Showing 57001 words to 60000 words out of 65015 words

Chapter 20 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

10

matan

ma basu kai watanni ukun ba. Dan bashi da hali ko kadan. Ya zagi iyayenki,ya zage ki, ga cin mutunci, babu abinci, babu Biyan kudin haya, babu kula da yaranki, ke hatta kudin wutar lantarki in baki biya ba sai dai a yanke ba zai biya ba.

Ga Ham

idah nan zan iya rubuto abinda ya taba kashe ma ta tun daga ragon suna zuwa yanzu, ba ta ci dubu darinsa ba. Haba Samha ni kuma wacce irin asararriya ce da zan zauna da mai karancin addini?

Wasu abubuwan ma ba zasu fadu ba saboda alfarmar aure d

a haihuwa. Danginsa su na kirana a ways su na roqo wai in dawo dan Auwal ba zai iya zama da kowa ba sai ni. Saboda ni kadai ce na iya yin zaman shekaru masu yawa da shi. Sun kuwa san wahalar da na sha da shi?"

Samha ta bude baki ta dafa haba ta c

e " wai! wai!! wai!! har abin na sa ya kai haka daman. Gaskiya wannan ba mijin zama ba ne. A haka kyakykywa da shi kamar wani gentle man."

Sharifah ta ce "kyawun dan miciji ne, shiyasa nake so 'yan mata su gane su rabu da kyawun sura, su zabi hal

i, duk namijin da bashi da hali mai kyau kuma addini bai ratsa shi ba toh kada su sake su aure shi, koda yana zubar da naira dan za suyi nadama duniya da lahira.'

Samha ta ce " gaskiya ne Allah Ya zaba miki wanda ya fi alkhairi kawata. Yanzu yaya kuke

ciki da Adamu da maganar yara? Sanda mu ka zo na ga Hamidah tana kuka rannan, ta ce min an sace yaran ne. Ke kuma mu ka jiyo kina magana da Shariqah a daki. Me ya faru ne?."

Sharifah ta kwashe da dariya ta ce "shine ku ka fice da gudu ko? Ai na san kun j

i shine har yanzu su Nana suke ta guduna? Ba su da hankali."

Samha ta ce " toh meye ya faru?"

Sharifah ta ce "da aka fara zaman sulhu sai aka ce in bashi yaran ya gani saboda sun shekara bai gansu ba. Kin ga ai ba zan hana ba tunda an ce sulhu, ga la

uyana ga lauyansa ga barista Aisatu ba zan kawo komai a raina ba ai ko? Kuma an yi Hutun makaranta a lokacin.

Na rantse da Allah mutumin nan dan bashi da ta ido sai ya riqe yaran ya hana su, har sati biyar, ke har ya saka su ma a wata makarantar. Kamar m

u na garin mahaukata inda babu doka. Ya manta a tsakiyar lauyoyi aka yi magana kuma an rubuta komai.

Ya tafi ya sami lauyansa wai ya zo su je wajen Bar. Aisatu a canja magana, saboda shi ya dauka kowa ne a Nigeria ya yake karbar cin hanci. Ai kuwa ta yi

masa fata-fata kuma ta tabbatar masa ya karya doka. Daman kuma lauyansa ya fada masa gaskiya babu in da zai je a goyi da bayansa, akan abin nan da ya yi.

Su Shariqah ne suka shiga damuwa dan ta na zo min akai-akai, ranta a bace dan bata cika yin magana

ba ma idan ta zo amma ina gane yanayinsa. Hamidah ce ma take ta kuka, shine a lokacin ku ka ji ina fadawa Shariqah gaskiya, cewa ta je ta kwanta wannan yakin na masu rai ne."

Tsoro ya kama Samha gami da daurewar kai ta ce "Sharifah na kasa gane abin

da kike fada idan kika ce Shariqah ta zo."

Sharifah ta yi murmushi ta ce "ai na fada muku a baya, ni na gani da idanuwana mamaci yana sanin abinda yake faruwa a duniya."

Samha ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce " kuma ya mutu mutuwar gaske,

amma ake ganinsa?"

