Showing 51001 words to 54000 words out of 65015 words

Chapter 18 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

23

yaran nan kanana

."

Sharifah ta yi dariya ta ce "Ah babu kowa a gidan sun tafi ziyara daga su har Hamidah sai gobe zasu dawo."

Samha ta sake fashewa da kuka ba tare da Sharifah ta tabe dan ta juya baya tana ta salati tana fatan ta cika da imani. Wayarta ta dauk

o ta turawa Aliyu sako ta ce ya yafe ma ta da wuya ya dawo ya same ta da rai.

Bai karanta ba sai da aka dade sannan ya kira a gigice.

Tambayoyi yake ta jero ma ta ama ta kasa amsawa kasancewar Sharifah ta tsura ma ta idanuwa b ata ko qifatawa. W

a ta magana ya fada sai da Samha ta girgiza.

Ya ce "saboda zaman kadaici ne ya sa na je gidan su Sharifah na fada ma ta baki da lafiya, ta zo ta taya ki zama ku wuni tunda Mama ba ta nan yau. Samira kuma in ta tafi sai an ganta dan kada a barki ke

kadai babu dadi.

Sannan kuma akwai wata tambaya da kika yi min akan Sharifah toh bani da amsar na san a cikin magagin bacci kika yi ta. Na tabbatar ba zai wuce labarin da Sharifah take ba ki ne, ba ku gama ba shine abin ya tsaya miki rai. Kika ce mi

n baqin kare ne ya ciji Sharifah sai ta kwanta ciwo. Ni ba na so ki dinga saka abu a rai shiyasa nake so ta zo ta karasa baki labarin baqin karen."

Haushin Aliyu ya rufe ta yayin da suka tsurawa juna ido ita da Sharifah. Duk da ma dai ta san Sharifah

bata jin abinda yake cewa

Samha ta kasa cewa komai. Wato Aliyu ne da hannunsa ya dauko ma ta ajalinta ya kawo ma ta. Ai shikenan zai ga karshen labarin baqin kare kuwa idan zuciyarta ta karasa fashewa, zai zo ya dauki gawa.

Samha ta kashe way

a ba tare da ta iya bashi amsa ba. Ya sake kira sai ta qi amsawa, da ya kira a karo na uku sai Sharifah ta dauka ta amsa

Ta na dauka ta ce " Aliyu ina tare da ita kada ka damu, yau zamu sha labari da kawata. Ka ci gaba da aikinka ga ni ina kular mak

a da ita."

Ya yi godiya ya yi ma ta sallama cikin jin dadi.

"Tashi ki zauna in baki yogot ki sha, na ga ga kaji ma ga fruits. Da yake a gigice na taho ban tsaya na saya miki komai ba amma kada ki damu gobe zan kawo miki kwadon zogale, kin ji q

awata."

Samha ta qi tashi ta zauna, sai da Sharifah ta dame ta da magiya sannan ta tashi ta zauna. Sai ta ji tsoron da take tsananin ji na Sharifah ya ragu, tunda yanzu ta san wanda ya bawa Sharifah labarin tana asibiti da kuma tagwayen da suke cikin

ta.

Tare suke shan kayan marmarin akan gado suke zaune, su na fuskantar juna

Samha ta ga gara ma ta tsaya ta saurari labarin Sharifah akan ta mutu saboda zulumi.

Samha ta kalli Sharifah da gefen ido cikin rashin fara'a ta ce " ki bani labar

inki da na Fanna, Musamman yadda baqin kare ya cije ki."

Sharifah ta yi murmushi ta ce "tabbas na yiwa mijinki alqawari yau zan zame miki radiyo mai jini za ki sha labari kuwa kala-kala, da na nan da na can ."

" Can ina? Samha ta tambaya cikin ra

shin tsoro. Dan abin ya zame ma ta dole ma ta tsaya ta ji.

Sharifah ta ce "duniyar rayayyu da duniyar matattu."

Samha ta gyada kai ta ce " na shirya sauraro. "

Ta na rufe bakinta Nana Anmad da Maryam Alqali ne suka murda kofa suka shigo han

nayensu dauke da fulasan abinci.

