Showing 48001 words to 51000 words out of 65015 words
ta jin haushina akan nasarar da na yi akansa an bani yaran kuma babu yadda ya iya. Sai ya shiga ba su wulaqantaccen abincin da ya tabbatar ba zai ishe su ba kuma ba masu
kyau ba. Dukkan abinda aka yanke masa ya ki bin doka.
Ko kallonsa ban yi ba kuma ban koma na kai kararsa ba. Allah Ya dinga bude min ta wasu hanyoyi daban-daban ina ciyar da su.
Bayan duk an yi haka ina zaune sai kawai na ga an kawo min sam
maci daga wata kotu, anan birnin Kano mai nisan gaske daga unguwarmu wanda a ka'ida gidana da gidansa su na kusa da juna ya kamata ya kai kotun da tafi kusa da mu amma aka tafi wata unguwa da take karshen garin Kano. Sai na yi tafiyar fiye da awa guda kafi
n in kai.
Ya na karata akan rabon gado, na rasa dalilin wannan karar, ga gado nan a hannunsa suke yana karbar kudin hayarsu. Gida daya ne mu ka yi hadaka da ita ni da Bello kuma a ciki muke zaune.
Na nemi shawarar masana dan su bani shaw
ara dan ba san kotu ba, ban taba zuwa kotu ba ko da rakiya ma. Da farko aka ce in dauki lauya nima, dan shari'ar yanzu in ba ka da lauya daman ka bar maganar samun nasara ma kawai. Sai daidaiku ne suke nasara.
Na sami lauya na biya shi ya je kotu ak
a fara shari'a muka saurari dalilin karar. Wai ya na kara akan rzbon gado ya zayyano komai, har da wanda guda biyu ne kadai muke hadaka da ita . Sai kuma na ji an kinkimo wani gidana an saka a cikin lissafin. Gidan nan nawa da ne taba siyar ma ta sannan t
a sake siyar min, cikon kudi kadai zan yi ma ta . Babu wanda bai san labarin ba har shi kansa ya san komai amma anan ya ce na ta ne.
Mu ka mayar da martani akan ba haka abin yake ba.
Abu kamar wasa sharia ta miqe ana ta zuwa kotu ba kakkautawa.
Shi yana da kudin da yake ta biyan lauyansa ni ce yake so ya saka a wahala amma da yake Allah ba azzalumin bawanSa ba ne na dogara ga Allah.
Hakan bai ishe shi ba sai su ka fara saye dukka lauyoyin da na dauka . Akwai lauyan da bai fada min ba zai yi
ba sai ana gobe zaa je kotu sannan ya kira ni a waya ya ce ya janye.
Yaransa su na ganin office din su ka ce sun taba zuwa da babansu. Wato ya siye su, lauyansa ke karbar lambarsu a kotu ya bi su ya siye su.
Ana cikin wannan hali sai na sake
jin kira daga wata kotu ta daban an kawo min sammaci, ita ma mai nisa ce sosai daga gidana. Ita kuma yana kara ta akan karbar yaransa."
Samha ta dafe kirji ta ce " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah irin rayuwar da kika shiga kenan? Amma hada
zuria da irin su Adamu ya zama masifa wallahi."
[3/5, 8:12 PM] Jamila Umar Tanko: 6
Sharifah ta tabe baki ta ce "mutumin da ya wulakanta matarsa tana raye kina ganin zai ji kunyar wulakanta ta ne bayan ta rasu? Ai duk abinda yayi min ba ni ya yiwa
ba Shariqah ya yiwa....."
Ba ta rufe bakinta ba wayarta ta dauki ruri sai ta dauko ta amsa, Fanna ce akan layi.
Nan da nan sai Samha ta firgice dan a halin yanzu ta fi jin tsoron Fanna ma akan Sharifah.
Sharifah ta ce "Fanna ga fim din
ki ina kallo fa 'walking dead', a MBC 2 na tabbatar shi kike kallo kema ko dan na jiyo saurin?"
Fanna ta ce "Ah ai ba zai wuce ni ba, ina son shi sosai."
