Showing 42001 words to 45000 words out of 65015 words
dukka kuskuren
sa da yadda ya munanawa Shariqah.
Ya firgita sosai dan ai ya zaci duk baa san musgunawar da yayi mata ba, tunda ya ji babu wanda ya taba tarar sa ya yi ma sa maganar.
Da yake yana so a bashi kuma ya tabbatar ya aikata din, ai bai yi musu ba,
sai ya shiga tuba gami da yin alqawarin zai gyara halinsa in sha Allah.
Har dai aka cika kwana arba'in baa sami matsaya ba, da yawa daga cikin dangi sun nuna rashin amincewarsu ta yadda zaa sake daukar karamar yarinya a bawa mutumin da kowa ya san
wahalar da ya bawa waccan. Hasali ma baqin ciki ne ya sa ta kamu da ciwon zuciya har ta rasu, babu wata kulawa da ya yi ma ta. Wannan abu a bude yake kowa ya tabbatar da hakan, an san halinsa an san halinda ake shiga a rayuwar gidansa.
Wasu kuma su
na ganin a bashi kawai saboda darajar yaran amma a ja masa kunne kuma shi ma da alama ya yi nadama.
Yarinyar idan an yi ma ta maganar sai dai ta yi ta kuka ba ta amsawa.
A zaman karshe wato ranar kwana arba'in Shariqah. Adamu ya so ace an ga
ma magana an daura masa aure da Dinar kawai sai ta tare a dakin yayarta ba sai an kwashe yaran ba, amma abu ya ci tura dan baa tsayar da matsaya ba.
Ransa ya baci sosai a lokacin da Bellocity ya tsura shi da tambayoyi ya ce "ka ce ba ka so a kwash
e yara, mu kuma yanzu an yi kwana arba'in, zamu watse. Yaya kake so a yi da yaran? Ina za ka kaisu dan an ji kana hayaniya da uwar gidanka ta yi rantsuwa ta ce ba zata riqe su ba? Ko ta amince ma ai ba ita ce da alhakin riqon su ba, a addini dangin uwarsu
ce. Sharifah ce ta fi cancanta ta karbe su, sai ta tafi da su. Wannan abu ya faru ne ba dan kowa ya na so ba.
Sai Adamu ya fusata ya fada cikin fushi "shikenan a tafi da su."
Ya tashi ya fice a fusace, ni na san kwarjinin Yaya Bellocity ne
ya cika masa ido, dan mutum ne mai kwarjinin gaske, kai idan ka kalli fuskarsa ka san babu wasa.
Ba ya so amma babu yadda Adamu zai yi muka kwashe kayan yaran, mu ka kulle kofar bangarenta, kowannenmu ya kama gabansa.
Mu ka kauro gidan da su
Hamidah suke zaune wato gidan da na kama haya wanda bashi da nisa da gidansa. A lokacin mutuwar ta dawowa kowa sabuwa fil, daga ni har yaranta da Hamidah. Haka muke lallabawa mu na rayuwa zuciya babu dadi.
Na dauko Dinar daga hannun Mahaifiyarta do
n ta zo ta taya ni zama da kuma kula da yaran, sannan na samo mai aiki.
Abinda ya fara damuna shine Adamu ya hana mu sakat, a koda yaushe safe da rana da yamma sai ya zo ganin yaransa. Sannan islamiyya ya ce bai yarda a saka su a ta kusa da mu ba, y
a ce sai dai kullum Hamidah ta kaisu islamiyyar kofar gidansa kuma ta koma ta dauko su.
Dan a zauna lafiya haka na takurawa Hamidah sai ta ajiye su sannan ta tafi ta su islamiyyar, sannan idan an tashi sai ta hau adaidaita ta dauko su. kullum sai ba
ya magrib suke dawowa gida.
Dokoki kala-kala dai mu na ta bi, bayan nan kuma ya ce duk asabar da lahadi a can gidansa zasu dinga yi, dan su dinga zuwa tahfiz tare da sauran yaransa.Nan ma na yi hakuri da hakan ake yin haka kullum.
