Showing 48001 words to 51000 words out of 64639 words

Chapter 17 - Wata-Unguwa-Compelete

da fa

ɗ

ar "Shalelena zata tare ne a sabon gidan dana gina mana, tun da na lura wacce na yi ginin don ita ba zata iya kula da shi ba."

Ji ta yi tamkar yana watsa mata ruwan zafi amma ya ta iya? Akan tilas ta haƙura, kasancewar dare ya riga ya yi, idan ma

tace zata fita yanzu to ina ta dosa? Tana neman wanda zai bata shawarar da zata fisshe ta a wannan lamari, sai dai _bakin alƙalami ya riga ya bushe._

Washegari da misalin ƙarfe takwas na safe aka

ɗ

aura auren Habibu da Amaryarsa Safiya akan sadaki Naira

dubu hamsin.

Bayan Amarya ta tare Habibu ya ci gaba da shariya da lamarin Biba sai dai ranar girkinta zai zo ya kwana, tun da safe zai fita ko magana ba ya yi mata da ta gaji ita ta nemi sulhu da kanta.

Bayan wata

ɗ

aya da auren Habibu wani mummunan

al'amari ya faru, domin Salmah ce ta fara wani ciwo da ba a gane kanta ba. Gata ƙanƙanuwar yarinya amma wari take yi, saboda matsalar da ta dame ta ba abinda take yi masu sai kuka tana nuna gurin da ke mata azabar.

Lokacin shigowar Habibu gidan kenan,ga

nin yadda uwar ta share ta ya saka ya matsa kusa don duba abin da ke damunta.

Da hanzari ya ja da baya yana tsattsaro ido tsikar jikinsa na tashi, cikin Muryar tashin hankali ya ce "Tsutsotsi a jikin 'yata? Wannan wane irin mummunan ciwo ne?"

Shin me

nene ya samu Salmah? Ya zata kaya tsakanin Biba da Habibu bayan ya gano sakacinta ne ya lalata mutuncin yarsa?

Ummu inteesar ce

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)

ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM

LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

27 Disamba 2021

PAGE 22

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Ta

ɗ

ago tare da share hawayenta ta ce"Ba fa komai 'yar'uwa."

Murmushi matashiyar yarinyar da ba za

ta gaza shekaru Ashirin da biyar ba ta jefe ta da shi sannan ta ce "Ki yi haƙuri, ba wai ina da burin na yi miki katsalandan a rayuwa ba ne, amma kin san ance _labarin zuciya a tambayi fuska,_ sannan shi kuka ai ba a yin shi sai da dalili."

Maheerah ta

sauke ajiyar zuciya tare da kawar da kanta daga duban matashiyar.

"Sister ki yi haƙuri, ki bar ni haka zuciyata da gangan jikina suna buƙatar hutu."

Tana gama fa

ɗ

a ta kifar da kanta akan cinyoyinta tana mai ci gaba da shessheƙar kuka.

Matashiyar t

a zuba mata na mujiyarta cikin alamun tausaya ga budurwar.

Wani matashi mai fa

ɗ

in rai dake zaune a kujerar gabansu ya juyo a hasale yana duban Maheerah cikin fusatacciyar murya ya ce

"Habah baiwar Allah! Gaskiya kina shiga haƙƙinmu, ki sani fa kowa da

ke nan ba ya rasa damuwar dake cin zuciyarsa amma ya jure."

Caraf matashiyar yarinyar ta kar

ɓ

e zancen da fa

ɗ

ar "Allah Ya baka haƙuri bawan Allah, amma baka san damuwar dake addabar zuciyarta ba, kada ka manta kuma, hawaye ruwa ne mai tsarki da yake rage

dattin damuwar dake zuciyar mutum ko da kuwa bai wanke damuwar duka ba. Me yasa kake son ƙara mata dafi fiye da dafin dake zuciyarta?"