Samha ta ji kirjinta yana bugawa ta ce a ranta "me ya hada mata da son kallon fim din Mat
attu? In ba rami me ya kawo rami ?"
Sharifah ta ci gaba da cewa "Fanna ya kike? Yaya yara? Meye kike so ki fada min rannan? Hamidah ta ce kina ta kira kin ce in kira zamu yi magana."
Fanna ta fara magana, Samha ta na jiyo ta tana ta ambaton s
unan Samha da Nana, sai ta tabbatar akan maganar rannan ce.
Sharifah ta dago da sauri ta dubi Samha. Toh fah akwai magana kenan sai Samha ta ji hankalinta ya tashi da alama ta shiga tarkon fatalwoyi, shikenan Sharifah ta san har yanzu ban gama yarda
da ita ba duk da labarin da ta ba ni. Wai ni wanne tsausayi ne ma ya kai ni yin qawance da Sharifah da Famna ne ma?" Samha ce ta fada a ranta.
Sharifah ta qurawa Samha ido tana kallo yayin da take sauraron Fanna tana ta magana. "innalillahi wa in
na ilaihi rajuun. Wanne tuggu kanuriyar nan take hada min ne?" Samha take karantowa a zuciyarta.
Sharifah ta katse Fanna ta ce "ina tare da Samha ma yanzu haka, in kin amince zan saka ki a hand's free sai mu yi hirar tare."
Fanna ta ce "ah a
i na fi son haka ma daman, ina neman Samha dan ina ta kiranta a waya ma ba ta amsawa."
Sharifah ta taso daga kujerar da take zaune ta zo kusa da Samha ta zauna yayin da ta bude muryar Fanna wacce take ta magana.
Fanna ta ci gaba da cewa " Samha
Ya kuke? Ina sauran kawayena su Nana?"
Samha cikin tsoro da takura ta ce" lafiya kalau mu ke Alhamdulullah."
Fanna ta ce "rannan mu na labari da ku sai kuma ku ka ajiye min waya babu sallama. Na dauka ku na neman ilimi ne akan rayuwar matattu
."
" Hmmm! Hmmm!!" Kawai Samha ke fadi ba tare da ta iya bada amsa ba.
Fanna ta ci gaba da cewa "wai ni kam shin menene abin tsoro ne a fatalwa? Fatalwa mutum ne fa kamar ku, ya mutu ne kawai sai kuma ya tashi ya zo wajen kawayensa ko 'yan uwan
sa dan ayi zumunci. Har na ba ku misali da ni kaina na ce kamar ni din nan da na mutu kuma na tashi. Ko ba haka ba ne Sharifah? Kuma ke ma ai kin yi ciwo kika mutu kuma kika dawo ko?"
Abinda ya daurewa Samha kai ya kara bata tsoro shine amsar da S
harifah ta bata.
Sharifah ta gyada kai ta ce " Haka ne Fanna."
Sai Samha ta zabura ta matsa daga kusa da Sharifah, ta ga ma dai gara ta tashi kacokan daga kusa da ita.
Ta fara tunanin nemo mafaka dan dai wannan abu ya wuce tunaninta.
Fanna ta ci gaba da cewa "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki ba ne, har ya zama ajalinki ba ne?"
Sharifah ta girgiza kai ta ce " ban bata wannan labarin ba dan na san kwakwalwarta ba zata taba ganewa ba Fanna. Mu kadai ne muke
gane labarin juna."
Samha ta fice daga falon ta isa farfajiyar gidan, sai ta fara tunanin ko ta fice ta shiga maqwabta duk da bata da gyale a jikinta, dan ba zata iya zama a kusa da ajalinta ba.
Ba ta ankara ba ta ji an dafa bayanta, sai ta d
aka tsalle ta waiwayo a gigice.
Sharifa ce dauke da mayafinta da mukullin mota da alama zata tafi. Wannan karon da Bello take magana a waya, ya na jiranta ne a gida zai fita da motar.
Ba su sami damar yiwa juna magana ba, sai dai suka da
gawa juna hannu, Sharifah ta fice da sauri.
