Showing 18001 words to 21000 words out of 65015 words
a cikin kabarinsa.
Shi
n mamaci yana sanin labaran rayayyu da abubuwan da suke gudana game da rayayyu? Ya na gane wadanda suka ziyarci kabarinsa? Shin wanda ya mutu yana gane wadanda ke yi masa addu'a?
Magana ma fi tabbata shine Matattu a cikin kabarurrukansu su na jin raya
yyun da suke cikin duniya kamar yadda Bukari ya fitar da shi wanda aka karbo daga Abdullahi bin Umar (R.A) cewa Manzon Allah S.A.W ya tsaya akan 'kalili badar' wata rijiya ce bayan an karkashe su abu Jahil, su abu lahab aka tattara su aka jefa su a cikin r
ijiyar. Manzon Allah S.A.W ya ce da su "shin kun sami abinda Ubangijinku yayi muku alqawari na gaskiya? Hakikaqa su a yanzu su na jin abinda nake fada. Aka ambaci Nana Aisha ( R.A) sai ta ce Manzon Allah S.A.W ya ce "Hakika su a yanzu wadannan kafuran Mak
ka na quraishawa sun san cewa yanzu abinda da nake fada musu gaskiya ne. Sannan sai ta karanta wannan aya.
Daga cikin zance mafi tabbata shine matattu su na jin rayayyu na duniya, yadda suke ji ne babu wanda ya san wannan tafiyar sai Allah.
Idan ak
a ziyarci mamaci a makabarta aka yi masa sallama yana ji kuma yana gane wanda ya ziyarci shi, duk da dai anan baa kawo wani nafsi ko hadisi ba. Ko da an yi masa kabari ko baa yi masa kabari ba, ko wanda ya kone, ko wadanda namun daji suka cinye shi. Abinda
yake tabbatar da haka shine Hadisin da Manzon Allah S.A.W ya ce idan aka binne mamaci bayan an saka shi a kabari yana jin takun takalman wadanda suka binne shi.
Akwai wasu hadisai da suke cewa tabbas mamaci yana jin wasu maganganu na rayayyu tunda Manz
on Allah S.A.W ya je wajen Rijiyar nan yayi musu magana ya nuna su na jinsa.
Haqiqa mamaci yana jin abinda yake dangane da rayuwar lahira na daukaka darajojinsa da kuma kara masa kyawawan aiki da kuma irin addu'oi da sadakar da iyalansa suke yi masa b
ayan mutuwarsa. Amma abinda yake gudana da rayuwar rayayyu, kamar daga cikin rayuwar aure da wasunsu daga cikin abubuwan rayuwar duniya, babu wani hadisi ingantacce da ya nuna haka cewa matacce yana sanin abinda yake faruwa a duniya.
Domin shi mamaci y
a shagala ne da rayuwarsa ta lahira, babu abinda yake da muhimmanci a gare shi sai wani abu da yake da alaka da lada wanda zai amfanar da shi dan tsirarsa a lahira amma ba rudin duniya ba."
Toh su ma su Aliyu a iya zurfin neman iliminsu wannan karatun s
uka sani.
Dan haka suka yi 'dimmmm' su ka yi shiru, har sai da Malam ya fuskanci akwai damuwa.
Ya takura da jero musu tambayoyi kala-kala. Daga karshe suka bashi labarin Sharifah kakaf da abubuwan da suka gani kuma suka ji.
"Tunda babu fatalwa a
duniya Sharifah da maqarrabanta kuma su menene kenan?"
Malam ya basu amsa game da tabbacin cewa " Sharifah da makarrabanta wani abu ne daban amma tabbas babu fatalwa a duniya. Mamaci baya taba mutuwa kuma ya taso ya fito ya shigo duniya. Akwai rayuwa ba
yan mutu amma a barzahu kamar yadda addini ya ambata."
