Showing 21001 words to 24000 words out of 65015 words
abin al'ajabi. Da alama kowa ya sake shiga rudani da firgici ba dan kadan ba.
Anas ya sharce gumi ya ce "badan-badan-badan ba da mun je gidan mun gani, amma fa da r
ana tsaka ido na ganin ido. Mu gayyato makwabtansu kakaf da manyan Malamai a Shiga cikin gidan a gani. Ko dai mu jira Malam Babba ya dawo? Tunda ya yi mana alqawarin daga ya dawo za mu je. Yanzu ya kusa satinuku da tafiya zai dawo nan da sati guda. Yaya ka
gani Aliyu?"
Aliyu ya goyi da bayan a bari Malam ya dawo dan idan aka yi tarwatu aka je aka ga ba haka ba ne, su za su ji kunya. Dan abi abin nan a hankali tunda akwai sarqaqiya.
Samha ta zama Jaruma har ta fi son a tafi yanzu kawai a yi ta ta qare
ita fa abin nan ya wuce daure kai ya koma tamke kwakwalwa. Aka bata hakuri akan a bari dai har Malam din ya dawo zai fi.
A daddafe aka yi mako guda a haka cikin firgici, Mama kullum sai ta kira Samha a waya dan ta ji lafiyarta ta kuma tambaya ko me zi
yara ta kawo ziyara. Samha ta tabbatar mata yanzu ko a mafarki bata ganinta. Sai dai abinda ta gani ne a shoprite ya tsaye mata a rai.
Alhamdulillah! Malam ya dawo gari, sun bashi kwanaki biyu kacal ya huta sannan su ka je suka tsaye masa akai. Ko ya q
i Allah dole ya taso ya biyo su dan tun ya na can yake karbar wayoyinsu safe da dare. Sai su ce gaisuwa ce kawai musamman Yaya Anas.
Sun fito da misalin karfe goma sha daya na safe, sun daidaici lokacin da kowa dai idanuwansu biyu wato dukka aljanu da
mutane.
An taho tare da kowa da kowa dan da har ance Mama ta zauna a gida, amma ta qi ta ce gara dai ta zauna a tsakiya ita baa gidanta ba balle Sharifah ta rutsa ta ita kadai, kuma ko sun je can ba za ta shiga gidan Sharifah ba za ta jira su a mota.
Samha ce a gaba-gaba da alama ta daina jin tsoro, mafita kawai take nema.
Sai dai kuma abinda suka tarar a cikin gidan shine abinda ya fi komai firgici. Ashe gara firgitar da, akan ta yanzu. Tunda Malam ma ya sallama kowa ma sai da ya sallama..
Ba su gushe da karanta kalmar "innalilahi wa inna ilaihi rajuun ba, hade da qula'uzai....."
Rigijigafji!! Shin Sharifah ba ta aiko muku da sako ta ce a fada muku ba ? Cewa kowa ya zauna a mazauninsa ba? Dan me yasa ku ka je ma ta gida ku ka dame ta t
oh???
🤔🤔🤔
Madalla da alqalamin jut
To be continue....
Tallah ! Tallah!! Tallah!!!
Mai talla shi ke da riba.
Ina manyan mata isassu 'yan kwalisa? Tare da yara 'yan gatan Baba da Mama?
Musamman yadda sallah ta karato, a zo wajenmu. Mu na kawo k
aya kala-kala..
Ko kun san?
👇🏻👇🏻👇🏻
PARADISE COLLECTION
Sun yi shura wajen kawo kaya daga kasashen waje, masu kyau da inganci.
Kayan mata 'yan kwalisa kamar leshina, mayafai, takalama da jakukunansu. Har ma da kayan kicin. Yara baa barsu a ba
ya ba, akwai kayan yara kala-kala mata da maza.
Dan ganin kalar kayanmu akwai Whatsapp grp dinmu, a tutube mu a wannan lambar: 07067501009. Mu na turawa zuwa kowanne gari.
Marmaza a garzayo dan siyan daya ko sari. Ko da kudinka sai da rabonka.
Mun
gode.
HIRA DA MATATTU.....12
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Tun kafin su shiga gidan sun cika da mamaki ganin get a bude ma'aikata masu gini na ta kai kawo daga waje zuwa ciki. Su na shiga farfajiyar gidan
suka ga yanayin gidan ya canja. Wannan himilin bolar babu ita, an share tas an kwashe. Tsakar gidan ya sha screeding da fenti babu wannan gansakukar.
