Showing 54001 words to 57000 words out of 65015 words

Chapter 19 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

25

ciyar da yaran ko kadan. Sai da ya shekara bai ga yaran da idanuwansa ba, ya daina nemansu.

A wannan shekarar ni ce cinsu, ni ce shansu, suturarsu, ni ce s

chool fees dinsu islamiyya da boko. Ni ma na rabu da shi ban neme shi akan taimakon komai ba. Ko Bello ba ya taimaka min da ko sisi haka a dangina babu wanda ya taba dauko kwayar taliya daya ya bani ya ce in ciyar da su.

Amma fa ina zuwa gidajen

su in ganin irin kayan alatu da Adamu yake kai musu kyaututtuka amma yaransa ya qi ciyar da su. Manufar ita ce idan na ji wuya zan mayar masa su da kaina.

Amma ina? Ya manta ko su waye Sharifah da Shariqah ne? Ai yadda ba zan iya daukar Hamidah in

'yar da ita ba, ba zan taba iya daukar yaran Shariqah in zubar ba. Idan bara nake za mu yi tare mu ci abinci.Idan a titi nake kwana zamu kwana tare da su.

A wannan lokacin rigimar nan hankalin Shariqah a tashe yake, kusan kullum sai ta zo min.



Ina yawan ganinta wataran ta yi magana wataran ba ta yi amma tabbas ranta a bace yake, shari'ar nan da ake yi akan yaranta na damunta."

Samha ta maimaita " ranta a bace yake kuma? Shariqah da kika ce."

Sharifah ta yi murmushin qarfin hali ta

ce "kwarai kuwa, ba za ki gane abinda nake nufi ba ne, sai nan gaba. Hmmm Samha! Sai a wannan karon ne na tabbatar Sharifah ba ta da dangi, daga sama ta fado saboda babu mutum daya daga cikin dangin uwata da na ubana da ya dauko kwayar taliya daya ko shin

kafa kwano daya ya ce ki dafawa yara.

Ba na so in zobe ladana amma na yiwa dangina bauta, da jikina da dukiyata. Amma sai su ka yi kamar ma basu taba sanin mu na shari'a ba saboda ya toshe bakinsu da abin duniya. Ko mun hadu babu wanda zai yi min ma

ganar case dina da Adamu kuma ana hango shi a gidajensu ana zuwa ana fada min da duk abinda ya kai musu.

Wai mutumin da bai wadata gidansa ba shine yake bin dangina ya dinke bakunansu da abin duniya, yana ta rabo kai kace dan takarar gwamna ne.



Sun bani mamaki wannan abu ba zan taba mantawa da shi ba, shine na sake gasgatawa ka saki mutum ka kama Allah Shi kadai kawai saboda mutum mugun ice ne."

Samha ta yi tagumi ta ce "kaina fa ya daure, innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Da ma kin tabo

ni kawata sai ki ga bare ya taimake ka jininka bai taimake ba."

Sharifah ta gyada kai ta ce "daman na dade da sanin haka, yawanci duk abinda na zama a rayuwa ta hanyar bare ne ba dai dangina ba.

Amma na girgiza matuqa kawata, sai da aka zo b

abbar sallah lokacin da kowa yake yanka rago, wasu shanu wasu rakuma. Har ana gobe sallah ga ni da yara basu da aiki sai loqawa makwabta su na ganin raguna, su na dawowa da gudu su na bani labari. Mu a gidan babu ko kazar da zamu yanka kuma bani da kudi.

A daidai wannan lokaci kuma mahaifinsu yana can yana raba raguna kuma ma rabon a gidajen dangina yake rabawa, kowa yayi kulas babu wanda ya fada min ko ya labari, balle ma su tare shi su ce ya kamata a a kaiwa Sharifah da yaranka."

Sharifah ta

yi shiru ta sunkuyar da kai kasa dan radadin da zuciyarta ke yi.

Samha ta girgiza kai ta ce "an ci amanar zumunci. Wani irin zamani ya zo wai dan uwanka, jininka ne yake so ya ga ka tozarta. Yaya kika yi kuma?"

