Showing 45001 words to 48000 words out of 65015 words

Chapter 16 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

18

aurensa da Dinar ya tabbata ba zan ba ta yaran dukka ba sai dai in ba ta masu dan wayon su biyu zuwa uku kanan sai dai in riqe su. wala in zauna da su a kasar nan ko in tafi da su kasar da nake zama. Wanda na san halinsa

ba zai yarda ba sai dai in an kai ruwa rana.

Mu na cikin wannan hali maimakon dangina su shiga maganar a sasanta.A' a sai zuga da ake ta kai masa, gulma kala-kala, sai da aka bata a alqata da shi gaba daya.

Wata rana ya zo ya same ni ya ce yan

a so akai masa yaran weekend su dukka har yar karamar da bata shiga makaranta ba. Na ce manyan dai su uku banda kananan ya ce su dukka yake so.

Hamidah ta ji hankalinta bai kwanta ba ta ce da ni "Mama kada ki bayar da su dukka kada ya hana su fa."

Na ce haba dai shima ba zai fara ba. Haka kuwa aka yi lahadi ta yi lokacin da ya kamata ya dawo da su yayi wato ranar lahadi da yamma saboda akwai makaranta ranar litinin. Wayarsa na ji ya kira ni ya tambaya ko ina gida? Na ce na fita amma ina hanya

, idan yaran zai kawo su Hamidah na gida. Sai ya ce ba yaran ba ne magana ce da shi akan gado in hado musu takardun dukka gidajenta in bashi, yaransa kuma ya kwashe."

Sharifah ta yi shiru saboda radadi da zugin da zuciyarta ke yi, yayin da Samha ta yi

shiru ita ma zuciyarta ce ke tafasa, dan takaici da tausayin Sharifah.

[3/3, 9:43 AM] Jamila Umar Tanko: 5

Samha ta ce "Sharifah na san ki a baya ki na da zafi bakya daukar raini. Yaya aka yi har mutumin nan ya sami dama yake taka ki yadda ya ke

so?"

Sharifah ta yi murmushi ta jingina a jikin kujera ta rufe ido kamar mai tunani har zuwa wasu 'yan lokuta sannan ta dago ta dubi Samha ta yi dariya.

Ta ce " ba ke kadai ba ma ko 'yar da na haifa Hamidah ta yi min irin wannan tambayar. Sam

ha wato na ga rayuwa, na tabbatar babu wanda ya Isa sai Allah, babu wani mai iko sai Allah. Dan Adam ba komai ba ne. Na qara yin imani, na koyi hakuri, na koyi tawakkali, ina so in gyara mu'amulata da Ubangijina, da kuma sauran jama'a. Me ya yi saura kuma

a duniyata? Babu Mama, babu Baba, babu Yayana Bellocity, babu Shariqah. Na dogara ga Allah gaba daya na miqa maSa wuya, ina ganin kamar rayuwar matattu ta fi irin rayuwar da nake yi yanzu dadi. Na karkata gaba daya na fuskanci kabarina, kullum ina jiran is

owar layi ya zo kaina.

Samha me kika sani akan mutuwa? Me ki ka sani akan rayuwa? Me kika sani akan halayyar dan Adam? Ana ganin idanuwan iyayenki ba zaki taba

gane masoyinki ba sai ranar da aka ce yau babu ran mahaifa za ki ga rashin kara da rashin

kunya.

Ko a sanin da kika yi min ada Samha, ba na neman fada ko kadan. Ina takatsantsan dan kada in shiga harkar wani in bata masa amma kuma bana so a shiga harkata a takura min. Idan na takura ne sai in fashe toh idan na fashe ba ta yin kyau.



Ai Adamu bai kai rabin neman rigimar mijina ba amma da ya kaini karshe bai ji da dadi ba. Na kan bawa mutum dama mai yawa kafin in gaji.

Ai yanzu na ke ba ki labarina da mijin Shariqah za ki ji yadda ta kaya. Sai ya tabbatar min ya kwashe yaran ba

zai kawo min kuma dan rashin kunya ya kira ni yana yi min maganar gado.