Su ka shiga falon kasa, wannan katon falon da ya cika da yana da kura duk an fita da komai, ma'
aikata su na ta aikin yin pop da screeding. Tun baa gama ba har kyawun wajen ya bayyana yayi haske tas.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi hudowar rana daga gabas ta fadi a yamma. Me nake gani ne haka?" Samha ce ta fada yayi da ta bude baki ta far
a mamakin wannan al'amari.
Aka hau kallon-kallo tsakaninta da Aliyu da Anas.
Malam ma ya dube su duba na tuhuma gami da takaici ya ce "yanzu a ina ku ka alamar fatalwa anan? Ga dai bil'adama a cikin gida su na aiki."
Wannan karon Aliyu
da Anas nauyin Malam ne ya kama su basu da bakin karin bayani.
"Amma mu je zuwa dai, dan baa yabon dan kuturo sai yayi shekaru arba'in da yatsu. Za ka ga abinda muke nufi Malam kada ka yanke hukunci." Anas ya fada a cikin zuciyarsa.
"Salamau a
laikum wararahamatullah. Sannunku da aiki. Ina masu gida? Bi ma'ana wadanda su ka saka ku wannan aikin." Malam ne ya tambayi ma'aikata.
Su ka amsa sallama sannan su ka tabbatar masa wanda ya saka su aikin yanzu nan ya bar wajen nan kuwa. Sunansa Al
lah Abdullahi Gama.
Anas ya tambaya "shima dan gidan ne?"
Su ka ce "ai gidansa ne, a unguwar nan yana da irin wadannan gidajen da yawa, kuma bashi da wasu ma'aikatan da suke masa aiki sai mu." Babbansu ya bada wannan amsa.
Aliyu ya za
bura ya ce "nan ai gidansu Sharifah da su Bello ne. Su na ina?"
Su ka tabbatar musu gidan nan ya dade a rufe babu kowa ya zama kwango. Mukullan ma sun dade a hannunsu, Alh. Abdullahi ya dade da basu aikin gyarawa.
Samha ta zabura ta fita
qofar gidan ta sake duba lambar gidan ko dai sun yi kuskure sun fada wani gida ne wanda ba shine ba. Tabbas gidan ne babu ko tantama.
"Kenan daman gidan babu kowa amma suke ganin su Sharifah a ciki, dukka rufa ido ne? Kenan su kadai ne suke ganin ka
mar akwai mutane a ciki? Ashe babu kowa." Samha ke tambayar zuciyarta.
Nan fa hankalin kowa a ya tashi a cikinsu.
Malam ya shiga yi musu wa'azi mai tafe da fada akan ko su fadi alkhairi ko su yi shiru. Kuma su daina raya abu a ransu wanda ba
a yi shi ba kuma ba zaa taba yin sa ba, wannan ba daidai ba ne ya zama zato.
Samha ta daga ido ta kalli saman benen, ta ga babu alamar bil'ada sai yana da qura a jikin wandunan. Alama ta nuna gyaran kasan aka fara saman ma baa kai ga taba shi ba, sa
i an gama gyaran kasan sannan zaa hau sama kenan.
Gida dai yanzu a takaice ba na su Sharifah bane sun ma siyar kenan da dadewa. Subhanallah! Wannan abu da me yayi kama kenan? Akwai sarqaqiya, akwai tsoratarwa."
Su ka fito a sanyaye suka raka M
alam wajen motarsa, bai daina yi musu nasiha ba har ya shiga cikin mota, direbansa ya ja su ka tafi abinsu. Ya na zarginsu da bats masa lokaci kawai.
Mama na zaune a cikin mota tana ta jan katon carbi tana lazimi, ta na mai fargabar abinda zai afku
a ciki. Sai kwatsam ta ga sun fito Malam yayi tafiyarsa. Kanta ya daure, fargaba ta karu, tana tsoro ko abin ya fi karfin Malam ne ya sa ya sulale ya arce ya bar su.
Su ka karaso wajenta a sanyaye suka bude motar suka shiga, yayin da suka zauna sa
nnan su ka fara bata wannan mummunan labari. Ta dauki dogon salati ta salance, ta tabbatar rayuwarsu tana cikin wani hali.
