Showing 12001 words to 15000 words out of 64639 words
/>
batar da kin tsaftace gidan kafin na dawo." Ya na gama fa
ɗ
a ya sa kai ya wuce abunsa.
Ita kuwa tsabar jin haushi ko Addu'ar Allah ya tsare ba ta masa ba.
Juyawa ta yi zuwa
ɗ
aki tana fa
ɗ
ar "Bari Hanee ko Sofi su zo sai in saka su share mun don ni ba z
an iya da kayan duƙe-duƙe ba, mutum da ƙuruciyarsa ana neman tsofar da shi ƙarfi da yaji."
Ko da ta shige
ɗ
akin guri ta nema kan gado tana shaƙar barcinta, haka ta bar ƙofar gidan bu
ɗ
e.
Can bayan rabin awa Salma ta farka tana kukan yunwa ga kuma tsam
in jiki. Sai dai me duk ihun kukan da take Biba bata ko sani ba domin tuni ta kai birnin sin a duniyar barcinta, Allah ya jarabceta da masifaffen barci kamar kasa.
Salma da ta ga haka, sai ta hau jijjiga ta tana fa
ɗ
ar "Mama tashi, yunwa nake ji, Mama." Ga
nin cewa duk abin nan da take yi mamanta bata yi ko gezau ba bare ta tashi, kawai sai ta sauko daga gadon tana neman abinda zata ci.
Nan ta shiga duddubawa tana bu
ɗ
e duk wani kwano ko kofin da ta gani bata ga komai ba, ga shi Madafar a rufe take ba za t
a iya bu
ɗ
ewa ba.
Kawai sai ta koma
ɗ
akin Maman nata inda ta ga ku
ɗ
i
ɗ
azu, ta saka hannu ta dau Hamsin ta fice daga gidan.
Kai tsaye ta wuce Gidan Baba Tsoho mai ice, da yake a gidan akwai yan haya biyu da ya saka a
ɓ
angaren da ba kowa, to
ɗ
aya daga c
ikin yan hayar ne ke siyar da abun kwalam na yara don haka ta nufi can don ta agaji cikinta da ke ƙugin neman agaji.
Gidan shiru kamar ba kowa, haka yarinyar ta shige, har ta sa kai zata wuce can ƙuryar don siyen abun da ya kawo ta.
Baba Tsoho dake
zaune kofar
ɓ
angarensa(dama shi ne fara isa) ya saka baki ya kira ta "ke yarinya zo."
Ba musu ta tako zuwa inda yake "Ga ni Baba."
"Me kike so?" Ya tambaya yana wani shu'umin murmushi irin na tsoffin Banza.
"Awara ko carbin Malam zan siyo." Ta ba
shi amsa cikin rashin maida hankali don kuwa hankalinta na can kan abinda zata siya.
"Tun safe haka, waya aiko ki?"
"Ba kowa yunwa kawai nake ji."
Wani murmushin ya yi mai ma'anoni ya ce "Zo mu shiga cikin gidana na baki abinci ki ci sai kin ƙoshi
kuma ina da carbin Malam
ɗ
in ma duk zan ha
ɗ
a miki."
Ko da jin haka yarinya ta hau tsalle-tsallen murna, ba musu ta bi bayansa. Suna shiga ya garƙame ƙofar gidan, da yake dama shi ka
ɗ
ai ke rayuwa a gidan don ba shi da mata ta rasu, ƴaƴansa kuwa duk sun
yi aure wasu har sun fara aurar da ƴaƴansu.
Biba tana can tana barcin asara ba ita ta farka sai wuraren 10:40am ko da ta farka bata ga Salma kwance kusa da ita ba, hakan bai dame ta ba, ta fito tsakar gidan a nan ta tarar da Salma raku
ɓ
e can gefe tana k
uka. A madadin ta matsa ta saurari matsalar 'yarta kawai sai ta ce "Ke wane irin iskanci ne kike yiwa mutane kuka tun da safe, kamar wacce aka daka?."
Ɗ
agowa yarinyar ta yi hawaye duk ya wanke mata fuska har wani ya bushe, ta tako zuwa gun mahaifiyarta
tana wata kalar tafiya a wawware.
