Showing 27001 words to 30000 words out of 65015 words

Chapter 10 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

15

Ni ban damu ba ma da kaina, yaro ne yake ta ihu yana ciwon kunne shima aka ce mu bude masa file, amma basu sami damar zuwa su duba shi sabo

da gaskiya hankalin likitocin duk ya koma kan 'yan hatsarin da aka kawo .

Shine na zo zan wuce sai na ga wata kamar mamarki ta windo, nake tambayar Zahra na ce na ga wasu da na sani kamar Samha da Mamarta a can dakin. Ta tabbatar min ku ne. Na tamb

aya me ya same ku ina fatan dai ba hatsari ba ne ko gobara. Ta ce ke kina da karamin ciki, Mama na fama da hawan jini.

Da mu ka gama shine na shigo na dan in duba ku, kuma na taya ki murnar samun cikin da aka dade ana nema."

Samha ta ji dadin

samun wannan amsar fiye da sauran haka Aliyu ma. Sai suka kalli juna suka yi murmushi.

Anas ya yi gyaran murya ya gyara zama ya ce "da Mama ta zo ta ce bata ga kowa ba sai bayan da ta koma gida kika biyo ta, kawai sai ta ganki a uwar daki."

Sha

rifah ta yi dariya ta ce "ba zan fito ba dan naga gaba daya ranta a bace yake amma tabbas mun boye a daki muna sauraronta, Bello ma gidan ya bari dan takaici.

Bayan an kwana biyu na tabbatar ta huce na je gidanta dannmu yi magana sosai in tambayi abinda n

a yiwa Samha da take cewa in rabu da ita.Na iske Yunus a falo da alama baya cikin hayyacinsa ya sha wani abu, na ce yayi min sallama da Mama ya ce in shiga ciki kawai. Har ya roqe ni kudi, na dauko na bashi.

Amma da na shiga dakin sai na ga Mama tan

a sallah daga baya kuma na ga ta yi ruf da ciki. Na zaci ta idar ne kuma bata jin dadin jikinta ya sa ta kwanta. Na bata hakuri na tafi.

Na je gidan Nanah ma na ga ta runtuma da gudu. Haka da na je gidan Maryam da Rukayya da Halima suka dinga gudu w

asu na faduwa su na shidewa. Ba komai ne ya kai ni ba illa akan mu tattauna akan yadda na fuskanci Samha da family ta su ka dauke ni. Su yi musu bayani ni ba aljana ba ce ba kuma fatalwa ba ce. Amma suka ki su tsaya mu yi magana su dukka suka dinga watsewa

da gudu. Ta tabbata dai a aljana nake ko fatalwa a wajenku. Daga baya ma abin ya shiga bani dariya maimakon haushi."

Anas ya ce "da mu ka zo da daddare, yaro ya ce Mamarsa ta mutu sannan ya ce tana sama akan windo, Hamidah ma haka ta ce mana."



Sharifah ta yi dariya ta ce "ai su ai Mamarsu guda biyu ne da ni da shariqah, idan ka ji sun ce ta rasu Shariqah suke nufi, idan sun ce tana sama ni suke nufi.

Ina yawan zama akan windo, wannan ba komai ba ne sarata ce daman, ina da son hawa bis

hiya ko windo a sakandire Samha ta sanni da wannan halin. Saboda in dinga hango waje ne, dan ina samun saukin kuncin da nake ciki.

Wannan ne kadai hujjarkular da ta sa zaku ce na yi fatalwa?"

Aliyu ya ce "mun zo tare da Malam kwanaki aka ce

gidan Alh. Abdullahi Gama ne, ba gidanku ba ne, aka ce kwango ne gidan ya dade babu kowa. Shima abin ya daure mana kai."

Shardifah ta yi dariya ta ce " eh Alh. Abdullahi shine babban yaron mahaifinmu tun kafin ya rasu, kadarorinsa dukka a hannunsa yake

kular masa.

Shine kawai da na tashi yin gyara shi na damqawa komai. Kuma ni da yara mu na sama mun.kue ko ina saboda kura ba ma sauka. Wataqila shi yasa zasu ce babu kowa a gidan. Idan ta kama mu sauka akwai kofar baya, kuma mu na da wani get anan bangar

en ba sai mun hadu da su ba."