Abin mamaki Hamidah su ka gani za ta shiga gidan hannunta dauke da qatuwar bakar leda, kamar wacce ta yo cefane. Ta juyo ta tsa
ya cak ta dube su, ta sake dubansu sosai, sannan ta shige cikin gidan.
Gaba dayansu suka ji kirjinsu ya harba. Toh wannan kallon qurillar da tayi mu su har da gyada kai na menene? Tabbas Sharifah ce wannan, kuma ta tabbata wannan ba mutum ba ce.
Aka rasa wanda ya iya yin magana a tsakaninsu sai salati kawai suke ta yi.
Samha ta zabura zata bi bayan Hamidah, sai Aliyu ya damqe ta ya ce "ki je ki ce musu me? Alhali ga abu ya nuna kiri-kiri ba mutane mu ke gani ba. Binciken na menene k
uma? Ai magana ta qare kawai."
Ta dage ita fa sai ta shiga ta ga in da Hamidah ta shiga. Aliyu da ya ga babu sarki sai Allah ta dage sai ta je, akan ta je ciki ta ga abinda zata sume cikin ya zube gara shi ya shiga ya tambayo ma ta. Dan haka da kans
a ya shiga.
A gigice ya tambayi ma'aikatan cewa ina budurwar yarinyar da ta shigo yanzu dauke da baqar leda da brown din hijabi ta shiga?
Su ka sha aradu cewa babu mace a gidan nan su ne kadai ma'aikata suke kai kawo a tsakar gidan nan.
Tabbas akwai sauran rina a kaba, rayuwarsu na cikin kwale-kwale kenan. Aliyu ya fito a gigice, ya nemi da su gaggauta barin kofar gidan nan tun kafin kuma a danna su a cikin gidan, su ma su fara bacewa.
Ya fi zaton ma wadannan ma'aikatan kamar su
ma ba mutane ba ne, dan ya ga wasu masu kama da fuskar Sharifah a cikinsu da kuma yadda suke amsa masa kamar ba normal ba ne.Baa ga kowacce yarinya ta shiga ciki ba, babu ma mace a gidan in ji ma'aikata.
Anas ne me tuqawa ya ja mota da sauri ya b
ar kofar gida.
"An kuma wato mace ta haifi mace." In ji masu iya magana. Wato Bello suka gani akan kwanar gidan a tsaye shi kadai. Ya zura musu idanuwa yana kallo ransa a bace.
Wannan karon babu wanda bai dafe kirji ba, dan firgici ga fuskar
Sharifah nan muraran.
Babu abinda ya sami lafiyar motar amma ta hau jarking ita kadai, ko da yake ba ita ke jarking din ba kafar direba ce ta shiga yanayin rashin kuzari.
Aliyu cewa yake "taka da sauri kada ka tsaya, wannan abu ya wuce tunanin
bil'adama a barwa Allah lamuransa kawai. Mu ci gaba da addu'a da neman tsari daga sharrinsu.
Mama ta barke da kuka ta ce "ni dai na fada muku mu rabu da bibiyar mutanen nan ko in ce fatalwoyin nan. Yadda suka fada kowa ya zauna a mahallinsa, In d
ai basu zo in da muke ba kada mu sake zuwa inda suke. Amma sam ba kwa jin magana. Samha kin nace musu, ki rabu da su haka."
Samha ta fashe da kuka ta ce "Mama kina ganin dai yadda Sharifah ta takura min duk ta in da na bi sai na ganta, ko a suffar ya
ra ko manya, mata da maza. Ta bude mana ido kawai ita muke gani a kasuwa, a cikin daki, a asibiti. Ina zan saka raina?"
Aliyu lallashinsu yake ya na fadin "a bar maganar kawai ni na san addu'ar da zan yi masu. Allah Ya fi su ba su isa su cutar da mu
ba."
Kowa ya tafi gida da sanyin jiki, basa rabuwa da yawan alwalla da nafilfli da addu'oin neman tsari ba kakkautawa.
*** *** ***
Kawayen Samha ne su dukka hudun har da karin guda daya ita ce ta biyar wato Fanna Baana wacc
e ta zo daga maiduguri suka kawo ma ta ziyara. Dan su duba lafiyar jikinta kuma a sake tattauna akan wannan annoba da ta addabe su wato Sharifah.
