Showing 36001 words to 39000 words out of 65015 words

Chapter 13 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

26

da cewa "Samha ai na fada miki Sharifah ba cikakkiyar mutum ba ce, kika nece kika ce kin tabbatar mutum ce, ai gashi nan zaa kashe mu."

Samha ta na ta nishi ta dafe kirji ta ce " Sharifah daman ta fada min, bayan ta yi rantsuwa da Ubangijin da

ya halicce ta Ya halicci Shariqah ta ce tana magana da Shariqah fuska da fuska kamar yadda take magana da ni. Ta sake yin rantsuwa cewa Mamaci ya na sanin abinda yake faruwa a duniya kafin mu bil'adama mu sani. Ta ce idan malaman garin nan ko na duniya ka

f zasu taru akanta su karyata ta ita fa ta fada ba za ta janye ba, cewa mamaci ya san abinda yake faruwa a duniya saboda ita ganau ce akan Sharqah ba labari aka ba ta ba."

Maryam ta zabura ta dafe kirji ta ce "wato dai yanzu Shariqah na cikin dakin

da Sharifah take magana, tare suke hira kenan? Ban taba ji ana HIRA DA MATATTU ba sai a yau. Mun shiga uku, innalilahi wa inna ilaihi rajuun.Wannan wacce irin Sharifah ce mu ka kwasowa kanmu?"

Hamidah ce ta bayyana a bayansu har yanzu idanuwanta na

cike da hawaye sun yi jajajur abin tsoro. Sai su ka razana su dukka, har wasu sun ruga da gudu baya mota sun sami mafaka.

Hamidah ta sharce hawaye cikin sanyin murya ta ce "Mamana ta ce ku hawo sama, ta fito falo yanzu, ta na jiranku."

Aka

hau kalllon-kallo a junansu.

Nanah ta yi karfin hali daga nesa ta ce "wacce Mamar ta ki daga ciki Sharifah ko Shariqah?"

Maryam ta nisa ta ce "tab! ai ni kam sai dai a kai gawata cikin gidan nan kuma."

Samha ta yi sauri ta katse su dan

ba ta so su sake ganewa har yanzu a fatalwa aka dauke su.

Ta ce " 'ya ta Hamidah ki fadawa Mamarki wani emergency kira aka yi mana zuwa asibiti. Ki ce ma ta za mu dawo a cikin satin nan in sha Allah. Ga abinci nan na dafa mu ku. Ku ci ke da kananank

i. Su na ina ne ban gansu ba?"

Hamida ta sharce hawaye ta ce " ba sa nan an sace su."

Samha ta zabura ta dafe kirji ta ce "an sace su kamar yaya?"

Muryar Bello su ka ji a bayansu ya dakawa Hamidah tsawa ya ce "ke Hamidah! shiga gida kuma

ki saka sakata kada in kara ganin kafarki a waje."

Jikinta na rawa ta shiga gida. Su ka juya su na kallonsa, ya na zaune a cikin motarsa yayin da ya wurgo musu wata uwar harara. Nan da nan kowacce ta hau laluben kofar shiga mota.

Samha ce ke t

uqawa dan Nana ta sha aradu ba za ta iya tuqi ba. Aka yi shiru babu wacce ta ke magana sai zulumi da tunani. Abin ya fi bawa Samha mamaki dan ada ta yarda Sharifah mutum ce dari bisa dari amma ta yaya take iya yin HIRA DA MATATTU?

Su daman su Nana

basu gama yarda Sharifah mutum ba ce dan haka ba su yi mamaki da yawa da ta fito a wata sabuwar sigar ba.

Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kowacce ke kira. Samha tuqi take kamar za su tashi sama saboda zuciyarta tafasa take ta yi kawai, wannan labari

ba za ta iya fadawa Mama ko Aliyu ba dan za ta iya saka babban kokonto a ransu bayan sun cire zargi a baya.

Nanah ta yi ajiyar zuciya ta ce "Samha yanzu duk nacinki dai za ki rabu da Sharifah ko kuwa har yanzu za ki sake bata wata damar kuma? Ni da

i na gama, na sallama ta, na hakura da kawancen nan, kawaye har sun yi min yawa dan na rasa ta ba komai, ni dai na yafe."