*** *** ***
La'asar sakaliya Nanah Ahmad ce take nishadi ita da yaranta a cikin farfajiyar gidanta, su na bawa korayen filawoyi ruwa da mesar ruwa.
Su na waqe-waqensu, wasu har su
na rawa su na tafawa.
Mace suka gani a gabansu ta yi musu sallama ba tare da sun ga daga inda ta diro ba.
Nanah na daga ido ta dube ta, Sharifa Nasir ta gani sanye da baqar abaya baqa, shigar baqaqen kaya ta yi daga sama har qasanta, tana yi mata m
urmushi.
Sai da zuciyarta ta kai qololuwar tashi sama sannan ya fado fafat dan fargaba.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" Nanah ta fada.
Ba ta yi wata-wata ba ta wurgar da Mesa ta bawa qafafuwanta hakkinsu. Ta manta ma ta taba haihuwa ta kanta kaw
ai take yi. Dankwaleliyar kaza ta zura da gudu, ta yaya 'yan tsaki za su tsaya? Sai su ma yara suka bi bayanta a guje.
Ga Nanah shirgegiyar mace ce mai qiba, wataran dakyar take tashi amma a wannan lokaci ko yaro dan shekara goma ba zai tsere mata ba.
Gudu suke RAF-RAF-RAF yara na kuka su na kiran "Mamah ki jira mu."
Amma ina! Yau babu wannan zance na tausayawa jarirai da uwa ta saba yi.
Jikin katanga ta nufa, tayi-tayi ta kama ta haura amma ta kasa, saboda tsayin katangar da santsi. Ta ciccib
i yaro daya karamin da zunmar ta wurga shi wajen katanga, nan ma ta kasa. Ba tare da ta yi tunanin idan ta wurga shi zai iya fashewa ba.
Ta rasa yadda za ta yi, ta na waiwayawa Sharifah ta sake gani a tsaye cak tana kallonsu. Wato ku gama gudun ina ji
ranku.
Su ka sake fafara da gudu suka yi wani bangaren, dakyar dai su ka lalubo inda get yake suka fice da gudu, mai gadi baya nan ya tafi bakin titi yawo.
Gidan makwabta suka fada a guje, a gigice tana karkarwa.
Sun jima su na yi mata firfita kaf
in ta dawo hayyacinta ta basu labarin abinda take tunanin ta gani wato fatalwar Sharifah.
Wannan kalma ta fatalwa ta basu matuqar mamaki. Ba su taba sanin ana fatalwa ba sai yanzu.
Ta nemi da su bata aron waya ta kira Samha dan Samha ce kadai zata
gane wannan yare.
Samha tana amsa wayar sai ta ji muryar Nana a gigice, nan da nan gabata ya fadi. Nanah fadi take " Sharifah nima ta fara bibiyata ta zo gidana da baqaqen kaya tana yi min dariya."
Samha zabura ta dauki salati yayin da mama ma ta
zabura ta ta batar maganar gizo bata wuce ta koki Sharifah ta canja salo kuma.
Ai da Samha ta bawa Nanah labarin abinda ya faru da su a asibiti sai Nanah ta karasa rudewa. A yanzu ta gasgata Sharifah ta rasu ta dawo tana bibiyarsu daya bayan daya. Ko me
take nema a wajensu oho??
Maqwabta dai ba su yarda akwai fatalwa a duniya ba, dan haka maza aka samo suka dauko makamai su ka Shiga gidan Nanah a bincika ko ina babu Sharifah babu alamunta. Daman zaman jiransu za ta zauna yi? Tab.
Talla
! Talla!! Talla!!!
Na kwance bai ga gari ba sai ya miqe. Magani a gonar yaro amma bai sani ba.
Azumi ya qarato dan haka mu yi yaqi da cutar gyambon ciki dan mu samu mu yi ibada yadda ya kamata.
