Showing 24001 words to 27000 words out of 65015 words
Da farko Fannah ta ki amincewa saboda tana so ta shiga kasuwa kafin magrib, dan za ta wuce maiduguri jibi.
Sauran kawayen dai su na kokonton bin su amma Samha ta ce su zo su je tare kawai.
Aliyu ta kir
a a waya ta shaida masa abinda ya faru ga Fannah da su Nanah zasu je a akai wajen Sharifah tare yanzu ayi ta ta kare.
Aliyu ya yi rantsuwa akan kada ta sake ta je gidan Sharifah, idan kuwa ta je zaa sami gagarumin matsala a tsakaninsu. Ya na bata
umarni ta zauna a mazauninta, Sharifah ta je can ta karata ko mutum ce ko aljana ce ba ruwanta.
Wai! Samha ta fusata babu yadda ta iya da shi, a dole ta hakura da zuwan daman dai ita ce mai son zuwa su Nanah 'yar luluta daman tana kokonton zuwa dan b
a zata iya fafarar gudu ba.
Fannah ma daman bata son zuwa nan da nan suka shiga lallashin Samha akan ta bar wannan maganar kawai.
*** *** ***
Bayan sati guda da faruwar wannan al'amari Aliyu yana ta dai karantar yanayin Samha, sam
bata da kwanciyar hankali bata walwala. Fushi take yi da shi da alama hankalinta ba zai taba kwantawa ba har sai ta tantance wacece Sharifar nan da take gani.
Babu zato babu tsanani kwatsam ranar wata asabar ya ce ta zo su je unguwa, ta nemi ya fa
da ma ta inda zasu je ya qi fada. A kofar gidan Yaya
Anas ya tsaya ya kira shi a waya shi ma ya fito a shirya tsaf da alama daman ya san da tafiyar.
Ita dai tana zaune a mota kamar gunki ta cika da zulumi da mamaki.
Ba su tsaya a ko ina ba sai
a kofar gidan su Sharifah. Samha zata yi magana.
Aliyu ya ce "kada ki ce komai damuwa da gaba da kike yi min akan na hanan ki zuwa wannan gida sun kare a yau, mu shiga ciki kawai.
Su ka yi ta leqe-leqe a kasa da alama an gama gyaran har an ru
fe kofofin. Su ka lalubi hanyar sama suka hau Aliyu ne a gaba da alama ya cire tsoron komai. Samha cike da fargaba tana biye da shi yayin da Anas ya kasa cewa komai yana ta jan kafa ga tsoro ga son girma.
Suka tsinci matattakala a wani lungu su ka
haye su na hawa suka ga kofar falo a bude suka fada.
Tsarki ya tabbata a ubangijin talikai. Fargaba babu irin wacce basu ji ba. Sharifah, Hamida,Bello da yara biyar suka iske a zaune a wani tangamemen falo na alfarma mai kyawun gaske. Ga fitilu ga
kujeru na alfarma, ga screeding da pop sabon tiles ne aka malala a ko ina, da alama gidan an yi masa gagarumin gyara ne.
Sharifa ce tas a kamanninta na asali sun ci kwalliya gidan yana ta kamshi girki kala-kala. Hamida na fitowa daga kicin ta na j
erawa akan dining table.
Aliyu ya yi sallama ya dan tsaya, babu wanda ya kalle su balle a amsa. Samha ma ta rada sallama amma shiru kake ji babu wanda ya kalle su, su na tsaye carko- carko da alama ma kamar ba su san mutane sun shigo ba gidan ba.
Samha ta kwalla da karfi Sharifah wajenki fa muka zo. ku ba musulmai ba ne ba kwa amsa sallam?"
Shiru babu amsa, Anas ya ce "kada mu shiga ciki dan na ga alama kina kokarin samun kujera ki zauna. Yanzu mu ne muke ganinsu su ba sa ganinmu."
Samha ta ci gaba da yiwa Sharifah magana amma shiru kake ji.
Hamidah ta gama hada komai ta shaida musu an gama. Sharifah, Bello da yara aka hau kan dining table aka fara cin abinci.