Maryam ta zabura ta ce "ai ko ita kadai ce kawata a duniya na yafe ma ta wallahi, itama ta yafe min mu yi sallama."

Rukayy

a ta yi ajiyar zuciya ta ce " daman ni da Sharifah ba shiri mu ke yi ba tun a jami'a, dan ta ga tana da kokari a jami'a ina cewa ta koya min karatu sai ta dinga yi min wani gani-gani. Daman can ma jinina da ita bai hadu ba, a dalilinku ne ma mu ke gaisawa.

"

Halima ta girgiza kai ta ce "kai Rukayya ko a bayan idon mutum ne ka fadi gaskiya mana. Babu wanda zai yiwa Sharifa shaidar baqin hali wallahi, ga kyauta ba ta da mugunta. Kawai dai yanzu ta zama abar a gudu dan ba ta da kammannin mutane sak."



Samha dai ba ta magana har suka isa gida suka fito suka shiga falonta aka zauna, aka yi jugum kamar gidan makoki.

Samha ta zabura ta jawo wayarta ta kira Fanna ta saka ta a hand's free.Fanna na dauka ko gaisawa ba su ba.

A gigice Samha t

a ce "Fanna! dan girman Allah me kika sani akan matsalar da ke damun Sharifah. Ba ta fada miki wasu daga cikin matsalolinta ba?"

Fanna ta yi dariya ta ce "ai kun yarda Sharifah fatalwa ce ta mutu ta dawo ko? Toh a je a hakan. Ban sani ba ko dan ni m

a mun samu matsala iri daya da ita ne shiyasa ba na jin tsoronta. Dan nima na yi ciwo na mutu fa, mata da maza sun cika gida an fasa kukan mutuwata. Har an yi min wankan gawa, an saka min likkafani, maza sun kinkimi gawa za su fita da ni waje, zaa yi min

salla a kai ni kabarina sai na farfado."

Samha da kawayenta su ka daka tsalle har da Rukayya da take sallah suka fafara da gudu, suka yi waje. Anan Samha ta bar wayar a yashe, su na jiyo dariyar Fanna, ta na ta dariya babu kakkautawa, irin ta mugun

tar nan. Wannan karon yaren KANURI ta juye harshe take yi. Ta na ambaton sunanta da na Sharifah da na Shariqah.

"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me yake shirin faruwa kenan? Fanna ma fatalwa ce ashe shiyasa bata tsoron Sharifah, an ce ta zo ta rak

a mu gidan ta ki zuwa." Nana ce take magana har da hawaye.

Su na ta kai kawo a farfajiyar gidan an rasa wacce ta iya shiga cikin falon. Su mayafansu ma suke so su dauko su tafi gidajensu. Kowacce

na tunanin in da za ta kaura ta kwana ko mutanen da z

ata biya ta dauko a cikin danginsu su taya su kwana.

Samha ta fi su dimaucewa ba ta so ta dawo gidan jiya na firgici da susucewa, kuma da alama dai sai ta dawo saboda duk yadda ta kai ga yiwa Sharifah kyakykywan zato abin ya ci tura.

Da kyar

suka samu suka yi jarumta suka shiga falon, ga waya nan a yashe a kasa. Da Samha ta duba 9 missed calls Fanna da 3missed calls din wata lamba wacce ta yi ma ta kama da ta Sharifah wacce ta taba kiranta da ita, ta gani.

Samha ta sha aradu ba za ta a

msa kiransu ba, ta ma kashe wayar gaba daya.

Su Rukayya da aka yi sallah raka biyu baa idar ba aka runtuma da gudu ta ce za ta rama sallar a gida. Wasu ma sun manta take way din da suka yiwa miji anan saboda gigita, kowacce ta suri jaka da mayafi j

iki na karkarwa ta fita. Daman dukkansu da motocinsu suka zo dan haka kowacce ta shiga ta ja ta tafi tana addu'a.