Ko kun sannan
👇🏻👇🏻👇🏻
BANAAT INSTITUTE
Ulcer me
dication
MU YI YAQI DA CUTAR ULCER. KADA KA BARI CUTAR ULCER TA CINYE LAFIYAR JIKINKI/KA
GAME DA MAGANIN:
Wannan maganin an kirkiro shi daga zababbun itatuwa da saiwoyi (herbals/Roots) da suke inganta lafiya.
An kirkiro shi daga zuma wacce take
gyarawa ta warkar da gyambo ciki. An gwada an tabbatar yana kashe kwayar cutar ne gaba daya ba kwantar da cutar yake yi ba, yana kashe ta ne har abada cikin ikon Allah.
DALILIN DA YA SA ZA KA BUKACI WANNAN MAGANIN SHINE:
*Ya na kashe cutar gaba daya.
*Ba shi da wata illa (side effect).
*Kowa zai iya amfani da shi yara, manya, maza da mata, mai shayarwa da mai ciki.
*Babu daci sannan zaqinsa natural ne.
*An tsabtace shi babu datti.
FARASHI:
400ml 8,000
700ml 15,000
1200ml 22,000
Contact no:
09092969299
Ana iya turawa zuwa kowacce Jaha a fadin kasar nan.
Marmaza ku garzayo ku karbi na ku. Ko da kudinka sai da rabonka.
HIRA DA MATATTU...11
NA
JAMILA UMAR TANKO
JUT
Ga Malam zai tafi Umra a dar
en yana ta shiri, dan haka ba zai sami damar amsa kiran da suka yi masa ba na cewa ya zo su je gidan Sharifah ya gani da idanuwansa ba.
Tirqashi! Malam kuwa zai doshi wata guda acan kafin ya dawo. A haka su ka taso jiki a sanyaye har suka iso gida.
Anas da Aliyu sun zaunar da Mama da Samha sun yi musu dukkan bayanan da Malam Babba ya yi musu game da fatalwa da tabbacin babu fatalwa a duniya dan haka su cire tsoron Sharifah a zuciyarsu su saka a ransu bata isa ta cutar da su ba, Allah S.W.A Ya fi ta.
A dukufa da addu'a kawai koma
wacece ko menene Sharifah Allah Ya fi ta. Kuma sun yi alqawari ba zasu gaji da bibiya ba har sai sun binciko abinda yake faruwa da bayyanar Sharifah.
Da alama Mama da Samha kansu ya daure matuqa. Tambayar da suke yi ita ce
"in har babu fatalwa a duniya, toh Sharifah aljana ce ko mecece?
Samha ta zabura ta na rusa kuka mai zubar da hawayen takaici, ta yi magana cikin fusata da kakkausar murya, sannan ta yi rantsuwa da Ubagijin da ya bus mata mata numfashi ta ce ita fa t
ana ganin Sharifah a wani launi wanda ba na bil'adama ba.
Aliyu da Anas sun gasgata kuma sun tabbatar mata da cewa su ma sun ga wasu abubuwa da idanuwansu game da Sharifah a lokacin da suka je gidan, wanda ba normal ba ne. Sun tabbatar mata a yanzu basu
dauke ta me shirme ba, kuma ba basu dauke ta marar hankali ba. Dan haka ta kwantar da hankalinta su na tare da ita dari bisa dari.
Sannan kuma maganar Sharifah da ta tayar mata da hankali na game da abinda yake cikinta ko ba mutum ba ne fatalwa ce ta
cire a ranta. Cikinta na nan daram kuma mutum zata haifa babu fatalwa a duniya sannan Sharifa bata isa ta yi komai ba.
Mama ta rasa ma abinda zata ce saboda kanta ya daure, tunda ake yayin aljanu ana faduwa, su na yara su na zuwa kallon garaya, 'yan bor
i masu kiran aljanu Allah bai sa ta taba yin gamo da aljanna ba, ta ganta kiri-kiri da hasken fitila sai akan Sharifah. Ga ta quru-quru su na hada ido tana mata magana tana ji.