"Kina da gaskiya 'yanmata, ka yi haƙuri bawan Allah nan motar haya ce dole sai an yi haƙuri, zama ne na

ɗ

an lokaci mu

na sauka kowa zai kama gabansa ba kuma lallai ne mu sake ha

ɗ

uwa ba a rayuwa." Wata mata dake gaba ta fara magana, sannan ta ƙarashe zancen tana duban matashin dake zaune kusa da ita.

A haka motar ta ci gaba da tafiya tsawon lokaci ba tare da Maheerah ta

ce da kowa ƙala ba. Ko da aka tsaya cin abinci ma bata sauka ba sai matashiyar ce ta siyo mata abin ta

ɓ

awa da ku

ɗ

inta, amma Mahee bata kar

ɓ

a ba, ta girgiza kai kawai ta ci gaba da zama shiru tamkar sabuwar kurma.

Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dar

e motar ta ci birki a tsakiyar tashar Babban birnin Balgori. Nan fa hayaniya ta kacame Fasinjoji suka fara sauka daga motar.

A tare Maheerah da matashiyar nan suka sauko daga motar, aka fara kunce kayan dake boot sauran Fasinjoji suka je

ɗ

auko kaya yayi

n da Maheerah ta koma gefe

ɗ

aya a cikin tashar ta samu guri ta raku

ɓ

e tana ƙarewa tashar da halittun cikinta kallo.

Tsawon lokaci ta shafe a haka tana nazari da zancen zuci 'Yanzu ina na dosa kenan? Rayuwa a birnin da bani da kowa kuma ban san kowa ba a

nya hakan zai haifa mini

ɗ

a mai ido kuwa?'

Dafa kafar

ɗ

arta da aka yi ne ya janyo ta daga duniyar tunani zuwa duniya ta zahiri. Kamar wacce ta farka daga dogon bacci ta juya a

ɗ

an razane ta kalli wanda ya dafa ta.

Matashiyar nan ce ta

ɗ

azu, don haka ta

sauke nannauyar ajiyar zuciya 'Hmmm' ba ta ce komai ba.

"Sunana Sorfina Salis inkiya London girl, na fahimci kamar baki san kowa a nan garin ba da alama kuma kina cikin matsananciyar damuwa shi ya sa na

kasa tafiya na bar ki, ya sunanki ne?." Ta fa

ɗ

a loka

cin da ta samu guri a gefen Maheerah ta zauna.

Murya a sanyaye Mahee ta ce "Sunana Maheerah Isah an fi kira na da Mahee."

"Maheerah! Nice name." Sorfina ta fa

ɗ

a sannan ta

ɗ

ora zancen da cewa "Am! Kin ga nan tasha ce, kuma yanzu dare ya yi, bai kamat

a mu yi magana a nan ba, idan ba damuwa ki biyo ni mu je gidana sai mu yi magana a can."

Kallon rashin yarda Mahee ta shiga yi mata don sai a lokacin ma ta ga yanayin shigar yarinyar da taimakon hasken ƙwayayen lantarki da suka kewaye tashar.

Tana san

ye ne da ƙananun kaya riga da wando

ɗ

amammu sai wani matsakaicin mayafi da ta rufe kanta da kafa

ɗ

unta da shi, a kanta kitso ne na attach ta zubo gashin a gaban wuyanta, hancinta kuwa yana maƙale da dutse irin abin adon nan na 'yan bariki. 'Anyah zan yarda

da wannan kuwa ko dai...'

Tana cikin zancen zucin ne ta tsinto muryar Sorfina tana cewa "Ki yarda da ni ba zan cutar dake ba, zan so dai ki bini ne saboda ki samu nutsuwa, amma ba zan miki dole ba."

Tana gama fa

ɗ

a ta miƙe ta yi gaba, ba tare da wani

tunani ba Mahee ta miƙe cikin hanzari ta bi bayanta.

Ta ce "Sister zan biki, na yarda dake."

Sorfina ta yi ƙayataccen murmushi sannan ta ja hannun Maheerah suka ƙarasa gaban wata dalleliyar mota da ba ta jima da yin parking ba suka shige, motar ta h

au titi cikin sauri.