Bayan ar
ba'in din Sharifah da sati biyu, kwatsam sai aka sanar da ni rasuwar babban yayanmu wato Yaya Bellosity ya rasu bayan yayi fama da gajeriyar jinyar kwana biyu."
"nnalilahi wa inna ilaihi rajuun."Sharifah da Samha ne suka hada baki, suka fada a tar
e yayin da kowannensu ya yi shiru ya yi tagumi.
Sharifah ta dago da jajayen idanuwanta ta ce "shine Bellon da nake sanar miki ya rasu na san baki san shi ba. A lokacin da muke yara har yayi aure, ya rasu ya bar mata uku da yara sama da ashirin shine b
abba a dakinmu.
Shine mu ke ganinsa kamar uwa kuma shine uba, shine yake tsaya min akan komai nawa. Magana kuma ta kare Sharifah ta zamanto ba ta da iyaye bata da dangi, kusan dukkan masoyana sun tafi."
Wannan karon Sharifah ta zubo da wasu haw
aye masu zafin gaske yayin da tausayinta ya kama Samha matuqa.
Samha ta sharce hawaye ta ce "sannu qawata ashe irin wannan tashin hankalin kika shiga amma baki taba nemana ba? Haba Sharifah ko dai ba zan amfane ki da komai ba amma mutum ai rahama ne
, idan ina kusa da ke ai zan baki shawara, kuma in jajanta miki ai za ki ji dan sanyi "
Sharifah ta sharce hawaye ta ce "na rantse da Allah ko motsi da kyar nake yi, ba na son yin magana ma, shiyasa bana riqe waya. Ba na bukatar taimakon kowanne bil'a
dama sai na Rabbul samawati.
Ana cikin wannan hali na gigita da tashin hankali ga waccan ta Shariqah ga wannan ta Bello amma bawan Allah nan Adamu kullum yana cikin yi min kuri da barazanar zai kwashe yaransa. Dan ya ga na damu matuqa da son rikon
yaran, kuma ina bin dokokinsa.
Sai ya zamanto ma ya fara na nuna min, ai dole ma in bashi auren Dinar ko kuma ya kwashe yaran.
Daga baya na fuskanci baya neman amincewar yarinyar dan ko ya zo bata kula shi ya san bata sonsa dan haka ni ce zan yi
ma ta dole.
Ko unguwa na fita sai ya fara bambamin fada yana kumfar baki wai na fita na bar yara zai kwashe su."
Samha ta kama haba ta ce "ikon Allah sai kace shi yake aurenki. Kullen da ya saba yiwa Shariqah ne ya dawo kanki kuma?"
Shar
ifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " ke ma kya fada. Ni ko can asali ma ban taba sanin auren kulle ba, balle yanzu, ba mijina ba komai ba ya ce zai takura min.
Da gadara yake tambaya sai ta, ya ce min yaya maganar aurensa da Dinar? Amsar da nake
bashi ita ce ga ka ga ta nan ai, ku daidaita.
Sai ya ce "ai ita yarinya ce ke za ki yi ma ta dole."
Na ce "ba zan yi ma ta dole ba ko da kuwa ni na haife ta balle ban haife ta ba, dan yanzu an wuce yin auren dole."
Samha ta ce " tab
daman har yanzu akwai mutane irin wannan mutumin. Tun yaushe aka daina irin wannan rayuwar?"
Sharifah ta ce "neman rigima ce kawai da nuna isa da izza. Irin wacce ya saba yiwa matansa, yana nuna musu mulki da sarauta shine abu ya dawo kaina. Da son
takurawa mutane da neman fada. Ya nunawa kowa bai isa ba sai an bi abinda yake so kuma yana ganin kamar bani da kowa.
Ashe ta karkashin kasa dangina da dama sun bashi goyon bayan ya yi min hakan.
Da na gane inda ya nufa sai na cire tsoro da
shakka, zuciyata ta dake. Da na ga ya fara bin dangina yana kama kafa da su sai na zuba ido. Anan aka sami mararsa kaunata da wasu masu kaunata.