Da faraa suka shigo sai kawai aka yi ido hudu da Sharifah da Samha da su.

Su Nana suka yi turus sula ja da baya su na zare idanuwa su kalli Sharifah su juya su kalli Samha.

Nana ta zabura ta ce " A a ba wan

nan dakin muke nema ba."

Sharifah ta ce "Nana nan ne mana ku shigo."

Ta taso da sauri za ta tare su. Wani uban tsalle da wuntsulawa gami da zubar da fulasan hannu su su ka yi sannan su ka fafara da gudu.

Sai Sharifah ta daga da fulasan

daga qasa, Allah Ya sa basu bude abin ciki ya zube ba. Ta bude kofa da sauri ta leqa, babu su babu kamanninsu.

Sharifah ta juyo ta kalli Samha cike da mamaki ta ce "kin san idanuwana ba sa gani sosai, kamar Nana Ahmad da Maryam na gani."

Samha

dan dariya har sai da ta kwanta, ta san abinda suka gani suka gudu.

Samha ta fada a ranta "Su ne mana, amma nima na yi mamakin yadda ta gansu. Ban san wanda ya fada musu ba ma ina asibiti.

Sharifah ba ta damu ba amma tabbas ta gane abinda ya sa

suke gudu. Ta bude fulasan biyu sakwara ce a daya, dayan kuma miyar agushi ce ta sha kaji da kifi.

Samha ta ce a zuba ma ta za ta ci sai Sharifah ta zubo musu tare. Samha har yanzu dariya ce take cin ta, amma sai ta dinga kunshe baki tana yi a ciki-

ciki.

Su na cikin cin abincin, wannan karon a kan kafet suka zauna suna ci.

Kamar daga sama Sharifah ta ce "su Nana Ahmad da Maryam Alqali kenan. Manyan gari Hmmmmm. Na gane su fa tun ba yau ba."

Samha ta na ta kawar da maganar dan bata

so a yi amma Sharifah ta ci gaba da yi.

Ta ce " basu san Sharifah ba ne ganinta kawai suke yi nesa-nesa amma nan gaba za su santa."

Samha shiga gyara magana sai murmushi kawai Sharifah take yi.

Sharifah ta ce "labarinmu mun tsaya a dai

dai in da na ce na amsa kira kotu ta biyu da ya kaini aka ce ana qarata ne akan in dawo masa da yara saboda ina da aure dan haka raino ya saraya a kaina. Ba ni da lauya ni kadai nake zirga-zurga daga wannan kotun zuwa waccan. Dukka dangina wasu 'yan mata n

e guda biyu da muke uba daya su ne suke tare da ni, sauran kowa ya yi shiru har ta da Bello ya koma gefe ya zuba min ido, shi ya fi so in bar masa yaransa kawai ni kuma na ce ba zan taba bari ba.

Cikar dangina da batsewarsu babu wanda ya kira Adam

u ya ce masa bai kyauta ba akan wulaqancin da yake yi min ba, sai ma wasu sababbin informations da zai yaqe ni yake ta samu daga gare su.

Ikon Allah kawai na tsaya ina kallo, na yi ta tunanin laifin da na taba aikatawa dangina na cancanci wannan huku

ncin. Amma sai aka ce min

wadaka da kudi yake yi musu, amma ban taba dauka cewa kudi zai sayi zumunci ba.

Kuma ban taba sanin Adamu mai kudi ba ne dan na ga gidansa bai wadata ba ni ce ma nake yin aikinsa da bai sauke ba. Saboda a bi bayansa dan ya

wulaqanta ni kudi yake ta rabo da kayan abinci da kayan dadi, har da ragunan sallah.

Aka yi min wata irin Shari'a wacce ban gane ba zuwa biyu kacal mu ka yi, aka ji ta bakina sai kawai aka yanke hukunci aka ce an ba ni mako guda kacal in kwashi ya

ra in mayar da su tsakar gidan ubansu.

Lallai kuwa tunda na kima hijabi har qasa, gashi na kode na jejjeme ai dole su yi zaton bagidajiya ce. A take na bude baki a gaban kotu na ce ban yarda da wannan hukuncin ba, kuma ina neman kwafin Shariah zan da

ukaka kara."

