Showing 39001 words to 42000 words out of 65015 words
ita. Ina so ta gama sakandire sai in zo in tafi da ita kawai.
Mu na can har mu ka shekara d
aman kamar yadda na fada miki a baya zamana da mijina a cakude a waje daya matsala ne, kullum fada.
Abin ya zamanto har da cin amana kuma na gano shi ya fara son wata kawata acan, na gane abinda ke faruwa kawai na sallame shi mu ka rabu, na kama g
aba na ya kama na sa gaban.
Daga baya ma ya kasa zama ya dawo Nigeria ya ci gaba da lalacinsa. Ni ce daman me zafin neman na ci gaba da gina sana'a ta a can ni da wata kawata mai suna Fatima kt mu na zaune tare. Ina samun abin rufin asiri ina turowa
gida ina taimakon 'yata da 'yan uwana musamman Shariqah.
*** *** ****
A satin da Shariqah za ta rasu na sami mai zuwa nan Turai na ce ta aiko min da gyararren wake da gyadar kunu. Kasancewar na san ba ta da kudi sai na turo ma ta da kudi na
kashewarta da kuma wanda za ta sayi komai. Aka ce ita ta gyara min da hannunta, dan tayi-tayi da mai aikin ta yi ta qi mayar da hankali, dan haka sai ta yi da kanta.
Ta rame sosai kasancewar ciwon ya na ta cinta. Na yi ta fama da ita akan ta turo min
hotonta in gani amma ta qi, ashe ba ta so in ga yadda ta zama ne ta san hankalina zai tashi. A waya dai ga muryarta nan tangararai ashe jikin ba dadi.
Koda yaushe muna hira a whatapp da sabuwar wayar da na turo ma ta, ta sare gaba daya ta ji a jikint
a zata rasu.
Muna hira na ce ma ta kwana biyu sai in ji zuciyata babu dadi, gabana ya na ta faduwa. Budar bakinta sai ta ce "ko ni ce zan mutu?"
Na rasa amsar ma da zan ba ta yayin da hankalina ya sake tashi.
Ana cikin wannan hali kwat
sam Hamidah ta kira ni tana kuka ta ce min " Mama sai in ji na kasa bacci kirjina yana ta bugawa, zuciyata na tsinkewa."
Nan ma na ji hankalina ya tashi matuka, na cewa Hamidah ta yawaita yin addu'a sosai da yawan alwalla da sadaka.
Shariqah
ta bani labari a waya ta ce ta kasance tana yawan yin barci mai nauyin gaske a koda yaushe, ba dare ba rana ba safe. Baccin da kowacce irin hayaniya ake yi ba ta ji, sannan kuma ayi ta tashinta ana girgiza ta dakyar take tashi.
Ta tabbatar min wat
a duniya take tafiya, tana ganinta tana biye da wani mutum. Mutumin ya na hawa saman duwatsu, tana biye da shi. Sai ta waiwayo ta dubi bayanta sai ta ga 'ya'yanta guda biyar din nan dukka a warwatse wancan a wani lungu wancan a yashe a wani waje daban, sai
ta zo ta na ta kokarin harhada su a waje daya amma sun ki haduwa. Sai ta hada wadannan sai ta sake hango wancan a can wani a wani waje, in ta dauko shi sai ta ga wancan a wani lungun. Tayi-tayi ta hada su a awaje daya ta kasa.
Da ta fada min sai n
a yi shiru dan akwai tashin hankali babba a cikin labarin mafarkinta.
Nima ina can ina yin nawa mafarkan, na ga daki guda ya kama da wuta, sai na fito a gigice da yara guda biyu a hannuna.
Da na fada ma ta sai ta ce "ko dai mutuwa zan yi"
Ban san ciwon ta ya kai haka ba, har nake ta kokarin ba ta kwarin guiwa, na ce ta fara yin business zan turo ma ta da kayan yara da takalma ta fara siyarwa. Ta amince nan da nan take ta murna.
Akwai wani gidana karami da na taba siyar ma ta, ba t
a fada min kai tsaye cewa mijinta ya qi kai ta asibiti ba amma ta ce min in karbi gidana in mayar ma ta da kudinta har ma ta yi mun ragin 500k hakan ya nuna a matse take da kudin.