Aka bar Samha ita kadai a gida tana muzurai, da sauki ma tunda Aliyu yana gari zai dawo komai dare, amma ta tabbatar zai neme ta a waya

kafin ya iso, ga shi kuma ta kashe wayar.

Ta hau kan abin sallah ta na lazumi amma fa dukka motsin da ta ji sai ta zabura ta waiwaya.

Aliyu bai dawo gida da wuri ba sai bayan qarfe goma na dare ta wuce. Lokacin Samha ta gama zabura-zaburenta

har ya zame ma ta jiki.

Wani irin tsoro mai tsanani ne ke damunta. Amma ta kasa bawa Aliyu amsa a dukkannin tambayoyin da yake jero ma ta. Musamman akan dalilin da ya sa ta kashe wayarta.

Amsar da ta bashi ba ta gamsar da shi ba na cewa babu caj

i. Sai ya kalli fitilar lantarki a kunne, ya jiyo ya dube ta.

Ta lalubo wayar ta kunna sakonnin Fanna ne ya shigo har guda uku.

Sako na farko ta ce "kin kira kina so ki ji labari kuma kin kashe waya."

Sako na biyu ta ce " ki kunna waya mana."

Sako na uku ta ce "in kina so in baki labarin matattu da fatalwa ki kira ni ki ji."

Ta na karantawa sai ta zabura. Aliyu ya tsaya ya na kallonta.

Can ya tambaya ya ce "kun sami zuwa gidan Sharifah kuwa? Me ya faru? Ko wata fatalwar kika gani

ne na ga kin susuce?"

Samha ta zazzare ido ta ce "fatalwa kuma? Ai an wuce wannan babin. Ba mu sami damar zuwa ba. Amma za mu saka wata ranar."

Da ya ci gaba da yi ma ta kallon tuhuma sai ta yi gaggawar barin falon don kada ya gane ta.



*** *** ***

Bayan kwana biyu da rana misalin karfe biyu, Aliyu yayi tafiya, Samha na zaune ita kadai a falo ta na kallon talabijin. Sallama ta ji a bakin qofar falonta ba tare da ta ji an taba get ba, duk da ma dai get din a bude yake amma t

ana jin karar sa idan an taba.

Muryar da ta ji ta daga ma ta hankali, ta yi kama da muryar Sharifah ko Shariqah ko Hamidah. Sai ta zabura ta miqe ta koma bayan kujerar lungu ta tsaya, ba tare da ta iya amsawa ba.

Ta ga an bude labule an shig

o sai ga Sharifah ta bayyana muraran, hannayenta dauke da manyan fulasanta na abincin da suka kai ma ta.

Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu sannan Samha ta tuna ashe bakuwarta ce, kuma sannu da zuwa da murmushi ake yiwa baqo.

Samha ta washe baki

ta yi murmushin karfin hali ta ce "yau Sharifah a gidana? Sannu da zuwa, ki zauna."

Sharifah ta yi murmushi sannan ta sami kujera ta zauna. Yayin Samha ta shiga kicin hannunta na rawa ta dauko lemo da ruwa ta kawo ma ta. Sannan ta sami kujera daga

nesa-nesa ta zauna. Kirjinta na faman dukan uku-uku.

Bayan sun gaisa Sharifah ta ce "daga makabarta nake wallahi, na ce dai bari in biyo in ajiye miki fulasan nan in yi miki godiya."

Samha ta dafe kirji ta maimaita "makabarta kuma? Me ake yi a

makabarta? Waye ya rasu?"

Sharifa ta shafa kai ta ce " na je ziyara ne. Na jewa Shariqata visiting. Kin san ana je musu visiting da guzurin addu'a ko?"

Samha ta gyada kai cikin matsanancin tsoro ta ce "eh haka ne. Ina zuwa."

Ta shiga

daki ta dauko takarda da biro ta rubuta wasiyya.

Ta ce "idan kun tsinci gawata ko an rasa ni na bace toh Sharifah ce, ta zo gidana ga mu mu na tare daga ni sai ita a gida."

