Showing 6001 words to 9000 words out of 65015 words
suka ga na warware na tare shi da murna na ce mu tafi gida daman motata ce ta sami matsala nake so ya zo ya tafi da ni.
Mama in zata yi magana sai in yi sauri in katse ta, nan da nan na ja shi da saur
i muka fita.
Mu na fita ina jiyo muryar Mama ta barke da kuka ta na cewa " babu sauran Samha. Samhata ta zare."
Mun isa gidana tare mijina Aliyu, amma yana ta jero min tambayoyi akan yadda na fita ba tare da na fadawa kowa ba. Ya san ba halina ba n
e.
Nan fa na dinga tsara shi har ya amince dan shi ya yarda da tarbiyya da riqon addina.
Babu walwala a tare da ni sai dai ina ta boyewa, daga na tuna Sharifa da muqarrbabanta sai in ji duniyar ta koma min up-side down.
Bayan na yi wanka na nuts
u, Aliyu ya fita ya siyo mana abinci kala-kala. Bawan Allah tunda ya ga ban dafa abinci ba ya tabbatar bani da lafiya.
Ga yunwa ina ji kwanana biyu ban ci abincin kirki ba kuwa. Na samu na danqari kazar nan sosai na qoshi.
Sai na fara dawowa daidai.
Amma duk da haka bana gane wasu daga cikin hirarrakinsa. Daman shi mutum ne mai yawan tunawa da mutuwa da maganar kowa ya shirya duniya ba matabbata ba ce.
Na gyara zama na fara jeho masa tambayoyi akan MATATTU da kuma yadda rayuwa bayan mutuwa take. A
dukkan bayanansa babu in da ya ce matattacce yana dawowa duniya ayi ta artabu da shi kamar yadda nake fama da Sharifah.
Na ce masa meya sani game da fatalwa? Ya tabbatar min akwai aljanu da su kan iya yin shigar mamaci dan su tsorata bil'adama.
Na
yi shiru ina kallon talabijin tabbas ko a cikin talabijin din idanuwana na nuna min mai kama da Sharifah.
Na zabura na ce "Aliyu mayar min da wannan tashar ta larabawa ko turawa."
Ya dube ni ya ce " Hausa fim ne fa, series dinki da kike bi."
Na
tashi da sauri na shige daki dan ni na san abinda na gani, kafin in fara baza hali a gabansa har ya fahimta toh gara in matsa.
Biro da littafi na dauko na rubuta kakaf masu bi na bashi da wadanda nake bi bashi. Da wadannan na munana na nemi su yafe min
.
Sannan na basu labarin ciwon ajalin da zai kashe ni kada su ji na mutu su zaci mutuwar fuju'a na yi, A 'a sam na yi jinya mai wuyar gaske wato artabu da fatalwa, da irin wannan jinyar ai gara cutar qanjamau.
"Me kike rubutawa ne?" Aliyu ne ya tamb
aya.
Ya yi mamaki da ya ga na zabura na wargaje biro da littafi kowanne ya kama gabansa, alhali a hankali yayi magana.
Na yi sauri na dauke littafin na boye, yayi-yayi in bashi ya gani na ce lissafina ne na masu pre-order kaya.
Ya nemi ya ji yaya
muka yi da alqalin da Yaya Anas ya hada ni da shi, wacce shawara ya bayar?
Oho na ma manta komai kuma na rasa amsar da zan bashi.
Duk hirar da ya dauko sai ya ga hankalina baya kai, ya ce in sha panadol in kwanta ko zazzabin ne. Na bar shi a daki na
fito falo dan dauko maganin da yace in sha .
Wayata ce a caji kasancewar a silent take ashe ana ta kira.
Na duba da sauri na ga bakuwar lamba ce bani da ita a cikin garin sunayen mutanena. Na amsa da sauri bana tantama na san daya daga cikin qawayena
ne suke kira dan su na so su ji yaya na isa gida, kuma yaya jikina.
Wata murya na ji wacce ta yi min kama da muryar da ta fi kowacce murya a doron qasa munin sauraronta, wato muryar Sharifah.
Tabbas bayan na yi sallama aka amsa sai na dafe qirji tun
kafin ta gabatar min da kanta.
Muryar ta ce " Samha Sunana Sharifah Nasir, ina so ki rufa min asiri ki......."
Daga wannan kalmar na fita hayyacina na saki wayar ta fadi ta fashe yayin da nima na fadi na fashe a gefe daya. Ina kyautata zaton suma
ne..
Na ganni akan kujera maimakon a qasa sannan kuma Aliyu yana yi min firgita yana yayyafa min ruwa.
