Showing 1 words to 3000 words out of 65015 words

Chapter 1 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

16

HIRA DA MATATTU .....1 (True life story)

Mun yi shekaru ba mu hadu ba sai rannan mu ka hadu a babban kotun koli ta garinmu. Da kyar na gane ta dan ni ban yi zaton zanga Sharifa a wannan qasar ba kuma a wannan waje ba, a iya sanina ma Sharifa bata

zama a kasar nan, tana zama a qasar Turai ne.

Mace mai kyau, fara tas 'yar gayun gaske, dirarriya , ga aji. Da farko da ta yi min magana ban yarda ita ba ce, sai da ta tabbatar min da sunanta sannan na yarda. Saboda gaba daya ta juye ta lalace, a 100%

babu 80% din kamanninta, da martabarta.

"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da Ya busa min numfashi kuma Ya busawa Sharifa. Kawata me yake faruwa" Tambayar da na yi mata kenan. Na riqe ta ina karkarwa.

A tunanina zata fashe da kuka sannan ta bani laba

ri saboda duk wanda ya santa a baya ya ganta yanzu ya san bala'in da ta shiga ba dan kadan ba ne. Amma sai na ganta a daskare cikin murya mai cike da jarumta.

Amsar da ta bani ita ta fi gigita ni, ta ce "Hmmm Sharifa daga sama ta fado, ita kadai ce

tal a duniyar da bata da iyaye, bata da dangi, sai Ubangijinta kuma Shi kadai Ya isar mata."

Sai na kalle ta kallo na tuhuma, babu tantama ta hadu da cutar tabin hankali, saboda na san iyayenta, da 'yan uwanta da suke ciki daya sun kai su ashirin da dor

iya, da sauran danginta na wajen uwa da na wajen Uba bila'adadin.

Kafin in sake yin wata magana wani dattijo ya leqo ya ce "Sharifa Nasir ki shigo"

Ko sallama bata da niyyar yi min, ta zabura za ta shiga. Sai na damqi hannunta na ce "zan iya raka ki

ciki?"

Dan idan ban shiga na ga abinda zata yi ba zan iya kasa bacci saboda tunani. Sannan ko zan taimake ta yadda take juya Hausar nan wacce bana fahimta, na san bata da niyyar bani labarinta.

Bata bani amsa ba sai ta jawo hannuna da sauri muka af

ka cikin ofis din. Wani tsohon alqali ne wanda daga ganinsa babu wasa ya dube mu. Ya tambaya "tare ku ke ne?"

Gabana ya fadi dan kada ace in fita. Ta bashi amsa " Eh ranka Ya dade tare muke."

Nan da nan na duqa na kwashi gaisuwa sannan na sami kuje

ra a gefe na zauna cike da ladabi da fargaba.

Ta zauna a kujerar gaban teburinsa bayan sun gaisa ya dinga miqa mata takardu yana yi mata bayanin yadda zata cike tana cikewa.

Abinda na fahimta a ciki Sharifa tana karar wani alqalin da bai yi mata ad

alci a sharia ba.

Turqashi alkali gaba daya ta maka a kotun qoli. .....

Ya tura ta wasu ofisoshi a sama inda zaa saka hannu sannan kuma zaa yi photocopy, sannan ya umarce ta da ta dawo da su.

Mu ka fito sai dai kash nima wanda na zo gani ya iso

kuma sauri yake zai fita, ya sanar da ni a waya har yana min fada akan na bata masa lokaci.

Na dube ta na ce "fada min abinda yake faruwa a takaice.."

Tafiya take kawai tana sauri da alama bata da lokacina.

Sai na sake zabura na ce "bani number

wayarki ta Nigeria zan kira ki."

Amsar da ta bani ita ce " Kin taba ganin matacce ya amsa waya?"

Na ji kaina ya sara zuciyata ta harba na waiwaye da sauri na kalli ofishin da muka fito yanzu, wannan karon qofar ofishin ma rufe da kwado babu alamar

an bude shi a yau, alhali yanzu muka fito.

Na juyo a gigice zan yi mata tambaya sai na ga wayam ta bace, na daina ganinta. Sama ta hau? A qasa ta nutse? oho. ...

"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" Na fada a bayyane yayin da na dafe kirjin da zuciya

r take bugawa kamar zata ballo waje saboda fargaba. Zazzabi ya rufe ni, jikina zafi qau.

Na cika da tsoro hade da da-na-sa-nin meye ma ya kawo ni cikin kotun nan a yau?

Mutumin da na zo gani ne yake kirana a waya. Qarar wayar ma ta firgita ni, na d

auka fatale ce ta dawo. .....

To be continue...

