallonsa har ya shige motarsa ya bar gun, sai da ta daina hango motar sannan ta bar gun cike da nishadi.
A bangaren Irfan kuwa ko da ya je gida ya tarar da abokinsa Ma'eesh a ƙofar
ɗ
akinsa yana jiran zuwansa.
Tun daga yanayin shigowar motarsa cikin gate
ɗ
in Ma'eesh ya fahimci akwai damuwa tattare da abokin nasa, bare yanzu da ya ƙaraso suna gaisawa kallo
ɗ
aya ya masa ya tabbatar da zargin da yake a kansa, Lallai ya na cikin damuwa sosai.
"Sannu da ƙarasowa
matumina." Ma'eesh ya fa
ɗ
a ya na kallon ƙwayar idon Irfan.
"Yawwa Abokina, yi haƙuri ka zo bana nan, wallahi na manta da na kira ka akan ka zo, shiyasa ban gayama ba da zan fita." Ya fa
ɗ
a ba walwala.
"Ah! Badamuwa Mutumina ko dai an je gurin Sahibar
ne?.." ya fa
ɗ
a yana yar dariya.
A maimakon Irfan ya ba shi amsa kawai sai ya saka maƙulli ya na ƙoƙarin bu
ɗ
e ƙofar, can ya
ɗ
ago yana fa
ɗ
ar "Mu ƙarasa daga ciki." Ba musu ya bi bayan Irfan
ɗ
in suka shige ƙayataccen
ɗ
akin nasa da ya sha ado da kayan alatu
, tamkar dai
ɗ
akin wata Amarya.
Zaunawa Ma'eesh ya yi yayin da Irfan ya ƙarasa gun firji ya dauko musu ruwa da lemo.
"Ko dai gimbiyar ta maka halin nata da ta saba ne?" Ya ji tambayar kamar daga sama.
Juyowa ya yi ya na kallon Ma'eesh "Me ka gani
ne?"
"Na ga damuwa tattare da kai wanda ba haka kake ba kafin awa biyu baya da muka yi waya da kai." Ya maido masa amsa.
Zaunawa ya yi zugudum bai ce komai ba, Ma'eesh ya matso kusa da shi tare da dafa kafa
ɗ
arsa yana fa
ɗ
ar "Ka ga Abokina wannan yarin
yar fa bata ƙaunarka rabuwa da ita shi ne kawai zai sama maka salama a zuciyarka."
Ajiyar numfashi Irfan ya sauke bai ce komai ba, sai Ma'eesh ne ya sake magana a karo na biyu. "Irfan ina mai ƙara gayama ka cire wannan yarinyar a ranka, ga tarin 'yanmat
a nan da yawa a gari? Ni na rasa me ka gani a jikin wannan busasshiyar 'yar talakawar duk da tarin ƴaƴan masu hannu da shuni dake ƙaunarka, amma ka maƙale sai ita, Sam ita ba ajinka ba ce Irfan."
Miƙewa tsaye ya yi yana Fa
ɗ
ar "Ban ga laifinka ba Ma'eesh
har yanzu baka san me ake kira so ba tunda ko budurwa
ɗ
aya baka da. Cire so daga zuciya ba abu ba ne mai sauƙi. Da zan iya a yau da na fizgo soyayyar Mahee daga raina na watsar da ita ko na samu Salama a zuciyata, sai dai abun takaicin har yanzu sonta dak
e zuciyata bai ko jijjiga ba bare ya tarwatse. Haƙiƙa wannan jarabawa ce mai girma, kawai ka taya ni da addu'a."
Girgiza kai kawai Ma'eesh ya yi yana jinjina girman soyayyar Irfan ga Mahee.
Ita kuwa Mahee tana shiga gidan ta wuce
ɗ
akinta cike da tak
aicin na ci irin na wannan mutumin. Tsaki ta ja tana fa
ɗ
ar "Mutum sai ka ce jikan Mayu? Ni na tsani naci a rayuwata wallahi."
Can ta lalibo ƙaramar wayarta tana yunƙurin kiran abun ƙaunarta Ja'afar. Kamar daga Sama Umma ta fa
ɗ
o
ɗ
akin tare da fige wayar
a hannun Mahee tana fa
ɗ
ar "Sannunki da zubar mana da ƙima, wai ke meke damun ƙwaƙwalwarki ne?
Ga Arziƙi ya na kiran ki kin toshe kunne, to wallahi bari in gaya miki tun wuri ki sake shawara kafin abun ya isa kunnen mahaifinki."
Turo baki ta yi tana fa
ɗ
ar "Ni dai gaskiya bana sonsa Ja'afar kawai zan aura, shi arziƙi ai nufin Allah ne."
Bige mata baki Umman ta yi sai da ya fashe ta ce "To marar