Aka sami wata da ta bashi labarin cewa anan qasan gidan da muke ma Dinar ta yi saurayi kuma ina sane amma
na bar ta take kula.
Ya zo a gigice kuma a fusace zai hau ni da fada wai ya ji labari Dinar ta yi saurayi kwanan nan kuma ina sane.
Na taka masa burki na ce ka sani fa Dinar ba jaririya ba ce 'yar goye kuma tana da zabi, sannan ni ba zan yi
ma ta dole ba kuma munafukar da ta fada maka haka ka je ka fada ma ta an yi din.
Kuma wallahi a lokacin ban ma san komai akan maganar wani saurayi da Dinar ta yi ba, abinda na sani yaron yana da shago a kofar gidan da nake yana da kirki yana taima
ka mana da aike da sauransu ko sunansa ban sani ba ma da farko. Daga na fita zan ga yana ta gaishe ni.
Shine har su 'yan waje da suke wata unguwa har su ka san da labarin yaron aka je aka dinga juya magana.
Nan fa ya fuska ya dinga zagaya
wa gidajen wasu daga cikin dangina aka barke da gulma kala-kala, ana zuga shi."
Samha ta ce "ikon Allah yanzu a danginku har a sami mai bin bayan mutumin da ya azabtar da 'yar uwarsu? bayan duk abinda ya yiwa Shariqah? Kai amma zumunci ya lalace walla
hi."
Sharifah ta gyada kai ta ce "me kika ji ma ai abu na gaba kawata, za ki sha mamaki ace jininka ne yayi ma ka haka.
Can kuma ga Shariqah ta kasa kwanciya a cikin kabarinta akan wannan dalilin."
Sai Samha ta zazzare ido ta ji gabanta
ya yanke ya fadi dan an dawo kan labarin matattu kuma."
Cikin jimami Sharifah ta ci gaba da cewa "Ga ni na da ita na farko a bakin wata rijiya ne, na ganta ta na zaune ita kadai ta yi shiru ta sunkuyar da kai qasa idanuwanta a runtse. Na yi ma ta m
agana, ba ta dago ba. Na jijjiga ta ta runtse ido ta qi dagowa. Daga nan ta bace min da gani, na yi ta duba ta ban kara ganinta ba."
Sai Samha ta dafe kirji ta ce " Ya salam! A bakin wacce rijiya kuma? Da safe ko da daddare?"
Sharifah ta ce "
gab da magrib. Daga nan na fara tunanin akwai abinda ake yi wanda ba ta so.
Ina tare da yaranta zuciyata na quna na rasa karamar kanwata, na rasa babban yayana wanda nake ganin shine namijin da zai tsaya min a dukkannin lamurana.
Rayuwa ta
tsananta a lokacin ba na so in ga kowa ko in yi magana da kowa. Lokacin mutuwar tana tsaka da cin zuciyata na tana cin zuciyar Hamidah sosai kowa a cikinmu babu kuzari. Yaran Shariqa musamman masu wayon su na cikin alhini su kan shiga daki su kwanta akan
kayanta su na kuka. Ina ta faman amsa tambayoyin kananan yaran, su na tambaya ta cewa Muminsu ta na asibiti amma me yasa har yanzu baa kai su sun duba ta ba.
Ina iya kokarina wajen kawar musu da hankali. Ina ta shirya karya kala-kala wajen kwantar musu da
hankali.
Kowa da irin yanayin da ya fi so ya kasance idan ya shiga damuwa, wani ya fi son ya zauna yayi shiru, wani ya fi son yayi ta barci, wani ya fi son yayi ta kuka, wani kuma ya na son ya shiga cikin mutane, wani baya san ya ga kowa a kusa da sh
i.
Nawa yanayin na fi son in zauna shiru a daki, bana so in yi magana, ba na so ayi min. Idan na kebe ni kadai a lokacin nake iya yin kuka ba tare da wani ya ganni ba.
A daidai wannan lokacin da bana so in ga kowa in yi magana da kowa shi kuma
mijin Shariqah ya kafa zarya a gidana yana kulafucin yaransa. Ya na ciyar da su yadda ya kamata abubuwan da bai basu a baya ba ma a yanzu yana kawowa, komai baja-baja amma bai dame mu ba.