Madalla da ALQALAMIN JUT

HIRA DA MATATTU ..2 (TRUE STORY)

Na tsaya cak ina makerketa na ji a raina kawai in fasa zuwa ganin alqalin da na zo gani. Yayana ne ya yi min hanyar ganinsa tun ba yau mu

ke fama ba sai yau Allah Ya yi.

Muryar yayana na ji yana daka min tsawa akan in zo mu je, mutumin na ta jiranmu ya karaso tun dazu. Shiyasa ma ya ce fara yin gaba saboda in fara koro bayanai kafin ya iso.

Na bi shi a baya ina rawar dari, ina shiga

ofishin ko zama ban yi ba na hango Sharifa ta gifta da sauri, sai na zabura na daka tsall, na sake daga labule na leqa ta.

Wallahi babu tantama ita ce kuma wannan ofishin da muka fito dazu ta shi ta shiga.

Wannan karon ba firgita kadai na yi ba z

atuwa ce. Yayana ya kai kololuwar jin haushina kamar ya mare ni ya rufe ni da fada yayin da dattijon alkali ma ya qule.

Kara zan shigar muka zo neman shawara a wajensa akan shariar pre order kaya da na lunkuba kudaden mutane na turawa wata amma babu

kudi babu kaya.

Amma wallahi gaba daya da aka tambaye ni lissafin da yadda aka yi tun da farko na manta komai.

Ba su sallame ni ba na fice da sauri na nufi ofishin da Sharifah ta shiga. A bude yake ban yi wata-wata ba na fada ciki, dan na ga mutane

na ta shiga su na fitowa.

Abin mamaki ba wancan dattijon ba ne wani matsayi ne a zaune akan kujerar kusa da shi.

Na daga hannuna mai karkarwa ina nuna kujerarar, na tambaya, na ce " me waccan kujerar shima ya mutu ko?"

Aka hau kallon-kallo a ts

akanina da su. Yayin da suka fara jeho min tambayoyi me nake cewa? Me make so? Wa nake nema?

Na hau kame-kame suka gaji suka koro ni waje, ina fita na ci karo da yayana ya dire kwandon masifa da zagi akaina. Yana cewa na kunyata shi gobe ma rana ce kad

a in sake cewa ina neman taimakonsa idan na dauko rigima.

Mu ka dunguma hanyar get ni dai ban tanka masa ba, amma kowa ya ganni ya ga kwantacciya.

"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ya ji na ambata a gigice na nufi bakin get da gudu ina kiran Shar

ifa, Sharifah. Ita na hango ta tare adaidaita zata Shiga. Ta waiwayo ta dube ni sannan ta shiga.

Yayana ya zabura ya damqo ni ya na cewa "ke yaya haka ne? Wacece Sharifah kuma?"

Na ce masa ya rabu da ni adaidaita zan hau. Ya ce ai da mota muka zo.

Kwalla kiranta nake amma bata waiwayo ba ta shige adaidaita ta tafi ta bar ni. Yayana ya Amince na yi gamo shigowata cikin kotu, daman ga bishiyoyin tsamiya nan.

Ya saka ni a mota yana min tofi. Yayin da ya dauki waya ya kira mahaifiyarmu yana tamba

ya daman Samha tana da aljanu? Mama ta ce ko kadan ban taba yi ba. Ya ce gamu nan zuwa gidan.

Mu ka tafi, a daidai danja(traffic light) muka tsaya sai ga Sharifah a cikin adaidaita. Na zabura na kwalla sunanta "Sharifah! Sharifah!!" har sai uku ta kal

le ni ta dauke kai.

Sai yayana ya fara karatu a bayyane har da gangarawa gefen hanya dan kada in bude qofar mota in fita.

Babu makawa ya tabbatar na yi gamo kuma sunan aljanar Sharifa.

A haka muka isa gida jikina da zazzabi ina karkarwa. Ni ba ab

in in ce na ga fatalwa ba a sake tabbatarwa da haukata.

Ana ta min addua har sai da zazzabin ya sauka na sami bacci. Abin mamaki sai na yi mafarkin Sharifa da alqalinta su na cewa in zo in tattara ledoji da takardu in share wajen zaa yi baqi.

Na fa

rka da wani mugun tsoro gami da gigita. Allah Ya sa da salati na farka ba da ihu ba.

Nan dai yan gidan suka sake taruwa a kaina ana ta min tofi, yawu kala-kala da me warin goro da na miyar kuka, har da na tabar wiwi dan muna da 'yan shaye-shaye wai su

ma agajin addu'a suka kawo min.

Allah mai iko, na fita daga gida lafiya na dawo a zauce.