"Ke Salma! Yau wane irin iskanci ne ya same ki, ji wata tafiyar iskanci, maza ki gyara ko na
ɓ
a
ɓɓ
alaki yasin."
Kuka kawai yarinyar ke yi ta ce "Zafi nake ji idan ina tafiya."
Kallon yarinyar ta yi a sheƙe "Je ki n
emi guri ki zauna, ni bari na fara wani abu, sauri na ke zan je gidan yaya Hanne."
Yarinyar ta kalle ta ta ce "Mama kinsan wannan mutumin mai itace, shi ne ya......"
"Ke ni don Allah je ki nemi guri ki zauna kin cika ni da surutu, Haba! Yarinya ƙaram
a sai iya gulma." Ta fa
ɗ
a cikin tsawa.
Sum-sum Salma ta ja ƙafafunta ta je
ɗ
aki ta raku
ɓ
e, ita ka
ɗ
ai tasan abunda take ji.
Daga waje Biba ce ke ta sababben surutun nata ita ka
ɗ
ai tamkar hauka sabon kamu.
"Wai yau ya aka yi ne mutanena ba su zo ba
kamar dai jiya? Gaskiya bari na nemo su ina da yunwar ganinsu musamman Hanee da nake so ta sammun tsamiyar dake jakarta."
Miƙewa ta yi ta ja yalolon hijabinta duk ya cukurkude ta sanya, yau ma daga ita sai
ɗ
aurin ƙirji take zaune tunda mai hali baya fas
a halinsa.
Kai tsaye gidansu Sofi ta wuce, a nan ta samu labarin abunda ya faru a bakin yaran gidan da suke shaida mata suna asibiti ga abinda ya faru.
Girgiza kai kawai ta yi ta fito tana ƙwaƙular hanci "Gaskiya abu bai yi da
ɗ
i ba, duk da na so a ga
bana komai ya faru na
ɗ
ebe ƙeyar ido."
Har ta
ɗ
au hanya kamar zata koma gidanta sai kuma ta miƙi hanya zuwa gidan yayarta tana Fa
ɗ
ar "Bari na ga ko da ragowar
ɗ
umame na sake ci ko na samu ƙarfin aiki, don ruwan tea ni basa riƙe ni."
"Assalamu alaikum
" ta shiga gidan da sallamarta "wa Alaikumus Salam ƙaraso." Yayar ta fa
ɗ
a tana daga ciki kan tela..
"A'ah! Yayata ana nan ana tara mana ku
ɗ
in ne? Kinsan ranar bikin Hafsarmu akwai shagali ba, don ko Abba baya so sai mun yi bidi'ar nan."
Dariya yayar
ta yi ta ce "Tsiyata dake kenan, mayyar bidi'a ce har kin manta waye Abbanmu, kuma kike yi da shi."
"Manta da zancen ko waye shi yaya, kawai in kina da
ɗ
umame ba ni inci dama shi ya kawo ni." Ta fa
ɗ
a tana nufar madafa.
Da kanta ta zubo dai-dai wand
a ya ishe ta ta zauna tana ci sai zuba surutu take, bayan ta yi naƙ ta miƙe ta nufi hanyar gidanta.
A can gidan nata kuwa bayan fitarta Zubairu ya shiga gidan da Sallamarsa "Biba kina ina? Zo ki ji yau fa ta samu." Shiru ya ji alamun ba kowa, har ya juy
a zai fita ya jiyo sautin shessheƙar kuka a
ɗ
aki da sauri ya nufi can don ganin miye.
Salma ya tarar ta Ha
ɗ
e kai da gwuiwa, nan ya tsaya yana kallonta a ransa yana wassafa abubuwa. "Gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce, idan ta zama budurwa ba karamar kyak
kyawa za'a yi ba, don har tafi uwarta kyau, sosai za'a huta anan."
Har ya juya da nufin fita zuciyarsa ta kwa
ɓ
e shi, wani
ɓ
angare na zuciyarsa ya ce "Zubairu kada ka
ɓ
ata damarka, tunda uwar bata nan ka rage zafinka anan duk da ba abun kirkin da zaka ts
inta anan
ɗ
in."