Babu mai iya ci, mai aikina ce da wasu kalilan daga cikin yara
n ne ma ke iya ci. Dinar da Hamidah ba komai ne yake burge su ba sai sun zaba.
Dokoki dai na takura barkatai alhali a lokacin bana son a takura min ko kadan abinda yake damuna shi yake damuna. Wannan dalilin ya sa ma na yanke alaqa da dukkannin kawa
yena ban sanar da su rasuwar ba ma dan bana so a dinga zuwa inda nake. Sauran kawayena wadanda na saba da su daga baya a harkar kasuwanci ko a gari su ma na guje su, babu wanda ya san a ina nake mo me nake ciki.
Abinda zai ba ki mamaki zai daure muku
kai shine na baro dukka abinda na mallaka na kasuwanci a hannun abokiyar kasuwancina Fatima kt. Ni ce karfin tsayawa har kasuwancin ya kafu, jarina ne ya fi yawa. Na rantse da Allah matar nan da yake bata tsoron Allah sai ta hada dukka ta cinye. Bayan ta
fada min bakaken maganganu ta yi blocking dina a dukka wata kafa da zan same ta.
Na sayi ticket zan je in hado kayana amma matsalar Corona ta ballo kai babu shiga babu fita. Haka aka soke tikitin ban Sami tafiya ba.
Ashe bala'i ya na gaba,
dukka wannan wasa ne. Ina zaune ina ci gaba da kula da yara su na zuwa makarantu islamiyya da boko ga kanwata ga mai aiki kowa yana iya kokarinsa.
Ban San yadda ake raino ba dan ban iya shi ba ma, saboda nawa rainon Shariqah ce ta yi min.
Yan
zu Allah Ya juya lamuransa ni ce nake yi ma ta rainon. Daman haka aikin alkhairi yake idan ka yi abin alkhairi ko bayan ranka za ka tsince shi a gaba. Ga shi dai yadda ta yi min wahalar raino ba tare da ta yi tunanin zan biyata.
Duk duniya banda yar
an Shariqah babu wanda zan iya riqewa haka. Na salwantar da duk abinda nake da shi na yarda in rasa komai, na yarda in takure rayuwata in zauna waje daya dan kawai in kula da yaranta.
Akan maganar auren Adamu da Dinar Allah shine shaidata na kira
Dinar na zauna da ita na bata shawara akan ta nutsu ta yi tunani ta gani ko za ta iya yin wannan jahadin ta aure shi dan ta riqe yaran 'yar uwarta.
Amsar da ta bani ita ce ta sa ban sake shiga maganar ba, ta ce dani ta rantse da Allah ko kwana da
ya ba za ta iya auren mutumin nan ba. Ta zayyano min wasu daga cikin mugayen halayensa wanda ta gani kuma wasu ta ji labarin wasu.
Na ce ma ta amma ai ya ce ya tuba zai gyara halayansa, daga yanzu mace za ta sami 'yanci.
Ta ce min "haba Aunty
ko watanni uku baa yi ba fa da na je gidansa aka boye ni dan idan ya gan ni kora ta zai yi. Mutumin da ina matsayin
kanwar matarsa uba daya amma bai san ni ba ban san shi ba, tsabar bai dauki danginta da muhimmanci ba."
Na gasgata maganata, maganar
kyautawa sam bai kyauta ba, amma yaya zaa yi tunda zuri'a ta hada, yara ba ba daya ba ba biyu ba har guda biyar.
Ni kaina ina neman mafita ne dan ba zan iya zubar da yaran nan in tafi ba, in dai ba na sami takamaimai in da na tabbatar zaa kula
da su ba ne. Idan kuwa babu dole in zauna da su, in hakura da komai nawa na rayuwa.
Wannan shine ma abinda zai fiye min kwanciyar hankali tunda 90% na tabbatar bayan uwar da ta haife mu ni da Shariqah babu mai riqe yaran nan kwatankwacin uwarsu iri
na.
Saboda haka ko da ace