Samha dai na tsaye yayin da Aliyu ya lura jiri na dauk
ar ta ya kamata ya zaunar da ita akan kujera.
Ta fashe da kuka ta ce "Aliyu! Wannan wanne irin abu ne? Ta yaya yanzu kuma Sharifah zaa ce ba ta ganinmu mu mu ke ganinsu?"
Aliyu ya ce "ai kin ce a zo a yi ta ta kare ko? Ga mu ga su ai. Ki kw
antar da hankalinki."
Samha ta zabura ta tafi gaban teburin ta tsaya ta kwalla kiran sunan Sharfah gami da kama Sharifah ta girgiza ta, ta ce "karya kike Sharifah ki na ganina kuma kina ji na ki bani amsa."
Sharifah ta fusge ta ci gaba da cin
abincinta ta ki yin magana.
Fargaba ya ruftowa Aliyu da Anas gudun abinda zai je ya zo yadda ta cakumo fatalwa haka.
Samha ta bi yaran tana girgizawa tana cewa "ku fada min gaskiya amma ku ku na ganina ko?"
Shiru babu wanda ya yi mag
ana a cikinsu. Aliyu ya ja hannunta ya ce ta zo su tafi kawai.
Samha ta sami kujera ta zauna ta ce yau ba inda zata je sai an yi ta, ta kare ko ma macece Sharifah sai ta gani ko da kuwa ajalinta ce.
Sharifah ta gama cin abinci ta taso ta zo
zata wuce daki. Samha ta yi tsalle ta tare gabanta, idan ta goce sai ta tare ta, idan ta canja hanya sai ta tare gabanta ta hana ta wucewa.
Samha ta fada cikin fusata "wajenki na zo kuma na shirya jin labarinki."
Yanzu Samha ta tabbatar Shar
ifah na ganinta tas. Dan haka Sharifah ta samu kujera ta koma ta zauna.
Samha na tsaye a kanta ta kama qugu tana girgiza wato yau ko a mutu ko ayi rai.
Sharifah ta ce "au Samha ashe babu dadi kana raye a dauke ka fatalwa, ko aljana. Da farko
ban gane haka ku ka dauke ni ba, sai daga baya na gane bayan zuwan mamarki da ta yi take zage-zage.
Anas da Aliyu dai na tsaye har yanzu sun kasa tantance abinda yake faruwa.
Sharifah ta cewa Samha "ki zauna mu yi magana tunda yanzu kin yarda S
harifah mutum ce."
"Anas da Aliyu ku na iya zagayowa ku zauna in har kun amince gidan rayayyu ne ba gidan matattu ba ne."
Samha da su Aliyu suka zauna amma har yanzu kansu a daure yake.
Da Sharifah ta fara bayani sai da su dukka suka
yi mamakin abinda yake fitowa daga bakinta .....
Madalla da
ALQALAMIN JUT
HIRA DA MATATTU ...13
NA
JAMILA UMAR TANKO
(JUT)
Bello ya gama cin abinci ya zo zai fita, Sharifah ta ce "Bello! Yanzu ka na ganinsu,
dan haka ku gaisa."
Ya dan bata fuska ya tsaya yayi shiru gami da yin dan siririn tsaki ya ce "Aunty Sharifah ki na ganin wulakancin da suke yi mana fa. Wannan group su zo su leqo sai su turo wannan group din, ashe mu a fatalwa suka dauke mu."
Zo ka ga idanuwan Anas da Aliyu sun yi carko-carko, har yanzu fargaba bata bar zuciyarsu ba basu gama yarda ba tukunna.
Sharifah ta yi murmushi ta ce "ba komai ka gaishe su."
Ya miqawa Aliyu hannu, sai da Aliyu ya dauki 'yan sakonni yan
a addu'a sannan daga baya yayi shahada ya miqa hannu suka gaisa dan har yanzu zuciyarsa bata gama tantancewa ko da cikakkun bil'adama yake zaune ba. Daman Anas tun baa zo kansa ba ya boye hannayensa a hamata. Daga nesa ya " Ah Malam Bello salamu alaikum."