Sosai ya gamsu da shawarar zuciyarsa don haka ya matsa kusa "Salma me ya same ki ne?." Ya fa
ɗ
a tare da
ɗ
aukar yarinyar ya
ɗ
ora ta kan cinyarsa a daidai lokacin ne kuma Biba ta Kunno Kai a cikin
ɗ
akin.
Tsayawa ta yi cak tare da zaro
ido domin abunda idonta ya gane mata a yau ya razanata matuƙa....
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*YAR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA (GAJEREN LABARI*
*HALITTAR ALLAH CE*
Ku biya biya ku
ɗ
inku ta wannan account
ɗ
in
Account name: Ruƙayya Ibrahim lawal
Account number: 0431343346
Gt bank
Ko kuma ku turo katin waya (Mtn) wannan number:08109634202
Sai kuma ka yi screenshot ka tura shaidar biya ta wannan number: 08109634202.
Ga mutanenmu na Niger masu buƙat
ar saye zaku biya 400F ta wannan number :+2250748153903 ku kuma tura shaidar biya ta jikin wannan number +2250748153903
Ko da ku
ɗ
inka....
..
Ummu inteesar ce
*WATA UNGUWA*
*(Labarin game da wat
a hargitsattsiyar unguwa mai cike da abubuwan al'ajabi)*
*ALƘALAMIN RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
11 June 2021
Free page 7
BABI NA BAKWAI
Jibgarta yake ba ji
ba gani, ko gani baya yi sosai tsabar
ɓ
acin ran da yake jiki. Tuni ya makance da hango duk wani aibu dake tattare da dukkan da yake mata, sai buga mata icen yake duk inda ya samu.
Umma da ta ga abun bana ƙare ba ne, kuma idan har ta zuba ido komai zai
iya faruwa ga tilon yarta mace, hakan ya sa ta ƙarfafi zuciyarta tare da shiga
ɗ
akin cikin hanzari.
"Don Allah Malam ka dakata haka, idan rai ya
ɓ
aci bai kamata hankali ya gushe ba, zaka iya raunata ta fa."
"Ki bari in mata dukkan kawo wuƙa Indo, ta ya
nda zamu raba raini, kinga gobe in har na
ɗ
ora mata doka ba za ta tsallaka ba." Ya fa
ɗ
a yana huci ka
ɗ
an ka
ɗ
an.
Icen dake Hannunsa Umma ta riƙe ta ce "Don girman Allah ka yi haƙuri Malam, idan kace zaka daka ta yaran zamani to lallai sai dai ka illata su
ka janyo wa kanka abun fa
ɗ
a."
Kar
ɓ
e icen ta yi daga hannunsa, har ya juya zai tafi ya dawo daga baya, ya fuskanci Maheerah ya ce "Ki ji ni da kyau, ni ne dai mahaifinki damar za
ɓ
a miki miji tana hannuna, don haka na ba ki nan da sati biyu ki yankewa ka
nki hukunci, in har ba za ki auri Irfan ba to ki samo madadinsa a tarbiyya, in ba haka ba zan aura miki duk wanda na ga dama."
Yana gama fa
ɗ
a ya fice cike da damuwa ya yi waje, sai da ya zo soron gidan ya tuna da ya bar baƙonsa a waje, don haka ya yi sa
urin ƙarasawa gunsa.
Daga cikin gida kuwa Malam na fita Umma ta kalli Maheerah "kin dai ga abinda kika jawa kanki ko? Ga irinta nan, a karon banza da wofi kin jawa kanki jibga. Ina gaya miki ki ajiye wannan girman kan ki yi biyayya gare mu ko kya samu t
sira a gobe ƙiyama."
Yunƙurawa ta yi daƙyar ta tashi, don duk jikinta ya yi tsami ta ce "Umma ba wai ina bijirewa zancenku ba ne, a cikin zuciyata ne bana son kowa sai Ja'afar a yanda nake ji zan iya shan guba idan na rasa shi."
"La'ilaha illallah! H
ar abun na ki ya kai da mummunan ƙuduri haka? Lallai kin yi nisa bakya jin kira, Allah ya shirye ki."
