Showing 15001 words to 18000 words out of 65015 words

Chapter 6 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

22

na hannu yana ta zufa.

Aliyu ya ce " daman har da wani alfanun da fatalwa take da shi a musulumci. Kai ma ka yarda kenan akwai fatalwar kenan?"

Anas ya ce "kai da baka yarda akwai ta ba, ai ta nemi ka sh

iga ayi maka iso, amma ka qi shiga."

Aliyu ya ja bakinsa yayi shiru yayin da ya sake kidimewa ya shiga zurzurfan tunani.

Tabbas yau ba zasu gushe ba sai sun sami manyan Malamai sun fayyace musu menene fatalwa? Shin akwai fatalwa a musulumci ko bab

u? Daga ina ake samun fatalwa? Menene dalilin bayyanar Fatalwa?

Amma shi abinda ya gani yau ya bashi tsoro, ya bashi mamaki, ya jefa shi a dimuwa.

Wannan abin kunya ne ma su koma gida a cikin wannan yanayin na gigita, su Samha su gansu a haka. Da g

askiyarsu Mama ashe, su sun san abinda su ka gani.

"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Su ke ta fada su dukka a lokaci guda.

Madallah da ALQALAMIN JUT

To be continue.....

HIRA DA MATATTU .....9

NA

JAMILA UMAR TANKO

JUT

Gargadi:

Baa

yarda wata/wani ya/ta karanta wannan littafi a you tube channel din ta/sa ba. Ba tare da izinin Marubuciya ba.

YOU TUBE: Jamila umar tanko channel

FACE BOOK: Jamila umar tanko

WATPAD: Jamila umar tanko

Zaa iya sauraron littafin kai tsaye a

kan you tube channel dina.

Sun isa gidan Malam Babba sun jima a karamin falo su na jiransa amma basu ganshi ba saboda yana ganawa da manyan baqi.

Anas ya na ta gynagyadi saboda ya gaji, ga yunwa ya dawo daga tafiya sai dai duk motsin da aka

yi sai ya zabura ya bude ido.

Aliyu ya buga tagumi da shi mamaki ya ishe shi yau ba kadan ba akan abinda ya gani, daman da labari aka bashi ba zai taba yarda ba.

A karshe dai Malam babba ya aiko a basu hakuri su tafi gobe sa dawo da yamma bayan la'as

ar.

Anas ya dage sai dan aike ta koma wajen Malam ya ce ko daidai da minti daya ne ya basu, lallai-lallai su na son ganinsa dan matsalar babba ce.

Aliyu ya hana dan aiken zuwa ya fadawa Malam dan bai kamata babban malami irin wannan a takura masa ba

.

Aliyu ya bawa Anas a hakuri akan su tafi gida kawai. Anas dai bai so ba dan har ya zabi kujerar da zai kwana, yana tsoron tafiya gidansa dare yayi ga matarsa da shegen tsoro ya rikita kowa.

Anas ya ce a sauke shi a gidansa, motarsa kuwa da ya baro

a gidansu da safe kaninsa Idris zai kawo masa.

Da ya zo fita daga motar ya ce "toh Aliyu a fafi juna, dan daren yau sai yadda Allah Ya yi. Please kada dadin hira ya dauke ka, ka fayyacewa Samha yadda aka yi dan sai ta raina ka ta raina ni. Ka ja bakink

a ka yi shiru yadda suke ganinmu jarumai a tafi a haka. Kaga Irin zagin da nake yi wa Samha akan Sharifar nan, yanzu a dawo ana cewa gashi-gashi, raini ne zai shiga.

Dariya Aliyu yake ta tuntsirawa ba qaqqautawa, har sai da Anas ya fara jin haushinsa. Y

a yi tsaki ya shige gida.

Aliyu ya wuce gidan su Samha dare ya fara yi domin karfe goma sha daya har ta gota. Ya na hawa barandar falon ya hango Yunus yayi day-day a kwance yana munshari ga katuwar muciya a gefensa, idan aka kara gaba kadan Bashar ne da

tabarya a kusa da shi. Mama akan doguwar kujera, Samira da Sultana su ma a gefe guda akan katifa karama. Samha na zaune tana gyagyadi ta dora kai a gefen kujerar Mama. Ashe dai yau gaba daya a falon zaa kwana kuma ba zaa kashe fitila ba. Su yunus masu gad

in fatalwa ne har da makamai.

Samha na ganin Aliyu ta taso cimak a rude ta fito.

Ta na tambaya "yaya? Gidan su Sharifar kuka je?"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "No! No!! Mun dai dan fita ne."

Samha ta ji abin banbarakwai. Tayaya zasu fita tare da

Anas, su je ina? Alhali ba abokan juna ba ne infact bayan gaisuwa Yaya Anas baya sakarwa kowa fuska.