Ina farkawa na yi salati na tambaya na ce "ina Sharifah?"
Ya ce "wacece haka?"
Na sake cewa "ina wayata?" Ya nuna min ita a qasa gami da cew
a " wayar ta fashe."
Na ce " Alhamdulullah gara da ta fashe dan na hakura da riqe waya har abada."
Ya tambaya "me yasa?"
Na ce "baa amfani da a waya a lahira ai."
Ya gyada kai ya ce " tabbas amma ke a duniya kike ai."
Na fashe da kuka mai tsanani.
Wannan karon Aliyu ya sake shiga damuwa, ya shiga tambayata in fada masa yanayin ciwon nawa dan ya san asibitin da zai kaini.
Na ce "idan akwai garin da idan mutum ya mutu kafin ya isa lahira yake rayuwa bayan mutuwa can zaa a kai ni. Wannan karon da
sauri ya miqe ya ja da baya yana kallona.
Ya fada a bayyane "ya kamata in kira Mama na fara tunanin daman akwai abinda Mama take so ta fada min amma kika hana."
Dan haka ya jawo wayarsa da sauri zai kira Mama na zabura na fusge wayar na hana shi. Na
tabbatar masa da lafiyata kalau.
Haka muka kwana ina zabura ina haurawa daga gefen hannunsa hagu in dawo gefensa na dama.
Maganar Sharifah ke dawo min a kunnuwana da ta ce in rufa mata asiri. Asirin me take so in rufa mata ne? Amma ni ta tona min n
awa asirin. Ina zamana lafiya ada yanzu gashi ta haukata ni.
Aliyu dai duk inda na haura sai ya yi addu'a ya toho min, ya ci gaba da barci dan ya gaji.
Barci barawo sai da ya sace ni amma fa mafarkin dai na ta ne, da ita da alqalinta. Wannan karon ha
r da qanjnta Bello.
Hasbunal lahu wa ni'imal wakil. Na ganni a tsakiyarsu ana walima. Wannan wacce irin masifa ce walima da matattu???
Madalla da ALQALAMIN JUT
To be continued....
HIRA DA MATATTU ...6
NA
JAMILA UMAR TANKO
JUT
Gari ya waye dakyar saboda ni a wajena dogon dare ne, sai a lokacin Aliyu yake fada min abokansa zasu zo su cin abincin rana a gidan nan. Sannan su tattauna akan tafiyar da yayi, daman tafiyar akan kasuwancinsu ne.
Ya san na
san abincin da ya kamata in hada, ya yarda da ni sosai a bangaren girki. Ya bani kudi mai yawa kafin ya fita ya ce in dauki motarsa in je cefane shi zai je gidanmu ya dauko tawa a gyara ya fita da ita.
Na zabura a gigice na ce ya tafi da motarsa ba sa
i ya je gidanmu ba, ni zan sa Yunus kanina ya dauko min ya kawo min. Saboda bana so ya je su hadu da Mamana ta fayyace masa labarin zautuwata.
Ya amince zai fita da motarsa, yayin da na ce ya jira ni in yi wanka mu fita tare sai ya sauke ni a gidanmu, d
an tsoron gidan nan nake a zahiri. Ya amince ya jira ni na shirya muka fito tare.
A gidanmu ya ajiye ni na shiga ciki shi kuma ya wuce, anan na roki Mama kada ta fada masa wannan larurar ta wa, na karanto mata illar da zai haifar idan danginsa suka ji l
abarin bani da hankali. Daman ga tsanar da suka yi min ana ce wa bana haihuwa ya qi ya kara aure.
Nan da nan Mama ta amince bayan ta hada ni da jarkoki cike da rubutun qur'ani mai girma da ta sa malaman unguwa suka yi min. Haka na yi ta sha
a gabanta d
an a zauna lafiya amma fa na san ciwona ba rubutun aljanu yake bukata ba.
Na sanar mata wayata ta fashe kada ma su neme ni idan ina nemansu zan kira da ta Aliyu. Mama ta bi ni da kallo ta san haukar ce ta fada min ba daidai ba na fasa wayar.
Na dauk
i kanwata Samira dan ta raka ni kasuwa don yin cefane. Mun Shiga kasuwar danyen kaya muna siyayya sai anjima na fara warwarewa dan ina tsakiyar 'yan uwana Bil'adama.
Bello Nasir na gani wannan karon ya qi yarda mu hada ido, cikin mutane ma ya kutsa ya
bace. Ni na san ba shi ba ne Sharifah ce, ni dai tunda na ganshi gabana yake faruwa na manta abin da ya kawo mu kasuwar ma.
