Showing 6001 words to 9000 words out of 64639 words

Chapter 3 - Wata-Unguwa-Compelete

kunya, ana nuna miki Annabi ki na runtse ido, wannan lalataccen yaron kike so mu aura miki, bayan ga nagartac

ce

ɗ

an gidan manya?"

"Ni dai shi nake so, da shi ka

ɗ

ai na ji zan iya rayuwa, aba ni shi ko in....." Ta fa

ɗ

a yayin da ta miƙe ta bar

ɗ

akin.

"Iyyeah! Lallai yarinyar nan abun naki azimun ne, bari malam ya dawo gidan..."

Da misalin ƙarfe tara na dare

Ja'afar ya shirya tsaf cikin ƙananun kayansa ya nufo gidansu Maheerah.

Malam isah na kwance ƙofar gida ya na tsaye ƙofar gida shi da baƙonsa kawai Ja'afar ya zo ya wuce su zuwa cikin Soron gidan ba ko gaisuwa sai bubbu

ɗ

awa yake.

Malam Hadi dake tsay

e tare da Malam Isah ya kama ha

ɓ

a tare da fa

ɗ

ar "Yau na ga abinda ya fi zare tsawo. Anyah! wannan yaron da ƙwaƙwalwa a kansa kuwa? Taya zaka zo ka wuce mai gida bako Sannu."

"Gane mun hanya dai malam hadi... Am! Ina zuwa bari na je na ji da wacce ya zo.

"

Yana gama fa

ɗ

a ya bi bayan Ja'afar zuwa cikin Soron...

Shigarsa ya yi dai-dai da shigowar Maheerah soron tana cewa "Kai! gayena ka ga yanda ka wanku kuwa?, yasin kamar na ha

ɗ

iye ka." Wata shu'umar dariya ya yi.

Jin hakan ya dasƙarar da Malam Isa

h gurin, ganin Ja'afar ya matsa ya na neman bata hannu su gaisa ya dawo da shi daga duniyar mamaki "Ke mutuniyar kawai!"

A tsorace ta

ɗ

ago jin Muryar mahaifinta, idanunta suka sauka kan fuskar dattijon mai farin gemu. Fuskarsa a murtuƙe take ba annuri,

ta yi saurin gano haka ne saboda wadataccen hasken gwalaf

ɗ

in lantarkin da ya mamaye ilahirin soron.

Nan take antar cikinta ta ka

ɗ

a.

"Za ki shiga ciki ne ko sai na tattakaki?" Ya kuma fa

ɗ

a cikin

ɗ

aga murya.

Ai bata san lokacin da ta shige cikin gi

dan da gudu ba tsabar tsoron da take ciki.

Juyowa ya yi ya na fuskantar saurayin "Kai kuma na dawo gare ka, waye ya baka izinin shigo mun cikin gida, kuma waye kai?"

"Amsar tambayarka ta farko yarka zaka tambaya ba ni ba. Amsa ta biyu kuwa ni

ɗ

an ƙwa

lisa ne wanda mata suke nacin so, ko ban zo ba za'a je mun Jafsee guy kenan."

Ya ƙarasa zancen ya na shu'umin murmushi tare da gyara kwalar rigarsa.

'Inda ranka ka sha kallo.' Malam isah ya fa

ɗ

a a ransa yana ƙarewa yaron kallo.

Ko ka

ɗ

an shigarsa b

ata yi kama da ta ƴaƴan hausawa ba, shi kallon arne-arne ma yake yiwa yaron duba da irin sunansa da ya fa

ɗ

a, ga wani uban gashi da ya tara duk ya mummur

ɗ

e tamkar hauka sabon kamu, sanye yake da wani

ɗ

amammen wando irin wanda gayu suke kira (crazy).

"Ba

shakka yaro ka cika marar ta ido, amma dai ba a nan unguwar kake ba ko?"

"Ka fa

ɗ

i dai-dai mai farin gemu, ban da albarkacin kyakkyawar 'yarka wato Babyna ban ga abinda zai shigo da ni wannan ƙazamar unguwar ba. Na san ba zaka rasa sanin Unguwar Dagarma

ba, (rigima ga mai ƙare ki idan a tafe kake to mu a hanya muka kwana, Dagarmawa kowa ya tara ya samu.) Kirarinmu kenan." Ya fa

ɗ

a.