Bayan tun lokacin da aka yi sadakar arba'in ake ta bin kansa ya zo a zauna ya qi. Ashe shi niyyarsa babu rabon gado daman shine zai gada daga shi sai yaransa, idan ya auri Din

ar sai ya dauki yaransa, ya karbe gado, sai ya yi gaba shikenan ya gama da shafinmu. Sai ya je ya ci gaba da mulkinka.

Kuma daman dukka kara da bin dokar da nake yi akan kada ya kwashe yaran ne, yanzu kuma me yayi saura tunda ya kwashe?

Na ri

kice ta inda na shiga ba ta nan nake fita ba, wani yanayi na shiga wanda ni da kaina ba yin kaina ba ne, har sai da Hamida da Dinar suka kwace wayar. Ina ganin bai taba jin maganganun da ya ji a ranar ba.

Daga nan ya tabbatar ko ya sha giyar wake b

a zai iya takowa ya zo gidana ba. Sai ya nemo Bello a waya. Sai ga kiran Bello ya na tambayata abinda ya faru sabanin abinda Adamu ya fada masa masa har ya shirya min wani sharri da karya karya kala kala.

Daga nan fa fada ya fara a tsakanina da Adamu

. Ya boye yara ba sa gidansa ba sa gidan iyayensa ya kai su ajiya. Ki duba fa ki gani wai yaran da suka rasa uwa yake yiwa wannan wulakancin alhali ga inda aka san darajar ake kaunarsa ya dauke su.

Mu ka yi samame mu ka je gidansa babu yaran, wata

'yar uwata ta nemo lambar mahaifinsa saboda dattijo ne mun yi tunanin bai san rashin arzikin da dansa yake aikatawa ba. Amma sai kalamansa su ka nuna shine ma yake zuga shi akan ya kwato yaran.

Tsohonsa ya yi rantsuwa su babu wanda ya isa ya riqe mu

su yaransu, su ne masu alhakin rikewa. Ashe ma dai shine ya dora shi akan wannan karatun na ya sace yaran.

Amsar da na bayar ita ce daga kaina kuwa za ku sauke wannan salon."

Samha ta gyara zama ta ce "ikon Allah wannan wacce irin rayuwa ce? D

aman ana yin haka?"

Sharifah ta langwabar da kai ta ce " Wallahi Samha tunda daga ranar da aka kwashe yaran nan Shariqah ba ta sake kwanciya a labarinta ba, kuma ba ta barni na kwanta haqarqarina ba."

Samha ta zazzare ido ta tambaya a gigice

"Kamar yaya?"

Sharifah ta sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani, ta ce " duk in da na jefa kafata Shariqah sai ta jefa ta ta qafar. Bi na a baya kawai take take yi. Sai in juyo in tambaye ta Shariqah menene? Sai ta yi shiru ba ta magana. Babu safe, b

abu rana, babu dare, Sharqah na biye da ni.

Sai daga baya na gane bin nan da take yi min ya na da alaqa da yaranta da aka kwashe ne fa, take so in karbo ma ta. Satin yaran nan uku cur baa san inda suke ba kuma ya qi fada. Haka itama ba ta taba yin

fashin barina ba, koda yaushe ina ganinta.

Ta biyo ni daga cikin gida mu ka fito kofar gida na shiga mota na zauna sai ta tsaya a bakin get, na ce ma ta ta zo mu tafi mana, sai ta

tsaya ta qi ta shigo cikin motar. Ta san na gane abinda take so ta nu

sar da ni, wajen yaranta take so in je dan haka ba ta biyo ni ba."

Kan Samha fa ya daure gaba daya, har hayaqi yake yi na rashin fahimta.

Ta sosa goshi cikin in-line ta ce " Sharifah da tsaya pls me kike cewa ne akan Shariqah?"

Sharifah

ta yi murmushi ta ce "abinda kika ji ina fada shine dai abinda nake nufi. Ke dai ki biyo ni kawai ki ji karshen labari.

Masana su ka bani shawara akan in kai shi qara wajen hukumar sulhu ta musulumci, su ne masu yin sulhu dan Allah da kuma fadar qur

'ani.