Samira ta lura da haka ta fara jero min tambayoyin da na kasa amsawa, jikina ya dauki rawa sai na koma cikin mota na zauna, na
ce ta karasa cefanen kawai .
Motata na kusa da ta Bello abin mamaki hannunsa babu komai ya zo ya zauna a motarsa ya kalle ni na kalle shi sannan ya kunna mota ya tafi.
Na fashe da kuka ina fadin "wai Sharifah menene haka? Me na yi miki ne? Me kike
so ki fada min? Yaushe na tona miki asiri da kike so na rufa miki? Na gaji da rayuwar, ki zo ki dauke ni kawai mu tafi duniyar MATATTU in huta."
Samira ce ta girgiza ni ta ce "Aunty lafiya kike surutai ke kadai?"
Sai a lokacin na dawo hayyacina, ta
ga alamar ba zan iya tuqi ba sai ita ta tuqa mu tafi gidana.
Ina fada mata yadda zata yi har ta dafa abincin, dan ni babu abinda zan iya yi kuma. Ina zaune shiru ina tunanin yadda HIRA tsakanina da MATATTU ta ke kasancewa.
Ko kwano Samira ta taba sa
i na firgita hakan ma ya sa na koma cikin daki na saka karamar riga marar nauyi dan komai nauyi yake yi min. Na saki labule daki yayi duhu na shiga bargo na kwanta, sannann na runtse idanuwa amma ba barci ba ne.
Wayar da ya kamata in kunna karatun qur'
ani ta fashe dan haka na ci gaba da addu"oin da na haddace ta neman kariya, ga barci ina ji amma na gagara yi.
Samira ta kammala komai ta jere akan dining table ta na sauri ta yi wanka dan tanada lectures a BUK har ma ta makara. Na bata kudi na ce ta ha
u mota. Na yi mata godiya ta tafi.
Barci ya fara daukana na jiyo muryar maza a falona na zabura na tashi na zauna. Aliyu ne da abokansa ashe. Ya shigo ya iske ni yana tambayata ko lafiya na ce lafiya kalau na gama yi musu komai. Ya jinjina min ya ce ai
sun ji kamshi tun daga bakin get.
Ya ce in fito mu gaisa da Nura da sauran abokansa, na ce bana jin dadi ya ce musu ina barci kawai.
Ya canja kaya ya fita wajen abokansa su na ta cin abinci su na hira da shewa, na ji dama ni ce su da suke rayuwa sa
k a doron duniya amma ni yanzu rayuwata rabi da rabi ce ina raye amma bana raye.
Ina zaune a duhu kamar mai gyangyadi kamar mai tunani. Aliyu ne ya leqo ya ce da ni kin yi bakuwa da alama ta gida ce. In ce ta shigo?
Dole ma ta shigo dan ba zan iya ta
shi in fita falo a cike da maza ba ina cikin wannan haki. Na ce masa " ka ce ta shigo."
Ta tura qofa ta shigo gami da matar da qofar ta rufe ina daga ido Sharifah na gani muraran wannan karon sanye take da jajayen kaya. Ban tabbatar ba sai da ta yi maga
na na gasgata murya. Ta ce "Assalamu alaikum wararahamatullah qawata Samha."
Na koma lummmm kan filo na fadi ina karkarwa yayin da na gagara runtse idanuwana. Ina kallonta tana kallona duk da duhun da dakin yake da shi akwai dan haske.
Ta zauna a
gefe na sannan ta gaishe ni ban iya amsawa ba.
Na yi karfin hali na ce "Ya Rabbil samawati ka dauki raina, dan kudirarKa da iradarKa, in huta wannan rayuwar duniya mai kunci.
Ta zabura ta ce " me kika sani game da kudira da irada ta Ubangiji? Aike
baki san komai ba ki tambaye ni. Ni za ki tambaya wanene Ubangiji sarki Allah."
Na gaskgata tabbas ta je in da ban je ba. Mu dukka magana muke cikin rada wanda idan akwai wasu a cikin dakin ma ba zasu jiyo abinda muke cewa ba.
Na fashe da kuka murya
ta na rawa na ce "ai sai ki bari in ga Azara'ilu nima in dandana dacin mutuwar da ake fada cewa kowanne rai sai dandana mutuwa kafin ki zakke min."
Ta ce " tabbas mutuwa tana da magagi Manzon Allah S.A.W ne da kansa ya fada. Amma na fi ki qaunar wannan
rana ranar da zan hadu da Mala'ikan mutuwata don babu abinda yake cikin duniya sai ukuba."