*** *** ***
Samha ta dawo falonta ta zauna yayin da idanuwanta su ka dira akan wannan fim din me firgitarwa abin ba kyan gani, matattune hagar naman masu rai.
Ta tashi da sauri ta kash
e talabijin din ma gaba daya sannanta sami dan saukin hayaniyar, ta hada kai guiwoyinta biyu ta takure, ta na addu'a ta rasa abinda yake damunta. Ta na son zumuncinta da Sharifah ya dore amma ba za ta iya ci gaba da zaman zulumi irin wannan ba. Gaskiya ta
na ta sake bayyana duk da tana kawarwa gefe, amma abu ya ci tura. Sharifah ba mutane ba ne wasu halittu ne na daban.
Maganar Fanna ce ta dinga dawowa cikin kanta da ta ta ce "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki har ya zama ajalinki ba n
e?"
Sharifa kuma ta amsa da "eh haka ne ban bata labari ba." Meye hakan ke nufi?"
Samha ta fara tunanin kawai ta yi irin yadda su Nana da Maryam su ka yankewa kansu shine sun hakura da kawance da Sharifah, ko da ita kadai kawarsu da ta rage a d
uniya. Samha ta ga hakan zai fiye ma ta alkhairi da kwanciyar hankali. Gara su yafewa juna dan duk iya yadda ta so Sharifah ta gyaru ta dawo daidai abu ya gagara, daga wannan sai a koma wancan.
Samha ta sirnano da hawaye ta fada a bayyane "tunda uwa
ta ta haife ni ban taba ganin masifa irin wannan ba."
*** *** ***
Bayan wssu kwanaki Aliyu ya dawo daga tafiya ya sami Samha a kwance ba ta jin dadin jikinta, Samira ta zo ta na taya ta zama. Amma a waya babu wanda ya fada ma
sa cewar ba ta da lafiya wato dan kada hankalinsa ya tashi.
Ya dinga fada musamman akan ba ta je asibiti an duba ta ba. Ko abinci bai zauna ya ci ba ya ce ta tashi su tafi asibiti. Sai da ya sami asibitin gyaneacology mai kyau da tsada sannan ya kai
ta, aka bude file.
Likita ta duba ta, ta duba abunda yake cikin cikin aka tabbatar lafiya kalau, amma an tabbatar mu su da cewa ba ta cin abinci kuma tana da damuwa da yawa da rashin bacci.
Nan da nan Aliyu ya nemi da a ba ta "bed rest" Samh
a ba ta kaunar kalmar nan ta "Bed rest" dan daga 'bed rest' ta shiga bala'in da bata shirya ba. Ziyarar da Sharifah ta kai musu asibiti.
Ta na addu'a wannan karon kada Allah Ya kawo ma ta Sharifah dubiya.
Kwanakin Samha biyu a asibiti wannan ka
ron kuwa ta mori bed rest dan ta huta sosai, ta yi bacci ta ci me kyau tana shan mai kyau.
Bayan Mama babu wanda ya san tana asibiti balle 'yan dubiya su dame su. Samira ce ke zuwa gida ta taho musu abinci kala-kala ta kawo, Aliyu kuwa duk da ya za
ma busy amma kullum kafin ya fita aiki sai ya shigo, haka da daddare idan ya taso sai ya biyo ya duba ta kuma ya biya asibiti maqudan kudade. Ana dai cin kudi bana wasa ba amma dai ana ganin kulawa.
Abin mamaki da rana misali qarfe goma sha biyu, A
liyu ya dade da tafiya, samira ta tafi gidan Samha dan ta dafa abinci, yayin da Mama kuma sun tafi yobe ita da Ana's gaisuwar mutuwa. Daman su ne kadai suka san tana asibiti,su kadai ne suke zuwa duba ta.
Sai ta ji an yi sallama an murda qofa an shigo
.Ta dauka ma'aikatan jinya ne wato (Nurses) amma ko su ne ai yanzun nan su ka fita. Me su ka manta, su ka dawo kuma?