Ban samu sun bar ni na sarara ba sai da daddare na sami damar kiran kawayenmu daban-daban da muka yi karatu a Jami'a tare, kowacce ta tabbatar min sun jima ba

xu ji doriyar Sharifa ba amma tabbas da ta mutu da sun ji. Wata daga ciki kuma ta ce ai jiya ma sun yi waya Sharifah na raye. Na ce ta bani lambar ta turo min na kira a kashe. Kuma layin ba mai register ba ne.

Innalilahi wa inna ilaihi rajuun toh magan

ar wa zan kama? Babbar matsalar ma dai ace dare yayi kowa yayi bacci ya bar ni, fatalwa ta bayyana.

Mijina baya gari dan haka na fada masa a waya, zan kwana a gida saboda yanayin ciwon. Dan an sanar da shi tunda rana. Nan da nan yayi Amanna .

A tsa

kiyar kannena na kwana bayan na hana su bacci, dakyar dai na samu bacci ya kwashe ni.

Washe gari aka hana ni fita in je gidan su Sharifa in gani, dan ana tunanin bana cikin hayyacina.

Aka karbe wayata dan sun gaji da wayar da nake yi ina ta kiran s

unan Sharifa! sharifa.

Na dauko hotunan bikina ina kallonta, ita ta yi min babbar qawa, ga ta nan a hoto ita da kanwarta kamarsu daya kuwa mai suna Shariqah.

Daga cewa zan zagaya bandaki sai na fice ban tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan su Shari

fah Nasir. Na gamu da wasu yara sai na tambaya ko an yi mutuwa a gidan nan?

Yaro daya ya zabura ya ce min " eh an dade da yi Sharifah ce ta rasu."

Sai daya yaron ya zabura ya ce "ba Sharifah ba ce ta rasu Shariqa ce."

Nan fa musu ya kaure a tsak

aninsu. Yayin da na dora hannu aka kamar mai shirin kurma ihu dakyar na daure.

Fitowa Bello Nasir ce daga cikin gidan ta sa na ji sanyi wato kaninsu Sharifah. Na tare shi da sauri na ce " Bello wai Sharifah ta rasu?"

Ya ce "Au Aunty Samha ba ki sani

ba ne? Ai an yi shekara da rasuwar Shariqah ba Sharifah ba dai."

Na zabura na ce " a a kai ma ka yi kuskure Sharifah ce ta rasu ba Sharuqa ba."

Sai na ga yayi min wani irin kallo na ai sai ki yi, ya kada kai da sauri ya Shiga mota ya tafi ya bar ni.



Ina tsaye a kofar gidan na kasa Shiga kasancewar na tabbatar uwa da ubansu sun dade da rasuwa kuma Shariqa tana gidan aurenta.

Abin mamaki sai na ga suffar Sharifah a jikin windo tana leqowa. Mun hada ido wallahi ita ce . Sai na tabbatar ni kadai

nake ganinta ba sa ganinta .

To be continue

Madalla da ALQALAMIN JUT

HIRA DA MATATTU....3 ( TRUE STORY)

Neman shawara:

Jut mai masoya, na godewa Allah. Na gode muku masu qaunar rubutana. Na yi niyyar yin dan short story sai na ga labarin zai t

akure gaba daya ko rabin sakon da zan isar ba zai iso ba. Amma ban yi niyyar sakin sabon littafi ba anan kusa .

Shin za ku siya in warware alqalamina in sakar muku labari part 123 ? Ko kawai in takure shi a kara page daya a wuce wajen.

Na san Mutum

guda ma zai iya siyewa ya ce a sake shi kawai kowa ma ya karanta

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

0023843938

Unity bank

Jamila umar tanko



Qafata daya a cikin get daya a waje ina zare ido dan ganina ya fara dasashewa, Tabbas Sharifah nake gani da daur

in qirji babu riga a jikinta,

yayin da dukka jikinta tun daga fuskar har kirjinta mamaye yake da wasu baqaqen kuraje.

Matar da a iya sanina bata da qurji ko daya a jikinta, tas-tas take fatarta mai kyau sai an wanke hannu za ka taba.

Kanta babu dan

kwali tattauran gashin kanta ne ya miqe carko-carko, alhali Sharifah gashinta mai laushi ne ya sauko har kafadata.

Wannan karon tsoro ne ya hana ni gudu dan na fita daga cikin hayyacina .

Jikina rawa yake ta yi kawai. Na kasa yin addu'a, na kasa taf

iya. Na tabbatar na shiga duniyar siradin tafiya lahira ni ma. Dan ko na rayu tabbas ba zan moruba dan na zauce.

Muryar Shartifah na ji a bayana kuma a cikin kunnena, kai tsaye har hucin numfashin na ji " matsa zan wuce ."

Na daka tsalle na fada cik

in farfajiyar gidan gami da kwalla qara na ce " Innalilahi, na shiga uku.'