Tabbas a halin yanzu dari bisa dari sun yarda Sharifah tana raye ba fatalwa ba ce, sun yarda da hujjojinta.

Samha ta gyara zama ta dafa hannun Sharifah ta ce "ki gafarce ni qawata mun yi miki mummuna zato. Ki ba

ni labarinki. Menene damuwarki gaba daya kika kode kika canja kika fita hayyacinki? Akan me kika je kotu? Waye ya kai ki ko wa kika kai har aka yi miki rashin adalci a Shari'a? Shariqah ciwo ta yi ta rasu? Ina danginku na ga ku na rayuwa a gidan nan ku ka

dai?"

Sharifah ta yi shiru yayin da ranta ya baci nan da na kamanninta suka canja. Ta dago da jajayen idanuwanta ta dube su.

Ta ce "na rantse da Ubangijin da ya halicce ni Ya halicci Shariqah babu gudu babu ja da baya akan abinda na saka a gab

a har sai na kwatar mata hakkinta duk da ta rasu. Idan duk duniya za su taru akaina su na magana su na karya ni, ba zan daina fada ba. Matattu su na sanin abinda yake faruwa a duniya tun kafin ma mu rayayyu mu sani, saboda duk abinda

zai faru sai na ga Sha

riqah. Ni da Shariqah mu na zama mu yi magana kamar yadda nake zaune da ke ina magana da ke haka."

Aliyu, Anas da Samha ne suka hada ido. Ashe dai tataburza da fatalwa bai kare ba. Sai kowannensu ya gyara zama dan jin wannan labari mai sarkaqiya.

Madalla da ALQALAMIN JUT

Alhamdulullah

End of part....1

KARIN BAYANI:

Na ji dadi da ku ka nishadantu, ko ba komai wannan labarin ya dawowa da wadanda basa son karatu sha'awar yin karatun.

Wadanda basu taba bibiyar Hausa novel ba, sun

bi shi.

Zan sami rana guda a facebook in kasance tare da ku saboda masu tulin tambayoyi akan labarin, zan amsa muku dukka tambayoyinku in sha Allah.

Wasa farin girki, anan ne "real true life story" din labarin ya ke. HIRA DA MATATTU ya kasance tsaka

nin Sharifah da Shariqah ne ashe. Na su Samha dukka zato ne. Ikon Allah! Akwai cakwakiya ba 'yar kadan ba nan gaba.....

HIRA DA MATATTU .....Part 2

Zai fito a complete decument PDF, ga wanda yake so ya biya 300 kacal.

A tuntube ni a lambar waya:

08037196708

Acct.no:

0112240731

Gt bank

Jamila umar tanko

HIRA DA MATATTU

Jamila Umar Tanko:

JUT

Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko

Copyright: Jamila umar tanko

Wannan littafi mai s

una HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne.

300 ne kacal Zaa biya

0112240731

Gt bank

Jamila umar tanko

Idan an biya a turo shaidar biya ta wannan lambar:

08061225337

Na gode

HIRA DA MATATTU .....1 (True life story)

Haqqin Mallaka: Jamila

Umar Tanko

Copyright: Jamila Umar Tanko

Saudaukarwa:

Na sadaukar da wannan littafin ga matan da suka yi jahadi wajen biyayyar aure ko su na raye ko sun rasu. Allah Ya duba yaransu ya raya su akan sunna.

Gargadi:

Baa yarda wani/wata ta juya l

abarin ban zuwa wata Shiga ba fim ko rubutu ba tare da izinin Marubuciyar ba. Sannan ban yarda a karanta shi a you tube channel, ba tare da izinina ba.



[2/28, 5:26 PM] Jamila Umar Tanko: 1

Sharifah ta ci gaba da cewa "duk wan

da ya san ni a duniya toh ya san ni tare da Shariqah dan kamar 'yan tagwaye mu ke. Mun shaqu sosai kamar yadda uwa take shakuwa da 'ya'yanta.

Bayan son Allah (S.W.A) da ManzonSa (S.A.W) daman wannan baa hada su da kowa, sannan iyaye su daban ne. Duk

duniya babu abinda na fi so irin yadda na ke son Shariqah, haka itama.

Ita karamar kanwata ce ba ita take bi na ba ma, Bello ke bi na ita kuma take bin sa.

