Showing 3001 words to 6000 words out of 65015 words
na bar shi na shige get.
Ina shiga get din gidan masu gadi zasu tare ni suka ga alamar babu burki. Gyalena na Jan kasa yayin da dan kwali ya dawo kafada haka a wuya na sakalo jakata. Allah Ya sa ma ba zani na
daura ba, doguwar riga ce.
Falon gidan na fada ban damu da yin sallama ba ko gaishe da mijinta da abokansa, da suke cin abinci a dining.
Dakinta na fada, na iske bata nan sai yaranta sun dawo daga makaranta suka gaishe ni ma ban amsa ba.
Daga
an yi magana ko an taba qofa sai in ji gabana ya yanke ya fadi, kwakwalwata na tafasa. Na baje akan gadonta ina ta juyi.
"Kai ku kira min mamarku. Ku ce ta zo dan Allah kafin in rasu." Na fada cikin galabaita.
Ashe tuni mijinta ya shiga kicin ya ce
ta zo ga Samha amma da alama an yi mata mutuwa bata cikin hayyacinta.
A guje Nanah ta shigo tana salati, ta kori yara waje sannanta fara jero min lugudan tambayoyi."waye ya rasu?"
Na ce "Sharifah Nasir ce ta rasu."
Ta dafe qirji cikin firgici t
a ce "innalilahi wa inna ilaihi rajuun shiyasa mana kullum bata hawa Whatsapp, layinta a kashe kuma ko an kira ta baya shiga.
Na ce ta dauko waya ta kira dukka kawayenmu ta sanar musu a tafi gidan gaisuwa.
Nanah ta ce "kafin ayi sadakar uku sai a s
hirya ranar zuwa."
Na ce "A 'a a yanzu zaku tafi kuma ku kadai banda ni, kawai ku je su tabbatar din."
Nanah ta kafa min ido tana yi min kallon rashin fahimta. "Kamar yaya mu je ba tare da ke ba, bayan kin fi kowa kusa da ita?"
Na ce ta kira dukka
kawayenmu su zo gidan nan a taru.
Nanah ta fara mamakin kalamaina amma duk da haka tana bin umarni duk wacce na ce ta kira sai ta kira ta sanar mata.
Salati da ihu kawai suke yi yayin da nake qarawa da bayanin su zo gidan Nanah gani nima na zo.
Rakky da Halima ne suka yi min musu cewa Shariqah ce ta rasu ba Sharifah ba kuma an dade ma fa. Sai dai in yanzu itama Sharifah ta rasu.
Nanah ta hau musu da su Shariqah bata rasu ba fa ta hadu da ita kwanaki a umra.
Abin dai ya sake cushe min ka
i. A cikin mutane tara da muka kira guda hudu sun sami zuwa muka taru.
Amma su na ta mamakin kidimewar da na yi har ta yi yawa, amma ba abin mamaki ba ne domin an san mun shaqu kawatace ta quttan.
Su ka tambaye ni, ni waye ya fada min? Nan fa gizo k
e saqar ban isa in ce na yi gamo da fatalwa ba ne. Dan kada a wuce da ni asibitin saita kwakwalwa.
Na daure dai ban ce komai ba, da suka dame da tambaya, na ce a radio aka sanar.
Aka tsayar da shawara aka ce a je gidan a gani. Na dage su je su kada
i su bar ni anan, abinda suka gani sai su sanar da ni.
Tabbas kowa ya cika da rashin fahimta ko kula ni ba su yi ba suka wawuri hannuna muka nufi motocinsu guda uku muka tafi.
Faduwar gaba nake kamar qirjin zai fita yayin da Nanah ke bani haquri, na
n kuwa ba ciwon mutuwa ya fi damuna ba gamo da fatalwa ne damuwa ta dan nima ji nake na zama gawa.
Mu na isa muka iske get din gidan a bude, kowa na baza ido ya ga maza da yawa a qofar gida amma qamas.
Aka Shiga jero min tambayoyi ni dai na yi musu
shiru.
Bello Nasir ne ya fito daga cikin motarsa yayin da ya gaishe mu sai aka shiga yi masa ta'aziyya, yana amsawa da Amin.
Su ka tambaya har an yi suturar ne muka ga babu kowa ?
Ya maimaita "suturar wa?" Su ka hada baki "Sharifah."
Sai
na ga ya dago ido da sauri ya dube ni ya san wannan maganar daga bakina ta fito.
Ya nuna mana get ya ce " ku shiga ciki, su na ciki"
Nan da nan suka gasgata maganata yayin da kowacce ta dauki salati. Jiki na rawa suka fada farfajiyar gidan. Ina tafe
a baya ina tafiya a hankali.