"Yaro fice mun daga gida, daga yau bana son sake ganinka a nan gidan, ita ma wace ta janyo kan zan yi maganinta ne.

Mala

m Isah ya fa

ɗ

a cikin zafin rai.

"Kwantar da hankali Malam yanzu kuwa zan bar maka kangon da kake kira a matsayin gida." A yanda ya yi maganar sai ka rantse

ɗ

an gidan wani hamshaƙi ne nan kuwa gidan da ya kira da kango ya fi nasu tunda har ya samu albark

acin ginin bulo, na su kuwa yun

ɓ

u ne.

Ficewa ya yi daga gidan.

Shi kuwa Malam isa ya shige cikin gidan tuni ya manta da wani baƙo da ya bari a waje tsabar

ɓ

acin rai.

"Indo! Indo!! Ke Indo!!!

Umma ce ta fito da sauri har tana tuntu

ɓ

e saboda jin

wannan gigitaccen kiran.

"Ga ni Malam lafiya?"

"Tambayata ma kike? Ki na aikin me Maheerah ta janyo mun wannan lalataccen zuwa gidana? da ƙimata da komai tana neman zubar mun da mutunci." Ya fa

ɗ

a ya na huci.

"Yi haƙuri Malam wallahi ban san lokac

in da ta fice daga gidan nan ba." Ta fa

ɗ

a cikin tsoro.

Haƙiƙa ta firgita ainun da ganin yanayin mijin nata.

"Tana ina Maheerar?" Ya fa

ɗ

a da ƙarfi.

Maheerah dake

ɗ

akinta kwance cikin tsoro jiyo Muryar Mahaifin nata yana nemanta ya ƙara sakawa ta ts

inke. Takurewa ta yi guri

ɗ

aya tana jiran sakamako.

Ita bata san da dawowarsa ba da ko giyar wake ta sha ba zata kira Ja'afar zuwa gida ba, saboda gudun hakan.

Ɗ

akin ya shigo ba ko sallama hannunsa riƙe da wata tsabgegiyar carbi da yake ja.

"Ke wa

ya baki izinin gayyato mun wannan mara tarbiyyar zuwa gidana?"

Shiru ta yi kamar ruwa ya ci ta.

"Waye shi a gare ki?" Cikin rawar murya da tsoro ta ce "Saurayina ne Baba." Ta san abunda kalmar zata iya janyo mata amma ta kasa jure rashin furtata, ta

yanke a ranta in dai akan Ja'afar ne sai dai a kashe ta ba za ta sauya ra'ayi ba."

"Lallai wuyanki ya isa yanka, ni kike gayawa haka bayan kinsan na hanaki kula kowa in ba Irfan ba?"

"Baba bana son Irfan, wallahi na tsane shi ni Ja'afar kawai nake so

."

"Waye Ja'afar kuma?" Ya tambaya cikin takaici da mamaki, shi a tunaninsa 'yarsa ba zata ta

ɓ

a samun saurayi kamar Irfan ba wanda ya ha

ɗ

a komai na nagarta ga kuma ku

ɗ

i, duk da cewa shi ba sune a gabansa ba kyawawan halayensa yake so.

"Shi ne ya zo y

anzu." Ta mayar mai.

Ai ji ya yi kamar ta daka masa wuƙa a kahon zuci, nan da nan zuciyarsa ta rufe ya yi kanta gadan-gadan carbin dake hannunsa ya shiga tsula mata iya ƙarfinsa sai ihu take. Can carbin ya tsinke ganin bai gama fanshe haushinsa ba ya ra

rumo wani ice dake rabe a bangon

ɗ

akin ta waje ya yi kanta ba ji ba gani........

Ku biya biya ku

ɗ

inku ta wannan account

ɗ

in

Account name: Ruƙayya Ibrahim lawal

Account number: 0431343346

Gt bank

Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan numbe

r:08109634202

Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.

Ga mutanenmu na Niger masu buƙatar saye zaku biya 400F ta wannan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903

K

o da ku

ɗ

inka....

..