Na waiwaya da sauri na dube ta, tabbas ita din ce dai ta shigo. Wannan karon sanye take da kayan makaranta. Yanzu kuma da suffar yara a bayyana 'yar budurwar da bata wuce sheka

ru goma sha shida ba."

Kamar yadda na kula a baya Sharifah tana yi min magana ba tare da ta hada ido da ni ba, yanzu ma haka. Sannan maganar a takaice ne, kuma kalaman ba irin na mutane ba ne sak.

Na dafe qirji ina rawar dari bayan na yi nesa da ita

. Muryata na rawa na tambaya "Sharifah me na yi miki? Dan Allah ki yafe min idan na yi miki laifi, mun dade ba mu hadu ba. Ban san ma ba kya raye ba."

Ta dube ni qasa-qasa ta ce " ba Sharifa ba ce, Sunana Hamidah ni 'yarta ce."

Na waiwaya da sauri w

undon da nake ganin Sharifah, babu ita ta b'ace.

Na tambaya a gigice "Ina mamarki?"

Ta yi dum kadan, yayin da idanuwanta suka yi jajawur cike da kwalla ta ce "ta ras "

Hankali ya sake tashi na na fada a gigice "Wacece ta rasu?"

Ta amsa " Mama

ta tun waccan shekarar."

"Wacece mamarki Sharifah ko Shariqah?" Wannan karon kallona ta yi da jajayen idanuwa mai dauke da hawaye masu kwaranya. Sai kawai na ji wani abu ya tsargo min yarrrrr tun saga qafata har cikin kaina .

Ta nufi cikin gida ba

tare da ta sake kula ni ba .

Na zabura na sake tambaya "yanzu wacece a cikin gida?"

Ta na tafe ta amsa min "Mamata ce."

Kamar daga sama na jiyo muryar Sharifa ta ce " "Hamidah! Hamidah!! Hamidah!!! ki saka sakata a gidan nan, ki cewa baquwar na

n ta shigo."

Hamidah ta juyo da zunmar saka sakata a get sai na na zabura na ce " Sakata kuma? Ba da ni ba, na fice da gudu." Sai a lokacin na shaqi iska mai sanyi don na fito daga cikin ukuba.

Hamidah ta tsura min ido tana kallo ban san tunanin da

take yi ba.

Can ta ce "Mamata ta ce ki shigo."

Na zare ido na ce " in shiga ina? Wacece mamar ta ki?Bayan kin ce ta mutu."

Amsar da ta bani ita ta sake tabbatar min wadannan ba rayayyu ba ne , ta ce da ni "Mamana ta fada min akwai rayuwa bayan mu

tuwa ai."

Na zazzare ido yayin da na fara nemowa kaina hanyar tsira da alama da Sharifah nake magana, ta canja suffa ta koma yarinya 'yar makaranta. Wato rayuwa take yi bayan mutuwa kuma tare da ni take so ta yi.

Na falfala da gudu, saura kiris adai

daita ya buge ni.

Zai min fada ya ga ina shidewa, ban yi wata-wata ba na afka ciki na ce "kai ni unguwar 'yankaba zan biya ka."

Tambaya yake "Hajiya lafiya?" Dan ya ga ina ta waiwaye.

Cikin ikon Allah mu na fara tafiya ba mu yi nisa da gidan ba sa

i ga Yara guda biyar sanye da kayan makaranta masu irin fuskar Sharifa na gani a jere sun shigo cikin layin mata biyu maza uku.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Laifin me na yi miki Shafifah? Har kamannin yara kike komawa mata da maza?" Na fada a firgic

e yayin da na fashe da kuka.

Yara na kallona ina kallonsu har suka shude. Babu wanda a cikinsu ba irin fuskar Sharifah gare shi ba, har dariyarsu da maganar dan su na ta surutu.

Mai adaidaita ya ga na miqe na kwanta yayin da ya fara leqe ta mudubi y

ana fadin "Hajiya kada ki mace min a adaidaita gaskiya. Ki kirawo wasu 'yan uwanki su kwatanta gidanku in kaiki na ga kin kasa magana.

Na ce "mu je na san in da zan je lafiyata kalau. Na yi gamo ne."

"Gamo kuma? Da aljanu?" Ya tambaya cikin gatsali.

Yayin da ya kwashe da dariya. Ya ci gaba da waiwayena ta mudubi.

Daman na san na zautu ni da hankali kuma sai gyaran Allah .

Mun shiga layi ya fi sau uku na manta gidan Nanah Ahmad saboda gigicewa, dakyar na gane.

Dubu guda na bashi zai tsaya c

iniki na ce na bar masa sadaka. Ya na godiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login