Ta ga dai Aliyu baya son maganar ta dauko jakarta suka tafi.

Aliyu ya tambaya " yaya na ga kowa ya baje a falo har da masu makamai?"

Samha ta yi

ajiyar zuciya ta ce " Hmmm duk abin Mama ne fa. Wai in Sharifa ta zo ta same ta a cikin iyalanta ko da kashe ta zata yi. Shine su kuma mahaukatan suka dauko makamai wai jiranta suke ta zo din."

Aliyu ya gyada kai ya ce "Hmmmm!"

A zuciyarsa ya na ce

wa "yaro bai san wuta ba sai ya taka. Sharifah ta wuce duk yadda suke tunani."

Samha tana ta karantar Aliyu kamar akwai abinda yake tunani musamman da suka isa gida komai aka taba sai ya razana. Irin yanayin da take ciki.

Ta kura masa ido ta na kallo

can ta ce " Malam ka fada min gaskiya, kun je gida su Sharifah kuma kun yi artabu da fatalwa yau. Wallahi baka bi na bashin rantsuwa na ga alamar haka a tare da kai."

Aliyu dai karatun qur'ani kawai yake yi yana gyaran murya yana daga mata hannu akan t

a yi shiru.

Sai ya sakankance sai ta buga tebur, sai ya zabura. Ya fusata ya ce "dalla Malama! wai meye haka ne ina karatu ki na zaburar da n?"

Ta ce " na dauka ka daina magana ne. Amma ada baka da irin wannan halin na tsoro kawai ka fada min gaskiy

a. Kun ga Sharifah ko?"

Aliyu ya ga babu sarki sai Allah Ya kwashe labari kaf ya bata amma ya ja mata kunne kada ta fadawa kowa dan yaya Anas baya so a fada.

Samha ta sulale ta zauna ta dora hannu aka ta fasa kuka. Ta na cewa "mun ga takanmu."

Ali

yu cewa yake "babu komai mun san ta inda zamu bullo mata ai."

Haka dai suka kwanta ana rigayen-rigayen shigewa lungun bango, Aliyu ya ce ita ce karama ta kwanta daga bakin gado. Su ka dinga tofa addu'oi a kowacce busurwa ta dakin kuma aka qi kashe fitil

a.

Bacci barawo yana surarsu kadan- kadan sai su zabura su bude ido har dai ya dauke su gaba daya.

Anas kuwa ranar matarsa Binta ta ga ta kanta. Gashi ya kasa bata labari. Ita bata ma san komai akan maganar fatalwa ba kawai ta tsaya tana kallon iko

n Allah. Sai addu'oin nan yake yana tottofawa, yana datse wanduna da kofofi. Alwalla kuwa yayi babu adadi.

Ita da yaransu kuwa basu isa su yi motsi ba, sai ya zabura ya rufe su da fada.

A haka dai aka kwana rabi barci rabi firgita. Ai kuwa babu wanda

bai ga Sharifah a mafarki ba.

Samha ta tashi babu lafiya sosai zazzabi mai zafi. Haka Mama ma da ciwon kai mai tsanani ta tashi dan haka Anas da Aliyu suka yi shawarar a kai su asibiti su sami 'bed rest' tension ne kawai na ganin fatalwa.

Aka kaisu

babban asibiti suka ga kwararren likita, bayan ya auna su ya basu magunguna. Sai su Anas suka nemi da a basu gado su kwanta dan su na bukatar hutu daga Mama har Samhar.

Aka kama dakin na musamman na kudi mai dauke da gadaje biyu kacal wato (Aminity)

aka kwantar da su.

Samira ce mai zaman jinya bayan an shaqe musu fridge da kan Loka cike da kayan dadi kala-kala irin su kaji, fresh milk, yoghurt, gasassun kifi, kayan marmari, lemo (juice) kala-kala aka ce su yi ta ci kawai, su na kwanciya su na hutaw

a.

Allah Ya sani Mama ta fi kowa jjn dadin wannan karramcin dan za ta huta da rigimar Yunus da Bashar.

A lokacin da agogo ya buga karfe goma biyu na dare kowa yayi barci hatta malaman jinya da masu jinya da ma masu zaman jinya sun kwanta sai daidaik

u ne ke hira daga kwance.

Mama ta yi barci ta farka ta bude ido ta ji alamar tana son ta kara dira akan kajin nan ta yi mu cin koshi dan Anas da Aliyu sun bata dama ta ci duk abinda take so, ta sha magani ta yi barci wannan shine bed rest.

Samira ma

i zaman jinya tuni ta baje a kasa kan tabarma da bargo tana tana munshari kasancewar ta gaji a makaranta.

Haka Samha barci take haiqan domin ita ciwon gaske take yi har jiri ne daukar idan ta miqe tsaye

komai ma ta kasa ci.