Da tambaya har na sami inda ofishinsu yake, na je na shigar da korafi. Nan da nan suka neme shi a waya, dakyar ya zo bayan ya gama kamun kafa da wani da ya sani a wajen. Amma maganar gaskiya kuma maganar cikin qur'ani baa canjawa.

Aka c

e ya dawo min da yara ni na fi cancanta na riqe su. Babbar matsalar da ta afku ita ce, a daren zaa fara kulle gari wato lock down, a lokacin Corona ne kuma a ranar zaa tashi da Azumi.

Aka yi ta fama da shi akan ya dawo min da yaran dukka biyar din,

saboda ana kan teburin sulhu ne ba kotu ba ce amma ya dage shi bai yarda ya kawo da su dukka ba sai dai ya dawo da kananan guda biyu.

Kasancewar dare yayi zaa rufe gari aka tafi akan hakan amma bayan sati biyu zaa bude gari aka ce mu dawo.



Yara biyu su na wajena, guda uku su na wajensa sai, ya fito da su daga inda ya boye su ya dawo da su gidansa.

Anan ma na sake ganin Shariqah, ta ce min in zo in gani. Ina biye da ita har mu ka isa wani gida mai qofofi guda biyu. Ta bude qofar farko

sai na ga haske sosai ga ranta guda biyu wadanda suke wajena kenan, su na ta bacci a cikin ni'ima. Sai ta bude qofa ta biyu sai na ga duhu na hango ragowar yaranta guda ukun da basa wajena, a cikin duhu da damuwa. Daga nan sai ta bace.

Kin ga kenan

ta na nuna min ga halin da wadancan suke ciki, kuma ta na so lallai-lallai su ma a dauko su kenan."

Samha ta fada a bayyane " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah wai me kike cewa ne?"

Sharifah ta qura ma ta wasu jajayen idanuwanta da s

uka cika da kwalla ta ce "wai me kika ji ina fada ne? Abinda nake fada shine kike ji."

Samha ta shafa jikinta don ta tabbatar ko tana raye. Eh tana raye tabbas dan ruhinta da gangar jikinta su na tare kawai dai ta na HIRA DA MATATTU ne.

In ha

r Sharifah mutum ce toh ba za ta dinga ganin matattu a fili haka ba, sai dai idan ita ma ta mutu din ne.

Samha ta sadddakar asan ita kadai matattun nan su ka zaba suke bi suke so a dole sai ta ji labarinsu. Dan haka ya zama wajibi ta sallama ta z

auna ta saurare su.

Daga nan kuma ta san karshen zancen zasu tafi da ita ne kawai. Ta fara yiwa kanta addu'ar cikawa da imani, da fatan Allah Ya bawa iyalanta hakurin rashinka kawai.

Amma ta fara gani kuma ta na jin abin da rayayyu ba sa ji, k

uma ba sa gani. Sai kwalla ta cika ma ta ido ta fara ban kwana da rayuwa kuma.

Sharifah ba ta damu ko bata ma kula da gumi da dimaucewar da Samha ta shiga ba, sai ta ci gaba da cewa "bayan sati biyu na koma hukumar sulhu aka ce bai zo ba kuma ya qi

amsa kiran da ake ta yi masa a waya. Haka dai har sallah ta qarato, ana gobe sallah sai na kwashi yara biyun

da suke wajena na aika masa da su. Don su yi sallah tare da 'yan uwansu, na kuma nuna masa cewar ni bani da niyyar raba shi da yaransa kuma shima

bai isa ya raba ni da sauran ba.

Ya cika da mamakina amma idan ya san wata ai bai san wata ba. Na shammace shi na dawo daukar guda biyun bayan sallah sai na hada guda hudu na tafi da su dan dayar ma tana ciki ne shiyasa ban hada da ita ba. Nima na

kai su wani gida ajiya."

Samha ta yi murmushin karfin hali ta ce "haba ni fa na san halinki kawata ba kya yafiya."