Wannan tunani na ta ba daidai ba ne wata mata ce ta shigo sanye da atamfa ruwan hoda da gyale shima ruwan hoda (pink color), ta na d
aga kai su ka hada ido da Sharifah.
Yadda ka san bom ya fashe haka karar bugun zuciyar Samha ta kasance. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ta fada a bayane. Yayin da Sharifa ta taya ta suka karasa tare.
Dan neman magana sai ta qi zama a kan ku
jerun da suke dakin ta zata zauna a gefen gadon kusa da Samha.
Samha ta koma ta kwanta yayin da take numfashi sama-sama.Sharifah ta dauka duk a cikin ciwo ne, sai ta zabura ta riqe ta tana yi ma ta sannu.
Ta dora da cewa "haba Samha kada ki di
nga jefa kanki a cikin damuwa mana, alhali kina dauke da ciki na 'yan biyu ba ma guda daya ba."
Samha ta sake gigicewa, ko ita kanta sai a daren jiya aka fada ma ta cewa tagwaye ne a cikinta. Ta ina Sharifah ta sani? Ita fa ba ciwo ba ne matsalarta
, daman Sharifah ce matsalar. Ga matsalar da kanta ta zo har da karin wata babbar matsalar ma, ta kawo ma ta.
Samha ta sirnano da hawaye ta na magana cikin sanyin murya ta ce "Sharifah! Ya kamata ki fada min gaskiya, maimakon ki bar ni ina ta wahala
. Shin menene labarin karen da ya cije ki har ya zama shine ajalinki kika mutu kika dawo? Yaya ake kike sanin boyayyen al'amari? In har ke mutum ce ba za ki iya sanin ina nan ba. Waye ya sanar miki yara biyu ne a cikin cikina? Sharifah idan na mutu wallahi
ke ce sila ba zan boye miki ba, ki na bani tsoro na kasa yarda da ke. Duk sanda na cirewa raina zargi akan ki sai ki aikata wani abu da kwakwalwata zata kasa dauka. Shin kin shiga wata kungiyar matsafa ne da kike iya bacewa ki ke ganin abinda baa fada mik
i ba?"
Sharifah ta kwashe da dariya har kamar za ta shide. Samha ta sake sankarewa a kwace, ta yi saranda ta fitar da rai daga ci gaba da rayuwa.
Sharifah ta jawo hannun Samha ta riqe, yayin da jikin Samha ya hau karkarwa.
Sharifah ta ce
"in har kowa bai yarda da ni ba, na san ke ce kadai a duniya za ki yarda da ni. Ba zan fada miki yadda na san kina nan ba amma lokaci zai fada miki, ba zan fada miki waye ya sanar da ni kina da cikin tagwaye ba amma mu na zaune za ki sani."
Samha ta
ce " na godewa Allah da Ya jarrabe ni da ciwo. Allah Ya bani mafita.
Sharifah ta ce " za ki sauka lafiya ki haife kalau ma in sha Allah."
Takaicin da ya sake addabar Samha shine har yanzu Sharifah ta kasa ganewa cewa itace ummul aba isin ciwon
ta. Idan ta fita daga rayuwata zata warke.
Aka jima babu wanda yake magana, Samha dai ta saka hannu ta dafe goshi kamar mai ciwon kai yayin da hawaye ya yi ma ta qawanya daga ido zuwa bayan kunne.
Sharifah ta tashi cimak ta linke gyalenta ta a
jiye tare da jakarta a gefen kujera.
Gami da cewa "an ce in zo in wuni tare da ke, in yi miki hira, in dauke miki kewa."
Sai hankalin Samha ya tashi ta kalli Sharifah da gefen ido dan bata da kuzarin waiwayowa.
Ta fada cikin sanyin jiki
"waye ya ce ki zo ki zauna da ni? Ko dai kin zo ki tare ni ne, nima zan zama ku?"
Sharifah ta ce "Mu su wa kenan? Ciwonki ai nawa ne Samha, dan haka ina nan har dare."
Samha ta ce " na gode amma da kin tafi gida dan ki kula da