*WATA UNGUWA*

*(Labarin game da wata hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*

*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*

*YAR GANTALI*

*RIKIC

IN MASOYA*

*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*

*HALITTAR ALLAH CE*



*AND NOW*

*WATA UNGUWA*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

4 june 2021

FREE P 4

BABI NA HUƊU

Cikin hanzari Maryam ta yi

kan Hanifa girgizata ta shiga yi tana fa

ɗ

ar "Yaya Hanee don Allah ki tashi." Shiru ta ji kuma ba alamun motsi a jikin Hanee, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinta.

Kamar wacce aka tsikara da tsinke ta zabura ta yi kan Sofi domin ta yanke ƙauna da samun

rayuwar Hanee.

Nan ma hawa jijjiga jikin Sofin ta yi. "Yaya Sofi tashi, ki tashi."

Nan ma ta ji shiru "wayyo Allah na na shiga uku ni Maryam kenan mutuwar kasko kuka yi?"

Ihu ta ratsa sai ga hawaye sun

ɓ

alle a idonta tamkar famfo, da tasan tashin

hankalin da zata zo ta riska kenan da bata tafi aiken ba ko meye zai faru da ita kuwa.

"Sadik je ka kira Baba ƙarami(ƙanin Babansu)" da gudu yaron ya fice Basma na take masa baya domin su ma sun firgita ainun, duk da cewa su yaya Mankas sau tari suna

ɗ

e

bo rigima har a raunata su, amma dai ba a ta

ɓ

a yi agabansu ba sai dai su ga rauni.

Bayan fitar su Maryam ta kasa jure kallon 'yan'uwan nata da jikinsu ke zubar da jini, Ba ma kamar Hanee da aka fasawa gefen ciki. Ta rasa abinda zata yi, hankalinta ya ka

i linta gurin tashi, ficewa ta yi daga gidan cikin hanzari ta shiga gidan Malam Hadi don ta kirawo shi, gani take duk bata lokaci ne ta tsaya jiran zuwan Baba ƙarami.

Can bayan minti biyar suka shigo gidan tare da Malam Hadi, da ya ga abinda ke faruwa

ya shiga damuwa Sosai ganin yanda 'yan'uwan biyu suka raunata junansu sakamakon biyewa son zuciya 'yan magana sun yi gaskiya da suka ce 'zuciya mugun nama.'

Sai da ya gama tantance yanayin da suke ciki ya

ɗ

ago tare da cewa "Ki kwantar da hankalinki Mar

yama, na fi tunanin doguwar suma suka yi ba dai mutuwa ba, bari na taro abun hawa sai ki nemo wa

ɗ

anda zasu kama mana a fitar da su."

Rufe bakinsa ke da wuya sai ga Baba ƙarami ya shigo har yana ha

ɗ

awa da gudu, sallama bata ko samu ba, tsabar

ɗ

imaucewa d

a ya yi domin shi a yanda Sadik ya gaya mishi wai sun kashe kansu ne.

Nan dai malam Hadi ya kwantar masa da hankali, sannan suka fitar da 'yanmatan zuwa titi, domin su ma Napep bata shigowa layinsu.

Ba iya layinsu ba, kusan duk rabin layukan unguwar

hakane saboda matsatsinsu.

Asibiti gwamnati suka nufa da su domin a basu taimakon gaggawa.

Duk wannan bidirin da ake Baba bai Sani ba don kuwa bai dawo ba sai ƙarfe shida na yamma a nan ya tarar ba kowa, har ƙananun yaran sun fice zuwa maƙwafta domin

neman abinda za su sakawa cikinsu.

Tabarma ya

ɗ

auko ya Shimfi

ɗ

a a tsakar gidan yana cika da batsewa, ba haushin matar gidan yake ji ba, yaran gidan ne suka hassala shi, to gidan Ubanwa suka je suka bar masa ƙofar gida a bu

ɗ

e.

"Amma yaran nan kwata-kwa

ta basu da hankali, dubi yanda suka bar mun ƙofar gida a bu

ɗ

e Salon a shigo a mana sata." Ya fa

ɗ

a cikin bambami

Idan ka ji yanda ya haƙiƙice sai ka rantse da Allah yana da wani abun arziƙi da za a

ɗ

auka a gidan, alhali ko Ɓeran Masallaci ya shafa masa

lafiya akan tsiya.

