Showing 12001 words to 15000 words out of 65015 words
jayayya da ke ba saboda ke uwa ce. Shin Mama ke ba uwata ba ce? Za ki iya raba kauna da zumuncin da ke tsakanina da Samha? Tun muna
yara fa. Ai da ba ki zo da kanki ba ma, idan kika aika in zo ni zan zo."
Daga nan na karasa sumewa, sama ta yi kasa ta yi oho. Na farka na ga Samira tana jijjiga ni ta dawo daga makaranta ta iske a cikin wannan hali.
Da gaskiyarki Samha wannan yar
inya bata raye dan daga ganinta na ji jikina kamar an yaryada min shocking din wuta.
Madallah da Alqalamin JUT
You be continue......
HIRA DA MATATTU ....8
NA
JAMILA UMAR TANKO
JUT
You tube:
Facebook:
Watpad
:
Aliyu ya na zaune a gefe yana kallonsu tun kwakwalwarsa tana dauka har ta daina dauka. Shin wacece Sahatifah? A ina ya taba jin sunan nan Sharifah? Ba bakuwar nan da ta zo ba ne da rana yayi mata iso cikin daki? Itama ta ce sunanta Sharifah?
Yaya aka yi ta zama matacciya? Shin idan an ce Samha shirme take yi yaya zaa yi ace Mama ta biye ta su na wannan shirmen alhali a iya saninsa Mama bata da wasa, bata yin irin wannan shirmen a rayuwarta.
Ya ji kansa kamar zai fashe dan haka ya gagga
uta barin cikin falon ya fita farfajiyar gidan. Wayarsa ya dauko ya kira Yaya Anas. Ya ce ya zo gidansu ya same shi gashi nan tare da Samha da Mama.
Hankalin Anas ya sake tashi dan daman Samira ta kira shi dazu ta ce Mama bata jjn dadi. Yanzu yake
shigo garin daga zaria.
Ya fara tambaya a gigice yana cewa "jikin ne? Ku kaita a asibiti kafin in zo da gaggawa."
Aliyu ya shaida masa babu wata matsala ya yi tuqi a hankali ya karaso a hankali kawai maganar tana son bincike da kuma nutsuwa.
Ba jimawa Anas ya karaso, suka shigo cikin gida tare. Da aka fara mayar da zance sai Anas ya fara jin haushin Samha, domin an ambaci sunan aljanarta Sharifah.
Ya harare ta ya ce "Au aljanar da kika dauko a high court shine kika shunawa Mam
a ita?"
Samha ma ta fusata ta ce "Sharifah ba aljanna ba ce matacciya ce."
Sai ya sake jin haushinta ya kama shi. Dakyar dai ya zauna ya saurari labarin su tun daga farko har qarshe.
Cike da mamaki ya ce "wai wacce Sharifah Nasir d
in? Yayar Shariqah kanwarta wacce na so in aura?"
Samha ta tabbatar masa "eh su amma duk sun rasu yanzu. Shine suke yi mana fatalwa?"
Ya fada cikin daga murya " fatalwa kamar yaya? Sharifah ai tana turai. Wai me yake damunku ne? Shariqah kuwa
na ganta kwanaki a layin masu awo da na kai matata har muka gaisa da ita."
Aliyu ya ce da Samha "wait! wait!! wai Sharifah Nasir kawarki da ta yi miki babbar qawa a bikinmu?"
Ta ce " eh su ne."
Ya ce "toh ai ita ce ta zo gida rannan kawai kamann
inta ya canja ne, na rasa in da na santa amma na dade ina tunanin in na taba ganinta. Yaya aka yi ta zama matacciya?"
Mama ta na magana cikin layi ta ce " ku daina kiran sunan nan gatsai ku dinga risinawa kuna hadawa da marigayiya Sharifah baa so ana
kiran sunan matacce haka tsirara."
Mamaki da tausayi da dariya suka kama Samha a lokaci guda, ta tabbatar Mama ta daku. Ko ba komai ta san zata sami saukin zagi da tsuyuwar da take samu daga wajen Mama. Dan ta fi kowa rashin fahimtarta. Amma yanzu d
a yake ciwonmu iri daya ne zata tausaya mata.
Anas ya fada a fusace "kai wannan abu yayi yawa, dole a yiwa tufkar nan hanci babu yadda zaa ta razana kanwata sannan kuma ta dawo kan mahaifiyata kuma in kyale ta."