Aliyu da Samha suka isa gida kansu a cushe, ga tsoro, ga haushi, dan wannan
karon su dukka sun hasala musamman akan cikin da aka dade ana addu'a ana nema ga shi ya samu kuma ya zo a wata kalar. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun suke karantawa kawai.
Samha ta rushe da kuka ta ce "ada na fi kowa son Sharifah a raina, bana son kom
ai ya taba ta, duk wanda ya batawa Sharifah kamar ni ya taba, sai in hau gaba da shi. Amma a yanzu bani da maqiya a duniya irin Sharifah, kuma na rantse da Allah ko ta ga bayana ko in ga bayanta, yanzu na daina gudu, na daina razana, na daina sarewa. Me na
yi mata? A lokacin da ta ja baya da kowa duk yadda zan yi in lalubo lamboninta na yi, ko ta canja lamba sai na nemo ta. A Facebook, a Whatsapp duk mu na chating. Har gidan Shariqah nake tashi in je dan in sami lambar Sharifah daga baya ma Shariqah ta tas
hi daga gidan da na sani na gaji na rabu da ita. Toh menene laifina? A iya sanina bana cikin maqiyan Sharifah da za ta addabe ni bayan ta shude."
Aliyu dai hakuri yake bata, sai kwantar mata da hankali yake dan baya so ranta ya baci da yawa ta baro masa
da cikin da ya dade yana nema. Ya ji dadin Jarumta da qarfin zuciyar da Samha ta fara samu, ta fara cire tsoron Sharifah.
Cikin ikon Allah a cikin satin ne sauran qawayen samba su ukun nan da suka je tare gidan Sharifah suka karbi bakuncin Sharifah. W
ato Rukayya, Maryam da Dijah daman Nanah ta dade da karba.
Dukka dai baa wanye lafiya ba,an sha gumurzun guje- guje da haure-haure. Wadanda ta kutsa musu daki ne ta iske su a kwance sun kasa motsi, su ta isarwa da sakon da take so ta isar zuwa Samha. C
ewa ita ba ta zo wajenta dan ta cutar da ita ba, ta na zuwa wajenta ne dan ta isar mata da wani saqo kuma ta bata labarinta a matsayinta na tsohuwar aminiyarta ta tun quruciya. Amma ta fuskanci Samha na tsoronta ta na gudunta, tana shidewa da suma idan ta
ganta.
Ta yi alqawari ta daina nemanta kuma su ma kowa ma ba zai sake ganinta ba har abada. Ba ta so a ita ma a takura ma ta ana bin ta har gida. Kowa ya zauna a matsayinsa. Bissalam.
Saqo ya iso kunnuwan Samha dan duk wanda ya ga Sharifah, ta na ba
cewa Samha ake fara kira a waya a shaida mata aminiyarta ta kawo musu ziyara su ma.
"Tsarki da yabo sun tabbata a ga Ubangijin Sharifah. Shin wacece Sharifih a yanzu? Me Sharifah ta zama ne haka?" Tambayar da Samha ke yiwa kanta da kanta yayin da ta d
ora hannu akai ta kurma ihu, sannan daga bisani ta baje akan kafet ta na birgima.
Damuwar Samha ta yi yawa, tausayin Sharifah ne kuma ya kamata. Shin ta yaya zata iya tsaywa ta saurari matsalarta, ta ji abinda take so ta isar a gare ta? Ta ji ko za ta
iya ta taimaka mata? Amma ina tsoro ya hana, ba za ta iya tsayawa ba.
Akan wannan dalili ya sa Aliyu ya dakatar da tafiye-tafiye yana rainon dan cikinsa, dan kada Samha ta razana cikin ya zube.
Wajen sayayya da shaqatawa ya kaita wayo shoprite dan t
a shaqi iskar 'yanci kuma ta ga bil'adama 'yan uwanta.
Ya ce su je cikin babban shagon ta zabi duk abinda take so ta ci na makulashe da na cefanen gida. Za su Shiga cikin katafaren shagon ne ta ci karo da Sharifah su kuma su na fitowa.