Samha ta rame ta kode babu kwalli balle 'yan kunne, baa maganar yin kwalliya daman. Abin tausayi ga yan
ayin laulayi da fargabar abinda yake cikin cikinta ma mutum ne ko aljan ko fatalwa. Dan ma ta dace da miji na gari mai sonta a ko da yaushe ya na tare da ita ya na kula da ita, ya na lallashinta. Ba dan haka ba ai da tuni ma ta shide ta mutu.
Aka hau
labari kowacce na fadar artabun da ta sha a lokacin da Sharifah da ta kawo musu ziyara.
Samha ta sake koro musu wani sabon labari wanda ya sake daure musu kai. Gidan nan dai da suka gani mai kama da kwango yanzu an gyara kuma ance ba su ne a a ciki b
a wasu ne daban, gida ya dade babu kowa a cikinsa. Babu Bello babu Hamidah, babu yaron nan da suka gani mai irin fuskar Sharifah da ya nuna musu get din fita.
Fannah na gefe tana sauraronsu amma ta kasa fahimtar abinda suke fada. Can dai ta yi musu
tambayoyi akan wacce Sharifah suke nufi wai? Su ka tabbatar mata Sharifah Nasir din dai da ta sani kawarsu da suka yi BUK ita ce ta mutu take yin fatalwa.
Fannah ta girgiza kai ta ce "da alama ku ne ku ka zare ba ku da hankali. Sharifah na raye ku
ma ta na nan a cikin wannan gidan na su. Ko shekaranjiya ma na tare har qanwata ta yi mata gyaran jiki da kunshi."
Sai suka fara tuhumar Fanna da ciwon hauka.
Fannah bata yi wata-wata ba ta jawo wayarta ta latso lambar Sharifah. Yayin da ta
saka speaker kowacce ta matso ta tattara hankalinta wajen sauraro.
Bugu daya aka dauka, muryar Hamidah ce ta amsa ta ce "Assalamu alaikum wararahamatullah Mama Fannah ina wuni."
Fannah ta ce " lafiya kalau Hamidah. Ina mamarki?"
Ta ce " gata a ku
sa da ni."
Ta miqawa Sharifah waya, ta amsa ga muryarta nan kuwa tangararai, dan tana da sanyin magana kuma wani lokacin tana jan kalma.
Ta ce "Fannah ya kike? Yaya aka yi? Ba ki koma ba ne? Ina jin dadin turaren wutar nan na ki. Ga Hamidah da
i tana tana ta turare mana gida."
Fannah ta ce " na gode. Wai ashe kin mutu yanzu na ji labarinki an ce kina yin fatalwa."
Sai ta yi shiru kadan sannan ta ce " in ji su Samha ko? Hmmmm rabu da su ba su da hankali."
Samha da su Nanah ne su
ka bude baki su na mamaki yayin da kowacce ta dafe kirji dan fargaba.
Komai Fanna ta ce sai Sharifah ta ce " Hmmm rabu da su ai basu da hankali." Amsar kenan da take ba ta.
Fannah ta kashe waya ta ce " kun dai ji da kunnenku, kowa anan ta san mury
ar Sharifah.
'"Innalillahi wa inna ilaihi rajuun." Samha da qawayenta ke kira yayin da kowacce ta miqe tana kai kawo, mamaki ya hana su zama. Musamman Samha abin ya yi mutuqar daure mata kai. Ta yi zaton ko mafarki take yi ma zata farka amma ina ba m
afarki ba ne da gaske ne Sharifah ce kuma tabbas da ta ganta a shoprite ta ganta da kunshinta ras, fatar nan ta sha gyara.
Fannah ta kasa gane abinda yake basu mamaki haka da daure kai. Shariqah dai kowa ya san ta rasu amma Sharifah na raye. Toh men
ene kuma abin mamaki haka?
Samha cewa take "dan baa garin nan kike ba ne shiyasa ba za ki taba ganewa ba, a baki labari ma bata lokaci ne."
Samha ta zabura ta ce "Fannah dan Allah ki yi min alfarma ki kai ni wajen Sharifah. Wannan zargin da wah
alar da take bani ya zo karshe."