Da gama fa
ɗ
a ta juya zuwa
ɗ
akinta tana mamakin wannan al'amari na Mahee, ko dai yaron nan asiri ya mata ne?
Bayan kamar mintuna arba'in Maheerah na
kwance tana jinyar jikinta da ya mata nauyi, ji take kamar wasu ga
ɓ
o
ɓ
in jikin nata sun karye. Ta tsunduma kogin tunanin abun sonta ko me Baba ya masa? Mummunan fa
ɗ
uwar gaba ce ta ziyarce ta, hankalinta ya kasa kwanciya.
Wani
ɓ
angare na zuciyarta ya shaw
arce ta da ta kira shi, domin tabbas ba lafiya, shirun ya yi yawa.
Hannu ta miƙa ta janyo wayarta da ke nesa da ita ka
ɗ
an, ta hau dubawa. Kamar dai yanda ta yi tsammani bai kira ba, bai turo saƙo ba.
Jikinta ne ya yi sanyi laƙwas, kamar wacce aka zar
ewa lakka ta
ɗ
aga wayar tare da kiransa, sai da ta kira sau biyar bai daga ba.
Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, domin tun da take Ja'afar bai ta
ɓ
a ƙin daga wayarta ba sai yau, babu shakka ko ba a gaya mata ba tasan fushi ya yi.
Tana nan cikin tashi
n hankali da tunanin mafita sai ga saƙonsa ya shigo wayar.
Da sauri ta fara karantawa kamar haka: "ke Malama, kada ki takura mun a daidai lokacin da nake tsakiyar shauƙin soyayya da Sahibata. Tun da har Abbanki ya kore ni shi ke nan, na yi masa alƙawar
in ba zai kuma gani na ba a gidansa indai ni
ɗ
an halal ne."
Zo ka ga tashin hankali gun Mahee bayan da ta gama karanta saƙonsa, duk da cewa a lokacin sanyi ne sai da ta ji wani gumi-gumi ya fara tsattsafowa a duk wata kafar gashin jikinta.
Da sauri t
a fara rubuta masa marta ni, cikin rubutunta wanda karantawa
ɗ
aya zaka masa kasan ba ƙwararre ya rubuta ba. Ga abunda take cewa "Don girman Allah Ja'afar kada ka azabtar da zuciyata da rashin ganinka ko jin muryarka ba zan jura ba. Yanzu dai ka gaya mun ya
kake so ayi, ina son ganinka."
Turawa ta yi tare da komawa ta lafe luf kan katifar cikin tsananin damuwa, abun ya ha
ɗ
e mata biyu ga zafin ciwon jiki gana zuciya.
A can
ɓ
angaren Ja'afar yana ganin saƙon martanin da ta mayar masa ya bushe da dariya t
are da kallon abokinsa Hanif ya ce "Ka gani ba Mutumina, dama na gaya ma ni nasan irin bishiyar ƙaunar dana dasa a zuciyar yarinyar nan, ina sane kuma na mata dashe mai ƙwari da zai yi wuyar tumbukewa."
Hanif yayı dariya irin tasu ta zagerun matasa tare
da buga Kafa
ɗ
ar Abokin nasa ya ce "Gaskiya Abokina baka da dama, kasan kan tsiya, yanzu dama duk wannan abun ba tsakani da Allah kake son Mahee ba?"
Dariya Ja'afar ya bushe da ita sai da ya yi mai isarsa, sannan ya zuƙi sigarin dake hannunsa ya fesar d
a hayaƙin kafin ya ce "Ina sane na tsara duk wannan, dama duk wannan shirin na yi ne saboda zuwan irin wannan ranar, ba ita yar Malamai ba? Yanzu zaka ga me zai faru don dole ta kawo mun kanta har nan, daga nan ne wasan zai soma."
"Ka bi a hankali dai,
Allah sarki Mahee, wallahi tausayi take ba ni, baiwar Allah duk ta
ɗ
auki son duniya ta
ɗ
aura akanka, ashe kai shirin yaudararta kake." Hanif ya fa
ɗ
a cikin tausayawa.