Wannan kalma tawa ce ta tabbatar musu da na san abinda nake yi ashe.

Samha ta tafa hannu ta ce da kyau 'yar gidana na jinjina miki."

Sharifah ta yi dariya ta ce "na rantse da ubangijin Musa da Haruna a lokacin na fara jin wan

i qarfi da rashin tsoro. Tabbas na ga mata a kotu su na ta wahala, ga rashin ilimi, ga rashin karfi, ga rashin wayewa kuma su na da gaskiya an danne musu haqqunansu amma basu da lauya basu da cikar kamalar da zasu iya tsawa su yi bayani. Abin tausayi, ya k

amata idan akwai lauyoyi musamman lauyoyi mata da zasu dinga leqawa irin wadannan kotuna su na bibiya su taimakawa irin wadannan matan.

Ina fitowa bakin kotu na hadu da mazigin nan da na fada miki a baya mai suna Idris, ya na murna sun yi galaba aka

ina.

Na ce masa "ka gama murna amma ka sani babu kotun da ta isa ta raba ni da yaran nan. Ka je ka fadawa Adamu ni da shi sharia yanzu muka fara."

Na fada da karfi cikin daga murya sai da kowa na cikin kotun ya waiwayo. Muryata radau har ciki

n kotu kowa yana ji. Bana tsoron kowa a lokacin banqi duniyar ta kife ba."

Samha ta gyara zama ta ce "toh yaya aka yi kuma?"

Sharifah ta ce "na shiga ofishin wani abokina lauya da yake babbar kotu wato high court a fusace na rufe shi da fada na

ce ka na garin nan amma samun lauya daya da zai tsaya min ya gagara. Kai me kake yi da ba za ka tsaya min ba?"

Ya ce "ni lauyan gwamnati ne ba zan iya tsaya miki ba amma ki kwantar da hankalin zan hada ki da wani lauya mai mutunci, malami ne, mai tso

ron Allah shine na tabbatar idan ya ce zai yi zai yi, ba zai taba yarda su siye shi ba."

Na yarda da maganarsa tunda ya ce tabbas shi mai tsoron Allah na san na gama dacewa. Ya kira shi a waya su ka yi magana sanan ya bani lambar wayarsa da addireshi

n ofishinsa wannan lauya shine Inuwa Ahmad. 'Yar uwata ce ma take ta kuka a lokacin, ni kuma na ce wallahi ba zan yi kuka ba, na daina bata lokacina in yi kuka akan mutumin da bai san darajar matar da ya aura da 'yayan cikinsa ba. Wallahi in raina zai sal

wanta a cikin yaqin nan, na yarda akan ina raye ina kallon yaran Shariqah su na wulaqanta.

Dan shi ba irin uban nan da na san zai kula da yaransa ba ne, haka gidansa ba irin gidan da zaa kai yaro ba ne ya rayu, matar da bata kula da na ta yaran ba ma tay

aya zata kula da yaran wata. Wacce ta tsana ma basu zauna lafiya ba.

Ya na yi ne dan ya wulaqanta ni sai dai Allah bai wulaqanta ni babu mahalukin da zai iya wulaqanta ni.

Ki hasko min maganar jifa irin na asiri, bana duba ba na zuwa a d

uba min amma Allah Ya na nuna min komai a mafarki, ka na taba ni zan

ganka. Ko a suffarka ko a suffar wata dabba mai cutarwa amma a ko wanne hali ko da dakyar ne dai ina kubuta, baa samuna na. Ina da nacin addu'a da kuma tsarkakekkiyar zuciya. Ban cuci kow

a ba Allah ba Zai bari a cutar da ni ba .

Masu bani shawara su na bani shawara akan in bazama neman magani a wajen malamai, in tashi tsaye da addu'a akan in yi rinjaye akansa a Shari'a, bayan haka kuma kowa ya dube ni ya san ana jifana da asiri asiri

a jikina

Ba na kuraje amma a lokacin wasu kuraje suka feso min, ciwo kala-kala da kasala da bacin rai.

