Showing 30001 words to 33000 words out of 65015 words

Chapter 11 - HIRA DA MATATTU COMPLETE

Unknown   

28 Aug 2026

21

gemu an tabo babin ustazai, ji yake dama ya hadu da wannan mijin na Shariqah ya yi masa nasiha.

Anas kuwa babu abinda yake yi sai gya

da kai yana tunano irin bautar da yake yiwa matarsa Binta, da irin 'yancin da ya bata na sakewa ta yi abinda take so, ta je inda take so amma bata gode masa daga ita har iyayenta.Ta na ta bin zugar qawaye da dangi. Ya ji dama Shariqar ya aura ta yi masa w

annan biyayyar shi kuwa ya jiye mata dadi. Dan ya so Shariqah a rayuwarsa, ya so ya aure ta Allah bai kaddara ba. Kwatsam kawai ya ga katin daurin aurenta ba dan tana son mijin ba sai dan kadararrar aure da ta haihuwa. Wanda babu mahalukin da ya isa ya han

a kaddarar bawa ta faru da shi. Wannan haka yake komai mukaddari ne kuma rubutacce ne.

*** *** ***

Sharifah ta ci gaba da cewa "Ko Shariqah tayi yunkurin fita daga gidan idan abin yayi ma ta yawa, mijin yana tsoratar da ita da cewa idan t

a fita ma ina za ta je? Tunda bata da sauran gata iyayenta gaba daya sun rasu, danginta babu hadin kai, babu mai kula da ita. Kuma idan zata fita bata isa ta tafi da yaransa ba har da na goye, duk kotun da zasu je sai ya kwace su.

Wannan rashin fa

himtar ita take saka mata da yawa ci gaba da zama a ukuba a gidan mijin da yake gallaza musu har su rasa rayuwarsu.

Ta kai ta kawo gidanta da suturarta da ta yaranta babu tsari gaba daya ba irin rayuwar da ta taso ba ce, ta fada wata rayuwar da ba aj

inta ba ne, ba ta saba gani ba.

Shariqah kyakykywar mace ta koma abar tausayi, baqiqirin ta rame babu maganar gayu ma.

Aure bautar Allah babu wanda ya damu da ita a dangi, wasu lokutan ne ma idan na ganta na kan hau fada ina cewa akwai abinda t

ake boyewa zan sami mijin in yi masa magana. Sai ta hana dan ya dora su akan kishiyarki na jin haushi dan na yi miki abu kaza dan haka ko marinsu yayi kokari suke su fito su na yaqe su na dariya kada kishiya ta gane an yi fada.

Ya same su ya dinga c

in karansa babu babbaka babu wanda yake yi masa magana. Bayan rashin wadatasu da kudi ga tsananin kulle, su ba zasu fita ba kuma baya so a zo.

Takai ta kawo yana korar baqinsu, Idan bakuwa zata kwana sai dai a boye takalmana ta. Kishiyar na lallaba

wa ta fada masa akwai bakuwa a gidan Shariqah. Sai da tsakar dare misalin karfe goma sha biyu sai yayi sumame ya shiga ya ritsa su...."



*** *** ***

Sharifah ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana saboda tsantsar radadin da take ji a

cikin zuciyarta tamkar fami labarin yake yi ma ta, akan katon gyambon da yake fafare a cikin zuciyarta."

Samha ta dafa kafadarta ta girgiza ta, ta ce "ki zubo da hawayen zai sa ki ji sanyi. Saboda Idanuwanki sun yi jajawur, zuciyarki ta na bugawa da

sauri."

Sharifah ta girgiza kai ta ce "haba Samha tun yaushe na wuce babin yin kuka akan bil'adama. Na yi rantsuwa da Ubangijin da Ya busa min numfashi ba zan sake yin kuka ba, sai dai in kai su kara wajen Allah wanda Shine gatana kuma gatan Shariqa

h, in roqe Shi ya nuna min hanyar da zan bulle wajen daukar mataki da fansa.

Na shiga bala'an da ya fi karfin kuka, mutane sun ba ni mamaki kuma sun ci amanata wanda a baya ban taba sanin haka mutum yake ba sai yanzu."

Samha ta fara tausayawa

Sharifah tun bata gama jin labarinta ba. Ta tabbata Sharifah ta shiga bala'in da a dole ma kamanninta suka canja, ta rame ta yi baqiqirin tayi kuraje.