Ina shiga farfajiyar gidan sai na ga Bello ya shigo ya na qoqarin rufe kofa ya garqame da sakata.
Na daka tsalle na tunkude hannunsa na ce "kada ka saka mana sakata da ranar Allah."
Ya sake cika da mamaki yayin da ya
bi ni da kallo har ya shige cikin gida.
Qafata daya a ciki daya a waje ina jiran arangamar su Nanah da fatalwa.
Tunda suka shiga suka nutse ban ji ko tarinsu ba. Daga nan na fara tunanin sun shiga duniyar da baa dawowa.
Ban ankara ba na ji mace
a bayana ta dafa ni gami da cewa "matsa zan wuce."
Ina waiwayawa Sharifa ce sanye da farin hijabi babu yadda zanyi in fita waje da gudu sabo ta dafe qofar.
Ta kalle ni da alamar mamaki sannan ta fashe da wata irin muguwar dariya, ganin yadda na raz
ana na tafe kirji ina karkarwa.
Ta ambaci sunana sannan ta shigo ciki, babban tashin hankalin sakata ta saka sama da qasa ta kulle gidan. Gami da nuna min hanyar shiga cikin gidan .
Wannan karon umarni take bani ba shawara take nema ba.
"wuce ci
ki." Ta fada cikin gadara
Zan yi mata musu sai kawai ta fisgi hannuna. Shikenan na yi ban kwana da duniya ba tare da na yi sallama da 'yan cikinta ba.
Salati da yawun bakina ya qare sannan na zubar da takalma da mayafi da dankwali anan, tafiya nake
kawai ba tare da na san in da zata kai ni ba.
Madalla da ALQALAMIN JUT
to be continue.....
😀😀👍🏻
HIRA DA MATATTU.....4
Abinka da qaton gida irin na attajiran da, mu ka wuce baranda sannan mu ka shiga wajen zaman jira kafin a yi maka is
o zuwa falo wato (reception). Mu ka isa bakin falo sai ta tunkuda ni ciki, kafin in waiwayo babu ita ta bace.
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya samar da ni Ya samar da Sharifah, babu alamar bil'a dam na zaune a gidan nan saboda yana da ko ina a lull
ube yake da qura. kansu kujerun falon baqaqe an rurrufe su da fararen gyallaye dan kada su yi kura, hakan ya nuna babu rayuwa a cikin gidan nan da dadewa.
Na qara fadawa tsoro mai tsanani yayin da na shiga barbaza idanuwa ko zan ga 'yan uwana bil'adam
a su Nanah Ahmad da na jawo musu, na dauko su na kawo su gidan halaka.
Abin tambaya anan shine shin ina Hamidah da na ga ta shigo dazu? Ina Bello da ya shigo tare da su Nanah? ina Su Nanah kansu suke?
Wannan karon Allah Ya bani ikon yin kalmar Shaha
da bayan na baje na kwanta a cikin qura ina birgima. Gara komai ya iske ni ina daga kwance ba a tsaye ba.
Bala'i ya kai bala'i. Na Shiga tunano laifin da na yiwa wannan baiwar Allah da ta addabe ni bayan ta mutu. Ban yi mata komai ba kawai dai na rasa
lambarta dadewa.
Kenan su Bello ma gaba daya ba mutane ba ne su Hamida, su yaran da na gani a hanya masu kamar Sharifah.
Sallama na ke ji da wasu lunguna na gidan domin katon gida ne mai dauke da dakuna ba adadi.
A iya sanina babansu ya rasu ya b
ar mata hudu da yara sama da ashirin kuma dukka anan gidan suka zauna sama da qasa. Toh duk su na ina yanzu?
Na runtse ido yayin da karkarwar da jikina ke yi ta jawo har kujerun da suke kusa da ni su na girgiza.
Cimak na ji an daga ni an tashe ni z
aune, na kwalla qara mai firgitarwa na ce "na rantse da wanda raina yake hannunSa ba zan bude idanuwana ba. Kazantar da baka gani ba taafta ce. Ga dai gangar jikina nan ku yanki in da yayi muku."
"Samha Mahmud lafiya? Ki bude idanuwanki, ki taso mu tafi
, banga alamar gidan nan akwai mutane ba. Mun leqa ko ina babu kowa da alama ma an dade baa rayuwa a gidan nan." Muryar Nanah Ahmad ce.
Ramatu Alqali ta ce "ni fa tsoron gidan nan nake ji ina ta ganin giftawar yara amma sai in ga wayam."
Na tabbatar
qawayena ne sai na miqe tsaye da sauri na ce da su "gidan MATATTU ne fa, ku zo mu fita. Sharifah ta rasu amma ni ina ganinta ita ce ma ta shigo da ni falon sannan ta bace. Ku fadawa iyayena da mijina su yafe min. Sharifah so take ta tafi da ni. Ni kadai n
ake ganinta."