Sharifah ta dago ta kalli Samh

a ta yi murmushi ta ce "kin manta ina da Allah? Wanda Ya rike Allah babu shi babu cewa na shiga uku. Na yi addua cikin dare na roqi Allah Ya rufa min asiri kuma Ya bani yadda zan yi Alfarmar yaran nan ya fitar da ni kunya.

Na rantse da wanda Ya zabi

Annabi Muhammad S.A.W Ya fifita darajarsa fiye da ta dukkannin halitta. Alert din dubu dari na tashi na gani, na wani tsohon bashin tikitin da na ce miki na biya zan koma turai in dauko kayana aka rufe ko ina saboda Corona.

Kudin ya fi dubu dari uk

u na tambaya har na gaji dan shima an so a cinye min Allah Ya kwatar min wannan, ba dan komai ba sai dan Ya yi alqawari idan mu ka roqe Shi zai amsa mana."

Samha ta yi kabbara ta riqe hannun Sharifah ta jijjiga ta ce "na baki kambun jarumta, haka na

baki kambun wacce ta yi jahadi saboda zumunci. Allahu akbar duk kin shiga wannan tsanani ba dan jin dadin kanki, ba dan na 'yarki ba sai dan 'yaya 'yar uwarki saboda zumunci. Ba za ki wulaqanta ba in sha Allah. Nasara na tare da ke kawata."

Sharifah

ta gyada kai ta ce "na tashi da asuba na ga wannan kudi sai na yiwa Allah sujjada na yi maSa godiya banda Shi babu wanda Zai yi min haka.

Bayan mun je sallar idi mun dawo gida, akwai wani bawan Allah da muke mutunci da shi tun Mamana ta na raye m

uka saba da shi, a Makka yake zama da.

Shine ya zo da mota ya dauke mu ni da Hamidah mu ka tafi can hanyar Wudil kasuwannin kauye, lokacin raguna sun karya cikon kudi kadan na yi akan dubu farin nan na sami raguna guda biyu manya-manya.

M

u ka zo muka yanka yara su na ta murna, mu ka yi layya kamar kowanne gida. Abinda ya bani mamaki har aka yi sallah aka gama bubu wanda daga cikin dangina ya aiko min da tsokar nama ko kwaya daya tal. Ashe da ban yi layya ba babu me bani nama. Innalilahi w

a inna ilaihi rajuun."

Samha ta ce "ikon Allah. Amma na cika da mamaki. Tabbas ke din Jaruma ce dan ba kowacce mace ba ce zata iya daukar abinda kika dauka. Ke a maza ma ba kowanne namiji ba ne zai iya irin wannan tawakkalin ba. Kin rasa kowa daga

cikin makusantanki, sannan kowa ya juya miki baya. Yaya sharia ta kasance?

Sharifah ta yi dariya ta ce "sharia ta farko wato ta rabon gado an cire me sharia an kawo wani wannan shariar ai an ja ma ta layi sai ya bibiyi abinda aka yi a baya. Fiye da

wata shida bai waiwaye mu ba ma.

Ta biyu kuma da ya kai ni dan a kwace yara, ita wannan shari'a ai babu ita tunda an mayar da ita teburin sulhu, tare da wannan matar barista Aisata da na baki labari a baya, da aka ce ta yi mana sulhu.

Mu na

zuwa ni da lauyana shima da lauyansa amma fa sai mu yi zuwa uku su sai su ki zuwa dan ba haka suke so ba, su so suke a kwace yara a basu wanda ba zai yiwu ba kuma."

Samha ta ce " sannu kawata shari'a har guda biyu, ya maka ki a kotuna daban-daban."

Sharifah ta tabe baki ta ce "na fada miki waccan kotun da ya dauko gidana ya hada da na su ya ce dukka nata ne kuma an goyi da bayansa, har an saka ranar da zaa zartar da hukunci. Allah Ya yi ikonSa, kacokan aka dauke mai shariar aka kawo wani.