Sharifah ta ci gaba da cewa "mijin Shariqah ya binciko bakuwar Shariqah, ya hada su su dukka ya c

i musu mutunci. Shariqah na kuka bakuwar tana kuka ya ce ya yi rantsuwa ba zata kwana a gidansa ba. A cikin daren ya kore ta daga gidan, kuma 'yar uwarmu ce daga wani gari me nisa ta zo Kano yin sari. Ba ta san yadda zata bi ta je unguwar wasu 'yan uwan na

mu ba. Yarinya budurwa ya kora a cikin dare dan qarfe goma sha biyu ta gota.

Akwai karamar kanwar mu wacce muke uba daya mai suna Dinar, watarana ta zo hutu daga makaranta kwana itama aka ce sai dai a boye ta, har ta gama yin kwanakin da zata yi ba

zai san tana ciki ba dan idan ya sani zai iya korar ta itama.

Ba ta san shi ba sai dai ta dinga leqensa ta windo, tunda bata nan aka yi aurensu kuma bata zuwa gidan.

Yaran Shariqah basu san danginta ba saboda baa kai su ziyara, toh uwar ma

bata je ba balle yaranta. Dan haka basu san kowa ba sai wadanda suke iya daurewa da wulakancinsa su je gidanta.

Asibiti ne kadai ya yarda ta je shima sai ya hada da tsine-tsine idan ta kuskure ta biya wani gidan. Wato ya san ta tara barka da gaish

e-gaishen mutuwa bila adadin dan bakar mugunta shine baya so ta je ta sauke nauyi.

Tunda ya fatattaki kawayenta da 'yan uwa ai zai fi samun damar da zai ci karansa babu babba akanta wannan ce manufarsa.

Ta koma baiwarsa ba matarsa ba, ko

generator zaa kunna sai idan yana gidan idan zai fita sai ya kashe, sai ya dawo zai kunna. Idan yayi tafiya kuwa idan zai yi wata guda ke matar gida ba ki isa ki kunna ba, ko da kina da kudin siyan man fetur.

Daman ita uwar gidan 'yar wahala ce bata

fito daga gidan dadi ba, ita Shariqah ce duk bata saba da wannan qangin ba. Akwai ranar da ta zuba mai a inji ta kunna. Ta kashe lafiya kalau amma dan annamimanci sai uwar gidan ta aiko danta ya yanke igiyar saboda idan ya dawo ya gan shi a lalace sai ace

Shariqah ce ta kunna. Haka kuwa aka yi, ya zo ya tambaya aka gada masa Shariqah ce ta kunna, ya ci ma ta mutunci tas.

Sunan kishiyar Talatuwa ita da 'yayanta suka dinga hada mata tughu kala-kala, a gaban Hamidah ake yin wasu abubuwan sai Shariqah t

a ce kada Hamidah ta fada min .

Abin ya kai har qawayenta da suka yi makaranta tare suka ga halin da take ciki ya kazanta. Hatta kujerunta na falo sun lalace idan baqo ya zauna akai sai ya zurmuka ciki sai an zakulo shi. Su ka hada meeting cewa anya

kuwa na san halin da Shariqah take ciki kuwa? Amma aka yi shiru aka zuba masa ido? Su ka yi niyyar su zo su same ni. Daga baya me suka gani dai suka fasa zuwa dan su na ganin zaa ce sun shiga abinda da ba ruwansu tunda tana da dangi babu wanda ya taba yi m

asa magana, su yaya zaa yi su tsoma bakinsu?

Wataran ledar pure water da za ta siya su sha ta gagare ta, bata da shi komai bai wadace taba.

Idan ma asiri ya yi ya rufe mana baki toh asirinsa ya ci dan babu wanda ya iya yi masa magana.

Ta

yi hakurin jiran kudin hayar gidanta na gado dan ta gyara kujerunta amma da kudin suka zo sai ya karbe. Ya ce shi zai samo mai gyaran. Ta san halinsa ba zai taba bari maza su shigo su kwashi kujerun ba, har gara ta lallabashi shi din ya gyara sai ta bash

i kudin.