Na riga ta yin aure da dadewa, amma a kullum tana gidana, idan ma bata zo ba ni zan j

e gida saboda ita, kasancewar mijina ba zaunin gari ba ne, yayi min lamuni idan baya nan zan iya tafiya gida in kwana. Kusan kullum tare muke kwana shinfidarmu daya, mu na raba dare mu na hira.

Baiwar Allah ta fi ni hakuri da hangen nesa, ko da zan

zazzage ta sai ta fada min gaskiya.Babu mai goyon bayana a duniya irin ta, komai girman matsalata tana tare da ni kuma ita kadai nake fadawa komai nawa.

Ko kwalliya na yi idan Shariqah ba ta ce na yi kyau ba toh ba na yarda akan na yi kyau din.



Na haifi 'yata Hamidah, na rantse da Allah bayan wahalar daukar ciki watanni tara da nakuda da shayarwa zuwa kwana arba'in ban san wahalar raino ba. Shariqah ce komai na game da kula da jaririya, duk wata kazantar jariri da zaryar zuwa asibiti ita ce.



A lokacin ina tafiya jami'a wani lokaci ma ina gida a kwance ita ke faman rainon Hamidah. Har fada ake yi da ni ina cewa idan ba za ta yi ba a bar 'yar a wajen.Mutane su cika da mamaki. Ta yaya uwar da ta haifi 'yarta zata ce haka? Saboda na san ai b

a za ta iya barin 'yar ba ne shiyasa nake cika baki.

Watanni takwas kadai Halidah ta yi ta na shan nono, na yaye ta, na damqawa Shariqah suka kaura gidansu gaba daya.

Hamidah ta tashi a tunaninta Shariqah ce mahaifiyarta, ta sanni amma ta dau

ka ziyara kawai nake kawo musu a matsayina na 'yar uwarsu.

Hamidah ta sha laulayi na jinya kala-kala haka Shariqah ta ke wuni a layin asibiti tana jinyar ta.

Samari da dama 'yan gayu sun sha ganinta a hanya su na so, daga sun matso suka gant

a da 'ya har tana kiranta mummy sai su yi kwana a zatonsu matar aure ce.

Qawayenta har tsiya suke yi mata cewa sai an yi kwalliya zaa fita unguwa kawai sai ta dauko musu 'ya tana bata musu tsari. ita kuwa sai ta ce idan zaa so ta dole a so ta da 'y

arta.

Ko tafiye-tafiye su ka yi qasashen waje da yake makarantar kudi ta yi kuma dukka qawayenta 'ya'yan masu hali ne ta kan fada musu ita bata son su siyo mata komai su siyowa 'yarta Hamidah. Ko ba ta fada ba ma sun san abinda zasu yi ya faranta

mata rai shine su yiwa Hamdah sayayya.

Daman gashi kamarmu daya ni da Shariqah dan haka Hamidah ta yi kama da ni sai ta yi kama da Shariqah.

Aure ne kadai ya raba Shariqah da Hamidah. Na tabbatar da ta auri miji mai fahimta da daman da ita z

a ta tafi amma bata yi wannan sa'ar ba. Aka bar Hamidah a wajen mahaifiyarmu.

Mahaifin Hamidah ba mutumin da ya san darajar gidansa ba ne, haka ba mai kula da haqqin iyalansa ba ne, shiyasa ma ya bar 'yarsa ake riqonta dan bai sauke nauyin da Allah

Ya dora masa ba.

Hakan ya fiye min alkhairi saboda idan na dauko ta na kawo ta gidana ma akan Hamidah kullum sai mun yi fada.

Mutum ne da baya son zaman lafiya ko kadan, Idan ya na so ya bani haushi ko ya takale ni da fada toh sai ya hau

azabtar da ita dan haka ne ma ta taso da tsoronsa kuma bata son ganinsa ma ko kadan.

Bai sauke haqqina da Allah Ya dora masa na ciyarwa, sutura, asibiti, muhalli ba, dan haka bai hana ni fita neman kudina kowacce kasa ba. Dan mutuwar zuciya ma na

wa yake so ya ci saboda zuciyarsa ta mutu.

Mahaifiyata na tsaye tsayin daka akan matsalolina da na 'yata dan haka da jarina da na ta nake juyawa.

Hakkinmu da ya tauye shine ya jawo masa koma baya, baya ganin daidai a dukka aiyukan da yake

yi. Kullum ana korarsa daga aiki ya na wahalar neman wani aikin. Wannan kuma na bar shi da Allah, na ci gaba da kula da kaina da 'yata da taimakon Allah da taimakon mahaifiyata.