Su ka gwale idanuwa yayin da suka fara waiwayen sama da qasa a tsorace, tabbas sun fara gasgata maganata.
Maryam Auwal ta ce " shin ina qanin nan na ta da muka shigo tare da shi har muka yi masa gaisuwa a qofar gida?"
Na zabura na c
e "ciki ya shigo amma ba a ganshi ba, ku zo mu fita daga gidan nan."
Jikina babu kwari haka suka rirriqe ni muka fito farfajiyar gidan, abin mamaki qofar get a datse. Idan Shariah mutum ce data tunkudo ni falo ta fita ai da an ga get a bude dan haka bat
a fita ba, tana cikin gidan ko kuma koda yake ina uwan fatalwa ma da kofa?"
Anan su ka tsinto min takalma da mayafina suka bani na qi karba na ce su bar ni. Me gawa zata yi da takalma kuma.
Nanah tayi-tayi ta zare sakata ta kasa. Wata karamar qofa na
hango wacce a baya ban santa ba. An huda katangar. Ban yi wata-wata ba na afka, dan na ga alamar zata iya kai mu waje, sai su ma suka biyo ni.
Karamin yaro ne a tsugunne a gabanmu yana wasa, sanye yake da farin wando gajere boxers da farar shima.
Na daka tsalle na ja baya dan da ya waiwayo fuskar Sharifah ce, ba ni kadai ba sauran ma sun razana.
Mu ka daka tsalle muka rungume juna. Farfajiyar tsakar gidan a cike take da datti, ganyen bishiyoyi da suka fado suka bushe in abin a kwashe ne zasu kai
cikin mota tirela, in da za ka tabbatar an dade baa yi shara ba, kura kuwa ma baa magana.
Ba mu tambaye shi ba ya ce "mamana ta ce in kun fito ku bi ta wannan get din."
Ya nuna mana wani get na daban.
Ramatu ta zabura ta tambaya ta ce "wacece mamar
ka, tana ina?"
Na toshe bakinta na wawuri hannunta na ce "ina ke ina tambayar mamarsa bayan amsar a bayyane take. Ku zo mu yi ta kanmu."
Yaro ya bi lungu da gudu ba mu sake hango shi ba. Yayin da mu ka ware injin qafafuwanmu muka fita da gudu ta ciki
n wannan get din da ya nuna mana. Sai gamu a gaban motocinmu. Motar Bello bata nan, Babu maganar tsayawa bayani ban san ma motar wacce na shiga ba a cikinsu.Kowa ma salati yake yana neman yadda zai ceto rayuwarsa.
Daidai kan kwanar layin na yi ido hudu
da su, ga Sharifah, ga Hamidah, ga yara 'yan makaranta nan guda biyar sanye da kayan makarantar islamiyya har da Sharifah.
Su ka bi mu da kallo kuwa har muka shude. Ni da Ramatu ne a motar duk da hankalinta na kan tuqi amma ta kalle su . Ba na so in fa
ra yin magana dan ko na yi ba ta masu hankali ba ce. Na fi son ta fada da bakinta.
Ramatu ta zazzare ido ta ce "kai ga wata mata mai shigen kama da Sharifah ta na kallonmu."
Na zabura na ce "Alhamdulullah na gode Allah da ke ma kika fara ganinsu. Sh
arifah ce fa fatalwa take yi min."
" Fatalwa kamar yaya? Daman akwai fatalwa? Haba Samha kamar wacce ba ki je makaranta ba? May be yayarta ce, kin san su na da yawa a gidan kuma kusan kamarsu daya su dukka."
Bello muka gani a bakin titi yana sanye da
fararen kaya ba kayan dazu ba ne a zaune a kan motarsa shi kadai. Sai yau kamanninsa da Sharifah ya sake bayyana, shima ya tsura min ido yana kallona ina kallonsa. Daga
dukkan alamu Ramatu bata gan shi ba hankalinta yayi titi wajen tsallakowa.
Ni na s
an ba Bello ba ne Sharifah ce take canja launi.
Kaina babu dankwali qawayena sunyi-sunyi in daura na kasa. Na dora hannu aka ina salati ina kuka. Yayin da Rsmatu ta kasa gane wannan lamari domin a ganinta damuwar ta yi yawa.
Ta ce da ni " wai ke samh
a menene damuwarki? Sharifah bata mutu ba tunda ga gidan babu kowa ma."
Na zabura na ce "babu kowa kamar yaya? Fatalwar da suke ciki fa? Na ga Sharifah da idanuwana har ta fisgo ni ta danna ni a cikin falo sannan ta bace.