Samha kin san ni nima na sanki, bin malamai da bokaye ba aikinmu ba ne. Ko da an takura ni na yarda na je to sau daya zan je kuma ba zan ko

ma ba, sai in ga kamar na zubar da gaba daya imanina ne sai na yi sabuwar kalmar shahada.

Abu daya na riqe shine in tashi cikin dare in roqi Ubangijin da Ya busa min numfashi, Ya raya ni, wanda raina ke hannuns

Sa kuma idan na mutu gare Shi zan k

oma. Shi yake da wuta kuma yake da aljanna.

Tunda kuwa na yi imani da haka na watsar da neman taimakon kowa, na daina bacci cikin dare, na dingi tashin dare ina rokonSa, Shine sarkin sardauna.

Nayi imani da Shi, abu na farko sai na daina fa

rgaba, na daina tsoron kowa. Duk wanda ya dogara ga Allah Shi kadai baya tsoron faduwa sai dai nasara a komai. Haka baya neman taimako daga wajen kowa sai Allah dan haka ya wuce wulaqanci. Baya gudun ko wani zai iya cutar da shi. Zai ji kamar duk duniya ya

na daidai da kowa ko da kuwa bashi da ko Sisi ko wani mai karfi. Zai ji a ransa zai iya tunkarar kowanne irin bala'i da ake binsa da shi. Zai ji zuciyar ta washe babu haushin kowa. Baya tsoron talauci ko ya ce wani zai juya masa baya ya hana shi wani abu.

Baya tantama ko kokonto akan abinda ya saka a gaba.

Kawata na ga aya, na ga mu'ujuza da isa irin ta Ubangiji. Da na matso kusa da mahalaccina Allah da Shi nake magana cikin dare ke kya ce ina ganinSa a gabana tabbas Shi Yana kallona idaniyata bata

ganinsa amma ruhins da zuciyata su na tare da shi 100%.

Bayan na yi sallar nafilfili ina yi masa kirari da kyawawan sunayensu tsarkaka guda casa'in da tara, sai in yi tawasali da kyawawan aiyukan da na aikata daga ni sai shi, bayan na tuba kuma na

yiwa masoyi salati SAW sai in yi magana da Ubangiji ke kya ce ina ganinSa, tabbas shi Ya na ganina amma zuciyata tana hasko shi. Buwayi gagara misali.

Na ce "Ya ubangijin kai ka halicce ni, bani da kowa bani da komai sai kai kuma da kai kadai na do

gara, kai ne ka ce mu roqe Ka, za ka amsa mana. Allah ka tsaya min da kanKa kada Ka bar ni da iyawata daidai da kiftawar ido dan ba zan iya ba."

Samha ta ce : Allahu akbar! kawata na ji har tsikar jikina tana tashi. Tabbas ba kowa ya gane wannan sirr

in ba. Dogara ga Allah Shi kadai babbar nasara ce."

Sharifah ta ci gaba da cewa "Allah Ya nuna mu su Shine Allah kuma baYa mantawa da bawanSa a lokacin da bawa Ya tuna da mahalaccinSa, na rantse da Allah Samha mai Shari'ar farkon nan kacokan aka dau

ke shi daga alkalanci ba zai sake alqalanci ba ma a duniya.

Shi kuma dayar kotun da ya ce zai kwace yara shine kika ganni a high court a sanadiyyarsa ne, yakardar da na cike ta kai can sama. Sannan ni da sabon lauyana mu ka fara shirye-shiryen dauk

aka kara.

Nan fa ma su duba sharia suka dinga zaryar zuwa group-group kowa ya zo sai ya ce a bashi kwafin shari'ar Sharifah da Adamu ya gani.

Daga nan ya tabbatar na maka karansa a can sama ne. Nan da nan aka dakatar da ni da lauyana daga

ci gaba da yin Appeal, sai aka hada mu da wata kwanciyar lauya mai kare hakkin mata da kananan yara mai suna Bar.Aisatu.

Ya ce ta shiga tsakiyarmu ta yi mana sulhu akan yaran, an fasa kwace su daga hannuna.

Adamu ya sha takaici ya dinga bacin

rai, sai da aka fi shekara baa gama sulhu ba. Dan an yi zama da yawa basa zuwa kuma ya daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login