Shi kuwa Ja'afar Banda dariya ba abinda yake, sai can kamar bayan mintuna talatin ya tu
ra mata amsar saƙonta, a lokacin ne kuma suka yi sallama da Hanif ya wuce unguwarsu.
Har zuwa wannan lokacin bata yi barci ba tana ta jiran amsarsa, taya ma zata iya kwanciya a cikin wannan yanayin? Fita ta yi waje ta yo arwala ta zo ta tada sallar isha
.
Tana idarwa ne kuma ta jiyo ƙarar shigowar saƙo a wayar don haka bata ko bi takan addu'a ba, ta
ɗ
auko wayar tana karanta saƙon a fili.
'Tabbas ba zaki ƙara ganina ba Mahee, in har kina son ki ganni sai dai ki zo da kanki har inda nake, in ba haka b
a kuma ki ƙaddara a ranki ruhinmu sun yi bankwana da juna, idanuwanmu sun ƙauracewa ganin juna. Address DAGARMA gida mai lamba 60.'
"Innalillahi wa innailaihir raji'un!" Ta furta a hankali muryarta na rawa. Ta maimaita karanta saƙon ya kai sau uku, kafi
n kowanne
ɗ
aya daga cikin kalmomin dake rubuce a saƙon ya zauna a kwanyarta daram.
Tashi tsaye ta yi ta shiga zirga-zirga a tsakiyar
ɗ
akin nata ita ka
ɗ
ai "Tabbas Babana ya
ɓ
allo mun ruwan da ba zan iya tarbe su ba." Ta furta a hankali.
Sai kai-komo t
ake tana surutu ita ka
ɗ
ai kamar zararriya.
"Ba zan iya aikata wannan aikin ba Jafsee, sai dai ka yi haƙuri. Ni ce wai zan bar gidanmu ba da sanin mahaifana ba har na je ga saurayi? Abun da kamar wuya."
Numfashi ta sauke sannan ta ce "Tabbas ina sonka
yanda ba zan iya misaltawa ba, zan iya komai a kanka amma wannan kuma ina fargabar aikatawa."
Can dai ta ji ƙafafunta sun kasa jure azabar zirga-zirga da take da su, ga shi dama duk Baba ya doddoke mata su.
Haka ta nufi shimfi
ɗ
arta ko karka
ɗ
ewa bata
yi ba ta kwanta, tana saƙa da warwarar abubuwa a zuciyarta.
Washegari Maheerah ta kasa tashi, har wajajen tara da rabi tana nan kwance jikinta ya yi tsami sosai, wasu sassan jikinta ma sun kumbura da alama ta ji ciwo a gun.
Umma ce ta leƙo
ɗ
akin tan
a fa
ɗ
ar "A'ah! Mahee yau kin yi nauyin barci ne? Na zata ma tuni kin wuce makaranta da kika leƙa kika ga ina barci."
Sai a lokacin ta bu
ɗ
e idonta da suka fara kumbura ta zubawa Umma su. Da ƙyar kamar mai ciwon baki ta bu
ɗ
i baki ta ce "Umma na kasa tashi
yau, jikina duk yayi tsami, har yanzu barci ne a idona."
Cikin tausayawa Umman ta ce "Ayyah! Sannu ai dole ki kasa tashi irin wannan dukan da kika sha, don ma Allah ya taƙaita. Barin
ɗ
ebo ruwan zafi na gargasa miki jikin ko za ki ji da
ɗ
i."
Bata ce k
omaiba ta lumsashe kumburarrun idanunta.
Can bayan wasu mintuna Umma ta shigo da 'yar roba da ruwan zafi a ciki hannunta riƙe da ƙaramin ƙyalle. Nan ta shiga aikin gasawa Mahee jikin.
Bayan ta gama ta kawo mata abincin kari har
ɗ
akin ta ci.
Ai kuw
a Mahee ta ji da
ɗ
in gashin ba ka
ɗ
an ba. Domin jikinta ya rage tsamin da yake wasu guraren da suka kumbura sun sace.
Can zuwa yamma abun duniya ya taru ya yiwa Maheerah yawa, ta kasa jure