Sharifah ta ce "ki dai mu je zuwa za ki ji komai. Ina zamana na ga an dawo da yaran, ban ce komai ba amma na fadawa lauyana duk abinda ya faru. Sai ya riqe Hamid dan yaron nan da nake yawo da shi wanda ya fi kowa sona a cikinsu, nima

na fi shakuwa da shi. Sai ya riqe shi dan ya san abin zai

taba min zuciya. Ya yi karya wai yaron bashi da lafiya, ashe har a makaranta ya saka shi."

Samha ta ce "Adamu fa ya sami matsala, ya rasa yadda zai yi da ke ne yake wannan kame-kamen."

Shar

ifah ta yi dariya ta ce "ya raina mata ne, bai dauki mace a komai ba sai ga shi ya takalo fada da mace ta hana shi bacci. Akwai mata ai kuma akwai mu na mata.

Bayan nan aka dinga zamansulhu amma an kasa cimma matsaya. Bar.Aisatu har tausayi ta bani, tana

ta kokarin yin sulhu amma abu ya ci tura. Ta na da abubuwa da yawa a gabanta, kullum a na layi a ofishinta, ga gidajen radiyo da dama su na yin hira da ita, haka take kashewa ta saurare mu amma mutumin nan ya dinga yi ma ta wasa da hankali.

Bar.Aisa

tu ta dube ni ta yi shiru can ta ce " har misali nake yi da ke, kuma na fadawa mijina labarinki ya yi miki addua. Tunda nake sulhunta cases ban taba haduwa da wacce ta jajurce akan sai ta riqe yaran 'yar uwarta ba sai ke. Saboda idan dan wani abin duniya k

ike yi an zo lokacin da ko ciyar da su ma ya daina, amma baki gaji ba kullum na ki ake ci ma.

Na sha ganin uwa da uba an rabu yana cewa ba zai riqe yaran ba ita ma tana cewa ba za ta riqe ba, sai mun shiga tsakani mun yi musu sulhu sai a raba yaran gida

biyu kowanne a bashi.

Amma ke gashi ba komai kike nema ba, a baki yaran 'yar uwarki ne kawai kike so ki riqe, tabbas na jinjina miki."

Sai ta sirnano da hawa ta yi min addua."

Samha ta langwabe kai ta ce "wallahi abinda nake ta tunan

i kenan a raina, nake cewa ko idan na mutu na bar yara nima anya Samira zata iya irin wannan jajurcewar kuwa ta riqe min yarana? Gaskiya ba kowacce 'yar uwa ba ce za ta yi maka haka bayan ka mutu ba. Allah Ya saka miki da alkhairi Sharifah, kin yi zumunci

ba za ki taba wulaqanta ba kuma ba zaki yin kukan babu ba, har abada da yarda Allah."

Sharifah ta ce "Amin . Allah Ya ara mana tsawon rai da lafiya da abinda lafiya za ta ci. Yara kuma Allah Ya sa masu albarka, Allah Ya raya su su zamanto sadak

atul jariya ga uwarsu da mu ba ki daya.

Bayan wannan tsohon alqalin da mu ka je da ke da na ce miki ya rasu daga baya, daman ai bashi kadai ba ne su ke handling case din ba, akwai wani dattijon arziki amma shi yana da zafin rai sosai.



Ana gobe zamu koma zaman sulhu sai na koma wajensa na sanar ma sa maganar sulhu fa ta gagara. Daman shi bai yarda da maganar wani sulhu ba, ya fi so a daukaka kara a kawo mu su case din gabansu can babbar kotu. Ya ce babu maganar a raba hankalin yara su

yi kwanaki anan su koma can gidan su yi kwanaki baya cikin tsarin raino.

A daren ne na washe gari zamu koma wajen sulhu da tsakar dare ina kwance sai na ga Shariqah a kwance a kusa dani.

Da qasusuwa a cikin bakinta, ta tauna ama ba

ta zubar ba.Ta hada fululluka na kwanciya har guda biyar ta tokare kanta. Kin san duk wanda ya jera fulo da yawa ya kwanta ai kinga ai ba zai iya kwanciya ya yi balance ba, sai dai ace yana zaune ya tukaro kai da su.To a haka na ganta, cikin daki mai duhu-

duhu da haske kadan, ga wundon dakin a bude wanwar.