Bello ya fice ya bar su anan wato su karata.
Sharifah ta sake juyawa ta dubi yaran ta ce "Hamidah yanzu ku na ganinsu ku zo ku gaishe su."
Hamidah da kannenta suka zo suka risuna suka gaishe su.
Su Samha suka amsa cikin sakin fus
ka mai tafe da yaqen dole. Amma sun kasa gane ma'anar kalaman Sharifah da take cewa "a yanzu ku na ganinsu" din nan da take ambata. Da gaske ne ada basa ganinsu kenan ko kuma abinda ta karanta musu kenan su nuna basa ganinmu?
"Kai Sharifa Ja'ira ce w
allahi." Samha ta fada a cikin zuciyarta.
Sharifah ta fara magana cikin nutsuwa, ta ce "na jima da dawowa kasar nan amma ban nemi kowa ba saboda ina cikin wani mawuyacin yanayi,
matsananci kuma marar dadi, ba dadi ne ya kawo ni kasar ba, na shigo Ni
geria a gigice.
Kwatsam ina zaune sai na gamu da aminiyata Samha, ba ki ganni ba amma na yi miki magana. Har ma na yarda ki shiga cikin ofishin da na shiga ko da kuwa za ki ji sirrin da babu wanda ya sani.
Samha ta ce "amma bayan mun fito da
ga ofishin sai komai ya canja, na ji kalamanki ba irin na mutane ba ne. Da na ce ki bani lambar wayarki kike ce ina ruwan matacce da amsa waya. Me kike nufi? Kin tsorata ni.
Sharifah ta gyada kai ta ce "eh na fadi haka ne a cikin alhini da bacin rai
saboda na tabbatar yaqin da na tunkara ba karami ba ne. Na kai karan babban alqalin da bai yi min adalci a sharia ba.
Kuma na sallama duniya ban qi in mutu a wajen neman gaskiyata ba."
Samha ta sake cewa da na juya ofishin sai na ga a kulle alhali
yanzu muka fito.
Sharifah ta ce "eh kin juya baya ne amma ni na ga fitowar alqalin daman yace min yana sauri zai shiga ofishin alqalin alkali."
Samha ta ce "da na juyo sai kema ban ganki ba kin bace."
Sharifah ta yi dariya ta ce "ba wani
abin mamaki ba ne dan ba ki ganni ba, in kika lura ai sauri nake kuma daman mu na tsaye ne a daf da kwanar da zan hau kan matattala, tafiyata kawai na yi."
Samha ta sake tambaya ta ce "sai na sake ganinki kin dawo kin shiga ofis din kafin in karaso
na rasa ki, babu ke babu alqali."
Sharifah ta yi ajiyar zuciya ta ce "nima ban same shi ba, sai wasu na samu a cikin ofishin na basu photocopies din takardun kawai su ajiye masa,ina sauri yara sun kusa dawowa daga makaranta kawai na nufi bakin get."
Samha ta gyara zama ta ce "sai na hango ki za ki shiga adaidaita sahu, ina ta kwalla miki kira kika qi tsayawa."
Sharifah ta yi ajiyar zuciya ta ce "na ji kamar an kira ni na waiga ban ga kowa ba sai kawai na tafi."
Samha ta ce "na ganki
a danja (traffic light) ina ta kiranki ba ki amsa ba."
Sharifah ta girgiza kai ta ce "hankali ne ke gani amma tabbas da na ganki da na tsaya."
Samha ta kalli Aliyu ta juya ta dubi Anas aka yi shiru sannan kowa yana tunani.
Sharifah ta ka
tse musu tunani ta ci gaba da cewa "saboda wannan dalilan ne kawai sai na zama fatalwa kuma?"