Mama tana magana babu ku
zari kamar ta sha biliyan, layi kawai take yi. Ta ce "Anas baa cika baki ka iya bakinka fatalwa ba wasa ba ce nima abinda na yi kenan ta zo min. Ka ga kai ne karfin gidan nan idan ka zauce yaya zaa yi a kula da gidan?"
"Anas ya zo kusa da ita
ya durkusa ya ce "Na rantse da Allah Mama babu mai taba ki in bari, ki bari kawai in je gidan in gani ban yarda ana mutuwa a dawo ba, babu wata fatalwa a duniya. Baa taba mutuwa an dawo duniya ba."
Mama ta ce "ba komai kowa ya riqe fahimtarsa kai
baka yarda ba, mu mun yarda ba sai an je ba. Kawai dai mu yi addu'a a hana ta zuwa mu kuma kada mu taka gidansu. A kira malamai su yi mana tsakani ba zamu gidansu ba, ba zasu zo gidanmu ba. Mu ne da laifi tun farko mu muke zuwa gidansu ko ba haka bane Samh
a?"
Samha dai na zaune a gefe ta yi tagumi dan tana gane karatun Mama, Mama na gane na ta.
Aliyu ya ce " Mama gara dai mu je mu gani din kada ki damu. Za mu dawo lafiya insha Allah.
Gaban Samha yana ta faduwa musamman da na ji mijinta
abin kaunarta shima zai shiga siradin tafiya.
Mama ta zabura ta ce " idan zuwan ya zama dole Aliyu da Anas kada ku je a tura Yunus da Bashar su je. Da in rasa ka gara in rasa su, daman sun ishe ni da shaye-shaye da dauke-dauke sun qi dainawa."
Yunus da Bashar suka zabura suka bude baki dan mamaki.
Yunus ya fusata ya cije baki, aka baje qafa ana baza hannu ya ce " Mumcy daman bakya kaunarmu ba mu sani ba? Har na daddage ina jero miki addua addu'a ina tofa miki. Haba dan Allah l
aifin me mu ka yi haka da za ki ce mu je wajen fatalwa? Eh toh gaskiya daga yau na san zaman da zan yi da ke wallahi."
Babu wanda bai kwashe da dariya ba a wajen.
Mama ta ci gaba da ce "karya kake ko addu'ar nan da ka ke ba dan Allah ka ke yi
ba, dan ina kallonka sai da ka dafe min dubu dayata, jira nake in warke wallahi sai na ci ubanka."
Yunus ya gyada kai ya ce "ashe kin ganni? Ba sai ki ce kawai in dawo da ita ba ai normal ne in ka dafe sai ka samfe amma in an ganka sai ka ciro
ta ka bayar daman can ajiyewa mutum ka yi. Daman na dauka ne da niyyar zan kaiwa Malam ya yi miki rubutu amma ga kayanki nan. Haba yaya zaa yi ma ki ce a tura ni gidan MATATTU? Gashi nan duk wannan jarumtar taki kema an kwantar da ke balle mu.
Bashar ya
cije baki ya ce "lallai Mumcy ni mamaki ma ya hana ni magana, d'an shaye-shaye dai da d'an samfe-samfe muna yi amma ai mu na biyayya mu ma, mu na da amfani.Aikace-aikacen gidan nan fa muna yi shara dai a tsakar gida duk muna yi tunda an hana mu shara a da
kuna. Kuma har ki ce gara mu je fatalwa ta kashe mu, ban taba ganin uwar da ta tura yaranta halaka ba sai ke. Dan dai uwa-uwa ce amma wallahi da na hada kayana na bar gidan dan baa sonmu."
Anas ya yi musu tsawa ya ce "ku rufe mana baki, ba kunce k
u jarumai ba ne, kullum ku na dauko wuqa da adda ku na yawon fada unguwa-unguwa ai ga abin fadan ya zo, ku je mana."
Yunus ya shafa cibiri-cibirin gashin kansa ya ce " yaya Anas fada shine tsakanin maza da maza, ka kai sara a kawo maka sara , maza na ki
rari cau-cau-cau amma fadan da ana ganinka baka ganin abu ai da matsala. Dambe da fatalwa fa, haba dan Allah. Ta yaya ma zaa ce mu je?"
Aliyu ya yi dariya har cikinsa yayi ciwo, Samha kuwa takaici da fargaba ya ishe ta wannan labari kawai suke yi basu s
an ma wacece fatalwa ba sai wanda ya gani. Mama ce kadai za ta gane wannan karatun.