Ni kuma ina kwance a gefe bakina ya na ta addu'a amma ko yatsana na kasa dagawa.

Ta cikin budadden wudon nan na ga mage ta shigo, ta zo daf da fuskata ta na kokarin ta yagushe ni, a

mma ta kasa ina ta tofa mata suratul Falak, nas, samad, hasbunallahu , da Auzubillahi minal shaidanur rajim.Tayi-tayi ta taba ni ta kasa, sai ta fita ta windo.

Sai ga biri ya shigo shima haka zai taba ni ya kasa, ina ta addu'a, amma fa na sank

are babu inda yake motsi a jikina sai bakina. Shima ya kasa taba ni, ya fita ta windo.

Ya na fita sai kurwata ta dawo jikina. Na miqe zaune da sauri, na dinga tashin Shariqah dakyar ta farka. Na ce ta je ta zubar da qashin da yake bakinki ta, ta

tashi ta je jikin windo ta tofar, na ce ta sake tofarwa da dukka sai ta zubar da su dukka.

Sannan na ce ta zo ta gyara kwanciyarta ta kwanta.Ta zo ta sauke fululluka ta rage saura guda daya, irin yadda kowa yake kwanciya ta kalli gabas da bangar

en dama ta kwanta.

Da gari ya waye na cewa Hamidah da Bello yau sulhu zai zo karshe, Shariqah ta koma ta kwanta lafiya.

Kin ga ban ma san a ranar mai duba shari'a ya je kotun yayi magana ba, a ranar zamu yi zaman sulhu a ofishin Bar.A

isatu muke zama da misalin karfe hudu aka ce, shi kuma da karfe uku ya shiga kotun. Shi kuma ya je da misalin karfe uku, lokacin ya rage saura awa daya mu fara zaman.

Ya na shiga kotun ya sami kujera ya zauna, sai ya ce a bashi file din shariar

Sharifah da Adamu.

Ni da lauyana mu na can mu na ta jiransu a ofishin Bar. Aisatu. Daga baya itama ta karaso sai ta ke fada mana cewar su Adamu fa sun yi mata waya, wai Adamu ya ce azumi yake ba zai samu damar zuwa ba.

Mu na cikin

maganar ta nuna mana itama fa abubuwan gabanta take kashewa ta takura kanka sannan take iya zuwa ta zauna, amma kalli yadda suke wahalar da mu kullum.

Ko bakinta bata rufe ba sai dai kawai mu ka ga Adamu da lauyansa sun shigo a gigice., bayan wayar

da su ka yi su ka ce ba zasu sami damar zuwa ba. Daga dukka alamu mai sharia ne ya fafaro su ya ce lallai su zo a gama sulhun nan a yau, dan shima ya samu ya huta ina ta turo masa inspectors daban-daban ."

Samha ta tsurawa Sharifah ido ta yi tagum

i tana kallo Allah ne kadai ya san lissafin da zuciyarta take yi. Kanta ya daure tamau idan aka zo maganar matacce ya bayyana a duniya ana jira da shi..

Sharifah ta ci gaba da cewa "yaro bai san wuta ba sai taka, nan da na suka nutsu aka gama magana

a ranar, abinda aka shekara ana jan magana. Nima ta roqe ni da in yi hakuri da wasu abubuwan ta san zan takura amma in sassauta in rabu da shi ya je dan kansa.

Ya amince ya bar yaran a wajena su yi makarantar islamiyya da ta boko, amma zaa raba hu

tu gida biyu rabi a wajena rabi a wajensa.

Sannan kuma za su dinga zuwa gidansa duk ranar juma'a su dawo gidana ranar lahadi.Daman tun farko akan wannan zuwa weekend ne da ban yarda ba ya sa ya kai ni kotu, saboda abinda nake yiwa yaran hange shine

zasu rasa makarantar islamiyyarsu ta yamma a ranakun asabar da lahadi. Yanzun ma a hakan ake, yara su na asarar karatunsu an a ta wuce su. Amma kuma na yi ma sa uzuri dan bai san darajar karatun ba ne.