Samha ta yi gyaran murya ta ce " A' a ba shi kadai ba ne, na zo gidan nan na ga wasu yara a waje na tambaye su ko an yi mutuwa a gidan nan? su ka hau musu,
wani ya ce Sharifah ce ta rasu wani ya ce Sharqah ce ta rasu, su ne suka fara rikita ni. Amma sai na hango ki daga kan bene babu riga, gashin kanki ya tashi sama, ga wasu kuraje a dukka fuskarki da kishinki alhali ban sanki da su ba, kika tsaya kina kallo
na."
Sharifah ta yi ajiyar zuciya ta ce " Eh na sami matsalar kuraje a fuska da wuya sannan daga wanka na fito a lokacin na wake gashina ne ban taje ba. Na ji an taba get sai na leqo. Ina cewa ki hawo sama amma ba ki ji ba. Da Hamidah ta shigo na ce
ta ce ki shigo, kuma ta saka sakata, saboda idan an bar get a bude mu na sama ana yi mana sata. Ki ka qi shigowa Hamidah ta ce kin fita da gudu, sai na yi mamaki.
Na raka yara islamiyya na hango ku da motocinku kun tsaya a kofar gidana, msganar gask
iya bana so kowa ya ganni a cikin wannan yanayi da nake ciki gidana datti, kamannina dukka sun canja. Shiyasa na bari sai da
ku ka shiga na bi ta kofar baya na haye sama na buya. Bayan na tura ki cikin falo dan a lokacin na lura tsorona kike ji.
Na je
gidanki dan in sanar da ke cewa ke kadai na yarda ki ganni ki daina gayyato min su Nanah. Tabbas su Nanah ba za su fahimce ni ba, gulmata kawai zaa dinga yi ana cewa ta kare min na dawo kasar nan duk na lalace. Kin fi kowa sanin halinmu na mata da gulma.
Mijinki ne yayi min iso har cikin dakinki amma ki dinga zabura kina shigewa. Na ji jikinki da zazzabi sai ban kawo komai a raina ba na zaci rashin lafiyar ce kina magana a hankali."
Samha ta yi shiru can ta ce " toh yaya aka yi ki ka san su Nan
ah na hanyar zuwa gidana, kika tashi kika tafi da sauri? Daga tafiyarki suka shigo kuma?
Ta yi dariya ta ce " a lokacin da na zo Aliyu ya fada min, ya ce "kin riga su karasowa, Samha ta fada min daman tare da su Nanah za ku kawo ma ta ziyara. Kin ji
inda na ji labarin zuwansu amma bana duba."
Samha ta kalli Aliyu alamar tambaya ta cika a idanuwanta.
Ya gyada kai ya ce "eh an yi haka na dauka dukka team dinsu daya ne, ita ta fara yin gaba.Tabbas na fada mata haka."
Samha ta yi ajiyar zu
ciyar samun kwanciyar hankali ta ce "a ranar kin fada Bello ya rasu kuma alqali ya rasu."
Sharifah ta gyada kai ta ce "ranar ma daga wajen gaisuwar alqalin nake tabbas haka ne. Bello kuma da na ce ya rasu ba wannan Bellon ba ne, babban yayanmu Yaya Be
llocity shine ya rasu kwanaki kadan bayan rasuwar Shariqah. idan za ki tuna sai da na tambaye ki ma na ce daman kin san shi ne? Ai ni ban zaci wannan Bellon ba ma kike nufi."
Samha ta ce " zuwanki asibiti da tsakar dare fa, kum yaya aka yi kika san i
na da ciki tun kafin ni kaina in sani? Wannan shine gagarumin abinda ya fi tayar mana da hankali."
Sharifah ta yi dariya ta ce "wannan gaskiya ne, abinda ya faru a ranar shine. ina fama da ciwon kafa likitana kuma baya gari, ya ce in yi sauri in tash
i in je emergency in ga wani likita da ya hada mu. Tun karfe goma na dare har zuwa karfe dayan dare mu na emergency ban ga likita ba saboda file dina ya bata.
Na gaji da jira sai na tuna da Metron Zahra kanwar kawata da muka zauna a turai. Da mu ka
yi waya da ita sai ta ce in zo ta duba ni ko ta hada ni da likita. A wannan ward din da ku take aikin kwana.