Wannan karon suma na yi dan ban san inda na tafi ba, na san dai na rasa hayyacina na wasu lokuta.
Sai gani na dawo fuskar Sharifa ce akan fuskata tana kallon
a.
Kalmar da na ji ta fada ita ce " Samha! idan za ki zo gidanmu ki zo ke kadai kada ki sake zuwa da su Nanah Ahmad, su ban yarda su ganni ba."
Hawaye na zuba yayin da ko yatsana bana iya dagawa, na ce da ita " me yasa sai ni? Laifin me na yi miki?
"
Ta yi murmushi ta ce "ke ce tawa. Mun fi kusa."
Sai na koma duniyar suma ban san tsawon lokacin da na dauka ba.
Na bude ido na ga Aliyu yayi sallama ya shigo, amma babu Sharifah babu dalilinta.
Ya ce " Ah bakuwar ta ki ta tafi ne?"
Na y
i magana cikin sanyin murya na ce " ba ka ga fitar ta ba ne kuma ka na falo?"
Ya girgiza kai ya ce "ban ga fitarta ba watakila hankalina na kan laptop lokacin da ta fita, kuma ma na shiga dakina neman wasu takardu. Za mu fita sai da yamma zan dawo."
Magana nake amma baya ji na, ina cewa "kada ka tafi ka bar ni ni kadai."
Amma ina bai ji ba sai ma ya jawo min qofa ya yi ya datse.
Sharifah ce ta bullo daga bandakina, na ji an bude kofar bandaki an fito na zabura na dube ta wannan karon kanta bab
u dankwali sai buyayan gashin nan ne a tsaye.
Na runtse ido ina karkarwa tamkar zan hadiye zuciya. Ta na bani labarin cewa alwalla ta yi ina ne gabas.
Ban san yadda na kwalla kara ba na ce " daman matacce yana yin sallah ne? Kin fi ni sanin gabas ai
."
Ta dawo ta zauna a kusa da ni ta sa hannu ta girgiza ni ta ce " Samha ! Na rantse da Ubangijin Ka'aba mutuwa ta fi rayuwar nan dadi."
Daga nan na tabbatar ta zo ta yaudare ni ne ta tafi da ni. Na amsa mata da "eh na shirya ki tafi da ni."
Sai
na koma duniyar suma daga nan na bude ido na ga tana sallah ban san wanda ya nuna mata gabas din ba kuma a daidai yake yi. Ta daga hannu sama tana addu'a a bayyane maganar dai ta neman tsari ce daga azabar kabari, da maganar Aljanna da neman tsari daga w
utar jahannama. Na amsa a zuciyata da Amin.
Sai ta dawo ta zauna a kusa da ni ta tsura min ido. Ta yi ajiyar zuciya ya ce " Samha! Mutane sun manta da mutuwa sun zabi kwadayi duniya alqalai babu adalci."
Na yi karfin hali na tambaya ina alqalin da
na gansu tare? Amsar da ta bani ta karkada ni matuqa sai ta ce da ni " Alqalin nan ya rasu, yau sadakar uku."
Na ce "daman can a mace yake."
Ta girgiza kai ta ce "shekaranjiya ya rasu."
Na ce "kin tafi da shi kenan? Shiyasa kika je kika cike mas
a form."
Na sake tambaya "ina Bello ta ce " Bello ya dade da rasuwa tsakaninsa da Shariaqa kwana hamsim da biyar."
Na ce "shiyasa duk inda na juya nake ganinsa?"
Ta tambaya cike da mamaki ta ce "daman kin san shi ne?"
Na ce "na ganshi a maf
arki sannan na ganshi a bayyane."
Na ce " na ce ina Shariqah?" Ta ce "ta rasu fiye da shekara guda yanzu."
Na sake cewa " Ina Sharifah kuma?"
Sai ta kwashe da dariya ta ce " ga Sharifah nan a gabanki kina magana da ita."
Ta yi cimak ta miqe
tsaye ta ce da ni "sakon da na zo in isar kenan bana so kowa ya ganni a wannan hali sai ke kadai ki daina gayyato min kowa kuma na ga alamar baki da lafiya na zo miki da wasu labarai masu girma ne, amma idan kin ji sauki ki zo ina nemanki idan baki zo ba m
a ninzan zo. Su Nanah na hanya zasu kawo miki ziyara bari in tafi bana so su ganni. Bissalam."
Da juya bayanta da suma ta dukka a lokaci guda ne, ban sani ba ko ta kofa ta fita ko