Mutumin nan ya karbe dukka kuma ya qi kawo masu gyaran. Mafarin da ta kamu da ciwon zuciya kenan."

[2/28, 5:50 PM] Jamila Umar Tanko: 2

Ban san ma ta je asibiti an ce tana da ciwon zuciya ba, sai daga baya take fada min a waya. Dan a l

okacin ba na zama a Kano, ina zama a Rivers ni da mijina.

A lokacin Hamidah ta dawo wajena tunda babu inda za ta zauna kasancewar Mamarmu ta rasu.

Na ji hankalina ya tashi matuqa na shiga damuwa ba 'yar kadan ba gami da tunanin me ya jawo ma

ta kamuwa da ciwon zuciya da kananan shekarunta? Amma ban yi mamaki ba domin kowa ya dube ta ya san bata jin dadin gidan mijin..Sai a lokacin ne Hamidah ta ke fada min wasu daga cikin matsalolin da Shariqah take ciki. Da irin cin kashin da mijin da kishiy

a da 'yayan miji ke yi ma ta. Su yi ma ta rashin kunya kuma su daki 'ya'yanta."

Sharifah ta juya ta dubi Hamidah wacce ke sharbar kuka ta ce " ki tashi ki shiga daki tunda ke zuciyarki ba ta iya jurewa idan ana labarin Shariqah."

Hamidah ta

ja kannenta suka shiga daki, masu wayon dai jikinsu ya yi sanyi sun ji an ambaci mahaifiyarsu, yayin da kananan suke wasansu basu kawo a ka ba ma. Allah sarki, Allah ba Ya barin wani dan wani ya ji dadi.

*** *** ***

Maman Samha ce take t

a kiransu a waya hankalinta a tashe yake, ta kira lambobi kowannensu bai amsa ba. Ta shiga gagarumar damuwa dsn ta na zaton fatalwar ce ta tafi da su.

Sai yanzu wayar Samha ta shiga girgiza, ta dauko da sauri ta duba taga 7 missed calls din Mama.

Ta dubi Anas da Aliyu a gigice ta ce "Mama ce fa take ta kira ashe. Waye ya ce ma ta mun fita ne?"

Anas ya tabbatar ma ta da cewa shine ya fadawa Samira, ko da ta Allah kan kasance aksnsu asan inda suka tafi . Kowannesu ya zaro wayarsa daga alji

hu ya duba ashe ta kikkira su babu adadi.

Anas ne ya zabura ya tashi da sauri ya ce "bari in sauka kasa in kira ta."

Ya na sauka ya kira Mama ya fara yi ma ta bayani.

Sharifah ta yi murmushin karfin hali ta ce " dole hankalin Mama fa

ya tashi, kun zo gidan fatalwoyi ta ji shiru, ku ce ina gaishe ta kuma zan kawo ma ta ziyara."

Sai su dukka suka kwashe da dariya har da Sharifah. Yayin da Samha da Aliyu kowannensu nauyinta ya kama su.

Anas dai ya na ta faman yiwa Mama bayani

n cewar ga su ga Sharifah da iyalanta mutane ne ba fatalwa ba, ta fayyace musu komai ashe duk rashin fahimta ne ya sa ake yi ma ta kallon fatalwa.

Mama ta ji bayanansa banbarakwai zuciyarta ba ta yarda ba.

Ta hau shi da fada ta ce "babu irin

sigar da shu'umar yarainyar nan bata iya biyowa ba, dan ta yaudare ku, ta halakar da ku. In ga fatalwa da idanuwana har sau biyu. Daya da yamma a gidana daya a asibiti da tsakar dare a sigar gurguwa yanzu ka yi min musu ka ce ta gyaru ta dawo mutum. Ka fad

awa Samha da Aliyu ku gaggauta barin gidan nan ko in yi muku baki."

Anas ya zabura ya ce "Ah Mama me ya yi zafi haka? Allah Ya baki hakuri bari in kira su mu taho. Menene abin yi mana baki kuma? Tunda ba ki fahimta ba shi kenan ai."

Anas ya ji

nauyin yadda zai shiga ya fada musu wannan sako na Mama a gaban Sharifah, ga labari ya kwaranyo dadi.

Anan ya tsaya ya tuttura musu text massages ta waya ya ce lallai-lallai su taso su tafi, ran Mama ya baci ta ce su taso."