Ka na ganinta fatalwa ma za ka ji kamar an zare maka laka ko yatsa baka iya dagawa, sai ka ci saa ne karfi zai zo maka ka yi magana wasu lokutan.
Aliyu da Anas su ka
nufi kofar waje, Mama cikin galabaitacciyar murya ta ce "Anas kada fa ku je . Ku bar ta da Allah, a kira Malamai in akwai abinda zaa abinne a get ta daina shigowa a zo ayi da gidana da gidan Samha.
Anas ya ce "muna kofar gida, ba can zamu je ba, shawar
a zamu yi."
Ashe da suka fita shawara suka tsayar su tafi gidan kawai su gani, sun tabbatar kawai gizo suke gani babu wata fatalwa.
Su ka shiga motar Aliyu suka isa gidan. Su ka tsaya a bakin get din suka jima a tsaye su na karantar kofar. Gidan a bu
de amma ciki duhu qirin ga duhun dare ga duhun bishiyoyi, sannan babu bil'ada da yake shiga ko fita.
Da saurinsu su ka tari wani mutum wanda ya fito daga gidansa, gida biyu a tsakaninsu. Su ka tsayar da shi bayan sun yi masa sallama sun gaishe shi, sai
suka tambaya "dan Allah Malam su waye a gidan nan yanzu?"
Ya amsa musu da cewa "gaskiya a iya saninna masu gidan iyayen duk sun rasu haka da yawa daga cikin yaran sun rasu, ban san su waye a ciki ba. Wataran get a bude wataran a rufe." Ya wuce da alama
sauri yake.
Nan dai suka tsaya carko-carko. Sai su ka sake ganin wani saurayi a tsaye a gefen gidan, suka isa gare shi, bayan sun yi masa sallama suka nuna gidan da hannu suka yi masa irin waccan tambayar da suka yiwa na farko.
Daidai lokacin wata
mota ta zo wucewa sai ta haska fuskarsa ashe harararsu yake yi, kuma abinda ya basu tsoro fuskar Sharfah da shariqah suka gani a jikin wannan bawan Allah. Ya harare su, sai ya ja dogon tsaki ya barsu a tsaye ya yi tafiyarsa hanyar bakin titi.
Aliyu da
Anas sai suka ji hantar cikinsu ta kada.
Anas ya ce" Aliyu! ka ga abinda na ga ni kuwa? Fuskar Sharifah da Shariqah fa na gani a jikin saurayin nan."
"Aliyu ya ce " ina ga shine Bellon da Samha take cewa shima ya rasu ne.
Anas Ya yi ajiyar zuciy
a ya ce "kada mu karaya mu shiga cikin gidan kawai."
Suka fara addu'a sannan suka saka kai farfajiyar gidan babu komai sai duhu da datti. Abin mamaki sai su ka ga giftawar wani qaramin yaro mai fararen kaya da gudu ya je ya dawo a guje.
Aliyu yayi
karfin hali ya ce "kai yaro zo."
Yaro ya taho amma ya tsaya daga nesa-nesa yaqi karasowa inda suke.
Aliyu ya ce " ina mamarka?" Yaro ya ce " ta rasu."
Su ka kalli juna sannan Anas ya ce " kai da wa ku ke zama a gidan yanzu?"
Yaro ya ce "tare da
mamata."
Nan ma suka sake jin faduwar gaba.
Su ka daure Aliyu ya ce "ina Mamarka take yanzu?"
Yaro ya ce "gata can a saman windo."
Ya nuna wani windo a saman bene.
su ka daga ido da sauri suka kalli inda ya nuna, ba su ga komai ba.
Kafi
n su juyo su yiwa yaro tambaya, babu kowa ya bace.
Nan suka fara tofa addu'oi kowa ya kasa magana.
Burum suka ji an shigo cikin get din, suka zabura suka juya, sai ga wata doguwar budurwa ta shigo.
Aliyu yayi sauri ya kunna fitila wayarsa ya hask
a ta innalilahi wa inna ilaihi rajuun kamarsu daya da Sharfah da Shariqah amma budurwa ce wacce bata fi shekaru goma sha biyar ba.
Su ka ga bata da niyyar tsayawa, ta yi ma kamar bata gansu ba.
Anas ya zabura ya ce " ke yarinya tsaya mana, salamu
alaikum. Ina Mamarki?"
Ta yi shiru zuwa wasu lokuta sannan ta ce "ta rasu."
Su ka hada ido da juna sannan suka dan ja da baya su ka hada baki su ka tambaya " da wa kuke zama yanzu a gidan."
Ta ce " da Mamata, tana ciki."