A haske suke tar, ga Ac

na firrfitasu, gadon Mama ne a bakin windo na Samha ne a lungu. Kowa ya san windon asibiti masu gilashi layi-layi kowa na ganin kowa. Kai na cikin daki kana ganin masu wucewa su ma su na kallonka.

Mama ce ta ga giftawar wata mace mai fararen kaya. Da m

atar ta wuce sai ta sake dawowa, tana leqen Mama da ke zaune akan gado da cinyar kaza a hannu.

Mama ta ji gabanta ya yanke ya fadi amma tana fatan ba abinda take tunani ba ne yake shirin faruwa.

Ta tabbatar matar nan da ta yi gaba ta dawo baya da gas

ke lekenta take yi, sai mama ta yi sauri ta kwanta can da aka jima Mama ta taso zaune a hankali ta sake ganin matar tana daddage tana leko ta, sai da suka yi haka har sau uku.

Sannan ta ji an murna qofa an yi sallama an shigo.

"Innalilahi wa inna ilaih

i rajuun Sharifah Nasir ce hannunta janye da wani ya yaro mai kama da ita dan kimanin shekaru shida shima da farar jallabiyya.

Ga haske muraran haka Mama da Sharifah suke hada ido. Cinyar kazar dake hannun Mama ta fadi yayin da itama ta yi baya yim ta

fadi akan filo, kamar an zare mata laka.

Babu inda yake motsi a jikinta sai idanuwanta da suke farfari tana addu'a gara ta mutu da Sharifah ta zo wajenta.

Wannan karon Sharifa a gurguwa ta zo mata tana tafe tana dingishi ta karaso jikin gadon Mama.

Ta tsaya tana ta magana ita kadai babu amsa.

Ta ce "Subhanallah Mama babu lafiya ne? Ai ban sani ba. Allah Ya baki lafiya."

Ta juya ta dubi Samha wacce ke cikin barci haiqan, sai ta karasa gare ta, ta zauna a gefen gado sannan ta kamo hannun Samha

ta riqe.

Mama magana take yi wacce baa iya jinta tana fadin kada ki taba min 'yata ni dai ki taba ni.

Sharifah ta kira sunan Samha a hankali yayin da Samha ta amsa a cikin magagin barci.Ta na dan bude ido su na kallon juna.

Sharifah ta ce "sannu

Samha ashe baki da lafiya haka amma ban ban sani ba? Sai dai rashin lafiyar ta dadi ce, ina yi miki murna kin sami cikin wata biyu. Da ma ni ce ke. Ki yi min kara ki sakawa baby suna Sharqah zan yi farin ciki."

Cikin barci da magagi Samha ta bata amsa t

a ce "bani da ciki ki yi min addu'a in samu."

Sharifah ta ce "kin riga kin samu kuma za ki haihu lafiya insha Allah."

Samha ta ce "me kike yi a duniya?"

Sharifah ta ce " lokaci nake jira ba dan ina jin dadinta ba."

Samha ta ce "tunda kika mutu

ai lokacinki yayi."

Sharifah " tabbas idan rayuwa ta tsananta za ka ga ka fara sha'awar na cukin kabari, ka ji dama ka zama shi. Zan tafi sai anjima. Ina yi miki murna."

Samha ta ce "na gode sai anjima."

Wannan baya jin magana ya dinga Jan yatsu

n kafar Mama da na samira. Mama na sanqame ta daskare ita bata mutu ba ita bata rayu ba, bata cikin hayyacinta amma tana kallonsu ta na jin su kuma.

Sai ka ji Sharifah ta ce "Hamid ka bari."

Ta ja hannunsa suka fita.

Samha ta yi firgit ta bude

ido ta dubi inda ta ga Sharifah, wayam babu kowa. Sai a lokacin kuzari ya dawowa Mama ta diro daga kan gado gaba daya suka haye gadon Samha su na ihu.

Mama ce ta take kan Samira a garin gudu, sannan Samirah ta tashi a gigice itama ta dane kan gado suk

a rungume juna.

Samha ta fada a gigice "mafarkin Sharifah na.yi ta zo ta ce min ina da ciki."

Mama ta ce "ba mafarki ba ne a ido biyu ne, ni na ganta.

Shikenan ta biyo mu asibitin ma."

Suka duba a agogo karfe daya har da wasu mintuna.

Babu ma

ganar kokonto Sharifah ba mutum ba ce. Amma.abinda badu gane ba shine dan me take bibiyar su haka? Kuma muddin ta tabbata Samha na da ciki tabbas Sharifah ta san abinda bil'adama baya gani.

Ma'aikatan jinya suka shigo a guje a gigice, suna tambaya ko la

fiya, aka tambaye su ko sun ga wata mata da yaro ta shigo yanzu. Su ka ce babu kowa ya shigo ba.