Mu ka bar Hamidah a Karkashin kulawar mahaifiyata amma kuma a koda yaus

he tana zuwa gidan Shariqah kasacewar gari daya ne kuma tazarar unguwannin babu nisa.

Allah Ya bawa Shariqah haihuwa a jejjjere ba tsayawa. Allah Ya jarrabe ta da auren miji mai tsanani da kishiya da 'ya'yan kishiya mararsa kirki. Babban abinda ya

kara kawo tangarda su na zaune su dukka a cakude a gida daya, bata jin dadin zama da su ko kadan.

Shariqah mace ce mai hakuri, komai sai ta rufe bata fadar damuwawarta. Hamidah ce kadai ta san komai ita ce abokiyar shawararta amma sai ta ce ma ta k

ada ta fada min. Saboda sun san ina da zafi wasu lokutan bana son rainin hankali.

Mahaifiyarmu mace ce mai son yara kuma a tsaye take akan matsalolin yaranta.Ko bayan rasuwar mahaifinmu ba mu ce wayyo Allah ba, saboda ba mu rasa komai ba. Mace ce mai

kamar maza ta yi nata ta yi na wasu ma.

Wahalar da Shariqah take sha a gidan miji bai nuna ba saboda ga ta a kusa da mahaifiyarta mai sonta mai taimakonta da dukiyarta da nuna ma ta so da kauna da bata shawarwari akan ta yi hakuri rayuwar aure iba

da ce.

Sai bayan da mu ka rasa Mamarmu sannan maraici dukka ya bayyana a jikin Shariqah.

Bayan masifaffen kulle wanda ko islamiyya baa zuwa a gidansa, daman biki ko suna da gaisuwar mutuwa, dangi dukka sun sallama ta baya bari ta je a cikin

Kano ma balle a wani gari.

Dukka kayan dakinta masu kyau masu tsada na kasar waje, sai da suka kwankwatse, baya gyara balle ya canja musu kuma ke matar gidan da kudinki ba ki isa ki kawo masu gyara su shigo masa gida su gyara miki ba. Har da mugunta

'yayan waccan matar suke zuwa su lalata mata komai dan ita bata magana.

Ta rame, ta yi baqi-qirin ta fita daga hayyacinta. Wataran kudin Pampers guda daya jal sai ta gagare ta balle na cerelec da zata bawa yaranta bata da shi, kuma shi babu wadanna

n a cikin lissafinsa.

Yaranta sun tashi babu kuzari da yawa ma tana goyonsu sai da suka kamu da ciwon tamowa wato na rashin balance diet. Yara kanana sai dai su ci mai da yaji.

Suturun da ta saba sakawa babu irinsu sai dai masu arha taron yuy

uyu, man shafawa da sabulun da ta saba yin amfani da su a gidansu dukka babu. Kuma ya na da halin da zai yi fiye da hakan amma baya yi."



*** *** ***

Sharifah ta yi shiru ta yi tagumi dan tsananin takaici ta kasa kuka amma radadin da zuciy

arta ke yi ya nuna a cikin idanuwanta. Sun yi jajawur, ranta a bace.

Samha ta dafa hannunta tana jinjinawa alamar tana ba ta hakuri.

Sharifah ta yi ajiyar zuciya ta ce "maganganun su na da yawa akan mutumin nan Adamu, ga shi sun haifi yara da y

awa tare. Alfarmar yaran nan ta sa ba zan iya fadar rabin azabar da ya bawa Sharifah ba. Ko rabin-rabin abubuwan da suka faru ba zan iya fada ba. Wasu ma har yanzu ban sansu ba, an boye min baa so a fada min. Wasu kuwa ta kunshe a ranta ta tafi da kayanta

ba zata iya fadawa kowa ba."

Samha ta gyada kai ta ce "na fahimce ki kawata ki ci gaba da labarinki ki fada mana wanda zai iya faduwa. Na jinjinawa mata masu jahadin zaman aure irin su Shariqah. Aljanna na nan na jiran mata irinsu da su ka rayu ciki

n ukuba su ka yi biyayyar aure. Kamar Rabi'atul Badawiyya(RA) matan aljanna."

Aliyu sai kabbara yake ya na jan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login