******""

Bayan kamar sa'a

ɗ

aya da rabi da saukar su Mahee tana zaune a ƙawataccen falon da ya sha kayan alatu sanye da wata doguwar riga pink mara hannu. Lokaci zuwa lokaci tana gyara rigar tare da saka hannunta tana kare jikinta

duk ta kasa samun nutsuwa, yanayin shigar bai mata ba sam. Sai ga Sorfina ta fito daga

ɗ

aya daga cikin daƙunan gidan ta ƙaraso falon tana jifar Maheerah da murmushi sannan ta zauna kusa da ita.

Ta ce "Ina fatan baki da wata matsala, sannan kin ƙoshi ba

bu sauran yunwa ko gajiya a tare dake."

Mahee ta gya

ɗ

a kai tare da fa

ɗ

ar "Eh, Alhamdulillah sai dai...."

Ta kasa ƙarasa zancen.

"Ki saki jikinki sister, ki

ɗ

auka cewa nan gidanku ne kuma ni yar'uwarki ce, ki fa

ɗ

a mini dukkannin damuwarki da burukanki,

in Allah Ya Yarda ba za su gagara ba kuma zan taimaka miki da abin da bai fi ƙarfina ba."

Ta ci gaba da gyara rigar jikinta tana kare jikinta da hannayenta.

Sorfina ta yi murmushi a ranta ta ce 'Da alama bata saba da irin wannan kayan ba.'

a zahiri

kuwa cewa ta yi "ina jinki sister, ki ba ni labarinki da abin da ya rabo ki da gida."

A take sauran annurin dake kan fuskarta ya

ɗ

auke lokaci

ɗ

aya ta ha

ɗ

e fuska tamkar limamiyar 'yan wuta. Can kuma sai ga hawaye sun fara wasar tsere a fuskarta.

"Oh

god! Yi haƙuri sister, ban san tambayar zata ƙona miki rai haka ba ki yafe min." Cikin damuwa ta yi zancen.

Mahee ta saka tafin hannayenta ta share hawayen sannan ta sunkuyar da kanta ta ce "Sister ki yi haƙuri ba zan iya amsa miki wannan tambayar a yan

zu ba, kuma bana son ki sake tambaya ta game da ni, amma ina da buruka guda biyu da nake so in cika wanda silar su ne na baro gida idan zaki taimaka mini."

Ta yi shiru tana sauraren amsar da Sorfina zata bata.

Cike da tausaya Sorfina ta kalle ta "ina j

in ki, wa

ɗ

anne buruka ne haka?"

Ta yi murmushin yaƙe ta ce "A'a sister ba yanzu ba dare ya yi, kuma ma na ga mijinki yana gida ki koma wurin shi kawai da safe idan ya fita za mu yi maganar In sha Allah saboda sirri ne."

Sorfina ta wadata fuskarta da

murmushi sannan ta miƙe tana fadar "Shi kenan zo mu je na nuna miki makwancinki."

Ta shiga gaba Maheerah ta miƙe ta bi bayanta a ranta tana cewa 'wannan matar da alama 'yar gayu ce tana son kwalliyar ƙananun kaya masu bayyana surar jiki.'

A dai dai ƙ

ofar wani

ɗ

aki Sorfina ta ci burki sannan ta tura ƙofar ta shiga tana fa

ɗ

ar "Daga yanzu nan ne

ɗ

akinki, har zuwa lokacin da kika gaji da baƙunci a gidan nan. Idan akwai abin da kike buƙata sai ki kira ni, kawo wayarki na saka miki lambata."

Sai a lokaci

n Maheerah ta tuna tana da waya ta ce "Ina jakata kuwa?"

Sorfina ta ra

ɓ

a ta gefenta ta wuce ba tare da ta amsa mata ba, ta

ɗ

auko jakar ta miƙa mata.

Maheerah ta bu

ɗ

e jakar ta

ɗ

auko wayar ta miƙa mata ta ce "Ga ta."

"Ita ce wayarki?" Ta fa

ɗ

a lokaci

n da take kunna wayar, domin a kashe take gaba

ɗ

aya.

Ta ce "Eh ita ce."