Yaron da muka gani ma fatal
wa ce, Bello ma fatalwa ne, ga Hamidah da sauran yaran. Ke ma da idanuwanki kin ga Sharifah yanzu "
Ramatu ta girgiza kai ta ce "ban ga Sharifah ba na ga dai mai shigenta. Sharifah fara 'yar gayu, wannan ai ko a mai aikinta ba zata dauke taba. Sai dai k
o yayarta ko cousin su na kama dai."
Shikenan abinda nake gudu ya faru, babu me yarda da ni, basa ganin abinda nake gani. Hauka ta tabbata a kaina.
Na fara tunanin asibitin mahaukatan da zan zabawa kaina na private amma dan kada a kai ni asibitin da
wanau. In hadu da masu yin ta gasken su lahanta ni. Abin sai ya yi min yawa ai kuma.
HIRA DA MATATTU.....5
Mun isa gidan Nanah kowacce kanta ya daure amma abin mamaki ba su razana da yawa ba, kamar yadda na razana dan ba sa ganin abinda nake gani.
Sun yarda da cewa ni ce ban fahimta ba amma Sharifah bata mutu ba kuma ma bata qasar tunda ga gidan nan alama ta nuna an dade babu kowa. Wataqila kanin nan na ta ne kadai a gidan da suka gani qofar gidan wato Bello shi kuma baya kula da tsaftar gidan shi
ne kawai.
Na tabbatar da zarar na ci gaba da yin musu zasu dauke ni zautatcciya, dan haka yin shiru ya fiye min alkhairi.
Bayan an jajanta sai kowacce ta fara shirin komawa gida dan magruba ta yi. Mun fi kusa da Maryam Alqali ta tambaye ni ko zan taf
i ta rage min hanya?
Ina tsoron komawa gidanmu dan zan hadu da fushin mahaifiyata da yayyayena ga mijina baya gari. Na manta ranar ma da ya ce min zai dawo.
Na bar wayata a gida dan haka sai na amshi wayar Nanah na kira number Mamana. Tana jin murya
ta yi ajiyar zuciyar jin dadi, gami da sauke haushin da ta dade tana ji, ta balbale ni da fada.
Ta ce ina na tafi ga mijina ya dawo a gari tunda rana, na bar waya na fita ba da izinin kowa ba.
Na fara yi mata bayani akan rasuwar Sharifah, daman ka
lmar da take so ta ji kenan na kira wato aljana sharifar da na yi gamo da ita. Mama ta manta gaba daya da babbar qawata Sharifah ita a dole aljana ce mai suna Sharifah ta shige ni.
Ai kuwa ta hada da ni da aljanna Sharifar ta cukuikuya ta nannarka mana
zagi. Ta ce ko in dawo gida ko ta zo gidan Nanah ta suburbude ni.
Hawaye ya cika min ido na ce "shikenan Mama tunda kin ce haka Allah Ya sa ki ga abinda nake gani za ki daina zagina."
Ta ce " babu ruwana da wata Sharifah, ko na ganta ubanta zan ci
ni."
Jikina a sanyaye na tashi tsaye, hannuna na rawa na daura dankwalina da mayafi na fito tsaf kamar mai hankali na bi maryam Alqali ta sauke ni a gida.
Tun daga qofar gida nake cin karo da hararar yayyaena. Na yi sum-sum-sum na shige gida. Anan
na ci karo da fadan Mama.
Maganar gaskiya da wannan tashin hankalin na gidanmu gara in tafi gidana ko ni kadai ce in zauna saboda zan fi samun 'yanci ihu da guje-guje. Amma anan da me zan ji ga zagi ga harara ga rukiyya.
Na harhada komatsaina zan n
ufi qofar gida, Mama ta ce "ga mukullin motarki fa."
Na ce "ina ruwan gawa da tuqi kuma? Mama ki dauki motar na bar miki."
Eh tabbas komai ya bayyana sai Mama ta sa qannena su riqo ni, domin ta tabbatar babu lafiya.
Na ga an zo an cicvibe ni an
dawo dani falo, kan ka ce kwabo an fara yi min karatu da tofi.
Maganar gaskiya gara ma in daina nunawa kowa halin da nake ciki dan ba zasu fahimta ba sai dai ma in sake jawowa kaina ukuba.
Aka kira mijina a waya aka sanar masa ya zo ya tafi da ni, s
annan ya ji bayanai akan ciwona.
Nayi-nayi kada su fada masa komai ni lafiyata kalau dan na san kawai ajina zasu zubar a gaban mijin, wanda yake ganina wayayyi kuma mai ilimi. Idan ya ji ina maganar fatalwa ba ma aljanu da aka fi yarda da su ba tabbas a
jina ma zai zube.
Ya zo a gigice abin mamaki sai