Kamar daga sama ta ji Sharifah ta kwalla ma ta kira, sai ta fito a gig

ice.

Sharifah ta kalle ta ta yi dariya, ta ce "canza min tasha ina so in kalli wani horror fim a MBC 2, zasu maimaita yau. Jiya na fara kallo na yi bacci. Fim din Matattu ne, su na fitowa daga kabarurrukansu. Daga sun ciji masu rai sai su ma su zama

su."

Samha ta ji gabanta ya fadi da alama yau ta zo ta cije ta itama ta zama su. Hannunta na rawa ta dauko remote ta miqawa Sharifah yayin da ta yi wuqi-wuqi da ido, ta yi baya-baya ta zauna daga nesa da ita.

Ana gama fim din da ake yi yan

zu zaa fara wancan fim din na matattun da take so.

Sharifah ta na ta yi ma ta hirar yadda abincin yayi dadi, sun sha santi.

Har aka gangaro hirar su ta rannan akan rayuwarta. Samha ta fara sakin jiki akan babu yadda za ta yi dole ne ma ta sake

.

Samha ce ke tambayarta akan a ci gaba da labarin rannan amma da alama ma yau Sharifah ba ta son hirar.

Samha ta ce "Su Nana sun ganki a wajen yayanta Barista kin je rannan sai suka ji tsoron yi miki magana saboda sun fi son su zo har gida su

baki hakuri. Sun yi miki laifi ba dadi su baki hakuri akan hanya."

Sharifah ta galla ma ta harara har sai da gaban Samha ya fadi. Sharifah ba ta bata amsa ba, ta ci gaba da kallon talabijin.

Sai can ta ce "ai kun zo har gida kuma ku ka sake

guduwa."

Samha ta sunkuyar da kai ta kasa bada amsa.

Sharifah ta kwashe da dariya har sai da Samha ta tsorata sannan ta ce " ku na bani mamaki, amma ba abin mamaki ba ne dan har yanzu ba ku san mutuwa ba ne ba ne, ba ku taba rasa wani makusanci

nku ba shiyasa har ku ke tsoron mutuwa da matattu."

Samha ta gyada kai ta ce "har da wannan ma."

Sharifah ta gyara zama ta ci gaba da cewa " Na tsaya a inda na ce a lokacin ina zama a kudu ni da mijina. A dalilin rashin lafiyar Shariqah na

ji gara kawai in dawo kano in zauna a kusa da ita. Na kauro Kano na kama haya a kusa da unguwar da gidan Shariqah yake bai wuce naira hamsin a adaidaita sahu ba, na samowa Hamidah makaranta ta ci gaba."

Samha ta ce maigidanki fa?"

Sharifah

ta tabe baki ta ce "a can na bar shi yana zuwa ina zuwa daman zamana da shi babu dadi na fi sha'awar mu rabu saboda daga ni har

'yarsa ba ma jin dadin zama da shi. Baya tsinana mana komai da albashinsa. Komai ni nake yi a gidan.Ya qi yin saki kuma baya kya

utata min. So yake mu yi aure irin na 'yan duniya mu daki juna, mu zagi juna sannan mu fito titi mu tarawa kanmu mutane sai kuma mu koma gida mu bawa juna hakuri mu ci gaba da zama.

Da na fahimci haka yake sai na ja masa layi ba na kula shi sam, abi

nda na sani shine aure bautar Allah ne aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta, idan haka ne ba zan taba samun aljanna ba a irin wannan rayuwar ta mu ba."

Samha ta gyada kai ta ce "wannan gaskiya ne, kin yi daidai."

Sharifah ta ce "Da

n haka na dinga baya-baya da shi dan kada ya illata mu. Na matso kusa da 'yar uwata dan na kula da ita kuma na taimaka ma ta sosai da kudina da kuma jikina da shawarata.

Kwatsam wata dama ta samu ni da shi daman mun nemi tafiya turai Allah bai yi

ba sai daga baya damar ta samu mu ka yi shawara mu kaura kawai.

Na bar Hamidah a gidan da na kama haya na dauko wasu daga cikin dangina suka zauna da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login