Dan haka nasarorin da Adamu ya hango ya fara samu kacokan sun juye, kai a kasa kafafuwa a sama. Haka duk abinda ya kashe ya yi asararsu.Dangina da suka ci kudinsa babu abinda zasu iya taimakonsa da shi. Ko sun sha giyar wake dai babu wanda ya isa ya zo

gabana ya zage ni balle ya fada min bakar magana akan riqon da nake yiwa 'yayan Shariqah.

Tunda dai su sun manta duk wahalar da ya bawa 'yar uwarsu, a haka kuma su ke bude baki su ce su na kaunarta.

Na yi addu'a Allah Ya tsare ni daga dariyar

makiya da mahassada. Allah Ya rufa min asiri kada in tozarta kuma har yanzu a haka nake, babu tozarci kullum asirina a rufe yake.

Hamidah da na haifa har ta gane tabbas Allah Ya na tare da ni a koda yaushe. Tun tana damuwa har ta daina idan na tash

i bani da kudi sai ta shiga damuwa ta tafi makaranta jikinta a sanyaye amma wallahi tana dawowa sai ta bude wayata ta duba ko tantama babu zata ga kudi an turo min.

Yanzu har abin ya zamar ma ta jiki, idan na ce bani da kudi sai kawai ta yi dariya

ta ce "Mama ke 'yar baiwa ce, Allah ba ya hana ki."

Samha akwai wani bashi da ya rikito min kudi ne mai yawa, cikin dare na tashi na yi sallah, na yi doguwar sujjada ina addu'a. Kawai ina idarwa sai na jawo wayata na duba. Wallahi Samha alert din du

bu dari biyar na gani. Kafin ma in duba in ga daga ina kudin ya zo sai kawai na turawa wacce take bi na bashin kudi, sannan ma na bincika daga ina alert din ya zo."

Su duka su ka yi kabbara a lokaci guda.

Samha ta ce "dan Allah Sharifah ki ban

i sirrin addu'oin nan . Da gaske kike? Waye ya turo miki kudin?"

Sharifah ta yi dariya ta ce "daman wasa ne ya tara mu anan? Wallahi daga CBN, kudin nan da ake rabawa na tallafin corona."

Samha ta ce " kin bani satar amsa in sha Allah zan tattar

a lamurana waje daya in miqawa Ubangijina Allah. Wato ma mutum ya daina neman shawara ko fadawa wani matsalarka, dukka bata lokaci ne da tonar asiri.Gara kawai ka kalli gabas ka fadawa Allah."

Sharifah ta ce "sosai Samha. Ga rashin lafiya dan a lok

acin idan kin ganni ba za ki gane ni ba, kawai kuraje suka dinga feso min, idanuwana ciwo, wani lokaci har bana gani sosai. Idan ina tafiya sai in fara haki, har ana so a dora min ciwon zuciya. Sanda kika ganni ma me ai na ji sauki akan da.

Addu'a ka

wai na tsaya ina ta yi, abinda na cewa Rabbil samawati shine Ya Allah zuciyata ba zata kamu da ciwo ba saboda a cike take da tsoronka da son matsayinka Annabi Muhammad S.A.W. dan haka zuciyata babu ciwo. Ya Allah kada ka kaddara zuciyar da ta cika da son A

nnabi ta kamu da ciwo.

Ina zuwa gwaji zuciya babu ciwo Samha, alhali ada komai na alamun ciwon zuciya ya tabbata. Kai duk wanda ya ce babu Allah bai yarda da Allah ba, tabbas ya na cikin asara babba."

Samha ta yi kabbara ta ce " gaskiya ki

n kama babbar madafa. Ina tare da ke 'yar uwa."

[3/6, 5:15 PM] Jamila Umar Tanko: 7

Lokacin sallar azhar ta yi dan haka su ka katse labari, Sharifah ta shiga bandaki don dauro alwallah.

Samira ce ta shigo a gigice har sai da Samha

ta ji tsoro.