Ashe lafiyarta ta ke so ta tafi ta nemo. Na Amince har na tura ma ta w
asu daga cikin kudin na fara biya.
Hamidah ta dauke ta a hoto ba tare da ta sani ba ta turo min "innalilahi wa inna ilaihi rajuun." Ashe babu Shariqah, a kashi goma saura kashi uku, Shariqah ta kare ta rame sai kashi ga gayo tana yi. Karfin hali kaw
ai take yi da take iya magana, ba ta daina aikin girki da yiwa miji wanki ba.
Bayan kwanaki biyu Hamidah ta kira ni a gigice ta ce ga Muminta Shariqah babu lafiya, ta zo gidan ta same ta a yashe a kasa a falo, mijin ya fita bayan yaran sun je da gu
du sun fada ma sa ba ta da lafiya, ya zo ya kai ta a asibiti. Ya ce baa fada masa da wuri ba, shi yanzu fita zai yi. Ko leqawa bai yi ya ga yanayin jikin ba.
Bayan Hamidah ta wuni a makaranta ta je gidan sannan ta iske ta a cikin wannan hali. Daga it
a sai yara kanana da mai aiki.
Na cewa Hamidah ta samo adaidaita ta kai ta asibiti, yariyar nan karama ita ta saka ta a cikin adaidaita sahu su ka tafi.
Kowanne asibiti baa karbe ta ba saboda babu gado kuma ba su da na'urar oxygen din da zaa s
aka ma ta saboda numfashi ya dawo sama-sama.
Hamidah ta kira su Bello da sauran dangi aka hadu da su aka dinga fama. Mijin nan bai dauki waya ba har dare, babu irin kiran da baa yi ma sa ba ya qi dagawa.
Karshe dai suka kai ta wani asibitin ku
di, tunda babu gado ana gwamnati kasancewar a lokacin ana wani irin anobar zazzabi. Aka ce sai can da daddare mijin ya zo ya na ta yi ma ta tsawa.
Wasu daga cikin dangi su ka hau kansa da fada sannan ya sassauta. Da kyar lokitoci su ka ceto rayuwar
ta, ta samu ta warware kadan, har muka yi magana a waya da ita.Bayan kwana biyu tana asibitin jiki ya sake rikicewa, na kira su a waya yadda na ji kowa a rikice na san Shariqah kuma babu.
Na yi addu'a, na yiwa Allah SWA bakance, na yi sadaka, na saka
dukkannin Malamai bayin Allah da na sani su sauke ma ta qur'ani akan Allah Ya jinkirta ma ta, Ya tashi kafadunta. Na yi tawasali da dukka kyawawan ayyukana da kaunar da nake yi wa Annabinmu dan gatan Allah Muhammadu Rasullulah (S.A.W)."
Sharifah ta
yi shiru kanta a sunkuye a kasa yayin da hawaye ke zuba kamar an kunna famfo.
Samha ma sharce hawaye take tayi ta yi dan yaqi tsagaitawa. Ta miqawa Sharifah tissue ba tare da ta iya magana ba. Sharifa ta karba ta goge ta face hanci, ta dago ta dubi S
amha da jajayen idanuwanta
Ta ce "Allah sarki Samha na zo na ba ta miki mood dinki, na tayar miki da hankali, na saka ki kuka."
Samha ta ce "in ban tsaya na saurari labarinki ba ba zan taba yafewa kaina ba."
Sharifah ta gyada kai ta ce "
Na gode da kulawa sosai."
Samha ta ce "ci gaba da labarin ina sauraro."
Sharifah ta cije baki ta ci gaba da cewa " Wane mutum, babu gudu babu ja da baya idan lokaci ya yi, ko sakon daya Allah ba zai qara ma ka ba.
Duk duniya babu mai i
ya hanawa, me afkuwa ta afku. Ba zan taba manta da yadda na ji baqin labarin nan ba. Shin mafarki nake yi zan farka ko da gaske ne? Haka nake shafa jikina dan in tabbatar.