Razanar da t
a yi ba dan Aliyu na kusa da ita ya dafe ta ba da sai ta fadi a qasa. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" su dukka suka fada yayin da suka yi tsalle gefe guda su ka kankame juna su na makerketa, da alama ya ga abinda ta gani. Shima a yanzu dai ta bude masa
ido ya ga Sharifah.
Ga Sharifah, ga Hamidah, ga Bello ga yara guda biyar su dukka takwas din nan kamarsu daya babu abinda ba iri daya ba.
Abin mamaki su dukka sun ci kwalliya da shiga mai kyan gaske. Wannan ita ce Sharifah ta asali dan ga kamannint
a nan tas ya bayyana na kyakykywar mace 'yar gayu, fara mai yawan ado. Ga kunshi ga kitso, ga wani dandashehen leshi mai tsadar gaske. Daman ita mace ce mai son saka takalmi mai tudu (high hill). Hamidah ma ta yi ado da riga da Wando irin na 'yan matan zam
ani masu kwalisa da suke tsakiyar ganiyar rawar kan an kusa candy. Yaran nan masu yawo tsamo- tsamo da jallabiya da kayan makaranta mazansu da matansu sun caba ado da kaya mai tsada. Wannan ba made in china ba ne sai dai made in UK ko USA.
" Me yake shi
rin faruwa ne Aliyu?" Samha ta fada a gigice.
Ta zabura za ta bi ta a baya ta yi mata magana, Aliyu ya damqo ta ya ce "kada ki sake jajubo mana ita, tunda bata ganmu ba ki yi kamar baki ganta ba kema. Kin manta saqon da ta bayar a baki cewa babu ke babu
ita? Ka da ki je wajenta ita ma ta daina zuwa?"
Samha ta fusge hannunta ta bi bayansu da gudu,kira take "Sharifah Nasir! Sharifah!!Hamidah!!! Bello!!!!
Amma ina a banza babu wanda ya waiwaya ya kalle ta.Ta tari gabansu tana ta kwalla kira cikin ikon
Allah basu ganta ba ma, balle du kalle ta. Surutunsu kawai suke su na tura manyan keken zuba kayan da suka ciko maqil da sayayya irin ta masu hali.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin Sammai da qassai. Aliyu ka ga Sharifah da iyalanta yau kuma su ne ba sa
ganina ni nake ganinsu."
Aliyu ya jawo ta dakyar ta daina binsu tabbas shi ma wannan abu ya daure masa kai. Sharifah ce fa gata nan kiri-kiri amma a yau ita ce bata ganinsu. Wannan abinda da me yayi kama kuma? Me kenan?
Samha ta fashe da kuka ta ce "
Aliyu ko dai mun mutu ne yanzu mu ne MATATTU baa ganinmu?"
Sai ya ji ya razana ya shiga tattaba jikinsa. Ya tambaya "shin ba yanzu muka tuqo mota mu ka shigo ba ne? Ta yaya za ki ce ko mun mutu kowa baya ganinmu?"
Ta zabura ta jawo hannun wata mata
a gigice ta ce "Hajiya ki na ganina kuwa?"
Matar ta tsaya tana kallonta ba tare da ta bata amsa ba ta wuce."
Su ka sake razana sannan su ka bazama yiwa jamaa magana dan su tabbatar ko ana ganinsu.
Sun tabbatar kowa yana ganinsu kuma yana jinsu
amma Sharifah da maqarrabanta ne kadai basa ganinsu.
Tabbas Sharifah da jamaarta ba mutane ba ne. Idan manyan cikinsu sun yi pretending sun ce ba sa ganinsu yaran dai ai zasu waiwayo, amma babu wanda ya kalle ta ko ya waiwayo har bayan ta tari gabansu
.
Samha da Aliyu su ka koma gidan Mama aka hadu har da Anas suka basu labarin wannan