Samira na ganin Samha sai ta yi ajiyar zuciya ta dafe kirji, har da wata kwallar farin ciki ce ta sirnano.

Samha ta tambaya a gigice "lafiya? ina su Mama?"

Samira ta ce " ba maganar Mama ba ne, ita yanzu ma mun yi

waya sun isa lafiya. Kawayenki ne su Aunty Nana suka zo gidanki nemanki, na fada mu su ki na asibiti. Daidai lokacin na gama sakwara sai na basu su taho miki da ita dan an kira ni a BUK ance mu kai wani wani assignment da aka bamu.

To ina can ma

karanta tare da kawayena mu na yi sai su ka hana ni sakat su na ta kira na a waya wai in kira Yaya Aliyu da 'yan uwa a je asibiti, sun baro ki kina cikin wani hali kina neman taimako. f

Fatalwa ta saka ki a gaba bakya iya magana bakya iya daukar waya,

kuma ba lallai ba ne ma likitocin su ganta ke kadai kike ganinta."

Samha ta jawo Samira da sauri ta toshe ma ta baki ta yi magana cikin rada ta ce "yi a hankali Sharifah ce fa, tana cikin bandaki kada ta ji ki ba zata ji dadi ba. Allah Ya shiry

e su, su kuma. Babu wata fatalwa qawata ce kuma aminiyata."

Samira ta yi tsaki ta na magana a hankali ta ce "daman Aunty Sharifah ce? su har yanzu ba zasu bar maganar fatalwar nan ba ne? Bayan an fayyace komai zance ya wuce. Wallahi sun hana ni

karatu sai waya suke, Anti Nana har da kuka take yi min a waya."

Samha ta ce "in ba ki gama Assignment dinki ba ki je ki gama kawai ki manta da su."

Samira ta gyada kai ta ce "ba mu gama ba na Taso wallahi. Allah Ya sa ma da motarki na

je da na sha wahalar neman abin hawa. Bari in koma da sauri."

Ta fice da saurin, yayin da Samha ta jawo wayarta, missed calls dinsu ta gani ya fi ashirin da sakonni da na su da na Samira.

Sakon Nana ne ta rubuta wai Samha ta fada musu

gaskiya idan itama ta zama fatalwar ne su rabu da ita, dan sun ga alamu har akwai munafunci tunda in an yi shawarar rabuwa da Sharifah sai ta sake jajubo musu ita.

Dariya ta kama ta ba mamaki ba, har sai da ta toshe baki, ta sha dariya ta gode All

ah. Sannan ta ajiye wayar daidai lokacin Sharifah ta fito daga bandaki. Itama ta shiga don yin alwallah.

Bayan sun idar da sallah ne Sharifah ta tambaya wacece ta shigo? Dan ta ji tana magana da wata?

Samha ta yi murmushi ta ce "Sam

ira ce ta zo ta dauki wani abu ta koma Makaranta."

Ita fa Samha har yanzu a labarin Sharifah ba ta ji an sauka a in da take so a sauka ba. Alaqar Sharifah da baqin kare da ciwo da mutuwa, sannan kuma da labarin Fanna yadda ta mu.

Sam

ha dai sai tsokano labari take Sharifah tana zuqewa.

Sharifah da Hamidah ne suka yi waya, Hamidah tana bata labarin cewa Mahaifinta ya kira ta a waya yana bata hakuri akan rashin kula ta da baya yi, ya san yayi kuskure zai gyara. Sannan kuma yana

so ta tubure ta cewa mamarta ta dawo gidansa.

Sharifah ta tabe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "Hmmm! Rabu da shi, idan ma mafarki yake yi to ya farka."

Bayan sun kashe waya Samha ta gyara zama ta ce "watakila ya canja halinsa,

ki yi hakuri mana ku koma."

Wannan karon wata katuwar harara Samha ta amsa daga wajen Sharifah.

Ta ce "kin san kuwa bayan rabuwata da shi aure sa nawa? Ya kai aure takwas yi, wata ma watanni uku kacal ta yi ta fita, wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login