" Innalilahi wa inna ilaihi òrajuun." kawai na ke ambato. Kamar in yi fuffuke in
diro Nigeria haka na ji.
An sanar min ga Hamidah ta suma ga Bello ya dimauce. Babu abinda zan iya yi, nima ta kaina nake yi, ni kadai a kasar da ba tawa ba, sai ni sai kawaye da abokan arziki ne ke kewaye da ni su na bani hakuri.
Na kasa kuka
ma sai kirana ake ta yi a waya, daga ko ina a fadin Nigeria saboda ni na fi cancanta a yiwa jaje akan rasuwar Shariqah.
Ban qi in kwashe dukkannin kudina da na mallaka a duniya dan in sayi sabon tikiti ba, in har zan samu tafiya a ranar.Mutumin ki
rki wani Alh. Musa ya yi min dukkan kokarin da zai yi, na hau kan return ticket dina ba tare da an kashe wasu kudi da yawa ba.
Ta rasu cikin dare ta yi kwanan kaso da safe aka yi ma ta Jana'iza, ana sanar min da komai a waya. An fadi irin taron jama
'a da suka sami halattar jama'izarta, ana yi ma ta kyakykywan zaton samun rahamar Ubangiji. Bayan ta cika da kalmar shahada kowa ya budi baki kyawawan halayanta ake ambato, fara'a, da kyauta, wasa da dariya, ta zauna kowa lafiya. Alhamdulullah ."
Sh
arifah ta yi shiru zuciyarta na bugawa da gudu yayin da idanuwanta su ka ci gaba da zubar da hawaye masu zafi.
Ta ci gaba da cewa "Wannan rana ta na daya daga cikin baqar ranar da ba zan mantawa ba. Baqaqirin kuwa, mai duhu gami da daci.
Ban s
ami tafiya ba sai washe gari cikin dare, kowa a cikin Jigin nan sai da ya gane ina cikin bala'i. Na kasa tsayar da hawaye, komai ma na kasa ci ko sha. Ma'aikata masu kulawa su ka dinga zagayowa su na bani hakuri haka fasinjojin da suke zaune a kusa da ni
su ka dinga lallashina.
Hawayen ya na kwaranya da kansa ne ba tare da ina so ba. Radadi nake ji a can cikin zuciyata kamar ana gobara, na tabbatar na yi rashi a rayuwata, na sake samun qibi wanda ba zan taba dawowa daidai kamar da ba. Farin cikin ra
yuwata fiye da rabi ya tafi, babu dawowa sai dai maleji."
Fuskar Samha ta jiqe sharkab da hawaye yayin da itama radadi da zugi ya mamaye zuciyarta. Ta dafa kafadar Sharifah ta na lallashi ba tare da san kalma daya tak da zata furta wacce zata kwanta
r ma ta da hankali ba.
Sharifa ta sharce hawaye ta ci gaba da cewa "Na isa airport din Kano masu zuwa daukana su ka zo suka dauke ni, ban ma kira dangina ba dan na san su na cikin alhini, na fi son su gan ni kawai.
Kwatsam dangina suka gan ni
na diro, kowa ya ganni sai ya fashe da kuka amma fa ni na kasa yi. Yaranta na fara nema aka kawo min su, kanana da su abin tausayi.
Allahu akbar! Na saka a raina kuma na furta a sarari "kun rasa uwa a zahiri amma ba ku zama marayu ba, tunda ina ra
ye."
A lokacin ban ma san ta bar wasiyya a fada min ba cewa kada in bar yaranta su rayu a wannan gidan ba."
[3/1, 2:17 PM] Jamila Umar Tanko: 4
Ashe tashin hankali na gaba, na baya dukka wasa ne. Mu na gidanta aka yi zaman makoki aka gama
kwana bakwai kowa ya watse.
A ranar aka yi zaman farko da mijinta akan maganar yadda zaa yi da yaranta. Da ni da wasu daga cikin dangi, ga kuma babban yayanmu yaya Bellocity. A lokacin Adamu mijin Shariqah ya fara wasu kame-kame wanda baa gane in da
ya nufa. Ya ce a bari ayi arba'in akwai wani tsarinsa da yake yi, aka bani hakuri aka ce mu zauna a gidan har a yi arba'in din.