Lambar ta saka mata sannan ta yi mata sallama ta fita a ranta tana mamakin wannan yarinyar mai ban al'ajabi, ga ta dai kyakkyawa ajin ƙarshe amma wace ƙaddarar ce ta fa

ɗ

a mata haka

? Kuma me ya same ta duk jikinta a farfashe kamar dai wacce aka yi wa tsinannen duka? A gaskiya ta ƙagu ta ji labarin Mahee, mai yiwuwa ta samu wani darasin mai amfani.

Washegari tun da asuba Maheerah ta farka, abinka da sabo da lokacin sallah ya yi du

k nauyin baccin da ke kanta matsawar tana cikin hayyacinta

to za ta farka. Don haka tana farkawa ta shiga ban

ɗ

aki ta yi alwala ta tada sallah.

Bayan ta idar ta koma bacci, sai wuraren ƙarfe tara ta farka kasancewar jikinta duk ya yi tsami sallar ma da ƙ

yar ta yi, ko da yake abin ne ya ha

ɗ

e mata ga gajiyar zaman mota ga kuma tsamin jikin dukan da ta sha a hannun Baba.

Da ƙyar ta bu

ɗ

e kumburarrun idanunta wa

ɗ

anda har yanzu ba su gama sacewa ba, ta yunkura da ƙyar ta tashi zaune. Sai dai me? Ta gagara sa

ukowa daga kan gadon hannunta na dama da ƙafarta ta hagu sun kumbura sosai.

Rashin sanin abin yi ya saka ta kai hannu ta lalubo wayarta ta dannawa Sorfina kira.

Sai da ta tsinke ta sake kira sannan aka

ɗ

aga. Murya ƙasa-ƙasa ta ce "Mahee ce, don Allah

ki zo na kasa tashi."

A ru

ɗ

e Sorfina ta jefo mata tambaya "Me ya same ki ne Sister?"

"Ta runtse ido, ina ganin na ji ciwo ne a hannu da ƙaf.." bata ƙarasa zancen ba ta ji kiran ya tsinke.

Cikin abin da bai fi mintuna biyu ba sai ga Sorfina ta sh

igo

ɗ

akin da gudu. Ta karasa gaban Mahee cikin hanzari "Sannu Sister zo na kama ki mu fita falo."

Ta kama Maheerah tare da saƙala hannunta a wuyanta suna takawa a hankali har suka ƙaraso falon ta ajiye ta akan doguwar kujera sannan ta nufi

ɗ

akinta da ha

nzari.

Bayan ficewarta daga falon ne Maheerah ta ji a jikinta kamar dai ana kallon ta. Ɗagowar ta ke da wuya, ta ha

ɗ

a ido da matashin da take kyautata zaton mijin Sorfina ne, yana zaune a dinning table ya kafe ta da ido ko ƙyaftawa ba ya yi, tamkar jik

an mayu.

Nan take ta ji ta tsargu sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, cikin tsananin jin kunya, ga shi ko hijab babu a jikinta doguwar rigar jiyan ce a jikinta sai hula, rigar kuwa ta kamata sosai, ko Sorfina dake mace ta ji kunyar ganinta da ta yi sanye da

rigar kasancewar a baya bata ta

ɓ

a shiga makamanciyar wannan ba. Ko gurin Jafsee da take zuwa suna hutawa ai da uniform ne.

Bayan 'yan daƙiƙu sai ga Sorfina ta shigo falon cikin hanzari hannunta riƙe da magani pain reliever ta taka zuwa gaban matashin sa

nnan ta ce "Lovely don Allah taimaka ka zuba mini ruwa a cup na bata magani."

Bai ce komai ba sai murmushi da ya yi ya tsiyaya ruwan ya miƙa mata, ita kuma ta kaiwa Maheerah tare da

ɓ

alla mata maganin ta sha.

"Sannu Sister, bari a kira likita ya duba

ki."

Ta juya ta koma gaban farin matashin ta ce "Lovely ka kira mana likitanka ya duba ta please."