Za su sake tambaya
sai su ka jiyo wata murya mai sanyi, sai an ja ta sosai sannan ake fitarwa. Muryar daga sama take fitowa, kamar daga kan bishiya kuma kamar daga kan rufin kwano. Kuma sau biyu ake maimaita kalma, ana fada wata murya daban na maimaitawa.
Aka ce "Hamidah!
Hamidah!! Ki saka sakata, ki hawo da baqin nan sama."
Hamidah ta nufi kofa da sauri zata sakace.
Aliyu ga boko, ga ustazanci ga tsoro, sai ya yi gyaran murya ya shafa dogon gamu da sauri.
Ya ce " Subahallahi No! No! Hey you girl, 'yan mata excu
se me dan tsaya, A'uzubillahi minal shaidanir Rajim. Bari ainahin mu dan fita daga waje sai ki sakace gidan."
Anas kuwa takalma ya cire ya soke a hamata, ya cire hula ya riqe a hannu. Shine a gaba, ya fice da sauri. Ya ma kasa magana.
Hamidah ta tsa
ya tana kallonsu, su ka fita suka yi carko-carko suma su na kallonta.
Ta ce " Mamata ta ce "ku hawo sama."
Aliyu ya harare ta ya ce "Subhanallah! Mu hawo ina? Wacce saman daga ciki? Kan gajimare, ko kan bishiya, ko kuma cikin silin. Alhali my na ji
n murya na fitowa ainahi daga kan bishiya ko cikin silin da kwano. Wacce saman kike rufi? Wannan abin na ku gaskiya is ....is..... ya rasa kalmar da zai karasa maganar ma.
Anas ya ce "kai ka tsaya ma ka na yi mata bayani. Wacce Mamar ta ta tukunna? Ita
da ta ce ta rasu. Mu je mu ga wa? Fatalwa? Ke ma ban yarda ke ba, ba mutum ba ce."
Aliyu ya ce " haramun ne mu shiga gidan matan aure da daddare, ainahi kuskure ne babba. Ki cewa mamarki mun fasa, mun yafe, daman gaisuwa ce."
Ta gyada kai ta ce " r
ayuwar duniya ta kan zama empty lokacin da dukka masoyanka suka shude. Ka ji kawai gara ma ka bisu. Dan an ce akwai rayuwa bayan mutuwa."
Aliyu da Anas suka riqe hannun juna.
Anas ya ce "Malam zo mu arce kafin su danna mu a cikin gidan nan da kansu ku
ma da karfin gaske.
Karar buga kofar ce ta firgita su basu san sanda suka rungume juna ba suka kankame, sun manta ma su surukai ne.
Saurayin nan me mai fuskar Sharifah na dazu ya dira a gabansu.
Ya sha kunu ya ce "kun gama? Malamai ku bar kofar g
idan nan kada in sake ganin kafar wani a qofar gidan, mace ko namiji ko tsohuwa."
Aliyu da Anas suka hada baki a tare "insha Allah yanzu kuwa zamu tafi. Ayi hakuri."
Su ka juya da sauri har sun fara tafiya sannan suka tuna sun zo da mota, suka dawo d
a sauri jikin na rawa.
Anas cewa yake ban ga takala na ba fa."
Aliyu ya harare shi ya ce "bayan wanda ka saqale a hamata."
Sai yanzu Anas ya san ya kai wa hamata ajiyar takalma.
Aliyu cewa yake "ina gilashina bana gani sosai fa."
Anas ya
harare shi ya ce "wanne gilashi bayan na idonka."
Haka su ka shiga mota jiki na rawa suka gaggauta barin kofar gidan, har suka fita titi basu gane a inda suke ba, kuma ta ina zasu je gida.
Manyan titian kawai suke bi su na zabga gudu. Kowa ya kasa
magana.
Anas cewa yake "ka daina bin titi mai duhu kuma kadan kara ainahin gudu na ga kamar baka sauri."
Aliyu ya ce a 80 nake tafiya zuwa 100. Ina zamu je ma?"
Anas ya ce " ina ga ai mu wuce gidan Malam Babba, mu kwana a can saboda idan muka
je gida a wannan yanayin akwai matsala, da tsakar dare ba mu san yadda za ta kaya ba. Gara a gidan Malam mu kwana muna karatu dan ya fayyace mana alfanu da rashin alfanun fatalwa a musulumci."
Aliyu ya kalle shi cike da takaici, dan har yanzu takalmans
a Anas na nan a sakale a hamata a manne, hula