Mu na zaune a gidan ni da yayata daya da muke uba ya daya sai kuma kanwar mahaifiyarmu. Sai yarinyar da Shariqah take riq
ewa 'yar yayarmu ce mai suna Nidal mai kimanin shekaru goma sha uku, da ita yaran su ka saba sosai duk inda ta yi su na biye da ita. Su na zuwa makaranta su na dawowa.
Sai kwatsam mu ka ji wata magana wai Adamu ya na so a bashi wannan karamar
yarinyar da take rikewa wato Nidal zai aura.
Yarinyar da take zaune a gidansa bai taba yin kara ya biya ma ta school fees ba, aka ce an sha koro ta daga makaranta idan Shariqah ba ta da kudi sai dai ta zauna a gida ta kusan cinye term amma ba zai biy
a ba. Da abu ya ci tura ma ta kasa Biyan private school sai kawai ta mayar da ita ta gwamnati
Kuma me shekaru goma sha uku ce za ta reqe yara biyar?
A lokacin ma babbar 'yar Shariqah ta na da shekaru tara, meye banbancinsu? Su dukka rainon
su ake yi. Dangi su ka yi masa caaa aka su ka ce ba zai yiwu ba, a ranar da ya furta kalmar nan a ranar aka zo har gidan suka dauke ta. Na kasa magana na zuba ido ina kallon true color sa, gaba daya kai na ya daure.
Adamu fa da gaske yake ya kamu da
son Nidal, har kama kafa ya je yana yi da iyayen yarinyar da kamanninta da sauran dangi, shi dai a bar shi ya aure ta, zata karasa karatun gidansa. Abin tambaya anan shine daman ya na son ta tun Shariqah na raye ne? Tabbas alamu sun nuna hakan, wato an ta
bbatar masa da cewa Shariqah za ta mutu har ya gama nasa plans din.
Ikon Allah! Kaina fa ya daure ina kallonsu kawai. Shi dai dubararsa ita ce kada a fita da yaransa daga gidansa.
Na dade da gane hakan, da ya fada min maganar Nidal, tambaya
daya kawai na yi masa daga ita ban sake ba. "Shin me shekaru goma sha uku ce zata iya raino da tarbiyyar yara guda biyar?"
Akwai wata yayarmu uba daya muke, bazawa ce, ta na da kirki sosai dan tunda aka yi rasuwar da ta zo ta dinga hidima da yaran n
an, ita ce goyonsu, wankinsu, dafa abincinsu, wankansu, wasa da dariya da su. Nima hankalina ya kwanta da ta aure shi muddin an saka masa doka akan babu zalumci da tauye ma ta hakki kamar yadda ya yiwa Shariqah. Ba zaa sake zuba masa ido ayi shiru ya na yi
n abinda ya ga dama ba kuma.
Saboda abinda na hanga na hango wannan hanyar shine kadai mafitar yaran dan muddin aka ce zaa fitar da yaran zaa sha rigima ba kadan ba. Ni kuma na rasa 'yar uwata na rasa dukkan wani farin cikina bana son wani tashin h
ankali kuma.
Na ga alamar itama tana so sai aka yi shawarar cewar ya aure ta mana.
Da aka fada masa sai nan da nan ya bata fuska ya ce shi sam babu tsarin auren bazawa a wajensa, haka ba zai iya auren babbar budurwa mai wayo ba. Sai dai 'yar
shila wacce zai aura ya juya yadda yake so. Kuma alamu sun nuna ba dan 'ya'yan yake son yin auren ba kenan, bai damu da wacece za ta iya kula da su ba, kawai dan sha'awar kansa ne.
Aka gama wannan sai ya gangaro maganar 'yar autarmu Dinar, 'yar kima
nin shekaru goma sha takwas, wacce na ce miki a baya idan ta zo hutu gidansa sai dai a boye ta dan idan ya ganta korar ta zai yi.
Ya ce itama a bashi zai aura, na ce masa ai gata ga shi ga kuma Mamarta. Anan na sami dama na fada masa