"Yadda kika ce gimbiya." Abin da ya fa

ɗ

a kenan sannan ya

ɗ

auki wayar shi ya miƙe yana fa

ɗ

ar "Ni zan fita, zan kira shi yanzun nan."

"Take care of

yourself bye." Ta fa

ɗ

a cikin sarrafa harshe da karairaya sannan ta raka shi ta dawo gun Mahee.

"Sannu Sister, yanzu zaki ga likitan ya zo."

"Ai ma na fara jin alamun sauƙi kada ki damu."

Ta

ɗ

an muskuta sannan ta ce "Yanzu zan fa

ɗ

a miki burina..."

"Ki bari ki sami sauki Sis." Sorfina ta katse ta.

"Ka da ki damu, jikina ne ke ciwo ba wai bakina ba, baki kuwa shi ke magana. Yanzu ne ka

ɗ

ai damar da zamu iya yin magana a tsanake tun;da maigidan naki ya fita."

Sorfina ta yi murmushi mai ma'anon

i sannan ta ce sannan ta ce "Ina jinki."

"Burina na farko shi ne ina son na fa

ɗ

a harkar bariki sannan na goge kuma na yi ƙaurin suna a cikinta."

Cikin hanzari Sorfina ta

ɗ

ago kai tare da zaro ido ta ce "Me nene?"

Murmusawa Mahee ta yi "Yi haƙuri y

ar'uwa na san zaki ji abin wani banbarakwai wai namiji da suna Zainabu, amma ba shakka wannan shi ne burina na farko, sauran burukan zan fa

ɗ

a miki idan lokaci ya yi."

Sorfina ta sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ta matsa kusa da Mahee tare da kama ha

nnunta ta ce "Na ji sister, kuma kamar yadda na miki alƙawari zan taimake ki, amma ki sani tun lokacin dana

ɗ

ora idona a kanki Allah Ya

ɗ

ora mini sonki, ina jinki kamar ƙanwata ta jini don haka zan ba ki shawara, ki haƙura da wannan burin naki domin ba zai

haifa miki

ɗ

a mai ido ba."

Maheerah ta janye hannunta daga cikin na Sorfina sannan ta kawar da kai gefe ta ce "Me ya saka kike son na janye burina da baki san dalilin kafuwarsa a zuciyata ba?"

"Saboda Barikanci ba sana'ar kirki ba ce, kuma ba a tsin

tar wata riba a cikinta face rasa mutunci da ƙima daga ƙarshe kuma takan jefa mai yinta cikin kogin nadama da ba zai ta

ɓ

a iya fita a cikinsa ba har abada. Na san bariki ciki da bai domin ita ce silar rasa komai nawa a rayuwa."

Duk da cewa zancen Sorfina

na ƙarshe ya jefa ta a ru

ɗ

ani har ta kasa banbamta

ɗ

aya da biyu, amma yana da kyau ta mayad da hankalinta akan burin da ya fantsamo da ita a duniya kuma ta bashi muhimmanci, don haka ta sake tamke fuska sosai ta ce "Na gode da shawararki sister, amma ba z

an iya tum

ɓ

uke wannan buri nawa ba. Idan ba zaki taimake ni ba ya kamata na sani tun wuri don na san inda dare zai yi mini."

Ummu inteesar ce

WATA UNGUWA

(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)

ALƘA

LAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)

AREWA WRITERS ASSOCIATION

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

31 Disamba 2021

PAGE 23

BABI NA ASHIRIN DA UKU

Sorfina ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ta ce "Shi kenan sister tun da wanna

n ita ce rayuwar da kika za

ɓ

awa kanki ban isa na hana ki ba, ko da ma ni ban taimake ki ba na san zaki fita farautar cikar burinki ne, a lokacin ban san wane hali zaki fa

ɗ

a ba. Har gara ki zauna da ni."

Mahee ta gyara zama ta ce "Na gode, ina so ki sani

ina da dalilina na fantsamowa duniya da neman shiga wannan harkar ido rufe."

"Kada ki damu bariki gida kika zo, domin ni ma nan da kike ganina duk kanwar ja ce, cikakkiyar 'yar bariki ce lamba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login