Kowannensu ya karan

ta sai suka hada ido su ka yi shiru, can da aka jima kadan sai Anas ya shigo ya sami waje ya zauna.

Sharifah ta duba agogo ta ce "ya kamata ku tafi Mama na kira nima.kuma ina da ganawa da zan yi da Matar gwamna akan wasu harkoki. In sha Allah za mu ha

du wataran ma karasa labarin."

Daga dukkan alamu ta fahimci abinda Mama ta ce da sakonni da Anas ya turo mu su a waya.

Sharifah ta raka su har kofar gida bakin get inda suka ajiye motarsu suka shiga su ka tafi.

Kowannensu zuciyarsu cika

da mamaki su na ganinsu kamar a mafarki, ga su tare da Sharifah da ake gudun famfalaqi idan an ganta, yau gata ga su har ta yi musu rakiya.

Tabbas su na cike da mamaki gami da samun nutsuwa da kwanciyar hankali da Allah Ya sa suka gane ba fatalwa ba

ce, sannan kuma dan cikin Samha mutum ne.

Gidan Mama aka wuce kai tsaye aka same ta a farfajiyar get ta na ta kai kawo ta kasa zama a waje daya dan fargaba.

Ta na ganinsu sai ta ji hankalinta ya kwanta bayan sun gaishe ta, aka dunguma zuwa cikin

gida. Bayani suka yi mata tsaf akan tabbacin Sharifah mutum ce ga dalilan abubuwan da suka faru har ake zaton ba mutum ba ce.

Wasu dalilan Mama ta aminta wasu ne basu kwanta ma ta ba, ita dai koma menene ayi baya-baya da Sharifah kawai.

Samha

da Aliyu suka sauke Anas a gidansa, kamar yadda suka dauko shi sannan suka wuce gidansu suma. Samha na shiga gida ta bugawa kawayenta su Nana Ahmad waya ta basu labarin Sharifah cewa mutum ce ba fatalwa ba ce.

Ta fada musu dalilan da ya jawo suke t

unanin ba mutum ba ce. Su ka tambaye ta ko ta bata labarin abubuwan da suka faru da rayuwarta ya jawo har kamanninta suka canja kuma menene maqasudin shariar ta a kotu?

Samha ta tabbatar musu Sharifah ta shirya bata labarin rayuwarta bayan rabuwarsu s

ai kuma Mama ta kira su ta tubure ta ce su bar gidan. Amma za ta samu ta lallaba Mama ta bar ta su sake haduwa da Sharifah don jin ci gaban labarin. Sai dai ba ta sani ba ko sirri ne tsakaninta da

ita, ko ita kadai ta fadawa ko kuma zata so kowa ya ji. Ida

n sirri ne toh ba za ta fada musu ba amma idan Sharifah ta amince kowa ya ji toh za ta sanar musu.

Su Nana suka nemi da ta samo musu lokaci su hadu su dukka su je gidan Sharifah su ba ta hakuri akan gudun ta da suka yi, a lokacin da ta kawo musu ziy

ara gidajensu. Samha ta tabbatar musu cewa zata fada mata.

Aliyu ya kula da matarsa ta dawo yadda take ada, ga hira da girken-girken da aka saba yi masa ana yi yanzu, bayan kwalliya da kalaman soyayya wanda dukka ya rasa su a baya.

Sai ya ji dad

i sosai kuma sai a lokacin ya sanarwa da 'yan gidansu labarin bayyanar cikin Samha. Dan duk tsawon lokacin nan bai fadawa kowa ba dan ana tunanin fatalwa ce ta yi ajiya. Amma yanzu komai yayi daidai dan haka ya daki kirji ya fada.



*** ***

***

Sharifah ce ke tukawa, ta tsaya sannan ta fito daga cikin wata tsaleliyar motar. Daidai lokacin Nana Ahmad da Maryam Alqali su ma sun fito daga cikin motar Nana. Sai kawai aka yi kicibus da su da Sharifah. Ko ba su fada ba ta gane sun razana.

Maryam Alqali da yake 'yar karama ce sai ta labe a bayan Nana Ahmad ita ce barkekiya, Nana ta hau muzurai ita ba abin ta taka da gudu ba dan lokaci ya kure, su na daf da juna. Duk da an fada musu yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login