Tsarki ya tabbata ga Allah Allah Subhanahu wata'ala maqagin Sharifah.

Samha Aliyu ta dinga kira bai dauka ba aka kira Anas ma bai dauka ba. Mama ta sa

Samira ta fara hada musu kaya bed rest kuma ya kare. Dan su na ganin ko cikin uwarsu suka qaura Shatifah sai ta biyo su. Me yayi saura kuma yanzu.

A zaune suka kwana daga su har ma'aikatan jinya, baccin da baa koma ba kenan.

Samha ta hadu da dimuwa d

a damuwa ga fargaba. In har ta tabbata tana da ciki shin cikin gaske ne ko Sharifah ce ta kunsa mata ajiya.

Sai da asuba su Aliyu suka ga missed calls sai suka kira aka basu mugun labari. Allah-Allah suke gari ya waye su karaso asibiti dan a gigice su

ka ji su.

Su Aliyu na zuwa abinda suka fara yi shine suka nufi wajen karbo result din fitsari da jinin da aka dauka na Samha.

Ma'aikaciyar ta ce likita ne zai yi musu bayani baa, bawa mutum result sai dai a saka a cikin file. Da suka ga hankalin Al

iyu a tsahe kuma ya dage sai an bashi ya duba a dole aka bashi. Tabbas Samha na dauke da juna biyu.

Sai ya sulale ya zauna kawai ya dafe kai. Shin wannan cikin gaske ne ko kuwa fatalwa ce ta shiga cikin zaa haifo ta?

Mama dai ta yanke hukuncin wanna

n cikin ba na gaske ba ne fatalwa ce ta kunsa mata a jiya dan haka a tafi wajen malamai a zubar.

"No! No! Mama ki daina cewa haka babu mai zubar da cikin nan sai ta haife shi ko da fatalwar ne mu muna so. Abinda muka dade muna nema fa." Aliyu ne ya fad

a a lokacin yake buga tebur.

Samha ta zabura ta ce "waye zai haifo fatalwar? Ni? A' a ba da ni ba wallahi."

Anas ya yi shiru ya rasa ma abinda zai ce saboda abin nan ya fara gagarar tunaninsa. Gashi jiya yayi tafiya, Aliyu ma ya je Kaduna basu sami k

omawa wajen Malam Babba ba.

Madalla da ALQALAMIN JUT

To be continue ...

HIRA DA MATATTU......10

NA

JAMILA UMAR TANKO

(JUT )

GARGADI:

* Baa yarda wani/wata su karanta a you tube TV din su ba, ba t

are da izinin marubuciyar ba.

*Baa yarda wani/wata su sayar su karbi kudi ba.

*Baa yarda a tattara pages a mayar dashi PDF ana sharing ba. Yin haka laifi ne babba.

SANARWA:

Ga masu bukatar sauraro an karanta shi a you tube channel dina.

YOUTUBE

CHANNEL:

https://youtube.com/@jamilaumartankochannel1167

HIRA DA MATATTU

Da alama 'bed rest' ya qare, Mama ta ce a koma gida kawai. Da tashin hankalin ganin Sharifah gara gwagwarmaya da 'yan shaye-shaye sau miliyan.

Haka su ka harhada him

ilin kayan dadin nan suka tafi da shi gida ba tare da likita yayi sallama ba, daman can su suka nemi da a basu gadon ba dan ciwon ya tsananta ba. Ashe rabon su Yunus su sha romo ne, dan an yi musu iyaka da kai ziyarar dubiya asibiti.

Anas da Aliyu su

na sauke su a gidan Mama sai suka zarce gidan Malam Babba da sanyin safiyar nan, gara su tare shi kafin ya fita. Su ka kasa suka tsare, Malam ya na gama karantarwa suka matso.

Bayani su ka fara yi masa cikin hikima da wayo, kai tsaye dai basu fada masa

sun ga fatalwa ba amma su ka nemi karin bayani akan: mecece fatalwa a musulumci? Addini ya yarda akwai fatalwa ko kuma ma babu ita sam? Idan babu fatalwa menene sunan abinda mutane suke gani suke danganta shi da sun ga matacce?"

Malam ya fahimci tambayo

yinsu dan haka ya fara bayani, ya fayyace musu daga wuri har wutsiya tare da kawo musu ayoyin alqur'ani da hadisai sahihai akan mamaci da kuma rayuwa bayan mutuwa. Kamar haka:

Malam ya ce "babu wata aya ko Hadisi da yayi magana akan fatalwa, sam babu w

anda ya taba mutuwa kuma ya dawo duniya, wanda ya mutu ya mutu kenan har abada.

Dangane da dawowa mamaci rai bayan ya mutu, an sami hadisi wanda Imam Ahmad ya rawaito ya ce " Manzon Allah S.A.W ya ce ruhi yana dawowa mamaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login