A can asibiti abun Duniya ya ishi Baba ƙarami, jini ake nema za'a yiwa Hanifa ƙari domin ita ce ta yi asarar jini mai yawa, gashi kuma banda

ɗ

ari ukun da ke aljihunsa bai da ko ficika tare da shi.

Ƙ

arin damuwarsa shi ne tun bayan d

a suka samu ganin likita Malam Hadi ya fice kuma ya gaya masa ba gida ya nufa ba.

Babban abun takaicin daga Inna har Baba ba wanda ke da ko cover bare waya sukutum.

Yanzu kenan taya zan sanar da su Halin da ake ciki?

Can wata dabara ta fa

ɗ

o masa a t

ake ya aiwatar da ita ba tare da ya musawa ƙwaƙwalwarsa data haska masa tunanin ba.

A can gida kuwa matar Baba ƙarami ce ta shigo gidan Malam Mudi bayan sallar Magriba, zaune ta same shi yana ta bambami shi ka

ɗ

ai kamar hauka sabon kamu.

"Yaran nan su

n gama raina ni fa. Bari su dawo yau zasu ci na jaki a gidan nan, ni da kaina zan sadaukar da sauran jarumtata don na nuna masu shayi ruwa ne."

Assalamu alaikum." Ladi(matar Baba ƙarami) ta shigo gidan da sallamarta.

Amsa sallamar ya yi yana Fa

ɗ

ar "w

aye ne? shigo" ya fada kasancewar ba wutar lantarki hakan yasa ya gagara tuna sababbiyar fuskarta da yi sabo da ita.

"Sannu da hutawa Malam Mudi."

"Miƙewa ya yi yana Fa

ɗ

ar yawwa sannu." Sannan ya fara matsowa inda take da fitilar hannu riƙe a hannuns

a yana haskawa a ƙoƙarinsa na son gano mai shigowar.

Murmushi ta yi ta girgiza kai "Malam Mudi Ladi ce, ina matar gidan? Ina tafe da muhimmin saƙo."

Ɗ

an murmushi ya yi "A'ah to,toh yanzu na

ɗ

au haske ashe kece, wallahi bata dawo daga ƙauye ba tun saf

......."

Kafin ya dasawa kalaminsa aya suka jiyo sallamarta daga waje alamun tana shigowa ne.

Hakan ya yi dai-dai da lokacin da aka dawo da wutar lantarki a take haske ya mamaye tsakar gidan.

"Shi ke nan ma, Hutaroro waken gizo ya ƙi yaya. Ga ta nan

ma ta ƙaraso."

Shigowa ta yi bayan sun gama gaisawa da Ladi, Ladi ta ce "Dama abinda ke tafe da ni, Baba ƙarami ne ya ce in yi hanzari in zo in gaya maku cewa Hanifa da Safiya suna Asibiti sakamakon raunata junansu da suka yi garin fa

ɗ

a."

"Inna dake

ƙoƙarin zama ta yi Zumbur tare da juyowa wa

ɗ

anne Hanifa da Safiyan ba dai nawa ba?"

"Luba kenan! Muna da wasu yaran ne masu irin sunan a zuri'armu?"

Juyawa ta yi ga Baba wanda shi ko akwalar rigarsa, hankalinsa kwance kamar tsumma a randa ta ce "Sai

ka yi ƙoƙari ka ƙarasa asibitin nan ta baya, suna can tun yamma har Maryam da shi kansa gabobinsu sun yi sanyi."

Tana gama isar da saƙon ta fice.

Inna ce ta shigar da kayan hannunta cikin

ɗ

aki sannan ta fito "Mudi tashi mu je ba mu ga ta Zama ba."

"Ke dai ki je in abun ya dame ki, Amma ni kam ina nan ina zaman jiransu, dole sai sun

ɗ

an

ɗ

ana ku

ɗ

arsu 'yan iska kawai, ni za su zubarwa jini a cikin gida, wato su ga sabbin 'yan daba ko?"