Sharifah ta yi murmushi itama ta ce " bana son rigima amma ya siyo ta da kudinsa wallahi. Ya shigo gidana a gigice yana tsawa y

ana ihu ya na cewa in fito masa da yaransa. Ko kallo bai ishe ni ba, da shi da wata 'yar uwata suka buga.Ya ce wallahi ba zai yarda ba zai kai karata. Na ce masa bismillah.

Sai na sami sammaci daga Hukumar Sulhu ta musulumci yana karata akan na je h

ar gidansa na kwashe yara na boye. Tarihi ya maimaita kansa ashe babu dadi. Daman su ma su na nemansa ya qi zuwa, yanzu da ya ji wuya ya kawo kansa.

Da ranar ta zo sai na je ana masa kira na tafi da yan uwana ya tafi da nasa. Aka fara magana irin t

a sulhu, aka tabbatar masa sai an bi dangin uwa goma sha daya sannan aka ambaci mahaigiyarsa ba ma shi ba. Aka ce ya dawo da dayar ya bawa wata yar uwata ita ce babba nima in kawo yaran wajenta. Amma tun a ranar na fara gane wasu daga cikin dangina da na s

ami barka su na bayansa. A ranar wasu suka bayyana na gane basa tare da ni.

Aka dinga kai kawo a Hukumar sulhu ta musulumci yayin da yake samun rakiyar wani wanda ba ma dan uwansa ba ne, shine aka wakilta ya tsaya masa dan kada in yi rinjaye akan

sa. Sunan dan zugar Idris ya dinga juya magana, sai an zo matsaya sai ya dawo baya har su ma hukumar suka gane shi, su ka tabbatar baya son ayi sulhu, dan basa shiri. Da aka tutsiye shi sai su ka gane bai san komai a addini ba ma amma yana ikirarin shima m

alami ne. Ashe da Adamu ya kwashe yaran gidansa aka kai su aka boye, su ka sami abin duniya, a sati ukun da yaran su ka yi a gidansa sai da aka azabtar da su da yunwa da kyara.

Aka yards zaa bani yaran dukka amma dokokin da aka saka min su ne: zan tas

hi daga gidan da nake zaune in dawo gidan iyayenmu wanda shine gidan da na gada ni da Shariqah da Bello sannan duk karshen sati zai dinga kwasar yaran zuwa gidan sa jumaa zuwa lahadi da yamma.

Ban yarda ba saboda babu tarbiyya ga yaran da suke da gida

biyu. Anan dai aka daddanne ni aka in yi hakuri in yarda akan hakan dan an fi wata guda ana zarya.

Na rasa dalilin da ya sa zaa tashe ni daga gidan da nake a kai ni wani gida alhali ba shi yake biya min hayar ba. Bello ya fi son hakan da wasu daga

cikin dangi suka ce in yi hakuri, zaman hayar ma bai dace da ni ba daman saboda Allah ya rufa min asiri ai saukina ne.

Na san halina ba zan iya zama a gidanmu ba kasancewar gini ne irin na da, komai ya kwararrabe. Na fitar da kudi mai yawa na far

a gyaran saman gidan kusan komai sai da na fitar da shi na zuba na zamani.

Mu ka tafi a haka, da na gama gyara na kaura can. Ya na aikowa duk karshen sati ana kai su. Amma sai ya shiga zuga su akan kada su yi min biyayya wato idan na gaji da halin

su sai dawo da su.

Uba ne da hannunsa yake batawa yaransa tarbiyya innalilahi wa inna ilaihi rajuun.

Ya ce in sun shigo gidan kada su gaida kowa su sha kunu su wuce daki. Sannan ni bani da kirki ban tsinanawa uwarsu komai ba bana kaunarta. Ki duba

ki ga wannan al'amari yana so ya wanke kansa alhali yaran sun san komai."

Samha ta dafe haba ta ce " ikon Allah wannan wanne irin mutum ne kenan?"

Sharifah ta ce "sai lokacin nima na gane haqiqanin halinsa na gaskiya. Dukka a dalilin haus

hin na qi yiwa Dinar auren dole. Ashe ma rigima baa fara ta ba sai a gaba.

Ya na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login