Aka zayyano ma sa abinda zai dinga basu duk wa

ta karshen wata n abinci, ya zauna ya na ta Jan magana ana ta musu da shi.

Yara har guda biyar amma ko abincin yara biyu baya kawowa. Bayan rashin kyau da inganci na abincin amma ban damu ba, fatana Allah Ya kara min budi in kula da su, ya je dan kansa.



Babu yadda ya iya da ni na fi karfinsa kuma na ci galaba akansa. Da shi da tawagarsa sun ji kunya kuma ya wahalar da kansa da dukiyarsa a banza bai sami yadda yake so ba. Alhamdulullah."

Samha ta ce "tabbas kin gama magana. Harkar tsiya ce

ace ka kasa ciyar da yaranka amma kana can kana burgewa a waje. Kada ya dauka ya ci banza, yaran su na kallon duk abinda yake yi ba zasu manta ba. Toh yaya maganar daya shariar da ya dauko gidanki ya ce na su ne?"

Sharifah ta ce " ina zamana lauyana

ya kira ni a waya ya ce ga Adamu da lauyana sun ce in zo a yi sulhu akan gidan nan nawa, ya yarda gidana ne ciko kawai zan yi ma ta. Sun yarda in basu cikon in riqe gidana. Na ce babu damuwa."

Samha ta yi dariya ta ce " wato da dai ya dauka ke ban

za ce ya shirya miki wulaqanci. Ni kuwa ina bayin Allah nan su biyu da kika ce Babanku daya, su ne kadai suke tare da ke suke bin bayani?"

Sharifah ta tabe baki ta ce "su ma ashe munafukai ne Samha. Hmmm! Har gara kowa ma da su, ashe har gara wa

danda suka fito fili tun farko su ka nuna basa tare da ni. Su biyu uwarsu daya ubansu daya. Sun ga Allah Ya rufa min asiri fiye da su, a jikina suka jingine suke samu. Ba na so in tsawaita fadar abin kirkin da na yi mu su saboda dan Allah na yi zan zube la

dana. Amma amfanin da na yi mu su ko Shariqah ba ta more yadda su ka more ni ba.

Dayar da ba ta da aure, kacokan a gidana take zaune, ni ce komai na ta duk da tana aiki amma sai ta boye albashinta nawa kawai take ci.

Kwanannan da ba

a dade ba, cikin dare Hamidah ta farka sai ta ji su a waya su na gulmata. Wai ashe bakin ciki su ke yi min duk tsawon wannan lokaci, musamman da na tafi turai ina samun kudi. Yanzu kuma murna suke yi na dawo ba ni da kudi ba ni da cikakkiyar lafiya, su n

a ta shewa fa su na cewa ta kare ma ta ai gashi nan ma bata da lafiya. Alhamdulullah. Sun godewa Allah zasu ga yadda zan yi kuwa. "

"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Subhanallah. Uba daya fa kika ce. Shin me zumunci ya zama ne a wannan zamanin

? Ashe wannan kiyayyar ta 'yan ubancin da ake fada da gaske ne?" Samha ta fada a gigice.

Sharifah ta yi shiru zuwa wani lokaci ta ce "Addu'a nake ta yi a kwanakin kuwa, duk sanda na yi sujjada inaroqom Allah akan duk wanda baya zaune da ni da

zuciya daya Allah Ya tona shi ya kuma cire shi daga cikin rayuwata.

Ke kin ji gulmammaki da su ka dinga fitowa daga gidaje daban-daban? kuma wasu ma dangina ne na wajen uwa nan suke zuwa su na yin gulmar. Ashe ma sun dade su nayi tun mamarmu tan

a da rai suke yi mana wannan baqin cikin saboda Allah Ya rufa mana asiri. Mamana ta fi uwarsu rufin asiri, duk riqon da mu ke yi mu su shekara da shekaru ashe hassada na karkashin zuciyarsu basa kaunarka ko kadan.

Gulma da kage da sharri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login