Cike da jin takaicin kalamansa ta shura takalminta ta bar gidan

bako sallama, a ranta tana fa

ɗ

ar "Bansan sai yaushe ne Mudi zai gyara halayyarsa ba, shi kullum ba ya furta kalmar alkhairi ga ƴaƴansa sai ta lalaci, bai san hakan ke ƙara lalata su ba."

A taƙaice dai kwanansu uku a Asibiti ba tare da Mudi ya leƙa su b

a, a wuni na hu

ɗ

un ne da yamma Lis Inna ta tattaro ƴaƴanta suka gudo daga Asibitin sakamakon ba su da ku

ɗ

in da za su siye magani, shi ne likitoci suka bar su nan a yashe, gashi har lokacin Mudi bai leƙa su ba acewarsa "Duk tsuntsun da ya ja ruwa ai shi ruw

a kan doka."

Cike da jin haushin wulaƙancin da aka masu ta yo gida da su.

Alhamdulillah! Jikin Sofi ya yi kyau, kasancewar ita

ɗ

inki ne aka mata a gaban Goshi, an bar ta ne ta huta dama.

Hanifa ce bata da ƙarfi kwata-kwata,

ɗ

inki aka mata a gefen

cikin ga shi sai da aka mata ƙarin jini, saboda ta zubar da shi da yawa.

Ko a Napep hanyarsu ta dawowa ma sai hararen juna suke daga nesa-nesa, Inna bata kula ba,Maryam ce ka

ɗ

ai ta ankara da hakan.

Lokacin da suka ƙaraso gidan Baba ba ya nan don h

aka hankali a kwance Inna da Maryam suka shigar da su

ɗ

akinsu tare da kwantar da su.

Hanifa ko dogon motsi ba ta yi saboda barazanar fitowa waje da kayan cikinta ke yi. Ji take kamar

ɗ

inkin zai farke...

Tana nan kwance ta ji ringin

ɗ

in wayarta da tun

i ta manta a wace duniyar ta bar ta. Haƙiƙa in lokacin rasa abinka bai zo ba ko a kasuwa ka ajiye

ba mai

ɗ

auka, domin da ba don haka ba tana da yaƙinin ba zata riski wayar ba, adai yanda

ɓ

eraye masu ƙafa suke yawo a gidan inda suka ga dama.

"Maryam don Al

lah miƙo mun wayar can." Ta fa

ɗ

a.

Maryam da har ta kai ƙofa ta juyo ciki da sauri, takawa ta yi zuwa inda wayar take cikin wata tsohuwar jaka. Ciro ta ta yi ta miƙawa yayar sannan ta fice.

A dai-dai lokacin ne kira ya shigo wayar a karo na biyu "Waye

zai takura mun ina fama da kain......"

Sauran maganar ce ta maƙale a can ƙasan maƙoshinta don ganin mai kiran HAJIYATA shi ne sunan dake yawo a saman fuskar wayar, sarai ta gane mai kiran Alhajinta ne wato Alhaji Saminu. Ta na son

ɗ

agawa ko don ta sana

r masa da halin da take ciki, sai dai kuma ba hali tunda ga Sofi kwance kusa da ita.

Tana nan tana tunani har wayar ta tsinke, kira ya kuma shigowa a karo na uku.

Sai da ta aikawa Sofi saƙon harara kafin ta daga wayar cikin Sarrafa harshe "Assalamu a

laikum Hajiyata."

Daga jin haka Alhaji Saminu ya ƙyalƙyale da dariya domin ya tabbatar tana

ɓ

oyon kurwa ne don kar wani ya gano halin da take ciki.

Hakan tasa ya ce "A'ah! Yau Babyn tsolaya ake ji? Ba wannan ba ina kika shiga ne na yi ta kiran ki kusan

kwana hu

ɗ

u kenan ina kiran ki bakya amsawa?"

"Uhmm! Ki bari Hajiyata na shiga dawa ne yin wata farauta, sai dai tafiyar bata yi kyau ba domin saura ka

ɗ

an Kurar ta kai ni ƙasa, amma dai yanzu haka ina kwance a gida ina jinyar raunukan jikina."

Da yak

e shi ma Alhajin

ɗ

an bariki ne kai tsaye ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login